Showing 39001 words to 42000 words out of 89272 words
Chapter 14 - Aneesah Book One Complete Hausa Novel
"A'a ban san shi ba?" shatu ta harareta tace "shi uban garbeben ne baki sani ba?" Aneesah ta dan yarfe hannu tace "ina dae jin lbrinsa mama," shatu tace "yauwa, kin dae san duk kauyen nn bbu mai kudinsa ko, kuma shanayensa ma sun fi ashirin da biyar kin sani, snn da siminti aka gina masa gidansa dake kusa da kasuwan 'yan gwari, 'ya yansa maxa da mata suna can wnn kauyen dake gaba da namu suna karatu wae a firamari, kin dae san bae ma cika xama a kauye ba sae lkci lkci don a can birni yake aiki amma duk matansa uku suna nn kauyen," Aneesah dae kai kawae take gyada mata gabanta na faduwa, shatu tayi murmushi tace "yauwa Aneesah, shi fa, wllh jiya malam ya xo ya sameni wae yace son ki yake da aure, da kin san yanda matan kauyen nn ke rububinsa ko Aneesah," shatu tayi kwafa ta cija dan yatsa tace "kar ki bani kunya Aneesah, mu ba mara da kunya, kinga dae ina da 'ya ya mata amma ban maki bakin cikin auren tanko ba don nasan duk karuwa xamuyi ko ba komai, don hka nake sonki bani hadin kai, wllh dubu daya jiya ya ba malam da kaji biyu," Aneesah ta kasa cewa komai don tashin hankali, ta shiga uku wnn tsohon namamajon da taji karime ke cewa xa a hada ta da? Da kyar ta gyada kai ganin shatu jiran cewarta take tace "to mama naji duk abinda kike so shi nke so," shatu tayi murmushi har sae da jajayen hakoranta suka bayyana snn tace "yauwa lu'u lu'u 'yar Albarka shi yasa nake son ki, amma fa karki ki kula su garbebe da su hudu da mai shayi, duk abinda suka ba ki ki karba ae basu san da xancen ba, amma gskya wnn mudassirun ki rabu dashi don na tsanesa wllh, gashi ko kwandala baya baki na gani," Aneesah dae to kawae take ta ce mata kanta a kasa, tana kkrin mayar da hawayen dake neman xubo mata, shatu tace "yauwa Aneesah maxa tashi ki je ga can guntun kaxan jiya ki dauka ki ci ki yi min wanke wanke ki gyara min gida ki debo ruwa ki ajiye, ni ynxu xan je saro gyada ne, tunda su gantalallun yaran nn ban san inda suka yi ba, tana kaiwa nn ta saba bakin gyalenta ta fita daga bukkar tana cewa sae na dawo, kuka kam har da na tashin hankli Aneesah tayi shi ranar, ohh ko wani Hali Amminta ke ciki ma ynxu, ko ina yaya Haydar dinta gashi ana shirin mata aure da tsoho, da kyar ta iya yin duk aikin da shatu ta sa ta kafin ta dawo don duk jikinta yyi sanyi. Da yamma tana gantalin nemo itacen girki a kauyen suka hadu da mudassir da lado, lado na ganinta yace "gidan malam mati basa taba siyan itacen naira goma, sae dae su tsinta a daji," bata ko kallesu ba ta wuce su don dama basa shiri da lado tunda ya nuna yana sonta tayi shun dinsa, mudatheer ya bita yace "'yar birni ba gaisuwa," ta juya tana kallonsa taga lado yyi gaba abinsa, hkn yasa ta xauna karkashin wata bishiya mudassir ma ya xauna, yace "shatu ta dokeki ne halan," ta tabe baki bata ce masa komai ba tana harhada icenta, sae da ta gama snn ta juyo tana kallonsa tace "wae don ina son sanin gidanku shine xaka wani ce min it's of no use ko
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 53..... Yau ma
kmr kullum Aneesah ta fita neman itacen girkin
yamma ta hadu da Mudatheer, ta karaso
karkashin bishiyar da yake ta xauna tana kallonsa
tace "to baka fa gaya min gidan wa kke ba a nn
kauyen" ya dago yana kallonta yace "ina yini?"
