Showing 6001 words to 9000 words out of 81312 words
Allah yakarbi rayuwar asma'u tabar 'yarta cikin wannan duniya mai ababen tsoro.
Rumanah kam zuciyarta bushewa tayi sosai tabawa kowa mamakin rashin kukanta har aka kai asma'un aka dawo.
Sultana zaarah lokacinda ta aika kiran rumanah tana zuwa ta durqusa gabanta kallon rumanar tayi batasan lokacinda hawaye suka taru a idonta ba tayi sauri shigewa qurya sai alokacin rumanah tasaki wani kuka daya tokare qirjinta ta zube agurin tanayinsa jakadiya tayi saurin jawota jikinta tana lallashinta.
Andauki tsayin lokaci kafin rumanah tasaba da rayuwa ba iyayenta ga 6angare guda mamani Sam bata qaunarta bare ta rage maraicin rashin uwa sbd da mamani da nuratu take kallo amatsayin jininta.
Sultana zaarah kuwa sosai take nuna qaunarta rumanah wanda itama rumanah tana qaunarta sbd ita take gani tana rage kewar ummanta.
Da haka rayuwa taja harsuka qara zama 'yan mata ta maida hankali sosai ga bautawa ummy kamar yanda take kiran sultana zaarah.
********
ABDULSHAMS IBN ABDALLAH MUHD shine sultan na yanxu dake mulki a meneelik wani yanki na babban birnin ethopia kamar yanda kakanni da iyaye suka bar masa,
Mulkinsu wani irin tsauri da zafi dashi ga wani irin qabilanci dasukedashi sbd Sam basa bayi ko borori da 'yan qasarsu saida akawo musu na wata qasar su siya shiyasa yawanci bayin masarautar daga qasashe dabam dabam suke mafi yawansu Nigeria sbd rashin tsaro na zama Dan qasa da 'yan Nigeria sukedashi.
Tun lokacin mulkin kakanni a wannan zuriar ta ABDALLAH muhd basuda yawan 'yaya maza saidai mata wanda hakan yayita kawo barazana ga barin sarauta da mulki daga zuriar.
Duk wani kalar arziki na duniya Allah ya hore musu shi kobana sarautataba amma banda yaya maza daqyar cikin yardar Allah suka samu namiji 'daya cikin 'yaya mata goma sha biyu da sarkin yakedasu daga matansa uku.
ABDULSHAMS shine yazamto namiji daya kuma ya gadi sarautar bayan rasuwar mahaifinsa ABDALLAH.
Tun yana yaro qanqani mahaifinsa yake cusa masa qaidoji da hukunce hukunce masu zafi sbd karsuyi sake sarauta tabar gidansu matuqar ba magaji sbd arubuce yaje a aje duk ranarda suka wayi gari sarki ya mutu ba magani to masarautar da duk wanda ke cikinta zasu zamo qarqashin ikon masarautar kilaimee tamkar bayi dundaga kan matan sarki da 'yayansa har bayinsu sbd wata tsohuwar muguwar gabace atsakanin masarautun.
Hakan yasa duk wanda yayi mulki basa tsayawa kan matansu da qwarqwarori suke qarawa amma duk da haka sunada qarancin maza sosai sai arzikin 'yaya mata.
Yanxu lokacin mulkin sultan abdulshams yanada matuqar zafi da tsanani amma duk da haka baiyi na iyayensa da sauran sarukan dasuka gabata.
Zafinsa yasa dukkanin fadin qasar da zagayen ake tsoron hukuncinsa shiyasa kowa a ankare yake ba'a take dokar sultan ko acikin matansa bare 'yaya kafinma akai ga 'yan qasa da bayi.
Matansa biyu sultana zaarah 'yar sultan jalaludden sarkin Libya.
'Sai sarauniya adama 'yar tsohon wazirin mahaifinsa.
'Yayansa goma cif duka mata sai yarima tak shine namiji.
Sultana zaarah keda yara hudu
Amatullah,hindu dakuma maryamah duk suna aure,
Amatullah da maryamah a Libya qasar mahaifiyarsu suke aure sai Hindu dake aure Kuwait,yarima shine qaraminsu.
