Showing 6001 words to 9000 words out of 83480 words
gaban juwairiya, laure ta taso dan ita kam gwana ce sosai wajen harkar kwalliya nan duk masarautar ita tayi fice wajen yiwa matan sarki kwalliya ta fitar kunya..
Wasu abubuwa naga ta hada sannan ta riko kyakkyawar fuskar juwairiya ..
Cikin minti goma ta kammala sannan ta kalli hansai tace,ya kuka gani?
Bude baki sukayi duka dan kuwa duk wanda zai kalli fuskar juwairiya sai yayi tunanin konewa ba'rin fuskarta tayi..
Murmushi sukayi cike da farin ciki,jakadiya ta miko mata wasu kaya ta amsa tana kallonsu,kayane manya manya dan se a saka irin ta biyu a ciki,yanzu wannan sune suturunki kinaji?,juwairiya ta gyada kai.
**************
'Da asuba kuwa sai ga fadawa uku sun shigo Rumfar bayi,du'bu ce tayi saurin tare su..
Lafiya?
Fadane daya ne yace,daga gidan GALADIMA muke,yaronsa GARBATI yaga wata baiwa acikin rumfar nan jiya shine ya turo mu mu tafi da ita..
Gaba daya hankalinsu du'bu ya tashi dan sun fahimci garbati ya siya talatune a matsayin SA'DAKAr sa (concubine)..
Dakin da talatu ke ciki du'bu ta shiga ta fito da ita tana kuka sosai,fadawa suka fosgota suka gaba da ita..
'Juwairiya dake rakube duk tana kula da abunda yake faruwa,
'hansai ce ta kamota ta maida ita cikin daki,
'sannan ta sake yi mata nasiha akan kada ta sake a san tabon fuskarta na karyane inba haka ba itama haka za'a zo a tafi da ita kamar yarda aka dauke talatu..
gari na yin haske haka laure ta shigo ta sake yi mata makeup din tabon ta.
Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita tana ta sharar baccinta.
Ruwan wankanta ta shiga ta hado mata sannan ta zauna a gefe ta tsunduma a cikin tunani..
Zainaba ce ta mike taci karo da fuskar juwairiya, da sauri ta dauke kanta tace,ke meya samu fuskarki haka?konewa kikayi?
Juwairiya ta mike da sauri tace Allah ya huci zuciyar ki ranki shi dade jiya ne ruwan zafi ya kifar min a fuskata.
Zainaba tayi fuskar tausayi Allahu akbar yanzu haka fuskar ki zata zauna kenan?ta yamutsa fuska
Juwairiya tayi murmushi kawai sannan ta sanar mata data hada mata ruwan wankanta..
'Da rana zainaba tace da ita suje gidan waziri..
Fafade daya suka dauka dan yayi musu rakiya..
Duk inda suka bi sai mutane su shiga nuna juwairiya dake bayan zainaba'
A haka har suka shiga gidan waziri..
Hajara matarsa ce a zaune tsakar gidan sai diyarta KHADIJA dake gefe tana wasan diyar ka'ra..
'Zainaba na shigowa khadija ta mike da sauri tazo ta rungume ta..
Idonta ne yakai juwairiya dake can baya..
Taja baya kadan tana yastine fuska..
Wannan fa?ta nuna juwairiya..
Zainaba tayi murmushi sabowar baiwata ce..
Khadija tace,au ni tsoro ma ta bani wlh..
Zainaba tace konewa tayi fa,sannan ta karasa wajen hajara ta gaishe ta.
Suna zaune suna wasan su juwairiya na rakube a gefe tayi shiru abunta.
Khadija tayi fari da ido tace,wai ina ya jalal ne?kinsan tun ranar dana zo wajen ki rannan ban sake ganinsa ba..
Zainaba ta tabe baki ai ke ya da'ma ni muna gida daya ma se mufi sati bamu hadu dashi ba..
