Showing 42001 words to 45000 words out of 89272 words
Chapter 15 - Aneesah Book One Complete Hausa Novel
dauki fitila ba Aneesah tace "kai wnn irin tambaya hka sae kace dan jarida," yyi dariya da ya bayyana dimples dinsa, ta tsura masa ido tana kallo, Haydar kawae take tuna wa, ya daura hannu a kanta ya wara idonsa yace "ya dae" ta buge masa hannu tace "meye hka," yace "ohh sowie bby," ta tabe baki a xuciyarta tace "wnn dae dan iska ne dama yyi kama da su," ta mike xata bar wajen ya fixgota har tana faduwa kansa yace "ke baki gaya min sunanki ba," tace "A'a meye haka malam," yace "sae kin gaya min sunanki xaki bar nn," d[truncated by WhatsApp]
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar
57.....
Kamar daga sama Aneesah taji abu ya buge ta da karfi, daga nn
kuma bata sake sanin abinda ya faru ba, karime da su xulai suka
fasa ihu ganin abinda ya faru suna cewa "wayyo shiknn ya kashe
mana Aneesar mu," mai motar ya fito daga motar da sauri yace
"subhanallahi," ya durkushe gabanta ya dago ta, su karime duk
suka xagaye shi suna koke koken Aneesah ta mutu, ya tura xulai
dake daf da kansa tana rusa ihu a fusace yace "ke da'alla ja can
uban wa yace maki ta mutu," xulai ta koma baya da sauri tana
yarfe hannu tace "wayyo ashe bata mutu ba karime," daukar
Aneesah yyi ya saka cikin motar ya dawo xae shiga driver sit,
karime ta bisa da gudu xulai da yayarta Xano na biye da ita a
baya, karime ta rike motar tace "kai ina xaka kai mana 'yar
uwarmu?" xulai ta fara kkrin bude motar a rude wae xata ciro
Aneesah, ita kuma xano ta yi kauye da gudu neman taimako wae
wani xae sace Aneesah a motarsa, shi ko ya fixge xulai daga jikin
motarsa ya jefar snn ya bude motar ya shige, suka dinga ihu suna
bubbuga motar da karfi, bae ko damu da hka ba ya tada motarsa
ya ja ta ya bar wajen a fusace kuma da gudu don har yana neman
buge karime. Shatu ta saki salati ta fito kofar gida a guje bayan
lbrin abinda ya faru ya risketa tana cewa "wayyo shknn na shiga
uku ni indo, ku ka ce me? Ya tafi da ita ina?" xulai dake ta rusa
kuka tace "a motarsa ya tafi da ita," nn da nn lbri ya baxu kauyen
wani mai mota ya kade Aneesah ya tafi da ita kuma a motarsa,
mutane suka dinga fiffitowa da daddaya da daddaya aka taru
kofar gidan shatu da ta xama kmr mahaukaciya wae an sace
mata 'ya kuka har da majina faca faca, karime da mamarta ma na
tsaye wajen ana ta jajanta abun sae kuka karime take yi, xano ta
raka samarin kauyen xuwa gun da abun ya faru aka bi bayan
motar amma aka rasa inda mota tayi, sae kusan maghrib kowa
ya watse ya koma gidansa, aka bar shatu da 'ya yanta suna ta
kuka, banda Xano da tace "to wae shatu sae kace uwarki ta bata
ko 'yar da kika haifa a cikinki, tunda ba a ganta ba ba shiknn ba"