'Yayan sarauniya adama shida dukkaninsu mata kuma duka sunyi aure sai autarta najwah.
Duk qwarqwarori da sultan yake kwana dasu Allah baiba ko 'daya daga cikinsu cikiba bare tahaifi 'da namiji
Hakan yake tsananin 'daga hankalinsa ga tsufa yafara kamasa yarima yafito fili yafada bayada ra'ayin mulki ko wani Abu daya danganci sarauta
Kwata kwata rayuwarsa bata yanayi damai sarauta sbd tunda yagama primary aka kawosa Greece karatu harya gama yacigaba da degree dinsa a los Angeles kafin yayi masters duk akan doctoring shiyasa rayuwarsa kwata kwata ta turawa ce,
Daga nan yadawo da rayuwarsa a Georgia inda Yayi settling yafara aikinsa anan.
Sam bai cika zuwa gidaba sbd yanayin aikinsa dakuma rashin son rayuwar masarautarsu koina mutane,koina bayi Sam shi bayason gurunda zai kasance da mutane sosai yanason free life bayason takura shiyasa yake ganin zama acan gida is a punishment.
#mamuhgee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡
*4*
Jingina jikinsa yayi jikin darnin ginin qasar dakin da kusan rabin ginin karane ya dafe goshinsa ahankali tareda rufe ido yana zuciyarsa na tsananta fargabar kar asanardashi ba'aga matarsaba kokuma ta rasu.
Qurawa qofar shigowa ido yayi yana sake tabbatarwa da kansa tabbas wata qasar suka fado sbd yanayin shigar Wanda yafita dazu da yanayin abincinsu da maganarsa tareda yanayin muhallin.
Ya jima yana tanane tunanen fargaba da rashin sukuni kafin wani dattijo sosai daya manyanta ya shigo dakin da gwararriyar sallamarsa.
Saurin 'dogowa daga jinginar yayi yatashi zaune daidai duk da rashin qarfin jikin dake tattareda dashi tareda zubawa mutumin ido Dan amatse yake dason jin ina matarsa take.
Kallon bulama dattijon yayi kafin yajuyo yakalli 'dansa dake bayansa cikin wani yare yayi masa magana kafin cikin hausarsu da bata fita yace,
Dama yatashi baka fadaminba kutti ?
Bai dadeba da tashi baabah magani natsaya bashi kafin naje kiranka saigashi kadawo.
Kallon bulama baaban yayi yace,
Sannu da kaji,yanzudai babu inda yakema ciwo ko?
Cikin qarfin hali yace,
Banajin komai yanxu qafardaice idan na motsata da 'Dan zafi,
Nagode sosai baabah amma Dan Allah ina asma'u mata.....
Kwnatarda hankalinka matarka nanan tareda kai saidai itama tayi jinya ta rasa cikin jikinta amma ta warke sosai.
Ajiyar zuciya yasake a6oye sbd ba qaramin dauke numfashi yayiba Dan gudun jin muguwar amsa.
Kutti ne yasake shigowa dakin wannan karon Asma'u na bayansa bakinta daukeda siririyar sallama.
Qura mata ido yayi sanye takeda kayan saqi irin nasu da wani juyayyen 'dankwali dako kanta bai rufe dukaba tayi wani irin mummunan baqi ta rame gabaki 'daya kamanninta sun fara sauyawa
Wani irin tausayinta Dana kansa ya rufeshi amma dai tunda sun tsira kuma suna cikin qoshin lafiya daidai gwargwado to alhmdllh.
Cikin sanyin jiki ta durqusa qasa tace,
Ina wuni baabah.
Lafiya lafiya mai sunan innejo mijinki ya farka daga yanxu kar asake kuka Dan ba'a kuka agidan baabah namiki uzirine kema.
Duqar dakai tayi cikin sanyi ta 'daga kai sbd akwanakin datayi agidan taga dokoki da sabbin alamuran rayuwa a gidan da mutanen garin wanda cikin qanqanin lokaci ta fahimci tsantsar jahilci da rashin wadataccen ilimin addini suke ciki Dan acikin duhu suke sosai.
