Showing 27001 words to 30000 words out of 83480 words

Chapter 10 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

975

amana sosai a can madafar kuma na fada mata sakon ki,ta amince zata rinka saka maganin acikin abinci gimbiya khadija.
surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa tace,aikin ki yana kyau umayma...

*************
"Khadija ta kalli rabi bayan fitar zainaba tace daga dakin,yadai kin ganta kuwa?
rabi ta fito da layar data kunshe acikin zaninta ta mika mata,khadija tayi saurin amsa tana fadin, ki kiyaye bakin ki!bana son jin sirrina yana yawo acikin wannan masarautar  kin gane?
Rabi ta gyada kai,khadija tace yauwa muje na koma sashena...

********************
Bayan sati daya...

   "A cikin yan kwanakin da suka wuce gaba daya jalal bai zauna ba,
kullum suna cikin fa'da aiki yayi masa yawa sosai,duk irin nemansa da matan sa keyi bai sa ya  kula kowaccen su ba.

   A yau ma dai sun samu dan hutu ne shine ya zo dan gaida mahaifiyar sa..
Gimbiya kilishi na hakimce akan kilisarsa..
Cike da kulawa tace, jalal kaga yarda ka koma kuwa? Ina tunanin lkc yayi da zaka canza bayin dake kula dakai kamar yarda al'adar masarautar  take..

   Jalal yace,ummana kenan,aikine fa kawai yakeyi min yawa,yadan langwabar da kansa ya sake fadin,kin san kuma ban saba da irin wannan aikin ba..

Kilishi ta girgiza kai ,gobe ka shirya dan dama mahaifinka yayi min mgnr da dadewa..
nace masa mu dan baka lkc ka kara hutawa,toh tunda dai na lura kai kullum acikin aikin kake sai nayi tunanin dole ne kawai na fitar da rana da kaina.

Jalal ya gyara zaman sa yana fadin,toh umma zan shirya idan har hakan kike so,kilishi tayi murmushi yauwa dan albarka ..

  Hansai ce ta shigo falon tana fadin,Allah ya kara maka yawan rai yanzun nan baiwar gimbiya khadija  tazo da sako a fada maka..
   Jalal yadan tabe baki,kilishi tace kai wannan yarinya da jaraba take..

Hansai tace, tace a sanar  maka tana son ganinka idan babu damuwa..
Jalal baice komai ba ya mike yana kallon kilishi,umma bari na tafi..

Kilishi taji gaban ta ya fadi,cike da bakin ciki tace,ban gane bari ka tafi ba duka duka yaushe kazo?
Kodan kaji kiran matar ka ne?

Jalal ya murmusa,haba umma ke kinsan danki ai..
Magaji ne na saka a kira min shi tun dazu kuma na tabbata yana jan yana jirana acikin Fa'da..
Kilishi tayi murmushi,toh yi maza kaje ai na dauka rawar jiki kakeyi wa wannan figaggiyar yarinyar.
Jalal na murmushi yayi ficewarsa..

"Khadija ta kalli rabi tace,kin tabbata sakona yakai gareshi?
Rabi tace,wlh a kan kunnena hansai ta fada masa..
Khadija taja tsaki,yanzu a kalla anyi  kusan 5hr amma shiru babu yarima..
Ta kalli rabi,jeki ki dubo min sashen surayya ko yana can..
Rabi tace toh ranki ya dade..

  "Rabi na isa sashen surayya ta shiga tambayar bayin dake waje ko mai martaba yana ciki?
Duk suka tabbatar mata da cewa baya nan kuma ya ma dade bai zo ba..
Ta dawo ta sanar wa khadija duk irin ruhoton data kwaso..
Dariyar farin ciki khadija ta saki dan a yanzu ne ahankalin ta zai samu kwanciya tunda dai ba ita kawai yarima yake sharewa ba...