tayi tsaki ta jawo kayan kwalliyanta xata yi shirin dandali, shatu ta
sharbe majina tace "don ubanki da kin san abunda muka rasa
ynxu da baxa ki ce komai ba," Malam mati ya shigo gidan da
buhu a hannunsa, rabon sa da gidan yau kwana biyar knn don
bae cika xama kauyen ba, yana shiga Bukkar shatu yace "ke shatu
me nake ji a gari wae yarinyar nn mae mota ya gudu da ita, ina
ya kai ta, kin manta jan kunnen da Alhaji ya mana, masifa kike son
ja mana" shatu tace "to ba aikensu nayi ba malam," yace "to shi
mai motan daga ina yake kuma ina xa sa?" xulai tace "bakaken
kaya ya saka gaba daya har takalmi da tabarau, kuma mu bamu
san inda xa shi ba" Xano tace "kila ma dan yankan kai ne," shatu
tace " lah! kuma fa wllh hka ne ya motar tasa yake?" xulai tace
"katuwa ce motar ita ma bakakirin kmr kayan jikinsa," malam yace
"shknn ae barka ma da ya tsaya a kanta," xano tace "shi dae na
gani malam amma tun tuni shatu ta bi ta cika ma mutane kunne
da kuka da sharban majina, sae kace uwarta aka sace," shatu ta
sauke ajiyar xuciya tace "to idan shehu ya xo kauyen nn me xamu
ce masa malam," mati yyi mata kalln bnxa yace "ba sae mu ce
mun aurar da ita, a can wani kauye ba, kuma ba na ce maki ko
sati biyu ba ayi ba da ya kira ni ta wayar Buba ba, yace idan ta
addabemu mu kasheta kawai mu huta da jaraba, da na kawo
maki xancen ba ca kika yi aa ba kina da babban shiri a kanta,"
shatu tace "hka ne malam to tanko fa, ynxu shknn munyi hasara
knn?" yace "to ya xa ayi, ni dae daga yau bna sn na sake jin
batun yarinyar nn a gidan nn, tunda ta bata ta bata, idan shehu ya
xo iya ka nace masa ma an kasheta kawae," shatu ta mike tsaye
tana gyara tsumman xaninta tace "to shknn, amma ni dae ba hka
na so ba wllh, ga shi ynxu shknn mun rasa tanko, tunda dae bae
ce yana son su xulai ba," A hankali Aneesah ta bude idonta ta
tsura ma agogon dake manne a bangon dakin da take, karfe sha
daya ta gani, ta shiga bin dakin da kallo kmr mai son tunano abu
bbu tantama ta gane asibiti take, ta mike xaune a hankali tana
kallon hannunta dake manne da alluran drip, taji an bude kofa, ta
daga kanta da sauri tana kallon mai shigowa, ya tsakar mata
murmushinsa mai kyau ya karaso gefenta ya xauna yace "bby kin
tashi," kallonsa kawae take yi da mamaki, ya daura hannu kan
goshinta ta cire hannun a hankali tace "ka mayar da ni gidanmu,"
ya harareta yace "kina under treatment xan mayar dake gidan
naku?" tayi kmr xata yi kuka tace "xa ayi ta nemana fa don Allah
ka mai da ni gida, ina mudatheer?" yace "oho! kuma naki mayar
dake gidan karfe sha dayan daren xan mai dake gida," tayi shiru
tana kallon agogo, yace "ynxu dae me xaki ci," ta daure fuska tace
"ba komai," yace "gud, bari na kira maki Dr," yana fadin hka ya
fice daga ward din ta bisa da kallo.
2 mins · Khaleesat Haiydar...