Fita baabah yayi kutti yabi bayansa ta 'dago kai ahankali takallesa sai kawai tasaki qaramin kuka ahankali tareda toshe bakinta.
Hannu yamiqa yajawota kusadashi ya rungumeta shima daurewa kawai yayi amma yasan gararin rayuwa yasamesu.
Rarrashinta yayi daqyar yana cewa,
Asma'u kiyi hkr insha Allah komai zai daidaita Dana sake warwarewa zamu koma gida mu fuskanci su......
Kallonsa tayi amatuqar razane tana girgiza kai tace,
Yaya Dan Allah mubar maganar komawa yanxu kwata kwata nan inda muke wani yankine dabashida suna acikin wani lungun daji mai nisa daya ruwa masu yawa ya raba tsakaninsu da Nigeria dakuma wasu qasashen,
Sunada kwanciyar hankali duk da suna cikin tsananin duhun ilimi da rayuwa,
Jin dadi ba komai bane idan ga kwanciyar hankali da Wanda kakeso,
Bamuda uwaye ko 'daya duk ankashesu su yakurah komawarmu yanxu zamu saka rayuwarsu acikin hadarine suma,
Mu gwada bawa rayuwa wani chance anan sbd kwanciyar hankali da nutsuwa,
Mubari gaba idan komai ya Dade da shidewa saimuje da zuriar da Allah zaibamu anan cikin kwanciyar hankali.
Shiru yayi yana kallonta sbd tagama kashe masa jiki tunowa da mutuwar iyayensu kuma tabbas komawarsu saka rayuwarsu yakurah ne ahadari.
Ganin yana tambabar yarda da zancenta yasa hawayenta tsananta cikin kuka tace,
Yaya kadaina tuno dukiya da rayuwarmu tabaya sbd rayuwa dakai anan yafimin komawa cikin daular dazata saka mu rasa juna.
Tsananin tsoro da figicin datake cikine yasa yayi saurin rungumeta yace,
Asma'u zamanki cikin kwanciyar hankali yafimin wata dukiya da daular rayuwa.
Satinsa biyu da farfadowa yafara miqewa kutti ne keta faman dawainiyar kula dashi
Ahankali yake koyan tafiya da sanda har waje suke fita suna zago qauyen Wanda tsaf yagama gano tabbas cikin duhun rayuwa suke sbd dajine zallah saidai akwai niima kasancewar zagaye sukeda ruwa.
Asma'u tuni tasaki jiki da matan gidan zuriar baabah Dan tuni aka ware musu fili acikin gidan da nufin bulama na warkewa yaje ya sassaqo icce ya Gina musu dakinsu acikin gidan.
Cikin ikon Allah ya warke sosai bai tsaya wata wataba yafara binsu kutti daji baji ba gani ya zage yazama nimiji sbd dolene yasaba da baqar wahala sbd itace rayuwar garin gashi garin koina hakine mai shegen tsawo Wanda wani gurinma idan kana tahowa baka ganin mai tahowa.
Cikin sati uku ya kammala musu dakinsu ita kuma asma'u matansu suka koya mata kara taringa binsu suna yowa tare harta hada musu gadansu na kara da tabarmar saqi.
Ahankali suka saje suka zama 'yangari suma baabah yabasu sunan zuriarsa kasancewarsa shine shugaba agarin nan kowa agari suka sakasu cikin zuriar gidan baabah.
Duk wata wahala ta rayuwa sun iya sunsaba yanxu sbd sun tasarwa shekara biyu agarin
Kwata kwata kamanninsu sun tashi daga nada sunkoma wasu kamannin daban duk wani kyau da tsari suncireshi sunkoma munana kamar sauran 'yan garin
Iliminsu na addini dasukazo dashi ya haskaka qauyen sbd sosai suka qararda 'yan qauyen yanxu ba laifi ilimin addini yadan yadu Dan yanxu wasunsu na wankan janaba idan sun sadu da iyalansu.