_"Gaskiya readers ina jin dadin ganin comments dinku ba kadan ba.._
_@RALLYN SAMEENA_
_@MEELANCY #team_ _jalaljuwai_
_Duk naji dadin_ _comments dinku wlh Allah yabar zumunci_

*GODIYA NAKE PHERTY*


Muje zuwa...👇🏽
Team RUMFAR BAYI...

   
[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:             *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 18
Wattpad @afreey101

*************

    "A can cikin gida kuwa, gimbiya kilishi taji shiru shiru babu yarima bai dawo ba gashi har an kusan gama sa lallen..
Fulani diyya ce ta kalli laure tace, jeki ki saka turaki ya fita ya nemo jalal,laure tace toh ranki ya dade sannan ta mike ta tafi.

  Surayya kam tana can gefe da wasu matan cousins dinsu yarima,sai wani murmushin farin ciki takeyi ganin yarda yarima ya tashi yayi tafiyarsa gashi kuma har yanzu bai dawo ba..

   Asiya ce ta kalleta,lallai kuwa surayya na yarda kin gama sace zuciyar yarima..
Karima ta saka dariya,gaskiya ne wannan,tun fa dazu daya fita har yanzu shiru bai dawo ba.
baiwar surayya ce tazo tayi mata rada a kunne,surayya ta kallesu kafin nan tace,ni zan tafi yanzu tunda dai dare ya soma yi kuma banga amfanin zaman mu a nan ba tunda har shima angon ya sallame kanshi ,gaba daya suka saka dariya..

"Turaki ne ya fito waje dan neman sa,sai hango sa yayi ya tunkaro gidan yana ta sakar da wani irin murmushi mai kayatarwa..
Mamaki ne ya kashe shi dan ya dade bai ga yarima yana irin wannan murmushin haka ba..

  Bai gama mamakinsa ba ya hango juwairiya ta bullo daga wajen itama,kuma ga babban mamakinsa itama din silent smile take fitarwa..

    Girgiza kai kawai yayi,dan yasan waye yarima yasan kuma halinsa dan haka  bazai zarge komai ba.
Karasawa yayi ya taro sa,yarima na ganinsa ya hade rai,ya akayi?
Turaki yace,haba yaya tun fa dazu kayi ficewarka gashi har an gama taron ma kai kawai ake jira a tashi.
Yarima yadan ja tsaki,kafin yayi gaba..

***********
Washe gari........

"A yau ne ake bikin daurin auren yarima jalal da kuma khadija,sannan kuma a yau din ne  jama'ar dake kasar daura zasu halarci na'din sarautar sabon sarkin su wato JALALLUDEEN...

"Tun safe masarautar take a cike tab da mutane daga kowane yanki na nigeria dama tsallake, makida sun zo daga kasar nijar sannan mahauta ma sun zo ana ta yankar shanu ana ban'karesu ana ta gashe su..

    RUMFAR BAYI  kanta a cike take,dan kamar yarda al'adar take,duk lkcn da ake wani na'din sarautar sabon sarki toh sarakuna da masu kudi da shuni suna bada kyautar bayi ga masarautar dake bikin, kamar wata kyauta ce ko wani abun bajinta ne hakan.

******************
"UMAYMA"
Surayya ta fada cike da murnar ganin baiwar ta dake mata hidima tun a can gidansu.
budurwa ce yar kimanin shekaru ashirin da haihuwa,bakace sosai amma fa akwai kyawu babu laifi..

Umayma tayi murmushin murnar ganin uwar dakinta bayan rabuwarsu tun lkcn aurenta..
Ranki shi dade nayi farin cikin sake ganin ki..

Surayya tayi dariya nayi kewar ki a kusa dani umayma,dole ne nayi wa yakumbo godiya sosai data turo min dake nan .
Umayma tayi wani irin shu'umin murmushi, sannan ta kalli sauran bayin dake wajen tace,ku bamu waje!