Sunyi fira sai da yamma sannan khadija ta shirya suka taho tare wai ita a dole sai taga yarima yau..
"Suna shiga cikin masarautar can a filin wasa doki ta kyallo shi a tsaye tare da wasu samari sa'annin shi..
Khadija ta kalli zainaba tana washe baki,lah kin ga ma yayan can ashe..
Kafin zainaba ta amsa mata tuni ta ka'ra gaba cikin saurinta,zainaba ta girgiza kai lallai bata san wane irin so khadija kewa ya jalal ba duk da wulakancin da yakeyi mata ita bata ko gani.
'Zainaba na cikin wannan tunanin ne khadija ta dawo da saurinta.
Zainaba tace,ah ah ya na ga kin fasa zuwan kuma?
Khadija tadan kwabe fuska ai bazan iya zuwa ni kadai ba kada ya gane dan shi naje wajen..
Ta riko hannun zainaba dan Allah muje ki rakani kinga se nace ki nazo yiwa rakiya muka ratsa ta wajen..
Zainaba tace,wa!ni?ah ah wlh ban kije ke kadai abunki..
Juwairiya kuwa dake baya tana jinsu ne kawai,khadija ta hau magiya,dole tasa zainaba amincewa,ta juya tace wa juwairiya mu karasa can juwairiya, kai kawai ta gyada sukayi gaba...
*************
"Yarima gaskiya ni kam kayi min wayo gsky,duk yaushe ka kware a kilisa(wasan doki) haka ne?
Yarima ya murmusa cike da girman kai..zayyi mgn su zainaba suka iso wajen..
Khadija ta yi saurin gaishe shi ko amsawa bayyi ba ya wani dauke kai.
Zainaba ta tabe baki dama tasan haka zai faru ai.
Khadija tace,yaya kwana biyu?
Yarima ya juyo da shirin dizga ta idanunsa suka kai kan fuskar juwairiya...
Ai da sauri ya dauke kai yana fadin..
Menene wancan abun?
Wayace kuzo min da wannan abun?
Da mamaki duk suke kallonshi..
Ya kalli bawan dake gefensa,fitar min da wancan abun!(kice da kyamata)
Ya nuna juwairiya...
Se sannan suka fahimta me yake nufi..
Zainaba ta turo baki,yaya baiwar tawa ce za'a fitar maka?
Ya balla mata harara,bakya ganin fuskarta ne?(in a irritating tune)
Khadija ta fisgo juwairiya ta shiga janta daga wajen..
Se da suka sha wata kwana sannan ta jefar da ita kasa tana fadin.
Kada ki kuskura ki kara tsayawa a gaban yaya kinji na fada miki..ta tayi gaba..
Juwairiya taji wani abu ya tsaya mata a makoshi,tsanar yarima ta dasu a zuciyarta, itace wancan abun?
Kuka ta shiga yi tana tunanin wacce irin rayuwa ce haka suke fuskanta dan kawai su bayi ne se ake kyamatarsu ana zaluntarsu...
Ta mike hade da kakkabe jikinta sannan ta rakube a gefe tana jiran uwar gidan ta zainaba....
***********
A gajiye ta dawo rumfar bayi, fuskar nan babu walwala..
Tana shiga ta hango yan matan bayi nata wasan fado'wa wasu na gefe na langa..
Hansai ta karaso wajenta tana fadin,sannu ya'ta se yanzu?
Ta gyada kai kafin ta karasa daki a sanyeye.
Har taci abinci ta kwanta,taga tunanin wulakancin da yarima yayi mata na neman yi mata yawa a cikin kwakwalwa hakan yasa ta fita waje itama ta shiga wasannin da akeyi abunta...
Wattpad @afreey101
[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )
NA Afrah bhai
Page 6
Wattpad @afreey101
*******************
**bayan shudewar shekaru bakwai**
'Gaba daya masarautar a war'gitse take.
