Showing 3001 words to 6000 words out of 81312 words
tayi da cewa,
Ba'a cire rai daga rahamar uban giji rumana,
Ki zamto mai gode masa da kowace irin niima,
Ke mai saa ce sbd koda kasancewarki baiwa kinfita dabam acikin bayi sbd ke abar qaunace ga sarauniyar datafi kowace mace matsayi acikin masarautarnan sultana zaarah kasancewarki 'ya ga amintacciyar baiwarta
Ko ahaka kika duba zaki godewa Allah da wannan ni'imar.
Ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda zare kanta ta juyo ta kalli nuratun tana tattare dogon gashinta tace,
Kibar kitson kiyi wanka kikoma bakin aikinki da wuri sbd gudun kwana gidan kason masarauta.
Tashi nuratun tayi tana jawo kayanda tafara maidawa tana cewa,
Bazan samu yin wankaba kuma sbd lokaci yashiga kuma wlh tsananin aikine asashen sarauniya adama sbd komai na sashen zaa canza har sitirunta kaf ko tsokalinda aka siyo jiya bazai shiga sashentaba sai sabo dal sbd kwanaki uku zuwa hudune suka rage ta kammala hukuncinta na sultan daya bata na ko qofar palonta na farko karta fito sai bayan shekara guda iyakacinta palonta na qurya zuwa bedroom dinta ko 'yayanta anhana shiga gurinta bare kuyangi iyakacinsu palonta na farko jekadiyarta kawai keda izinin shiga sbd kamata da laifin sa likita yaje gidan 'yarta gimbiya amatullah yayi mata allurar tsarin haihuwa suda ake fatar samun 'da namiji a zuria sbd.....
Rufe mata baki rumana tayi tana kallon qofa tace,
Ya isa idan wani yajimu kinsan rayuwarmuce zamu qarasa a kurkuku.
Saurin kallon qofa nuratu tayi ido a firgice zufa na karyo mata sbd shaf idan tafara barin baki mantawa takeda abinda zaibiyo baya sbd masarautar takasance maitsananin hukunci babu sauqi ko bata lokaci sbd tsagwaron mulki da iko ke yawo a jinin masarautar kasancewar sarkin masarautar mai tsananin zafine da zallar mulki babu sauki gurin daidaitawa kowa kansa,
Kwarjininsa ikonsa kesa ko matansa da 'yanyansa ke matuwar shakkar hukuncinsa shiyasa kowa a kiyaye yakeda umarninsa bare 'yan fada da sauran hakiman sarki.
Kusan atare suka fito daga dakinsu suka jawo dakin suka kowa yanufi gurin aikinsa
Kai tsaye rumana sashen sultana zaarah takoma inda ta tararda dukkanin wasu kuyangin sashen a qofar sashen sun jeru zai zufa suke sbd tsayuwa gashi babu ikon zaunawa haka itama tabi layinsu suka cigaba da tsayin jiran lokacinda uwar dakinsu zata gama hutawa sukoma ciki domin hidimarta.
Saida rana tafadi lis kafin ta matsa sbd lokacinda ake diba nabawa sarauniya Hutu yayi idan bata fitoba ana shiga aga lafiyarta
Matsu tsaron bakin qofar sashen sukayi saurin bude mata tashiga tana goge zufanta ta tsaya a palon farko saidatayi mintuna kusan shida atsaye AC ya butsarda ita kafin ta nufi palon gaba tashiga da sallama Mara qarfi sbd gudun yin hayaniyar da ammyn bataso.
Shigarta yayi daidai da fitowar sultana din daga bedroom dinta cikin doguwar riga maroon dataji adon sequence stones masu masifar kyau sai qyalli suke wannan karon babu adon sarqar zinari a gashinta da wuyanta kamar koyaushe saidai wasu awarwaron zinari masu kauri da girma sosai hakama babu kwalliya afuskarta kamar koyaushe sbd sultana zaarah takasance yar sarautar qasar Morocco koyaushe cikin tsananin ado da kwalliya take musamman gwalagwalai naban mamaki hakama bazaka gantaba kace tanada babban jarumin 'da sbd zamanta kyakkyawar mace mai kyawun jiki.
Durqusawa tayi cikin tsananin ladabi tace,
Barkada fitowa ammy da fatar kinhuta lafiya.
Zama ammyn tayi kan 'daya daga cikin royal chairs din palon batareda takalli rumanarba ta 'daga kai kafin tace,
Rumana 'yau banason dogon motsi bare hayaniya Dan haka kisanarda sauran ayi komai cikin qanqanin lokaci kowa ya fice kema ki kammala kije kihuta bana buqatar kowa.
