Showing 69001 words to 72000 words out of 81312 words

Chapter 24 - Tarayya Book 1 Hausa Novel Complete

Mamugee   

17 Dec 2024

253

gskia ko ita bazataso rumanah ta zubar da jiniba sbd sauyi suke fatar samu daga gareta...

Itace sarauniya ta farko a tarihin qasar gabaki 'daya data hau sarauta batareda jinin sarauta a jininta ba bama 'yar qasarba baquwar haure daga wata qasar,

Qaddara ta koro iyayenta daga gida suka fada wani gari inda daganan Allah yasake jefasu hannun masu kamun bayi aka kamosu zuwa nan qasar aka haifeta amatsayin baiwa
Wata qaddarar tasa ta auri yariman masarautar,

duk wannan qaddarar data koro iyayenta ta zamtowarta cikin lissafin masu mulkin qasar ne wannan kawai ya tabbatarda akwai abinda Allah ke nufi da hakan Wanda suke fatar sauyine na alkhairi mezaisa suso ganinta tana aikata abinda sauran sarakunan suka aikata.

Tasan tabbas maheer yayi hakan ne dan bazai iya bari ya rasataba dan idan ta cigaba da zubarda jinin karagar mineelik zata shiga jikintane sosai ta yanda zasu rasata har abada.

Dakinta tashigarda ita ta kwantarda ita kan gadonta ta rufeta tareda shafa kanta ta fice taje palo ta zauna tareda kallon Jakadiya data shigo duba assultana jin shiru dan tuni aka zagaye sashen ammyn da tsaro kasancewar tana cikin.

Dafe goshi ammy tayi cikin tsananin damuwa da rashin sanin mafita tace,

Kije kisanarda sarkin fada haroun assultana ta 'daga hukuncin zuwa wani lokaci batajin dadi yanxu.

Cikin girmamawa da jimami tace,

To""ta fice taje ta sanar atake akai sanarwar aka watse tareda tsananta tsaro sashen ammy.

Har dare tana sashen ammy kwance ko motsi bata yi
tayi wani irin sanyi idanuwanta sunyi jajir.

Shigowa ammy tayi cikin nutsuwa ta zauna bakin gadon tareda sauke numfashi ahankali cikin kulawa da sanyin murya takira sunanta.

Bata motsaba ta bude idanuwanta dasuka kumbura batareda ta amsaba.

Duk wani 'da na halak bazai iya kallon makasan mahaifansa ya qyalesuba matuqar yanada halin daukar mataki ko fansa akansuba..
Saidai kuma dangana da bariga Allah ta wata hanyar shine sasanci da kawo qarshe ga kashe kashen.,
Ummu-rumanah har abada haqqin asma'u da bulama bazai bar ko 'dayanmuba koda kin yafe mana saidai kuma ina sake roqon yafiyarki a maimakon mu duka 'din,
Wlh rumanah ina kallonki amatsayin 'yar dana haifa,
Ina qaunarki da sonki har cikin zuciyata fiyeda wasu daga cikin 'yayan dana haifa shiyasa bazan iya bari naganki cikin wata muguwar rayuwa.

Kisan bashine mafitaba bashine zaisa kiji sanyi a mutuwarsuba saima lalata rayuwarki dazakiyi ta hakan sbd har abada bazaki yafewa kanki abinda kikayiba zaki tsinci kanki cikin baqin ciki da damuwar da muma muke ciki ayanxu,

Mijinki yana miki sonda bazai iya bari ki fada wani mummunan haliba bawai yanayi ne dan karki kashe mahaifinsa saidan yana tsoron hakan zai qarasa gusarda imaninki ne.

Amatsayina na uwa ba sultana matar sultan mahaifiyar maheer ba nake baki shawarar karki kashe mahaifin mijinki ki bar iyayensa da haqqin ran iyayenki wlh Allah zai kamasu sbd baya taba barin haqqin wani akan wani dan haka kiyiwa magana nazari.

Miqewa tayi jiki asanyaye tabar dakin tana fatar rumanar tayiwa zancenta kyakkyawan fahimta.

Qofar da ammy ta fita ta qurawa ido idanuwanta nasake kadawa sbd zancen ya shigeta saidai fadanta da maheer ya kasa barin zuciyarta ta nutsu da daga bakinsa wainnan kalaman suka fito tabbas zuciyarta bazata tsaya wasi wasin daukarsu ba,,

Meyasa zai fada mata kalaman dasukafi dalma zafi gurin tarwatsa kunnuwanta da zuciyarta?????
Meyasa zaiyi fushi ya iya furta mata kalaman rabuwa da ita bayan alqawarin dayayi mata badan mutuwaba dashi da ita bazasu rabeba????
Wasu irin hawaye masu radadi suka gangaro mata ta rintse ido tana qoqarin danne kukan dake qoqarin zuwar mata.