Duk suka fice suna mamakin iko irin umayma sai kace itama din ba baiwar bace kamar su..
   Surayya ta gyara zaman ta tace,da magana a bakin nan naki umaymah,kwararo min su naji...
Umayma ta  matso sosai gaban surayya, ta fito da wani kulli acikin rigarta,ta kwance shi ta fito da wani garin magani..

Ungo wannan gimbiyata ,surayya ta amsa tana juya kullin maganin,menene shi din?

Umayma ta gyara zama tace,yakumbo ta aike ni wajen malam jatau dake can yobe,ya bani wannan maganin na daukar cikine da wuri..

Surayya dadi ya mamaye zuciyarta,tace,da kyau umayma..amma kinsan fa shi yarima ba kullum yake son yin abun ba,gashi har ma yau amaryar sa zata tare kinga idan har ya kwana da ita tana iya samun ciki a daren farkonta..

   Umayma ta gyada kai cikin gansuwa sannan ta mike taje tayiwa surayya ra'da a kunnenta..
Take naga surayya tayi wani shewa tana kyalkyata dariya, gsky naji dadin zuwanki umayma dan aikin ki na kyau!!!...

*************
"Karfe biyu na rana aka daura auren.
sannan karfe hudu na yamma mai martaba yayi murabus daka mulki, a take kuma aka na'da YARIMA JALALLUDEEN  a matsayin SABON SARKIN daura ...

  Shewa da murna mutane suka shiga yi cikin tsananin farin cikin su...
Masu kirari suka soma kwararo shi kamar haka...

"LAFIYA DARZAZA AMALEN SARAKUNA
"LAFIYA BA HAU DA WANI BA SAUKA WANI
"LAFIYA BANGO MADAFAR BAYI..
"LAFIYA TORON GIWA...
"AN GAISHE KA SABON SARKI MAI SABON ZAMANI"

Yarima dake cikin shiga irinta sarakuna yasha nadin sa ga alkyabba ta alfarma yasha,sai kyalli yakeyi yana daukar ido...

Duk wanda ke wajen sai da kyasa sa,magaji na gefensa hakama hamza da turaki sai washe baki sukeyi....
      Karfe shidda na yamma aka fara shirye shiryen tafiya liyafa...

*************
"An kawo amarya khadija sashen gimbiya kilishi,hansai ce ke ta musu hidima dan zainaba na can sashenta tana shiryawa yau rabin ranta Mustapha zai zo shima tare da abbansa wato wamban kano..

Juwairiya ta kalli zainaba data sha gayu kamar a sace ta..
Cike da sha'awa tace,gaskiya yau gimbiyata sai kin rikita Mustapha wannan kyau haka..?ta karashe mgnr tana cike bakinta..

Zainaba ta murmusa cikin tsananin murna tace,Allah ko juwairiya nagode da yabawa sosai..
Juwairiya ta dauko turare daga cikin akwatin karfen zainaba tace,kada ki manta da wannan...
  Zainaba tayi dariya yauwa aminiyar nagode,juwairiya na dariya ta shiga fesa mata turaren a take kamshi ya gauraye dakin..

    Zainaba ta kalli juwairiya,kayan jikinta na nan jiya e yau,tace,haba juwairiya yau fa ya kamata ace kema kin dan canza ko?,kin manta yau fa babbar ranar farin ciki biyu ce a wajen mu, auren ya jalal da khadija da kuma murnar nadin sabon sarkin mu "AMALE" (wato SARKI JALALLUDEEN)

   Juwairiya tayi murmushi,  har ranta take taya shi farin ciki,amma tasan a yanzu yayi mata nisa sosai, ko samun lokacin yi masa wannan murnar ma baza ta samu ba...

  Zainaba ta dauko wasu kaya ta mika mata,amsa nan..
Juwairiya ta kalli kayan,kafin ta amsa,zainaba tace,fulani ce ta saka ayi miki su..bana son gardama kije kema ki shirya yanzu dan ina so muje sashen umma babba wajen khadija..
  Juwairiya tayi godiya sosai,sannan ta fice..