A sanadiyyar bakin dauren auren YARIMA JALAL da diyar sarkin adamawa wato gimbiya SURAYYA da akeyi a ranar ta yau, wato shidda ga watan sa'tumba.
'Mutane ne tan'kam cikin masarautar ko ina ka kai idonka bayi ne keta hidima ana ta shirye shiryen amsar dan'gin amarya dake tafe daga kasar adamawa...
"Can na hango yan wasan doki suna ta kokarin shirya KILISA(wasan doki),A gefe kuwa yan busan algaita ne ke tayi masu kanguna ma nata bugawa take masarautar ta dau sautin ki'da me kayatarwa,yan wasan wuka da yan farauta ma nata nuna tasu bajintar..
*************
'Tun asubahi duk baiwar dake cikin Rumfar bayi bata zauna ba,rabinsu duk suna cikin madafa ne ana ta hada'hadar dahuwar abinci na gani na fada.
dan shanaye sun fi dari da mai martaba yasa aka yanka su banda kuma kaji da wasu kananan dabbobin.
"Hansai ce na hango duk hidima tayi mata yawa.
can sai ga wasu kuyangi sun shigo,wajenta naga sun nufa cikin saurinsu daya daga cikinsu tace,hansai wai ina JUWAIRIYA ne gimbiya zainaba na can nata faman nemanta.. tace idan mun ganta mu sanar mata da cewa su hadu da ita a can sashen gimbiya kilishi...
'Hansai ta girgiza kai...
lallai wannan yarinyar wato bata tashi ba kenan duk dukan da nayi mata da asubahin nan..
Laure ta kwashe da dariya,ai ni kam gara da Allah yasa zainaba ce uwar dakin juwairiya da ina fada miki tuni yarinyar nan zata jawo mana musiba sbd shegen son jikinta..
Jakadiya tace,haba kun manta aikin data sha ne jiya daddare duk fa itace ta ba're wancan danyen waken.
jakadiya ta sake kallon laure dake faman wanke wanke tace,ke laure tashi kije ki sanar mata sakon uwar dakin tata ..
'Lkcn da laure ta shiga dakin juwairiya ta hango kwance akan taburmar ka'ba tayi dai'dai tana ta kwasar barcinta hankali kwance dan shaf ta manta da wani daurin aure da akeyi a cikin masarautar..
Laure ta shiga tashin ta..juwairiya maza ki tashi...!
A firgice ta farka tana gogar idanunta dake cike da barci..
Ni kuwa afrah na saki baki ina kallon kyakkyawar fuskarta,laure tace,se ki tashi dan yanzun nan uwar dakin ki tayi aiko a sanar miki daki same ta a sashen gimbiya kilishi...
Ai tun kafin laure ta rufe baki juwairiya ta mike da sauri ta zari gyelen ta tayi waje da gudu duk kiran da laure keyi mata bai sa ta tsaya ba .....
Gudu takeyi sosai dan shaf ta manta da maganar da sukayi jiya ita da zainaba..
Yau ta shiga uku!
Me ya same ni haka ne?
Wane irin bacci ne nayi haka!oh Allah!
'Abun mamaki tana zuwa sashen gimbiya kilishi ta tarar da sashen wayam babu kowa a wajen duk kuwa da cikar da masarautar tayi a yau..
Ta karasa ciki tana kalle'kalle ko zata ga zainaba tunda tace kayan biki zasu zo amsa a wajen gimbiya kilishin...
'tana faman leke'leke kawai taJi kamar wani ana kokarin shigowa..
Tsoro ne ya kama ta sosai dan kuwa tasan idan har aka kamata a ciki ba tare da zainaba ba kuma babu kowa acikin sashen toh kashin ta ya bushe...
Bayan wani lalube ta boye jikinta na tsananin rawa..se addu'a takeyi Allah yasa ba gimbiya kilishi bace ta shigo ita tsoron matar takeyi..
bata ankara ba sai Jin takon mutum tayi kawai..