A cikin daren takoma sashenta tareda guards inda ta bada gargadi mai qarfi akan batason ganin kowa.

Kwana biyu tayi bata fito ko qofar part dinta ba..
Abincin safe rana dare haka ake kwashesa bata fitowa saidai ammy tazo dakanta har bedroom tasata cin abinci dole.

Duk iya yanda take jin kewa da soyayyarsa na cin zuciyarta dannewa tayi sbd har lokacin zuciyarta cike takeda zafi da radadin kalamansa shima kwana biyun bai nemeta ba hakan yaqara quntata yanayinta.

Nuratu data rungumi qaddara da hannu bibbiyu akan mahaifiyarta still itace ke kulada rumanar amintacciyar baiwarta duk da da farko anso hanata ko kusantar inda rumanah take saidai rumanar ta hana sbd tasan suna tsananin buqatar juna sbd sukadai suke ganin junansu amatsayin jininsu tunda mamani sunanta matacciya.

Sultan kuwa a rubuce ta aikawa harooun da takardar a tsananta tsaro a sashensa kowama yanxu ta hana yashiga gurinsa
Hakan kuwa akayi nan take aka cika umarninta tareda bada gargadi ga duk Wanda yaje kar abari yashiga.


Kwance take kan doguwar royal chair 'din shaqatawa dake qaramin palonta dakeda manyan qofofi guda biyar dasuke ta bayan garden din shashaqatawarta,

A rufe idanuwanta suke saidai Sam ba baccin takeba iskar gurin mai sanyi take kado mata ta shara sharen labulayen winduna da qofofin palon dan ragewa kanta zafi da quncin datake ciki.

Ahankali ta jiyo kukan jariri na shiga kunnenta ta bude idanuwanta a hankali sbd tasan kukan abeel ne tunda kaf masarautar babu jariri bayanshi.

Tashi zaune tayi cikeda kewar 'danta da tausayinsa na rashin 'dan uwansa dakuma 'dumin jikin mahaifiyarsa
Miqewa tayi ta nufi qofar bakin window ta tsaya tana hango cikin bedroom din suhailat da itama ta iska ke daga farin labulenta....

Rungume take dashi a tsaye tana jijjigasa cikin tsananin kulawa da damuwar kukan nasa
Ta 'dagosa tafa duba fuskarsa cikin qaunarsa tayi kissing kumatunsa tana cewa,

Abeel please kayi hakuri mummy bazata sake baka maganin zazzabi ba kaji pls my little prince forgive mummy......

Hawayen datake ruqewane suka gangaro mata na tsananin soyayyar 'danta da qaunarsa saidai kuma bazata iya karbarsa daga suhailat na....

Tunda ta shigo rayuwarta ta sanadinta ta rasa komai,

Ta rasa jin dadi,kwanciyar hankali da soyayyar mijinta sbd ita,
Ta rasa babynta sbd jin mijinta ya aureta,
A yanxuma ta rasa jemal ne sbd ita Dan 'yayanta akaso kashewa duka tsautsayi yasa aka kashe mata jemal kuma gashi ta rasa mahaifarta har abada...
Gashi ta riqe 'dan kishiyar datai sanadin rabata da komai da zuciya 'daya tana qaunarsa tamkar itace ta haifesa,,,
Wace irin soyayyace takewa maheer??sbd tasan tana tsananin qaunar abeel ne sbd shi 'din tsotson maheer ne.

Idan suhailat ce a matsayinta na yanxu zata iya kashe mahaifin maheer?

Duk wainnan abubuwan da suhailat ta rasa ta dangana bata riqe kowa araiba gashi tana rayuwarta gwargwadon iyawarta batareda tasaka damuwar duk Wanda ya cucetaba koya tauyeta.....meyasa ita takasa hakan?
Suhailat tafita son maheer ne???

Girgiza kai tayi tareda durqusawa a gurin tana zubarda sabbin hawaye masu radadi da ciwo gabaki 'daya ta rasa nutsuwarta da sukuninta rashinsa atareda ita jitake tanason zubarda jinin duk Wanda ya cutatar da ita da iyayenta da 'yayanta SBD kalamansa dasuke yawo cikin kanta suna qona zuciyarta...
Cikin kuka tace,

Bakasan rashinka taredaniba ha'darine dan zan iya aikata abinda bakason dan Allah kadawo gareni maheer.