Suna cikin kwanciyar hankali sosai sbd ana qaunarsu har mantawa akeda su 'din ba asalin nan bane tuni aka zama daya,
Asma'u ma tuni tashiga jerin surukan gidan baabah babu bambamci
Matar kutti MAMANI ce kawai ma suke samun matsala wasu lokutan sbd kishin matan sauri.
Shekaru sunja sosai manyanci yafara kamasu amma har lokacin babu haihuwa sai 6ari takeyi data samu ciki kusan 6arinta biyar gashi girma yazo musu.
Lokacinda baabah yabuqaci bulama ya qara aure bai musaba sbd bin umarnin baabah din
Haka aka hadasa da wata 'yar maqocinsu sbd shi baabah 'yayansa mata takwas duk sunyi aure.
Tuni bulama ya duqufa aikin sassaqo itace ba dare ba rana sbd yiwa kantali 'dakinda zaisata idan anyi auren danma wata uku aka dibarwa bikin sbd yasamu yin dakin cikin nutsuwa.
Cikin ikon Allah asma'u Ashe tanada shigar ciki har wata biyu amma tayi shiru sbd kar ayi tunanin fasa auren Dan ko yanxu tana tunanin bazai tsayaba.
Sauran sati biyu bikin cikin na wata biyar tuni yafito kowa yafahimci cikine da ita nan murna ta kaure sbd cikinta baita6a wuce wata biyu zuwa ukuba.
Duk da haka tace kar bulama yafasa auren ayi kawai ta yanda zai samu 'yaya da yawa tunda yafara manyanta ba haihuwa,
Hakan datayi yaqara kawo fahimta da shaquwa tareda qaunarta ga matanen qauyen tuni aka fara shagulgulan biki irin nasu na al'adarsu.
Ana saura kwana biyu 'daurin aure da tsakar dare asma'u ta fito fitsari ta nufi bayinsu na kara dake baya na kowa da kowa na gidansu
Tayi tagama harta juya saitaga kamar tana hango hutattaki na tahowa cikin qauyen ta bude idanu da kyau saitaga tabbas kamar mutane ne da yawa ke shigowa qauyen.
Sakin butar qasar hannunta tayi ta nufi bukkarsu da sauri tashige jikinta na rawa ta tayarda bulama,
Cikin sauri da magagi yatashi Dan yadauka cikinne yasamu matsala yana kallon cikinta da sauri yace,
Innaje lafiyanki kuwa?sbd shine sunan datun zuwansu ake kiranta dashi sbd sunan mahaifiyar baabah ce tuni aka manta sunan asma'u.
Murya na matuqar rawa tana kallon qofa qasa qasa tace,
Mutane ne da hutattaki suka shigo qauyen nan na hangosu kuma......
Ihu da hayaniyarda qauyen ya 'dauka ne ya katse maganarta suka kalli qofa afirgice tayi saurin cakumosa tana cewa,
Kajiko wlh mutane suke kashewa...
Zabura yayi ya miqe tareda damqo hannunta suka fito tsakar gidanda kowa yafito cikin tashin hankali da firgici.
Baabah cikin tsananin firgici da tashin hankali yace,
Dukkaninku kubi ta bayan gari ku gudu karku tsaya saikun kai iyakar ruwa Ku shiga Ku lafe qasan ruwa masu kamen mutane ne su sayar wata qasar amatsayin bayi.
Gaban bulama da innaje ya buga da mugun qarfi ya qara damqe hannunta tareda kallon fuskarta yace,
Duk tsanani asma'u kadaki rabu da hannuna.
'Daga masa kai tayi hawaye na gangarowa idonta.
Dukkanin zuriar gidan sukabi ta qofar baya suka fara gudu suna waiwaye cikin tsoro da tashin hankali suna tsallake gawarwakin wainda aka kashe kwance cikin jini sai gudana yake
Ihun yara da mata tareda na maza saitashi yake ga huta da aka cinnawa wasu bukkokin.