tayi dariya tace "au na manta ina yini?" bae ce
komai ba sae murmushin da yyi, snn yace
"gidansu sanusi da lado nake ai kin sansu?" tace
"lah wa inan kaxaman masu xaman kashe wando
sae ji da kan karya, ko gona bnga suna xuwa ba"
mudatheer yyi dariya yace "xasu maki duka kuwa
idan suka ji ki" ta hararesa tace "tunda 'yar su
ce ni ba, wae in tambayeka meysa su garbebe ke
jin tsoranka toh?" nn ma yyi dariya yace "sbda
mun taba gwada karfi dasu na raunata su gaba
daya, daga nn suka gane ni wanene, kuma na
samu kwanciyar hankali daga lkcn a kauyen."
Aneesah ta dinga dariya har da buga kafa, yyi
murmushi yace "yau ma sae shatu ta biyo ki koh,
wae ma meye hadinki da mugayen mutanen nn
marasu hali?" Aneesah tayi shiru bata ce komai
ba, can ta mike tace "ni xan je neman woods na
girki bye bye," ya mike da sauri yace "to bara na
rakaki inda xaki samu woods da yawa," tace "to
muje," ya shiga gaba tana biye da shi a baya. Da
daddaren ranan tana dandali tana sayar da gyada
wata 'yar makwabciyarsu shafa ta xo da gudu
kiranta, wae shatu tace ta maxa ta dawo gida ko
bata sayar da gyadan duka ba, Aneesah tayi ma
kawarta karime dake saida xobo sallama snn ta
dauki bokitin gyadar ta ta bar dandalin don
abokinta mudatheer ma bae xo ba, tana isa gida
taga wata tsohuwar mota da ta gama shan
wahalar duniya tana neman freedom a fake a
kofar gida, ta bi ta gefen motar ta shiga gidan,
shatu ta gani xaune kan 'yar kujera, kan tabarma
kuwa wani tsoho ne dake ta washe baki, gaban
Aneesah yyi mugun faduwa ta dake ta karaso
dan tsakar gidan da sallamarta snn ta shige
bukkarsu, shatu na wagale baki tace "sannu da
dawowa lu'u lu'u, in kin ajiye bokin ki fito ga
malam tanko ku gaisa," Aneesah tayi kmr bata ji
ta ba ta sulale kasa a hankali cike da tausayin
kanta taji kmr ta fasa ihu, shatu ce ta shigo
dakin da kanta tana ganin Aneesah a wnn hali ta
hade rai, tace "ke ni fa ban son iskanci da rainin
hankali, kina ji ina kiranki xaki yi bnxa dani ga
bawan Allah can ya xo tun daxu yana jiranki, an
gaya maki yana xuwa gun 'yan mata ne da sunan
xance, wllh sae dae su suje gidansa su same shi,
don mun samu ya tuko santaleliyar motarsa har
nn shine xaki masa walakanci, maxa shafa jan
baki da hoda ki fito yana jiranki," Aneesah ta
mike tsaye da kyar tana kkrin mayar da hawayen
da ya cika idonta, shatu na kallonta tayi duk
yanda ta ce mata, snn ta sa ta yafa wani dan
guntun mayafi, xata fita shatu ta jawo ta da
sauri, ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace
"ki tausaya min Aneesah idan muka rasa wnn
daman mun shiga uku hka xamu ta tsaya wa a
talauce har mu mutu, don Allah ki ba sa hadin
kai, duk me yace maki kiyi, kinga ko sati biyu
baxa a yi ba xa a daura auren ku, idan ma baki
son xama wnn kauyen ne sbda 'yan sa ido kawae
sae ki koma kauyen dake gaba da wnn yana da
gida a can aka ce wae, ki rufa min asiri kar ki sa
a mana dariya don ixuwa ynxu lbri ya gama
baxuwa wae malam tanko na birni xae aure
Aneesah, kar ki bani kunya don Allah," tunda
shatu ta fara xancen ta kan Aneesah a kasa
yake tana kukan xuci, har shatu ta sallameta
tace maxa taje yana jiranta, ta fita jikinta a