Suhailat data shigo palon dan kawo mata abeel tagansa sbd ta hangota lokacinda take kallonsu tayi saurin tsayawa cak jin abinda rumanar tace.

Numfashinta taji yaqara gudu tayi saurin juyawa dan ficewa tun kafin rumanar taganta
Saidai tana juyowa tagansa tsaye bayanta idanuwansa sunyi wani irin zurfi ya qureta da ido.

Tsawon kwanaki kenan itama bata sakashi a idoba 6acin ran rumanah duk yashafesu saidai Sam bata damu sosai da rashin ganinsaba sbd tasan irin radadi da zafi da zuciyarsa ke ciki na fada da abinda kafiso fiyeda komai.

Rabasa tayi zata fice sbd ahankali ya kira sunanta ta tsaya cak
Rumanah kuwa tun shigowarsa taji qamshinsa saidai bata juyoba sbd wani irin bugawa da zuciyarta keyi.

Hannu ya miqa ya dawo da suhailat gabansa cikin murya mai bada umarni yace,

Miqa mata 'danta.

Arikice takallesa itama rumanah a firgicen ta juyo takallesa.

Fuskarsa a matuqar 'daure yace,

Kibata 'danta.

Wasu irin hawayen soyayyar abeel da qaunarsa suka gangarowa suhailat takalli abeel din takalli fuskar maheer din taga babu sakewa ko kadan ta juya tana tsiyayar hawaye qafafunta na rawa ta nufi rumanah datai mutuwar tsaye cikeda mamakinsa.

Siririn kuka suhailat tasaki tareda 'daga hannuwanta ta miqawa rumanah abeel.

Cikin rawar murya rumanah ta bude baki daqyar tace,

Nabar miki shi.

Girgiza mata kai suhailat tayi tana wani irin kuka mai ciwo da qaramin sauti.

A firgice tasake cewa,

Wlh na barmiki shi....

Girgiza mata kai suhailat tasakeyi tareda ajiye mata shi kan kujera ta nufi qofa da gudu tana toshe bakinta sbd kukan dayaci qarfinta.

Dawo ki daukesa.

Cak ta tsaya tareda juyowa takallesa da sauri

Ki daukesa nabakishi bar abada 'dankine.

Da sauri tadawo ta daukesa ta rungume tareda dawowa gaban maheer din ta rungumesa cikin tsananin farin ciki tace,

For a moment I thought na rabu da abeel har abada..nagode.

Kallon rumanah data zuba masa ido yayi cikin kulawa yace,

Suhailat idan babu so biyayya na jawo soyayya fiyeda komai,
Idan akwai so rashin biyayya na rusashi komai qarfinsa..
Har abada suhailat matsayinki daban yake cikin zuciyata bazan ta6a daina ganin girma da qimarkiba.

Sanyi jikinta yayi masifar yi sbd gane amfani yayi da ita gurin isarda saqo ga rumanah...

Wani irin ciwo da radadi taji yana tasowa a zuciyarta akaro na farko data kasa riqe abinda yake zuciyarta tasaki wani irin kuka mai ciwo tareda ficewa tana dafe qirjinta dayake mata zafi sosai.

Gabanta ya qaraso ya tsaya yana kallon cikin idanuwanta dake zubard hawayen abinda yayi yanxu dan ta tabbarda ita yake fadawa magana bada suhailat din yake.
#mamuhgee.
[8/5, 5:22 AM] ummul aulad: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*41*
_Not edited_
_*Marubucin gskia baya rubuta abu acikin labarinsa batareda yayi bincike ko tambaya ba yayiwa abin cikakken sani kusani marubuci ba jahili bane sbd wata tambayar ko comment din tamkar wanka da jirwayene akewa marubuci dan haka kusani ni bana rubuta abinda banida sani akansa.*_


Juyawa tayi tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar 'yayansa kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama baza'ace bata masa biyayyaba,,,,

Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya...sabon ciwon hakan taji ta rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida kukanta.

Riqo hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.

Kujera ya nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin nutsuwa da kulawa yace,

Kina tunanin wannan itace mafita???
Kina tunanin a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan abinda nakeĀ  buqata nakuma baki umarni?....
Kina tunanin sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???

A musulince duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.

Kina tunanin sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata zaman takaba babu adadi,
Duk kina tunanin yin kansa ne kokuma ra'ayin kansa ne???
Dana barki da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha'dari dan kuwa da yanxu jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki...