Sun kusan isa bakin ruwa innaje tayi tuntu6e da wata gawa ta fadi tareda sakin wani razanannen ihu tana rawar jiki
Mamani dake bayansu da cikinta itama tayi saurin ra6esu da gudu zata wuce qafar innaje dake qoqarin tashi ta kifarda ita
Bulama cikin tsananin hanzari ya riqosu duka su biyun ya tayar suka wuce da gudu amma sai wani tashin hankalin sukayi arba dashi domin kuwa su kutti da sauran yan gidan sun 6ace musu.
Kallon mamani yayi cikin tsananin tashin hankali yace,
Inane hanyarda baabah yace wadda mu bamu saniba?
Tsabar musiba da tashin hankali ya rudata takasa ganewa sai rarraba idanu take tana tsima cikin kuka.
Fizgarsu yayi suka nufi wata hanya da gudu Dan tsira
Qaddara ta Riga fata sai gashi tsaye turus agaban shugaban qungiyar.
Saurin kallon qasa yayi gaban shirgegen mutumin idanuwansa suka sauka kan gawar baabah kwance cikin jini ga rigarsa harta faraci da wuta.
Bai ankaraba yaji saukar dukan gora atsakiyar kansa ya dafe kai idanuwansa suka rufe ya yanke jiki yafadi agurin.
Suna ganin yanada sauran rai suka jasa aka jefa cikin qaton jirginsu na ruwa hakama innaje da mamani.
Sun samu nasarar kamo mutane zama da sittin maza da mata banda yara suka gargada jirginsu na ruwa suka tafi.
#mamuhgee.
[7/29, 9:29 PM] Hauwa'u inna: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association_💡
*7*
Maheer mutum ne mai ra'ayin kansa wanda wani baya saka masa ra'ayi,
Abokansa mafi yawansu turawa ne sai 'Dan uwansa kuma abokinsa dasuka taso tare khaleefa duk da kasancewar basa guri 'daya shi khaleefa yana turkey ne amma suna yawan kasancewa tare idan zasuzo gida kokuma idan sun tafi wata qasar Hutu,
Shiru shiru ne baida doguwar hayaniya bare son dogon zance amma ahaka so silent dashi Allah yayisa mai tsananin son rayuwar hutawa da shaqatawa batareda takurawa ba sam shi mutum ne maison life shiyasa kana ganinsa zakaga wayayyyan mutum da ilimi ya kustsa sosai tareda Hutu da naira.
SUHAILAT BOUKAR itace gidanta yake kusadana maheer 'yar asalin Mali karatun masters dinta takeyi anan qasar
Sosai take shiri da maheer kasancewar sunfara sanin junane sanadin abokinsa bell dayake itama friend dinta.
Sunfara gaisawa ahankali harsuka saba kasancewarsu wayayyu masu ilimi yasa suke jin dadin zama da juna sbd kowa yasan abinda yakeyi kuma kowannansu is living a free life.
Itadai suhailat tana tsananin son maheer amma ganin babu wannan ataredashi yasa tayi amfani da iliminta ta danne tareda 6oyewa koda wasa babu wanda zaice yaga alamar sonsa atareda ita sbd sanin ita mace ce meye amfanin iliminta ta wannan fannin idan bazata iya danne soyyayyar wanda baimasan tanayiba.
TAKE NOTE 'yan mata pls mu koyi boye soyayyar wanda baisanma kanayiba ki daraja kanki na zamantowarki mace.
Sultana ma ba laifi sundan saba da suhailat harkiranta tanayi ta gaidata.
Duk lokacinda yazo gida maganar sultan 'dayace wato yayi aure asamu 'da namiji sbd dukkanin hope dinsu yanxu akansa yake
Shi alamarin na matuqar basa ciwon kai da mamaki idan ana cewa yayi aure ya haifi 'da namiji
He is man of his own now baiga dalilin dazaisa ace anason dole yayi aureba duk lokacinda yaji yafara buqatar kasancewa da mace zaiyi auren amma ba haka kawaiba yanxu yayi aure.
Ammynsa nason yayi auren amma ita lalla6asa takeyi bakamar sultan dake son nuna masa qarfin iko ba kuma tasan tunda sultan yace maheer 'din yayi aure to kobai tashiba sai yayi masa koyasan matar kobai santaba.