Angama ammy.
Miqewa tayi taje tasanarda sauran kuyangin tadawo ta nufi bedroom din ammyn tafara gyara ta canza zanin gado sbd kwana daya 'daya yakeyi acire asaka sabo tana gama gyara koina ta sassaita AC daidai yanda ammy keso sanyinsa ya kasance takunna burners qamshi yafara tashi ta shiga toilet tayi gyaran dazatayi ta fito taje takarbo abincinta a manya manyan tururuwa ta jera a makeken royal dining din dake palon ta dawo gabanta ta durqusa a ladafce tace,
Allah yasa ahuta lfy yakuma tasheki lfy.
Ficewa tayi lokacin tuni aka fara kiran magriba daidai zata fito dake jakadiya dake qoqarin daidaita nutsuwarta tashigo.
Tsayawa jakadiya tayi a palon farko tafitarda numfashi mai zafi sbd sotake ta daidaita kanta sbd da rayuwartace amatuqar tsaka mai wuya duk tabari fargabarta tasa sultana tagano hukuncin da sultan ya yanke akan alamarin dake damun masarautar shekara da shekaru.
Tunda suka baro gurin sultan dazu tasake komawa sbd kai saqon banhakuri da tubar uwargijiyarta bisaga saqo Mara dadi data kaimasa na haihuwar mace da matar yarima tayi.
Abakin qofar fadar ta wuni tsaye cikin rana Dan nuna banhakurin uwargijiyarta Wanda saida rana ta fadi lis sarki ya aikoda izinin shigowarta.
Jiki na rawa ta zube gabansa cikin tsananin girmamawa tace,
Allah ya huci zuciyar sarkin sarakuna,
Sarkinda yafi kowane sarki adalci,
Da yardar Allah sai anmaka takwara harsai andarje a jininka,
Ba 'daya za'a samuba ba biyuba dozin ne da yardar ubangiji saika gansu saika aurensu
Allah ya sake hutar zuciyarka.
Gyara murya yayi cikin wani irin iko da umarni dake nuni magana daya yakeyi yace,
Jakadiya aje aciro 'yan mata biyar dasukafi kowa kyawu acikin kuyangun masarautarnan a killacesu afara kintsasu daga yanxu harzuwa nanda shekara daya lokacinda yarima zai dawo
Za'a kaisu sassansa amatsayin sa dakokinsa duk wadda ta haifi namiji ayimata albishirda tazama uwar sarkin wata rana.
Amatuqar kidime jakadiya zufa ya keto mata murya na rawa tace,
Angama sarki mai adalci,
Cika umarninka zaifara ne daga yanxu,
Allah dai yaqara hutar zuciyarka
Nabarka lafiya.
Fitowa tayi saida ta tabbatarda tayi nisa da sassasansa ta tsaya gefe tareda sharshe zufar daketa faman karyo mata tayi shiru tsawon mintuna zuciyarta na tumamin hukuncinda sarki ya yanke dakuma sanin waye yarima akan tsantseni matarsama da yaya akasamu yayi auren bare sa 'daka har biyar...
Sake sharce zufa tayi cikin tsananin fargaba gashi abakacin ranka matuqar sarki ya yanke umarni katsaya sanarda wani batareda ka cika umarninba Dan haka batada ikon fadawa kowa saidai kawai aiwatarwa.
Nufar sassan sultana tayi cikeda fargaba da tausayinta ta yanda hankalinta zai matuqar tashi duk randa taji zata fara shirin tarbon jikokinta na sa'dakoki.
#mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡
*3*
Asma'u bilalu bulama shine asalin sunan mahaifiyarta asalinta 'yar qasar Nigeria ce ubanta bilalu dan Maiduguri sai mamarta ummu-rumana shuwah ce.
Bilalu bulama Nada tarin dukiya mai yawa hakama matarsa ummu-rumana kasancewarta tanada gadon iyayenta dasuka barmata.,
'Yarsu qwaya 'daya tak aduniya Nana asma'u wadda duk wata soyayyarsu da burinsu sun 'dorasa akanta.
Bilalu bulama Nada qanne biyu jabir bulama da salmanu bulama
Kowannensu matarsa 'daya da 'yaya uku uku banda bilalun dakeda 'ya daya,
Jabir babban dansa shine ishaq sai qannensa mata biyu hassana da husasaina,
Salmanu kuwa sunan babban dansa bulama sbd sunan mahaifinsu yaci sai qaninsa babaye da yakurah.