Kinga abinda mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,

Kinason yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar kisar iyayenka Wanda hukuncinki kwata kwata baiyiba a musulunce sbd kai tsaye fansa ne kika dauka,,
Kafin sultan anyi kashe kashe da dama wainda ma sukafi nasa dan haka...

Ina sonki bazan iya bari kibi hanyar da sauran sukabiba,
Bazan iya bari rayuwarmu ta lalace ba sbd rayuwata zata lalace ne daga lokacinda taki ta lalace dan haka bazan iya bariba,
mahaifina tun tuni naso na kubutardashi daga hakan amma yayi aiki da qarfinsa na zama mahaifi agareni ya nesantani da kansa dan haka bazan sake aikata wannan kuskuren ba sbd ke din ikona ce.

Na auri suhailat shekaru shida zuwa bakwai yanxu...,
A cikin shekaru bakwai dinnan bantaba fada suhailat ta fadaba sbd soyayyarta gareni mai girma ce irin girmanda yake sakata shanye duk wani tauyewa dazai fito daga gareni.,

Kece rayuwata,kece abinda zuciyata tafiso fiyeda komai saidai gaskiyar maganar shine suhailat itace nutsuwata......itace mace mafi girma da qima a idanuwa na bayan mahaifiyata...

Rintse idanuwanta tayi da qarfi zuciyarta na tsananta bugawa jikinta na daukar rawa hawayenta na tsananta.

Kallon yanayinta yayi cikin damuwa yace,

I can't lie to you amma steps dinda kika fara son dauka sun fara ankarar dani babban kuskuren danake shirin aikatawa na barin suhailat ta fita daga rayuwata and idan kika cigaba da qoqarin binsa to tabbas zaki rasani......

Wani irin kuka ta fashe dashi mai qarfi da shiga zuciya tareda zamewa qasa ta zauna ta cusa kanta cikin qafafunta tana jin sabon nauyi cikin zuciyarta sbd dukkanin rayuwarta ta hargitse ta juya ta zama wani abu na daban,
Tana tunanin zatayi rayuwar aure mai dadai saidai gabaki dayama rayuwar auren data kowama ta lalace tun haihuwarsu masarautar ta hargitse takoma gidan baqin ciki sbd kowa yarasa gane inda aka dosa.

Dafata yayi ahankali tareda furta,

I love you queen ummu-rumanah bulama,
Ina sonki zanci gaba da sonki har numfashina na qarshe.

Miqewa yayi ahankali yabar dakin idanuwansa na qara kadawa zuwa jajir.

Sabon kuka tasaki bayan fitarsa tanajin maraici da baqin cikin wainda sukayi sanadin barowar iyayenta da gida har sukazo nan aka haifeta..wace irin rayuwa tasamu kanta ne aciki..

Tabbas tanason yankewa sultan hukuncin kisa ne badan ya cancanta ba sai dan daukar fansar kisar dayasa akayiwa iyayenta,
kwata kwata zuciyarta takasa yarda tayi masa hukunci akan dukkanin abubuwan dayayiwa bayin Allah kanta kawai da iyayenta take gani Wanda idan tayi masa kisa akan hakan sun zamo daya babu banbanci a tsakaninsu.

Kuka takeyi sosai tanason ko nauyin dake danne da zuciyarta ya sauka amma saima wani sabon qunci dake qara mata nauyi.




Kuka takeyi sosai tareda dafe zuciyarta dake mata tsananin radadi da ciwo,
Kukan datakeyi ayau yafi na ko yaushe sbd duk wani hope datake dashi akan zai sota wata rana ya rusashi dan kuwa ta tabbarda zuciyarsa ba ita takesoba kuma bazata ta6a sontaba.
Taso ta zauna dashi har qarshen rayuwarta sbd qaunarta garesa mai girma da tsafta ce saidai kuma hakan bamai yiyuwa bace sbd tasa zuciyar takai qololuwa gurin son wata
Saisai Bazataga laifin rumanah ba sbd tun kafin aurenta tasan babu soyayyarta a zuciyarsa saidai qauna da girmamawa zuciyarta ta dauki wannan sbd babu wata a zuciyarsa tana fatar tashiga wata rana saidai yanzu dayakeda wadda yakeso rayuwarsu su duka na neman lalacewa sbd soyayyarsa dan haka yau duk wani abinda takeson tabbatarwa ta tabbatar dan kuwa har abada bazai ta6a sonta tunda bai sota sbd 'yayanta da shekarun dasuka diba ba.