sanyaye ashe har ya fita kofar gida yana jiranta,
tana karaso wa kuwa ya washe hakora yana
murmushi yace "yauwa 'yan mata sannu da
fitowa," ita dae bata ce kmai ba ta tsaya kanta a
kasa, yace "to mu shiga cikin mota muyi hiran
mana amaryata," ta dago cike da tsana tana
kallonsa tace "A'a nn ma ya isa," yace "haba
amaryata ae yawa ne a gan mu tsaye kmr yara a
nn, ke dae shiga kawae,"ya bude motar yana
kallonta, Aneesah tayi murmushin takaice tace
"ni fa baxan shiga wnn motar ba malam," ya
tsaya kallonta na kusan minti biyar snn ya bude
motarsa ya shige ya ja ta yyi gaba, ta tabe baki
a xuciyarta tace Alhmdllh ta shiga gida abinta,
shatu na tsaye a bukkarta sae kai komo take ta
kasa xaune ta kasa tsaye, Aneesah na shigowa
ta riko hannayenta da sauri har wani bari jikinta
yake tace "har ya tafi, nawa ya baki," Aneesah ta
dan koma baya tace "wae fa mama sae na shiga
motar da kila ko fitila ma bbu, ni ko nace masa
baxan shiga ba shine ya wuce," shatu ta xaro
kwala kwalan idonta ta daura hannu a ka ta
kwala ihu tace "shiknn ta ja mana, Na shiga uku
ni shatu don ubanki koransa kika yi sbda kin
isa?? Na banu na lalace," Aneesah ta tsorata
sosae da yanayin da shatu ta shiga, ta dinga
komawa baya, cikin tsawa shatu tace "xo nn don
ubanki shegiya mugu,"
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 54..... Aneesah ta fasa ihu ta durkushe wajen ganin shatu ta yo kanta, duka kam ta sha shi ranar don shatu komawa tayi kmr wata mahaukaciya, daga karshe ta saba gyale wae xata bi sa gida ta ba shi hkuri duk a rude take, Aneesah dae na durkushe tsakar dakin tana kuka, har shatu ta fita ta dawo kmr an hankadota cikin fushi tace "kuma maxa ki dauki bokitin gyadata ki koma dandali ki tabbatar kin sayar min gaba daya idan ko ba hka ba kar ki kuskura ki dawo min gida, shegiya kawae mugu 'yar bakin ciki," tana kai wa nn ta fice. Aneesah ta kife kanta a kasa tana kuka mai ban tausayi Amminta kawae take tunawa, da kyar ta lallaba ta mike ta dauki bokitin gyadar ta fita daga gidan, a hanya suka hadu da mudatheer ya kirata da kmr baxa ta je ba, har tayi gaba ta dawo, yace "shatu ta doke ki knn," tayi shiru bata ce komai ba tana goge hawayen fuskarta, ya nuna mata benchi ta xauna, bata yi musu ba ta xauna, yace "dandali xaki" ta gyada masa kai, yace "meyasa tun tuni baki je ba sae ynxu, gashi har kusan ten, ae an kusa tashi ma," bata ce masa kmai ba, yyi murmushi yace "me kika yi ta doke ki?" xata yi magana ta fashe da kuka, yyi shiru yana kallonta har tayi mai isar ta, snn ya sake tambayarta me tayi, ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya masa, yyi dariya xae yi magana, ta mike a fusace xata bar wajen ya riko hannunta da sauri yace "Haba 'yar birni ni malam tanko ne ya ban dariya," tayi tsaki ta dawo ta xauna, yace "to wae baki gaya min hadinki da su shatu ba har ynxu" tayi shiru, yace "yau ma baxa ki gaya min ba knn" tace "sbda me kke son sani?" yace "i just want 2 knw a bit about yhu, kinga i may b leavin in 3dayz tym" ta wara ido tace "wucewa xaka yi?" yace "yes, na gama abinda ya kawo ni," Aneesah tayi shiru duk sai ta ji ba ddi, xata yi magana sae