Kowannensu nada arziki daidai gwargwado amma ba kamarna bilalu ba sbd shi ba qaramin arziki Allah ya hore masa Wanda hakan yasa shedan yashiga kwadaitawa qannensa dukiyarsa nan kowannensu yafara qoqarin ganin ya cusa dansa gurin Neman 'yarsa Nana asma'u,
Tun kowanne natura babban 'dansa a 6oye gurin neman soyayyar asmaun hardai kowa yafito fili yanuna buqatarsa tason nemawa 'dansa auren,
Alhaji bilalu baiyi tunanin komaiba saima farin ciki dayayi saidai abun daga baya lalace sbd fada da tashin hankali daya shigo ciki sbd tuni kawuna suka rarrabe sbd alamarin ganin haka sai alhaji bilalu yace abari asma'u tazaba Wanda takeso acikin yaran dakanta sbd ya fahimci bulama shine Wanda tafiso kuma maganar gaskia yafi ishaq nutsuwa da tarbiya ga hankali amma shi bazai fadaba saidai ita asma'u tafada Wanda takeso dakanta.
Tashin farko da'a tambayeta gaban kowa ba 6oyo ta za6i bulama
Hakan datayi shiya qulla wata irin qiyayya da sabani tsakanin jabir da yayyunsa bilalu da salmanu.
Bayan auren da wata biyar aka wayi gari gidan alhaji bilalu ya qone qurmus dagashi har matarsa ummu rumana babu Wanda yafita kuma a iya binciken da akayi aka gano wutar dai kunnata akayi da man petrol.
Haka akayi zaman makoki aka watse dakyar aka samu asma'u ta dangana Wanda saida aka hada da adduoi da sauke al-qur'ani kafin tadawo daidai.
Duk inda hankalin alhaji jabir da ishaq yake yasake hargitsewa sbd sai yanxu kukaga wautarsu ta kashe su alhaji bilalu sbd yanxu duk tarin maqudan dukiyarsa yarsa zata gada tokuma ai mijinta da uban mijinta suzasu juya dukiyar kenandai alhaji salmanu yayi arzikinda ba ranar qarewarsa shikenan shi yatashi abanza.
Cikin watanni hudu shida ishaq sunkasa sukuni suna qulla yanda zasu qwato dukiyar su raba su salmanu da ita.
Ranarda suka gama qulla suka aika 6arayi gidan alhaji salmanu tsakiyar dare,
Gurin karbar takardun bulama da mahaifinsa sukai gardamar bayarwa Wanda yaja nan take aka harbe alhaji salmanu da matarsa bulama naganin haka ya buge babbansu da flower verse ya fizgo matarsa asma'u suka gudo tareda takardun dukiyar
Yakurah da babaye dama suna schools hostels suke zama.
Gudu suke sosai atsakiyar ko gani sosai basayi sbd duhun dare amma haka suke gudu hannunsa damqe Dana asma'u suna keta duk hanyarda suka samu sbd sunajinsu abayansu biye dasu.
Basu ankaraba suka gansu har sun fara barin anguwanni suna qoqarin ketawa daji amma haka suka cigaba da gudu agalabaice cikin tsananin wahala da gajiya
Can wajen gari sukaga wani kangon gida daya qone suka shige tareda boyewa.
Wani irin kuka asma'u tasaki jikinta na karkarwa
Bulama yayi saurin saka hannuwansa ya toshe mata baki sbd takun su ishaq da barayin daya jiyo yana kusantonsu.
Dudduba koina sukayi suna haskawa Allah yasa basu gansuba
Iska ishaq ya daka cikin zafi da tsananin 6acin rai yana huci yakira abbansa yafada masa
Cikin takaici da baqin ciki abban yace,
Kutafi tashoshin motar duk garinnan kudubasu banason kowannensu da rai takardun kawai nakeso Ku karbo saiku harbesu
Hakama atura su tiger duk wata station su zauna daga nesa da anhangosu sunzo station kafin sushiga aharbesu.
Aje wayar yay yakallesu yace kumuje tashoshin mota amma wasu su tsaya anan sbd nasan idanma sunanan kusa idan gari ya waye zasu fito idan sun fito Ku harbesu kawai.