Ahankali ta tsaida kukanta saidai hawayenta dasuka kasa tsayuwa cikin muryar kuka da tsananin karaya tace,

Ka tarwatsa duk wata soyayyarka dake raina maheer.

Kallon abeel dake kwance tayi tabbas tana qaunarsa saidai bazata rayu dashiba dan kuwa zama a tsakanin iyayensa ya qare mata har abada.

Hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta share tareda miqewa ahankali ta nufi wardrobe dinta ta bude.

Ahankali ta fidda dukkanin kayanta ta hada na abeel tareda duk wani abinsa dake gurinta.

Acikin daren babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd babu Wanda yake cikin nutsuwa kowannensu tunanin step 'din dazai dauka dan kawo sauyi arayuwarsa mai kyau yakeyi.

Suhailat tagama yanke shawarar rabuwa dasu takoma qasarta sbd tabbas kota cigaba da zama zaman takurawa juna zasucigaba dayi musamman yanzu dayake buqatar lokacinda zai daidaita komai na masarautar ta hanyar matarsa dan haka tafiyarta shine mafita ga dukkaninsu gabaki 'daya.

Tsaye yake bakin windon palon sama na gidan khaleefa ya qurawa waje idanuwansa dake cikeda rashin bacci da damuwa..

Khaleefa dake zaune yana kallonsa cikin tsananin kulawa yace,

Kaine shugaba kuma kaine haqqin kawo gyara acikin zamanka da matanka ya rataya akanka.,

Tun farko kaso kawo gyara batareda ka hau ba Allah bai nufa ba sbd lokacin yanke ijabar baiyiba amma yanzu lokaci yayi sbd Allah yabaka dama da ikon kawo sauyi ta hanyar matarka dake qarqashin ikonka itace sarauniya....

Saidai kuma saikayi taka tsantsan gurin gyaran sbd zai iya kawo rashin fahimta da matsaloli ga rayuwar aurenku musamman suhailat......

Juyowa yayi ya zauna ahankali tareda rintse ido damuwarsa na ninkuwa sbd sanin rayuwace zasuyi sarqaqqiya sbd har abada bazai hada soyayyar dayakewa rumanah da wadda yakewa suhailat ba sbd soyayyar rumanah a jininsa take tun haihuwarta..

Yanayin iya qoqarinsa gurin ganin bai tauye haqqin suhailat da 'yayansa ba saidai zuciya batada shamaki akan abinda takeso wani lokacin Wanda hakan yafara jawo masa tsana daga suhailat abinda bazai taba fatar yakasanceba.

Dafasa khaleefa yayi cikin sanyin murya yace,

Musulunci ya yardar maka da kasaki matarka idan har babu sonta a zuciyarka sbd gudun shiga haqqi dan haka zaka iya duba hakan sbd a yanxu bazata iya jure abinda ta jureba lokacinda take ita kadai....

Rintse ido yayi da qarfi jin wani irin zafi daya soki zuciyarsa da khaleefa yayi maganar rabuwarsa da suhailat.

Miqewa tsaye yayi tareda nufar qofa ya fice batareda yace komaiba.

Kai tsaye part dinsa ya nufa harya kai qofa ya tsaya cak.

Juyowa yayi ahankali ya kalli qofar sashen suhailat da ake fita da akwatinanta.

Ya saki numfashi ahankali cikin wani irin yanayi na damuwa sbd yasan za'ai hakan.

Tabbas yana qaunar suhailat har cikin ransa kuma a shirye yakeda yin rayuwa da ita har mutuwarsa sbd abinda bata ganeba shine tanada wani matsayi mai girma a zuciyarsa na qima Wanda ko rumanah dayake so batadashi sbd ita zai iya rufe ido yayi mata wani abin amma bazai iya yiwa suhailat ba sbd akwai kunyarta mai girma a idanuwansa saidai bazai tilas ta mata ba ga duk abinda ta zaba akansa sbd ta cancanci abarta da abinda take raayi ayanxu.

Juyowa yayi ya nufi sashenta a karo na biyu duk tsawon zamansu Wanda hakan na yasakasa jin wata sabuwar gagarumar kunyarta.

Carolina ce a palo tana qoqarin fitowa da akwatinan qarshe wainda suke na abeel ne tana fitowa ta nufi sashen assultana dasu.

Bedroom dinta ya shiga alokacinda ta dauki handbag dinta da abeel zata fito.

Kallon juna sukayi dakyau
Ganin yana qureta da kallo yasata sauke kanta ahankali tareda kwantarda abeel ta 'dago ta qura masa ido ganin yanda duk ya rame

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login