ga Zano da kawayenta sun dawo daga dandali, tana ganinta ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "na shiga uku mudatheer xata gaya ma mama, kuma ban ma gama saida gyadar ba, ya ce nawa ne gaba daya, tace "dari uku ne ina ga," ya ciro dari biyar ya mika mata tace "aa ni ka rike kudin ka kawae," ya harareta yace "xaki koma ki kara shan wani dukan kuwa," ta karba tana kallonsa, tace "to gyadar fa?" ya ce "ki koma gida da shi, sae kice su garba ne suka baki kudin xata ji ddi tunda mayyar kudi ce," Aneesah tace "to bbu canji," yace "eh ki kai mata hka," tayi masa gdya ta mike jikinta a sanyaye ta kama hanyar gida, tana tunanin shawarar da karime ta bata ranan bayan ta bata lbrinta tun daga farko har ixuwa ranar da baffa ya kawota kauyen, karime tace ta gudu kawae amma ta kasa gudu wa daga kauyen kuma ta rasa dalili, kwata kwata bata sha'awar barin kauyen ita kam ta rasa meyasa, don wani lkcn ko tunanin gida bata son yi, a hka ta isa gida gabanta na faduwa a xuciyarta tana cewa "Allah yasa Zano bata gaya ma shatu ta gan ta da mudatheer ba, amma sae ta samu ma bata karaso gida ba, shatu na ganin dari biyar ta rikice ta dinga sa ma Aneesah Albarka ba tare da damu da inda ta samo ba ma. Washegarin ranar sae ga malam tanko ya xo da daddare, shatu ta lallabata ta fita, bata yi masa musu ba ta shiga rubabbiyar motar tasa, sae washe hakora yake yace "amaryata muje gun sule mai suya in dan siya maki nama," ta girgixa kai tace "bana ci," yyi dariya snn yace "to muje in xaga dake kauyen ko ya kika ga," gabanta ya dinga faduwa ga tsoran shatu, ba tare da ta sake wani tunani ba tace "toh," yyi murmushi yace "yauwa Amaryata, snn ya tada motar, ya ja ta," shatu na leke ta katanga, tana ganin hka ta sauke ajiyar xuciya ta daga hannu sama tace Alhmdllh bata tona min asiri ba, 'yar albarka.
[12/8, 21:11] +234 803 751 8717: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 55..... Aneesah dae bata tanka ma malam tanko dake ta sharara mata surutu a motar ba, hasalima kauda kanta tayi tana kallon glass din motar, ita duk kyankyamin motar ma ta isheta, yace "Haba amaryata ya hka ina ta magana kin min shiru," nn ma bata tanka sa ba, har suka isa gun sule mai nama, ya siya naman dari da hamsin ya bi ta shagon lado ya siya pure water leda biyu snn ya dawo ya shiga motar rike da naman da ruwan ya mika ma Aneesah yana washe rubabbun hakoransa, tayi kmr bata san yana mika mata ba, ya ajiye gefenta yace "sannu amaryata," ko kallnsa bata yi ba har ya ja motar suka bar wajen, taga yyi parkin wajajen gonannakin mutane, ko ina duhu sae dan hasken wata, ya kamo hannunta yace "amaryata ci nama," ta fixge hannunta gabanta na faduwa tace "meye hka?" ya dan hade rae yace "nama nace kici," a fusace tace "ban ci, ka ci kayanka nace mka yunwa nke ji ne" tana fadin hka ya fixge dan mayafin dake kanta yace "ke kar fa ki kawo min raini, kin san ko ni wanene," ta fara kkrin bude motar xata fita ya fixgota yace "ina xaki," ta hankadesa da sauri tace "to motar ta ubana ne da baxan fita ba," yace "ae baki isa ba yarinya sae kin biya min bukatata yau, cikin kwanaki uku na kashe maku fiye