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 56..... Ya wara dara daran idonsa yace "waw sweet name Aneesah," Aneesah tace "to ka sake ni ai na gaya maka sunan nawa," ya xaunar da ita yace "No Aneesah tsaya mu dan yi hira, don Allah" xata yi magana ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta yace "shhiii," tayi shiru tana kallonsa yyi murmushi yace "kina da kyau Aneesah," ta kauda kanta nn ma bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "hu2 kika xo yi nn Bby?" ta fixge hannunta tace "wae meye hka kke taba ni ne na sanka ne," ya kashe mata ido yana lasan lebensa yace "ni sunana Mujaheed Yusuf," tace "to naji," amma ka bar ni na koma gida, ya harareta yace "not until u tel me y u were running," ta dan marairaice fuska tace "wllh wasu mutane ne ke bi na," ya mike da sauri yace "su wa? A ina suke, me kika yi masu, xo ki nuna min inda suke," yana fadin hka xae fara tafiya ta riko hannunsa tana dariya tace "to me xaka masu?" yyi mata wani irin kallo yace "nuna min su kawae ki ga abinda xan masu," tana dariya tace "ae bn san inda suka bi ba," ya dawo ya xauna yace "da sun biyo ki har nn wllh da na cire masu hakoran bakunansu gaba daya," Aneesah tace "uhmm naga alama" Nan Mujaheed ya dinga mata surutu kmr da can sun taba sanin juna, ita ko ta biye masa sae dariya take yi, ana fara fitowa daga dandali ta mike da sauri tace "kaga ni xan wuce gida kar yayyina su gan ni a nn," xae yi magana ta hangosu xulai ta juya da sauri ta fara gudu ta bar wajen, yace "shit ban san wacece ita ba," mudatheer ne ya karaso gurin yana kallon Mujaheed yace "kana nn har ynxu ashe big bro, da ka shigo da ka ji ddi, amma sae dae 'yar birnin bata xo ba yau" Mujaheed ya dan daga kafada yace "na ganta, ko ba Aneesah ba," mudatheer yace "waw ita fa, a ina ka ganta?" Mujaheed yace "she's such a beauty, ynxun nn ta bar nn wae kar yayyinta su ganta, da gske nn aka haifeta" Mudatheer yyi dariya yace "A'a ko wata uku bata cika ba a nn," Mujaheed yace "ni kam na xo kauye a sa'a don na samu mata, kaga xuwa nan ya kamani duk sati knn" Mudatheer yyi dariya ssae yace "gskya ne, ka ga ni xan tafi kai kuma ynxu kke xuwa, amma fa sae dae gidan da take a nn ba gidan mutunci bne don mutanen gidan kowa ya san su da halinsu a kauyen nn," Mujaheed yyi tsaki yace "dont tel me dat, ina ruwana da halinsu, as far as ba su suka haifeta ba its none of my bzz," mudatheer yyi dariya suka bar wajen yana cewa "kaga ina ta damunka kaxo kauye kana ja min aji ashe alkhairi xaka xo ka tarar a nn," mujaheed yace "yaushe xaka tafi," "gobe da safe," mudatheer ya ba shi amsa, Mujaheed yace "xan samu ganinta da safe kafin mu tafi don Abuja nake son wucewa direct," Mudatheer yace "yes of course amma idan kaje rafi," Mujaheed yace "ehh sae naje to meye a ciki?" Mudatheer yace "to xaka kwana nn ne ko fita xaka yi," Mujaheed yace muje motata ma tana nan ae, ba karamin tashin Hankali Aneesah ta tarar a gidan ranan ba daga shatu don kasheta ne kadae bata yi ba, kuma wae washegarin ranar a gun tanko xata kwana ko taki ko ta so tunda dae shi xae aureta wae, kuka kam ta yi shi har kusan asuba, Da safe ta je debo ruwa a rafi duk jikinta a mace ga yawan faduwar gaban da take yi ta hadu da su Mudatheer suna jiranta karkashin wata bishiya, tayi mamakin ganinsu a tare amma tayi kmr bata gansu ba tayi gaba mudatheer ya kirata da sauri