Sashen fulani ta fara zuwa,ta same ta sai hidima takeyi da mutane,da kyal ta samu laure tayi mata iso wajenta tayi mata godiya sosai,kafin ta tafi se data nuna wa laure kayan ta gani itama..

"""Rumfar bayi ta wuce kai tsaye..
Bayi ta iske suna ta hidimar su,wajen du'bu ta fara zuwa ta nuna mata kayanta cike da murna,du'bu ta yaba sosai sannan ta shige dakinsu ta hau shiri...

   Kayane na zamani riga da zani,sai dai rigar ba irin tasu bace mai kai wa har gwiwa,ita wannan karamace sannan tadan kama jikinta kadan.
Madubi ta dauko tana karewa fuskarta kallo...
Ina ma ace zata iya fita a haka ba tare da tabon fuskarta ba...

Ta shafa fuskar tana lumshe ido,fuskar yarima kawai take hangowa acikin zuciyarta ,ta girgiza kanta da sauri,meke damun ki juwairiya? Kin manta waye me wannan fuskar, sarki ne fa!A'kul dinki!
   Tadan ja lumfashi kafin ta maida tabonta,
ta mike tsaye ta sake gyara zaman mayafinta sannan ta fito..

A kofar Rumfar bayi zata fita kenan taci karo da mutum..
Taja da baya tana dago da kanta...
  Ido hudu sukayi da umayma...
Ba'kin ta ne yaso tsorata juwairiya..

Ita kuwa umayma dama ba mai fara'a bace dunkum da ita.
da kallo tabi juwairiya tana kyasa kyaun dirinta,amma konewar fuskarta ne yasa tadan ja tsaki,ai da ace itace me wannan dirin babu abunda zai hanata jan hankalin mazan masarautar nan,hasken fatar juwairiya ya sake daukar hankalinta..

      Juwairiya kuwa ganin yarda umayma ke binta da kallo yasa tace,yi hakuri ban lura bane..
Umayma tadan yi murmushi babu matsala kema baiwa ce a nan din?

Juwairiya tace kwarai kuwa, amma ban taba ganinki ba ko yau kikazo ne kema?
Umayma tace ,eh yau aka kawo ni,ina sashen surayya uwar gidan sarki...

  Juwairiya ta tabe baki a zuciyarta, amma a fili tayi murmushi, ni ina sashen zainaba kanwar sarki kuma diyar sarki..
Murmushi sukayiwa juna kafin juwairiya ta fice abunta..
Umayma kuwa ta daure fuska, wacece wannan?shine tambayar dake cikin zuciyarta..

*****************
"Gimbiya kilishi ta kalli hansai tace,an kai wa khadijan kayan da zata saka?
Hansai tace na kai mata ranki ya dade, jakadiya ce ta shigo tana sanarwa kilishi sakon tsohon sarki Abdul-Jabbar yana neman ta a sashensa.
kilishi tace,gani nan zuwan ina fata shi jalal din ya gama shirin sa ko?jakadiya tace,ai tun dazu Ya kammala shirin sa,kilishi ta murmusa cikin tsantsar farin ciki sannan ta mike ta fice dan amsa kiran mijin ta..

***************
"Taro yayi taro an ware wa amarya da ango (sabon sarki jalal)wajen zamansu,sannan aka tadanarwa iyaye da manyan baki wajen su suma,bayi kam na can daga baya suna leke..

Zainaba tare da juwairiya suka shigo filin,Mustapha ne ya taso yayi saurin taro su yana washe baki..
Juwairiya ta gaishe shi ya amsa a sake yana karewa zainaba kallo..

     Sai da suka karasa wajen zamansu sannan juwairiya ta juya dan komawa wajen bayi yan uwanta ta tsaya itama..