Bugun zuciyarta ne ya linku...
Ta dafe kirjinta...ganin inuwar mutum a gabanta yasa ta runtse idonta gam dan ta sadakar da an gama kama ta....
Shi kuwa yarima jalal mamaki ne yakeyi ganin inuwar mutum a cikin labule dan kuwa ummansa ta shaida masa data kori kowa daga sashen na ta dan kawai yaje yayi shirin sa tunda nashi sashen cike yake da ya'yan sarakuna abokansa da sukazo dan daurin aure...
Bai bata lkc ba ya yaye labulen cikin zafin nama....
Idanuwansa ne sukaci karo da wata kyakkyawar fuska mai daukar hankali...
Gabansa ne yaji ya fadi..haka kuma yaji gaba daya tunaninsa ya tsaya tsak..jinin dake jikinsa ma ya gaskare waje daya haka gangar jikinsa..
Juwairiya kuwa ganin an yaye labulen sai ta bude idanuwanta da suka fara cikowa da kwalla..
Ganin yarima jalal a gabanta sai ta dafe kirjinta.....
Abunda ya bata mamaki shine ganin bashi da niyyar hukunta ta sai ma wani kallonta da yakeyi..
Hakan ne Yasa tayi saurin zubewa a kasa dan ta sadakar yau ta'ta ta ka're....
Yarima kuwa baisan lkcn da yabi ta kasan ba shima,yana mata wani irin kallo data kasa gane na menene shi..
Can tabi kwayar idonsa ta fahimci fuskar ta yake yiwa wannan kallon..
Ai da sauri ta ware idonta tana saka hannayenta ta shafi fuskar ta..
Taji ta fayau,yau na shiga ukuna!
A Haka na fito?
Banyi tabon ba?
Ta mike ba saurinta jiki na rawa ta gudu tayi waje hankalinta a mutukar tashe....
Shi kuwa yarima sai dai kawai yaga bata wajen dan ya lula cikin tasa duniyar.....
Da sauri ya mike yabi bayanta,amma ina....bai ga ko keyarta ba a wajen...
Ya dafe kirjinsa dake bugawa..
Me ya faru dashi yanzun nan?
Wacece wannan aljanar yarinyar?
Ya lumshe ido yana tuna kyakkyawar fuskarta,kafin ya shige kur'yar dakin mahaifiyar sa yana tube kayansa yana murmushin da shi kansa bai san yanayin shi ba..
Juwairiya kam direct rumfar bayi ta koma cikin saurinta,Allah ya taimaketa duk babu jama'a a wajen suna can madafa, ta shige daki ta zube a kasa tana jin kirjinta nata bugawa..
Idan yarima ya gane ta fa?idan ya gano tabon karya takeyi fa?
Ta dafe kanta sannan cikin kankanin lkc ta maida tabon fuskarta sannan ta sake ficewa..
****************
"Tana shiga sashen zainaba ta zube a kasa tana neman afuwa..
Zainaba data zama cikakkiyar budurwa mai kyau da aji ta saki murmushi, ina tunanin kin manta da yau din bikin ya jalal ne ko..
Juwairiya tayi kasa da kai.. na sa ni ranki shi dade a gafarce ni...
Zainaba ta murmusa babu laifi,tashi muje sashen fulani...
'Koda suka zo shiga lkcn shima Turaki yake karasowa saurayi ne me cike da kamala sam yanayinsa ba kamar na yarima bane dan kuwa kullum shi kam fuskarsa dauke take da fara'a ..
Yana ganinsu ya saki murmushi yace, gimbiya da kawarta,dan haka yake kiransu.
A tare sukayi murmushi kafin juwairiya tayi kasa da kanta ta gaisar dashi.
Ya amsa a sake sannan suka shige ciki a tare..
"Karfe biyar na yamma dangin amarya suka iso daga adamawa..