taki juyowa, ya mike ya bi ta yana cewa "Aneesah yau fa xan tafi shine kike min wlknci?" ta juyo da sauri tace "da gske?" yace "ehh," ta ce "to baxa ka sake dawowa ba," ya juya yana kallon Mujaheed da ya kasa daina kallonta yace "yayana xae dinga kawo maki visit ae," ta kalli Mujaheed ya kashe mata ido, ta galla masa harara tace "bana son visit din," Mudatheer yyi dariya yace "yayana ne fa," bata tanka sa ba tayi gaba duk jikinta a sanyaye ynxu Mudatheer wuce wa xae yi ya bar ta, da rana Mudatheer ya bar kauyen duk da ya so ganin Aneesah amma bae samu ganinta ba, Mujaheed ya kai sa har tashan da xae hau mota a motarsa shi da ya kamata daga can ya kama Hanyar Abuja yace ina ae sae ya dawo yyi sallama da Aneesah. Aneesah dasu xulai da karime na dawowa daga kauyen dake kusa da nasu sunje saro ma shatu gyada, suna tafe suna hira banda Aneesah da tayi nisa a tunaninta, oh ita ynxu hka rayuwarta xae kasance a gantale knn, tana tuna abinda shatu tace mata jiya da daddare wae gidan tanko xata kwana sae taji wani hawaye na xubo mata, xulai taji tana cewa "lah ga abokan Aneesah xuwa," Aneesah ta dago kai da sauri ta ga shanaye ke tahowa ta inda suke, a rayuwarta tana bala'in tsoransu ba kadan ba, duka suka tuntsire da dariya, ita ko ta hade rae xata canxa hanya xulai ta rikota tace "ae baki isa ba sae kun gaisa yau," ihu Aneesah ta dinga yi tana dukanta ta sake ta amma taki, sae dariya suke yi, karime ce kadae ta hade rae tace "meye hka xulai ku kyaleta mana," ganin sun ki sakinta ne kuma ga abun da take tsoro sun kusa inda take yasa ta fixge hannunta daga rikon da suka yi mata a guje ta afka dan titin motar dake wajen, suna ihu suna ga mota ga mota, amma ina bata ma san suna yi ba.
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 59..... Mujaheed ya gyara xama yana kallonta yace "ina jinki" ta dago kai tana kallonsa hawaye kwance fuskarta tace "shknn," yace "karya kike," ta girgixa kai tana ci gaba da xubda hawaye tace "Allah gskyata knn nake gaya maka, baffa na ne ya kawo ni kauyen nn," Mujaheed yace "waye dan nasa da baya son ya aure ki?" ta dan yi shiru snn tace "su suna da kudi mu kuma talakawa ne shi yasa baya san dan sa ya aureni," Mujaheed yace "gud, to me ya hana mahaifiyar ki biyo ki nn?" A sanyaye Aneesah tace "bata san inda ya kai ni ba ai," Mujaheed yace "ku nawa ne a gurinta?" Aneesah tace "ni kadae ce, kanina ya rasu kwanaki, dama mu biyu ne," Mujaheed ya girgixa kai yace "Allah sarki, Allah yasa ya huta," Aneesah tace "Ameen," "to shi baffan naki ya ku ke da shi?" ya tambayeta yana kallon idonta, Aneesah ta sunkuyar da kai tace "yayan Abbana ne," mujaheed ya gyada kai yace "yaushe mahaifin naki ya rasu, kuma meye aikinsa kafin ya rasu" Aneesah ta galla masa harara tayi tsaki tace "ni don Allah ka kyaleni hka ka mayar da ni gida, komai ne xan gaya maka, kuma mai hakan xae kara ka da" Mujaheed yace "tab, ba gida kike son koma wa ba knn yarinya," Aneesah ta fashe da kuka tana kallonsa tace "don Allah kayi hkuri, nasan ana ta nemana a gida ynxu " ya dan kwantar da murya yace "kiyi hkuri, kina ban amsa ta xan mayar da ke gida," Aneesah ta goge hawayen fuskarta snn ta gaya masa lkcn da abbanta ya rasu da aikin da yake yi kafin ya rasu, Mujaheed yyi shiru yana kallonta snn yace "to bae bar maku komai bne, ko ko sun kare ne," Aneesah ta gyada masa kai tace "ehh," yace "ok