Caraf ta hango shi a zaune cikin kayan alfarma yayi kyau har ya gaji..
Kirjinta ne ya buga ganin surayya da khadija sun saka shi tsakiya..
   Ji tayi kamar kafafunta na rawa,tayi kokarin tafiya taji ta harde da zanin jikinta.....
ta tafi zata fadi sai ji tayi an riko hannunta...
   A tsorace ta dago suka hada ido da Turaki..
Murmushi ya sakar mata...

"Kamar ance ya dago da idanunsa..
Aikuwa can ya hango su hannayensu a sarke da juna,ji yayi zuciyarsa ta fara zafi..

   A take annurin fuskarsa ya dauke..
Surayya ta kallesa tana narke murya,haba sarkina kadan saki rai mana,kai fa a yau kafi kowa murna a duniyar nan.
khadija dake gefe ta tabe baki,lallai dole sai ta san irin zaman da zatayi da waccan matar dan ta lura munafuka ce ta karshe..
Da gefen ido take kallon jalal,fuskar nan a tamke,tadan sauke ajiyar zuciya, ita dai tana son shi a haka...
  
"Kwace hannunta juwairiya tayi tana kasa da kai,nagode ranka shi dade, Turaki yace,babu damuwa sannan ya wuce itama tayi gaba..

Can kusa da rabi ta tsaya,sai ga umayma tazo taja layi kusa da ita,kallonta kawai juwairiya tayi batace komai ba,umayma kuwa murmushi tayi tace,zanso mu zama kawaye idan bazaki damu ba?
Juwairiya tadan yi murmushi tace,ai duk baiwar dake cikin Rumfar bayi yar uwa na dauke ta,umayma ta danyi yake tana ki'tsa wani abu acikin zuciyarta..




Na Afrah bhai
[9/18, 3:19 PM] Aysha Galadima:         *RUMFAR BAYI*
    (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 19
Wattpad  @afreey101

*wannan naki ne didi @Fertyma Zarah*

**********
"An sha shagali sosai har kusan tara na dare kafin taron ya watse..
    Sarki jalal ne ya shiga babban turakar sa (sashen sa) inda aka canzawa tsari daga tsarin na mahaifinsa wato tsohon sarki kenan..

    " Jakadiya ce ta shigo da kuyangi har cikin makeken dakinsa,ta fada musu yarda zasu hada mishi ruwan wanka da sauran hidimarsa,kuyangi biyu ne suka shige cikin dakin suka gyara shi tsab dan kwanar amarya..

A can wajen khadija amarya kuwa,bayan ta dawo daga taro a gajiyenta, gimbiya kilishi ce ta aika mata da hansai da kuma sabowar baiwarta wato rabi, nan hansai ta shiga nunawa rabi yarda zata kula da uwar dakin nata,rabi sai washe baki akeyi tana murnar samun karin girman da tayi..

  An gama shirya khadija tsab cikin kaya na gani na fada.
suna shirin fitane dan zuwa kai ta can turakar sarki jalal sai ga surayya tare da umayma sun shigo cikin sashen..

   Wajen zama rabi ta nuna musu,sannan ta dawo kusa da khadija dake ta jin haushin tsaida su da akayi ta zauna..
   Surayya ce tace, su amarya an sha kamshi,dama nazo ne dan nima na bada tawa gudunmawar tunda dai ban samu lokacin bayar wa ba ko..

  Umayma ce ta ajiye tiren dake hannunta wanda dashi ne suka shigo.
surayya tadan yi murmushi kafin nan ta sake cewa,
wani tsumi ne dama da aka kawo min shi daga kasar Cameroon, nayi amfani dashi kuma na yaba sosai,tunda dai ba karamin rikita sarkina yayi ba a lkcn,ta karashe mgnr cike da kissa..

   Khadija taji wani abu ya tsaya mata a wuya,sarkinta?ya rikice?lallai ma wannan matar..
  Tadan dago kai tana murmushin yake kafin nan tace a takaice ,toh nagode..ta shiga kokarin mikewa..