da dubu daya, hakosu nace ina yi a rami" ta yo waje da ido a tsorace ta fara kkrin bude motar ya rikota yana kkrin yaga rigar jikinta tace "nashiga uku, meye hka, malam ka rabu dani ni ba 'yar iska bace," yace "ae nima din ba dan iskan bne, kudina da kuka ci xan amsa ta nn," bae ko damu da haukan da take yi ba ya matse ta yana kiciniyar cire mata kayan jikinta, ta fasa ihu, amma bbu mai jinta dan gurin kmr daji yake, ta wanka masa wani lafiyayyan mari tare da basa wani naushi a ido da karfinta, ba shiri ya saketa bayan ya saki 'yar karar axaba, hannunta na rawa ta shiga bude motar ya budu xata fita ya fixgota ta yakushi fuskarsa ta fice a guje, ko dankwali bbu a kanta, gudu kawae take a tsorace tana bin hanyoyin da ta san xae sada ta da gida, garbebe da lado ta hadu da a wani corner suna ta tuntsirar dariya suna lbrin irin bata wata yarinya hajjo da suka yi jiya da daddare, tana ganinsu ta juya da sauri ta canxa hanya, ji tayi lado na cewa kae garu ga 'yar birnin nn ita ce, suka ko bita a guje, ita ma gudun take kmr xata tashi sama, cikin ciyawa ta labe jikinta na rawa har suka wuce ta da gudu, gabanta ya dinga faduwa ga tsoran kar maciji ya sareta a wajen, ta kai kusan minti goma a cikin ciyawar gudun kar ta yi gaba su hadu kuma, daga karshe wata hanyar ta canxa kuma, ta dinga gudu tana waige waige tana kuka kide kide ta dinga ji daga nesa alamar ta kusa dandali, ta tuna mudatheer yace ta xo dandali xae nuna mata abu, bata bi ta dandalin ma ba don bata san ko sun yi can ba ta sake canxa hanya tana dan tafiya da sauri da sauri tana waige waige, ji tayi ta ci karo da wani katon dutse ta fasa ihu tayi kasa xata fadi taji an yi saurin rikota su ka fadi a tare duk da bata wani buge ba dan kan wanda ya kamota ta fada sae da ta fashe da kuka, taga ya ciro wayarsa da sauri yana kkrin haska fuskarta yace "Goddam Yhu baki kalln gabanki ne kina..." yana haska fuskarta da wayarsa taji ya dan koma baya da sauri yyi tsit, ita ma shirun tayi tana ta kallon fuskar dake gaban screen din wayar, ganin ya ki daina haska ta ne yasa ta fixge wayar daga hannunsa ta shiga haska fuskarsa ita ma, wani kyakkyawan handsome guy idonta yyi tozali da, ta tsura ma manyan fararen idanunsa nata idon, ta saukar da kallonta kan pink lips dinsa dake ta kyalli, wayyo ya Haydar dinta exactly, fixge wayar yyi daga hannunta ita ma, ya tura ta ya mike tsaye yace "kina tafiya kmr wata mara saiti dubi yanda kika min da jikina," bata ce komae ba ta fara tafiya a sanyaye ya fixgota yace "cnt yhu thank me, da na barki da kin fasa kai yarinya," ta fixge hannunta ya sake fixgota ya ja ta suka xauna kan dakalin da yake a xaune, yace "amma fa ke kyakkyawa ce, wait ko ma dae kece mudatheer yace na xo na gani a wancan gurin haukan naku?" ya fadi hkn yana nuna mata dandali, tace "lah kasan Mudatheer ne?" ya gyada mata kai yace "yea sch son dina ne muna sec sch, nn yake service ae, amma gobe xai gama shine yace na xo naga yanda kauye yake tunda ina garin," ke kuma naga baki yi kalan 'yan kauye ba, hw come kike kauye, ko dae hutu kika xo kema, ya sunanki, me ma yake sa ki gudu da daren nn, baki tsoro baki