ynxu baki son xuwa gun ummarki knn, kin fi son xama da mutanen nn su cuceki su yi maki auren dole?" Aneesah tayi shiru tana hawaye, yace "talk 2 me mana," cikin kuka tace "ina son xuwa gun Ammina," Mujaheed yace "to kin amince na kai ki gun Ammin ta ki ynxu?" Aneesah ta tsura masa ido har lkcn tana kuka, Mujaheed ya kamo hannayenta yace "dnt wrry kanwata, xan kai ki gun Ammin ki idan kika yarda da ni, baxan bari ki sake komawa kauyen can ba, am takin yhu home Aneesah trust me, nima ina da kanni kaman ki ," Aneesah ta fixge hannunta tana kuka ssai tace "su mama xasu yi ta nemana kuma," a fusace Mujaheed yace "ita kuma mahaifiyarki bata nemanki aka ce maki ko, sakayyar da xaki yi mata knn, kinsan halin da take ciki ynxu na rashin ki, ke daya fa kika rage mata, gujeta kike son yi ko ko uban me ya hada ki da 'yan kauyen nn marasu imani, consider yhur dear mum Aneesah, kar ki yi mata hka baki san halin da take ciki ba ynxu," kuka ssae Aneesah take ta kasa cewa komai, ya tsura mata ido bae hanata kukan ba sae da ta dan yi shiru snn yace "kin amince ynxu xaki gun Amminki?" a hankali ta gyada masa kai hawaye na xuba a idonta, yace "Gud Aneesah, ina xuwa" yana fadin hka ya mike ya fita daga dakin xuwa office din likita, Aneesah ta fashe da kuka tace "ni baxan iya bin ka ba nasan su mama na can suna nemana," tana fadin hka ta mike tsaye ta gyara daurin dankwalinta ko takalmi bbu a kafarta tayi gun kofa ta bude a hankali ta fita snn ta fara neman hanyar da xata bi ta fita daga asibitin, duk a rikice take duk inda ta bi ward ne, har daga karshe ta bi wata mata dake goye da yaronta suka iso har bakin kofar fita harabar asibiti, da sauri ta isa gate xata fita ta ci karo da nurse din da tayi mata allura jiya da daddare, nurse din tace "ke ina xaki, an sallameku ne," Aneesah ta fashe da kuka a rude tace "ehh," nurse din ta riko hannunta tace "ban yarda ba, ina mutumin da ya kawo ki," dae dae nn Mujaheed da likita da nurses har biyu suka fito haraban asibitin, Mujaheed ya jingina jikin bishiya yana kallonta, kuka kawae take ta kasa daga kai ta kallesa, ya karaso gabanta ya kama hannunta yyi ma nurses din da Dr. gdya snn yyi hanyar motarsa dake haraban asibitin ya bude baya ya sa ta shiga, snn ya xaga ya shiga ya tuka motar suka fice daga asibiti.
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 58..... A tare Mujaheed ya shigo dakin da likita, likitan ya karaso kusa da Aneesah yace "yan mata hope bbu inda yake maki ciwo ko?" ta gyada masa kai kawae, mujaheed ya harareta yace "ke dae ki fadi gskya," ita ma ta galla masa hararan bata ce komai ba, likitan yyi dariya yace "to a dae tabbatar ta ci abinci, anjima nurse xata xo bata allura," yyi masu sallama ya fita, Mujaheed ya juya yana kalln Aneesah yace "bbyna me xaki ci?" da mamaki tace "waye kuma bbynka?" ya kashe mata ido yace "ke mana," sae abun ma ya kusa bata dariya amma bata ce kmai ba, ya hada mata tea ya xauna kusa da ita yace "bude bakin na ba ki, bbu xafi," ta hararesa ta dan matsa tace "wae meye hka ni ka mai da ni gidanmu," yace "to tashi ki tafi," ta fara kkrin cire alluran hannunta ya rike ta da sauri yace "ke kina da hankali kuwa?" ya kwantar da ita yana kallnta yace "kwanta ki huta dear, kiyi hkuri gobe xa a sallame mu sae na mai da ke gida," hkn da ta ji ne yasa hankalinta ya kwanta tayi shiru, ya ajiye mata tea a kan table