Umayma ce tayi saurin fadin,ah ah gimbiya khadija ai  kamata yayi ki dan nuna karamci,ta shiga zuba tsumin a kofi..
Surayya ta amsa kofin ta mikawa khadija,kidan sha ko kadan ne na tabbatar miki gobe se kin gode mini..
    Khadija tadan kalli rabi,rabi tayi mana alama da kada tasha,khadija tadan tabe baki..

  Jakadiya ce ta rangwada sallama tana sake nanata musu sarki jalal na jiran amaryar sa..
Khadija data ka'gu sosai data tafi wajen rabin ranta...
cikin sauri da jawar jiki ta amsa kofin ta kafa kai ta shanye shi tass tana nunawa su surayya cikin kofin (irin am done zaku iya tafiya).

Surayya tayi murmushin murna,yauwa ko kefa kinga nima se naji dadi ai,rabi ce ta kamo hannun khadija sukayi gaba abunsu..
Umayma da surayya suka kalli juna suna murmushin mugunta  cike da gamsuwa..

**************
"A wajen Jalal kuwa yayi wankansa ya saka kaya masu saukin gaske,se kamshi yakeyi ..

  Yana zaune a saman darduma ta alfarma yaji sallamar khadija daga can falo..
  Bai motsa daga inda yake  ba har ta shigo dakin cike da yangarta ta sauke idanunta akan sa..
Wani irin kyau da kwarjini yayi mata har bata san lkcn da ta saki murmushi ba tana wani kafe shi da ido..

  'Idan kin gama karemin kallon se kije ki kwanta"

  Khadija tadan waro ido kunya duk ta lullube ta.
  Jalal ya mike cike da kasaitarsa ya juya mata baya..sai ji kawai yayi an rungumo shi ta bayan..

Khadija ta kwantar da kanta a bayansa tana fadin..
"Haba ya jalal meyasa kake bawa zuciyata wahala ne?kasan fa yarda na damu dakai tun muna yara...amma se ka ringa wani share ni..ta karashe mgnr a shagwabe..

Yarima yaji jikinsa yayi sanyi,idan har yace bai san khadija ta mutu a kansa ba toh karya yakeyi wa kansa..

    Lumfashi yaja sannan ya kamo  hannunta ya maido da ita gabansa yana kallon fuskarta har kwalla sun fara cikowa a cikin idanunta..

   "Meyasa kike Sona?
Khadija tayi saurin kallonsa,dama ya san tana sonsa kenan?
Meyasa?
Ya sake maimaita tambayar..
Khadija ta shagwabe fuska,nima ban sani ba ai,kawai dai komai naka wlh burgeni yakeyi tun bansan cewa sonka nake ba har na girma na fahimci hakan..

Yarima yaja lumfashi,sannan a cikin zuciyarsa yake ganin wautar tambayar da yayi mata,juwairiya ce ta fado masa a rai,meyasa ya damu ita sosai?shima dai kamar yarda khadija ta fada,bai sani ba..

    Jin khadija a jikinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunaninsa..
Rungume sa tayi tsam...
A take yaji wani irin yanayi a gaba daya jikinsa..
Ya lumshe ido ya bude su ahankali ,kafin ya dauke ta cak ya ajiye a kan gadon dake gabansa..

**************
"Juye juye kawai takeyi a kan taburma,ta rasa meke damunta, duk yarda taso tunanin jalal ya fita daga cikin kwakwal'warta kasawa tayi..

Mikewa tayi zaune tana kallon gefen da ummanta take a kwance,sai sharar barcinta takeyi..
   Fita tayi daga cikin dakin dan zuwa ta dauro alwala...tayi nafila ko zata samu nutsuwa.

   Motsi taji daga can cikin madafa,mamaki ne ya kamata dan kuwa duk mutanen dake cikin rumfar bayi a wannan lkcn sunyi barci..
   A dan tsorace ta karasa kofar madafar tana leke..

   Ba'kin ta kawai yasa ta gane wacece a wajen ,duk da kuwa babu wani isasshen haske a wajen..
Umayma ta furta a hankali me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login