Barin gurin sukayi sukuma su bulama najin haka koda gari ya waye sake lafewa sukayi sukaqi fitowa saida duhu yasakeyi suka fito cikin sanda suka fice tareda qarasa kutsawa cikin dajin suka fara gudu
Jini sosai qafafuwansu ke fitarwa sbd ko takalmi babu maishi acikinsu ga yunwa ga wahala da kishirwa amma hakanan suka cigaba da tafiya sbd komawarsu nada matuqar ha'dari yanxu.
Basu hadu da qauye ko dayaba har asuba tayi musu atsakiyar daji gashi tuni asma'u tafara riqe ciki tana murqususu cikin tsananin azaba ta durqushe agurin awahalce tace,
Bulama marata zan mutu.
Da sauri ya aje takardun ya durqusa ya tallafota jikinsa shima daqyar yake hade yawu sbd bakinsa daya bushe qyam ko yawu daqyar yake samun na hadiyewa a maqoshinsa ga wata irin rana mai tsananin azaba,
Ko tsuntsaye babu adajin sbd a bushe yake babu damshin ruwa ko kadan itatuwan dajinma duk abushe suke babu mai inuwa.
Jinin dayaga yanabiyo qafafuwantane yasa yayi saurin kallonta murya na rawar wahala yace,
Asma'u cikine dake dama bansaniba?
Innalillahi-wainnalaihirrajiun.
Ganin tana Neman fita hayyacinta yasa ya goyata tareda daukar takardun yacigava da tafiya daqyar shima sbd shima yafara daina gani daidai.
Ahaka rana takuma faduwa wani Daren yayi musu a tsakiyar jeji wannan karon kam ya tabbatarda wata duniyar suka fado sbd kalar yanayin dajin ya sauya sosai
Tun yana gani har duhu yasake yi dare Yakuma tsalawa sosai cak ya tsaya tareda yanke jiki ya fadi asma'u dake bayansa ta fado da qarfi kafin ya bude idanu daqyar Dan taimakonta sai ganin yayi kamar tana gangarawa
Bude idanuwansa yayi awahalce da sauri saiyaga Ashe bakin cliff suke mai tsananin zurfi da ruwa masu tsananin yawa yana miqewa daqyar kafin yakamota idanuwansa suka rufe yasake yanke jiki yafadi tareda fadawa shima.
********
Ahankali ya bude idanuwansa dake gani dishi dishi harsuka bude daqyar suna kallon sama,
Lumshe idanuwan yasakeyi yabudesu yaga tabbas rufin sama bukkar karace yake ciki,
Qoqarin motsawa yakeyi Dan ya yunqura yatashi aka shigo bukkar yayi saurin dagowa.
Tashin namijine kamarsa dago fari tas sanyeda kayan saqi na fulani.
Qarasowa yayi da sauri tareda dafasa yana cewa,
Yi ahankali kana kariya aqafa.
Kallon qafar bulama yayi sai alokacin yaji azaba ya lura da 'dauri amma bai damuba cikin dasashiyar murya da fargabar amsarda za'abasa yace,
Ina matata?
Inane nan?
Ina takardun dake daure ajikina?
Kwana na nawa anan?
Cikeda mamaki da rashin isashiyar hausar fahimtar me bulaman ke fada yake kallonsa kafin ya gyara masa zaman qafar mai 'dori yace,
Kayi hkr sbd bansan mezan fada makaba amsa daya zan iya baka shine kwananka takwas anan sauran tambayar anjima idan mahaifina yadawo ya amsa maka.
Yana fadar haka ya fice
Saigashi yadawo da qwaryar magani da akushin wani irin abinci kamar tuwa kamar kunu ya zauna tareda miqawa bulama yace,
Gashi kaci saikasha magani.
Kallon abincin bulama yayi yaga shi kama ma abincin yayi masa da aman tuwon semo amma sbd yunwa da matsuwar jin inda matarsa take ya karba ya dauke numfashi ya shanye.
Ruwan magani ya miqa masa suma ya karba ba musu ya shanye.
#Mamuhgee
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡
*6*
Sashen sultana zaarah aka nufa da Asma'u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.
Lokacinda aka kaita gaban sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.
'Dagowa tayi cikin wani irin farin ciki da murmushi takalli asma'u cikin sanyin lafazi tace,
Allah yayiwa yarima albarka bisaga wannan kyauta.
Sake kallon asma'u tayi dake durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa jakadiyarta.,
Akaita abata 'daki sashen bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara aikinta.
Angama sultana.
Daki aka bawa asma'u kuma cikin sa'a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da'din zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da 'yar tasarsa
Anan ne asma'u suka hadu da bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.