Gimbiya kilishi tare da mai martaba da fulani ne suka taro su da tarin bayi da yan ki'da...
"Bayan awa daya da aka basu dan hutawa da cin abinci..
Sai aka fito kuma babban fili a inda aka shirya musu babbar liyafa...
Zainaba ta kalli khadija dake ta tabe baki tana yatsina fuska.
'Ke wai har yaushe zakiyi yawo ne,da ajinki ki zauna ana ta miki rashin mutumci..
Khadija ta shagwabe fuska,ai kin san dai ya jalal mijin mace hudu ne ko sannan kowa ma ai ya sani auren hadi ne akayi masa...
Juwairiya ta girgiza kai dan kuwa har ta soma gajiya da surutan khadija kullum bata da abun mgn se ta yarima,ta tabe baki ita kam ko a kafa aka daura mata shi kwancewa zatayi ta yar ta tsani girman kansa da shegen gadara mtsw......
A tare suka mike bayan an aiko musu da sakon cewa za'a fara liyafar.
Khadija ta banka wa juwairiya harara.
Ke ina zaki?
'A hakan zamu tafi dake ki sake tsorata ya jalal din?
Zainaba ta daure fuska,kinga khadija bana son shishshigi,abunda ya faru da dadewa shikenan kin din ga maimaita shi..
Khadija tace haba zainaba,kalli fa shigar ta ki gani ga fuska kuma a kone..
Zainaba tabi juwairiya da kallo,ita bata damu da tabon dake fuskarta ba amma kayan ne ko irin su jakadiya ma da uwar soro da du'bu ai ba saka irin su sukeyi ba..
Zainaba ta koma daki ta fito da wata jar atamfa...
Ta mikawa juwairiya amsa ki canza zuwa wadan nan..
Juwairiya ta ware ido ni?ta nuna kanta..
Khadija tace,da' wa?
idan ba ke ba uhm?
Juwairiya ta amsa a sanyaye sannan ta shiga ta sanyo kayan..
Tana fitowa sukabi ta da kallo...
Duk da dogowar riga ce a jikinta amma sai da shape dinta ya bayyana..
Ita kanta sai datayi mamakin irin dirin ta tunda dai bata taba saka kaya irin wannan ba...
ko kadan bataso ta saka kayan ba amma babu yarda zatayi tunda baza ta iya musawa hakan ba.
Khadija ta tabe baki babu laifi... (nan kuwa kishi takeyi.)
Zainaba kanta sai data tsorata da ganin canzawar da juwairiya tayi amma ta da'ke tace muje...
'Wuri yayi wuri mutane kamar ba gobe..
Su khadija suka zauna a inda aka tanadar domin su..
Juwairiya kuwa ta koma layin yan uwanta bayi sai kalle kalle takeyi kada su ummanta su ganta da wannan shigar...
Wattpad @afreey101
[9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction )
Na Afrah bhai
Page 7
Wattpad @afreey101
******************************
"Ta'ro yayi taro anci an'sha anyi kuma wasanni sosai..
' sai wuraren karfe goma na dare sannan aka tashi,an kai amarya sashen ta dayaji gyara cikin tsari na gargajiya.
'Surayya an sha wanka cikin turare ga turaren jiki kuyangin nayi mata kamshi kam ba'a mgn.
Wata riga ta saka marar nauyi sannan aka daura mata alkyabba mai kyan gaske..
Tana nan a zaune bayinta na ta kara gyara cikin dakin sai ji sukayi ana sanar da shigowar yarima.
Ta kallesu fuskar nan ba a daure tace,ku fita duka!
Jiki na rawa duk suka fice da saurin su..
'Da sauri Ta sake gyara fuskarta tana kokarin rufe fuskarta taji shigowar ango..
'Yarima cikin kasaita ya karasa gaban gadon yana bin'ta da kallo...
ya rasa dalilin daya sa mahaifiyar sa ta matsa masa akan ya amince da auren wannan yarinyar..