Hakan yasa sultana take kaiwa maheer 'din ziyara idan aka 'danja lokaci tana rarrashinsa amma dai still babu alamar zai takura kansa yayi yanda sukeso 'din shiyasa ta hakura lalla6a sultan akan abi maheer din ahankali abarsa har zuwa lokacinda zaiji ra'ayin yin auren.
Wani shu'umin murmushi sultan yasaki lokacinda tagama fadar zancen wanda yasa gaban faduwa sbd tasan itama fada kawai tayi ko za'a dace yaji shawarar tata amma tasan sultan Sam baya 'daga qafa ga wanda ke masa garaje.
Washe gari tun agurin sallar asuba aka bada shelar saqon sarki na bayan sallar juma'ar satin nan za'a 'daurawa yarima aure.
Koda labarin ya iso kunnen sultana ajiyar zuciya kawai tayi ahankali batareda tace komaiba Dan tasan dole haka zata faru tayi magana asata kullen shekara.
Haka dai cikin dauriya sultana ta daure tagabatarwa da sultan SUHAILAT amatsayin wadda yarima yake kulawa acan inda yake.
Tsaf tabasa bayanin komai akan suhailat babu bata lokaci akai aike ba laifi 'yar manyan mutane ce ita da yayanta kadai iyayensu suka haifa rayuwarsu ba takura suna yin rayuwarda duk sukeso amma sbd wadatar ilimi yasa Sam basa iskanci amma rayuwa tajin dadi da Hutu babu wadda basayi musamman arziki da Allah yahorewa iyayensu.
Sanin waye maheer da mugun ra'ayi akan abinda baiyi niyaba yasa sultan cewa sultana Zaarah ta koma masarautar mahaifinta batareda bawa ko 'dayaba harsai ranarda matar maheer zata shigo masarautar sushigo tare.
Rintse idanuwa tayi cikin ciwon rai da tausayin maheer sbd daga ita har maheer da kowa yasan abinda sarki ke nufi da hakan
Wato tayi gidansu harsai maheer ya aminta da zaiyi aure bayan yasan hakan zai ta6a tarihi da sunan masarautar mahaifinta.
Kwana biyu tayi tana hada kayanta sbd tuni akayi mata booking ticket 'din jirgi.
Lokacinda labari ya iso gurinsa rintse idanuwa yayi cikin daci da radadin zuciya sbd yasan me sultan ke nufi da hakan,
Duk lokacinda yakeson wani Abu daga garesa da ammynsa yake yaqarsa.
Bude jajayen idanuwansa yayi yakalli wayarsa ya dauka babu bata lokaci yakira sarkin isarda saqo yana 'dauka da wata irin murya mai nuna 6acin rai dayake ciki kai tsaye yace,
A isarwa da sultan saqon abar ammynah ta tarbi matata ranar dayakeso.
Angama sarkin saqo yafada cikin matuqar girmamawa kafin ya garzaya da hanxarinsa ya isarda saqon.
Murmushin manya sultan yayi yace,
Kasanar masa ranar juma'a ne saiya shirya dawowa idan kuma baidawoba ranar asabar sultana zata kawo masa matarsa har inda yake.
Koda aka sake Isar masa da wannan saqon datse wayar yayi tareda rintse ido ya budesu jajir sbd baqin cikin yanda idan sultan nason quntata masa yakeyi ta hanyar ammynsa
Banda son a xafafa zuciyarsa ace idan baijeba mahaifiyarsa za'asa takawo masa mata har wata qasa sbd anraina masa ita....
Wurgi yayi da tumbler din hannunsa a qule yace,
Wat did he think of himself sultan dayake masa haka bayan yasan he can't tolerate seeing his ammy being disrespected.
Baigama shan haushi da mamakiba saida yakoma yatararda lbarin suhailat ce amaryarsa
Duk inda ransa yake saida ya sake 6aci sbd rashin tunanin dama tun farko ita 'din yagabar tun kafin aci zarafin ammynsa sbd yasan idan ya auri suhailat kowa zaiyi rayuwarda