Duk wanda aka bawa samun guri yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.
Daga ita harshi ba wanda ya iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.
Kwanansu biyu da zuwa jikinsu ya'dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd Sam babu yunwa ga bayin masarautar.
Asma'u da bulama iyakacinsu da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.
Ganin basuda yunwa kuma babu azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga ayyukansu damuwar bulama 'dayace cikin jikin asma'u da mamani.
Sosai asma'u ta dangana ta rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana sake mata ba laifi.
Aiki da bauta takeyiwa sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.
Tunda sultana zaarah ta lurada cikin jikin asma'u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa hkr ta tsare asma'un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.
Cikin tsananin tausayawa sultana tace,
Karki damu asma'u Allah baya bacci kuma insha Allah za'a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba nasan zasu dawo.
Sosai sultana tasa jakadiya sassautawa asma'u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana keyiwa asma'u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita cinsu.
Kasancewarsu kusan sa'anni yasa sosai sultana tasa asma'u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta 'Dan sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna 'Dan ta6a fira wani zubin harda jakadiya.
Cikinta na isa haihuwa cikin ikon Allah suka haihu rana 'daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.
Dukkaninsu 'yaya mata suka Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.
Shiru yayi cikin jinjina alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.
Koda bulama yaga 'yarsa hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.
Huduba yayi mata kafin ya 'durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,
Kece kika cancanta daki za6a mata suna.
Yarima daya fito sashen sultan yaqaraso sashen sultana yana shigowa yaji zancensu kai tsaye yakalli yarinyar yakalli sultana yace,
Asaka mata UMMU-RUMANA..
Kallonsa sultana zaarah tayi fuskarta daukeda murmushi tace,
Mahaifiya kayiwa takwara maheer.
Mayar mata da murmushin kawai yayi tareda jinjina kai ahankali ya shafo fuskar jaririyar yace,
Allah ya raya ummu-rumanah.
Yana gama fadar haka ya wucewarsa sultana takalli bulama tace,
Allah yaraya ummu-rumanah.
Amin sukace cikin farin ciki da godiya harda jakadiya.
Yarinyar mamani ma shine yayi mata huduba mamani tasawa 'yarta suna NURATU.
Tunda asma'u ta haihu hankalinsu yasake kwantawa itada bulama tuni suka maida hankali ga bautarsu
Idan zatazo sashen sultana adaki suke barin 'yayansu itada mamani daga baya sultana tace tariqa zuwa da ummu-rumanah
Sosai lokaci yaja tuni ummu-rumanah ta fara girma
Daga ummanta sai sultana da jakadiya tafi sabo dasu sai nuratu dasuke wasa tare a can sashen bayi mahaifinta ta saba dashi sbd ana 'Dan basa damar zuwa ganinta itada ummanta wasu lokutan da haka rayuwa tayi nisa sosai.
Sultan an wayi gari baida amintaccen bawa kamar bulama sbd takai ko fita za'ayi wata qasar da amintaccen bawansa bulama yake zuwa gashi da tsananin biyayya da taka tsantsan sbd sultan nada qarfin mulki da iko sosai da wasu irin dokoki.
Ummu-rumanah nada shekara goma sha hudu cif aduniya Allah yayiwa bulama rasuwa sanadiyar ciwon ciki.
Anji mutuwarsa duk da kasancewarsa bawa hakadai asma'u da rumanah suka dangana da rashinsa saidai rasuwar ta ta6a asma'u sosai,
Ta rasa lafiya da nutsuwar zuciya tun tana daurewa tuni ciwo ya kwantarda ita hakan tasa rumanah karbar ragamar aikinta a sashen sultana.
Kwanciyar hankali tuni ta qauracewa rumanah ganin babu uba ga uwarta na jinya sosai
Sultana ma tana cikin damuwar ciwon asma'un Dana matuqar tausayin rumanah sbd jin asma'u takeyi tamkar 'yar uwarta ta jini rumanah kuwa dama amatsayin 'ya take agareta sbd tun tana shan nono tayi sabo da yarinyar.
Anyi maganin har andanga anbarwa Allah ikonsa amma jikin yaqi sauqi ganin haka sultana ta 'yantata nanda nan aka shelar an 'yanta baiwa asma'u.
Rumanah ga abin farin ciki amma Sam batajinsa ita kadai tasan yanda takejin zuciyarta ganin mahaifiyarta sai qarayin nisa takeyi.
Cikin dare