'shi dai yasan ko'da ya fara ganinta lkcn da mai martaba ya matsa masa akan yaje zance dan su fahimci junansu kwata kwata batayi masa ba..
Tunawa da wannan kyakkyawar fuskar da ya gani dazu yayi,wacece ita?a ina kuma zai sake ganin ta?
'Surayya dake lullube taji wani irin haushi ya turnike ta,
miye haka zai wani shigo ya zauna shiru kamar ya manta da anyi ajiyar ta..mtsw....
Ni kike wa tsaki...?
Taji an fada da murya me cike da gadara da kasaita..
Ware ido tayi dan kuwa duk a tunaninta a cikin zuciyarta ne tayi tsakin..
Shiru tayi masa tana runtse idonta..
Yarima ya mike tsaye..yace...
'Naga alamar tun ba'a kai ko ina ba kin fara raina ni ko...
'Surayya tayi shiru tana jin haushin kanta data bari har tsakin ta ya fito fili..
Yarima yaja gundun tsaki,sannan yace bana mgn kana shareni kin gane?..
Surayya tace a sanyeye, kayi hakuri..
Ya sake tabe baki,
bude fuskarki...
Ta saka hannu a nutse ta yaye lullubinta...
Yarima dake tsaye agabanta ya kura wa fuskarta ido..
Ko kadan baiji kwatankwacin abunda yaji dazu ba..meyasa?
Yadan ja tsaki..
Ya sunanki ma?
Surayya taji wani irin abu ya tukare mata wuya,mai?miye sunanta?dama bai san sunanta ba kenan?amma ai koda sukaje gidansu ta tabbata yaji sunanta..
'Tadan daurefuska, baka san sunana ba ashe..
Yarima ya shafa sa'jen dake kwance a fuskarsa..
Tambaya kike?ko mamaki kikeyi?
Surayya ta dan murmusa idan nace duka biyun banyi laifi ba..?
Yarima daya so gundura da mgnr yace..
Bana son ana maida min tamabaya ta da wata tamabayar..
Surayya tadan tabe baki,lallai wannan mutumin akwai son mulki..
Sunana SURAYYA...ta fada tana kafe shi da ido..
Yadan gyada kai,toh surayya dan matsa min na kwanta nima yayi mgnr yana karasawa gefen gadon..
'Surayya haushi ne ya kama ta,wane irin daren farkone haka ta matsa mishi? bashi ma da niyyar yin komai ma kenan?ita dai ba haka taji ana fadin daren farkon ba...
tana kallonshi ya rage kayan dake jikinsa yazo ya tsaya yana mata nuni da ido irin ke nake jira dinnan..
'Surayya taja gefe da sauri yarima ya hau ya kwanta yana runtse idonsa..
Duniyar tunani ya tafi,meyasa yake jin hakane?kodan baya son yarinyar ne?yadan bude idonsa,yasan cewa gobe dole ne gimbiya kilishi ta turo a duba mata ko wani abu ya shiga tsakanin sa da surayya tunda haka al'adar take,ya sake runtse ido,baya jin ze iya kwanciya da yarinyar can a yau, tunani kawai yakeyi har barci me dadi ya dauke sa cike da mafarkin wannan kyakkyawar fuskar daya gani..... .
********
'A wajen juwairiya kuwa,bayan taro ya tashi suka taho tare da zainaba,suna tafiya juwairiya taji kamar takon wani a bayansu,ta kalli zainaba a tsorace itama kanta zainaba haka jikinta ya bata,da sauri juwairiya ta jawo zainaba suka boye bayan wata bishiya,zainaba tayi kasa da murya..
Waye yake bin mu?
Juwairiya ta girgiza kai nima ban sani ba ranki ya dade..
Zainaba ta matse hannun juwairiya cikin nata tace..
Yanzu ya zamuyi ? mun shiga