Showing 30001 words to 33000 words out of 83480 words

Chapter 11 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

979

takeyi a wannan lkcn?

Gani tayi umaymar ta juye wani abu daga cikin jug,tasa ruwa da yawan gaske ta wanke jug din tas,sannan tayi murmushi me ma'anoni dayawa...
    Tana kokarin juyowa juwairiya tayi saurin barin wajen,tana tunanin wat is umayma up to?

***********
"Da safe jakadiya ce ta shigo dakin jalal bayan fitarsa.
Can ta hango khadija a kwance jikinta duk yayi tsami ga zazzabi me zafi ya rufe ta..

  Subhanallahi ranki ya dade!
Nan jakadiya ta shiga kiran kuyangi dan su taimaka mata..
Sai da aka kimtsa ta sannan jakadiya tace ko a kai ki sashen gimbiya kilishi ne dan ki dan samu shan magani?
Khadija ta girgiza kai,ah ah sashen fulani zani..
Jakadiya ta kalli rabi tace,taimaka mata kuje..

"Fulani diyya ce da kanta ta shiga kula da khadija,labari kuwa yaje har kunne kilishi, haushin khadija ne ya kamata sosai,wai tana so ta jawo mata raini.

"Juwairiya tare da zainaba ne suka shiga sashen fulani dan ganin jikin khadija kamar yarda lbrn ke ta yawo acikin masarautar.
   A daki suka tarar  da ita kwaryar magani a hannunta sai yatsine fuska take rabi na ta lallashinta tasha..

Zainaba ta zauna a kusa da ita..
Matar sarki jalal na zata ai ke jaruma ce ..
Khadija ta banka mata harara..
Juwairiya kuwa sai faman kallon khadija take tana jin wani abu yana tsirga mata acikin zuciyarta..

Khadija ta ware ido tana dafe kirjinta tace,wayyo Allah na yau na shiga uku?
,zainaba tace me ya faru kuma yanzu sarkin ra'ki?khadija ta matso kadan tayi mata a kunne (akan she forgot her underwears a dakin jalal)
Zainaba tayi kasa da murya,kada ki damu,ai su jakadiya zasu dauke miki komai,khadija ta girgiza kai nidai bana son ne wannan matar tasa taje ta gani na jawa kaina wani sabon rainin a banza..
Khadija ta jawo rabi tana mata rada akunne cikin mgn kasa kasa tace,ki koma sashen ya jalal a dakinsa ki dauko min wata bakar laya dana manta acan,kada ki kuskura wani ya gani!gyada kai rabi tayi sannan ta mike zata fita..
   "Zainaba ce ta kalli gefen da juwairiya take tace,juwairiya kuje tare da rabi sashen ya jalal din....

Khadija ta dan harare ta ki bari rabin taje ita kadai mana?
Zainaba tace,ah ah ai juwairiya tafi ta sanin jakadiya ,khadija ta tabe baki..sannan da ido tayi wa rabi gargadi...
juwairiya kam bama son zuwan take ba dan wani abu take ji yana mata yawo a makoshinta,
Ta kalli rabi tace muje,rabi tace toh sannan tabi bayanta suka fice.

khadija ta dafe kirjinta tana addu'ar Allah yasa jalal bai ga wannan layar data fadi daga jikinta ba jiya ,goggonta ce ta bata ita akan idan ta kwana dashi da wannan layar ajikinta toh tabbas zata samu waje acikin zuciyar jalal,ko innarta ma bata san sunyi wannan sirrin ba..

***********

""Suna shiga makeken sashen na sarki jalal suka tarar da jakadiya tare da wasu kuyangi suna ta hidimar su.

Juwairiya ta karasa wajen jakadiya ta gaishe da ita,jakadiya tace,meya kawo ku nan juwairiya,da fatan dai komai lfy ? kunsan fa baku da ikon shigowa turakar sarki ba tare da wani babban dalili ba..

Rabi ce tace, uwar dakina ce gimbiya khadija ta aiko mu daukar wani sako aciki data manta..
Jakadiya ta jinjina kai,sannan ta kira wata kuyanga tace takai su dakin jalal su duba amma kada su dade..
   
"Tunda suka saka kafa a cikin falon juwairiya ke kallon ikon Allah,lallai an kashe duniya me tarin yawa a wajen nan,wani ado ne na zinari ta hango daya mutukar burke ta sosai..

     Rabi kam da sauri ta shige dakin tana waiwayen juwairiya, can ta hango ta kamar an dasa ta a gaban wannan frame din,ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shige da saurinta ta shiga neman inda zataga layar..

  Ita kam juwairiya tana nan a tsaye babu kowa a cikin falon sai ita kadai dan kuyangar data shigo dasu ma ta fice..
  Wata kofa ta hango a bude iska nata kadata..
   Hakanan take son ganin ina ne wajen shi kuma,tasan dai daga yau bazata taba sake samun damar shigowa nan din ba..
   A hankali ta karasa wajen kofar tana leke.....

      Bude baki tayi da idanu gaba daya cikin tsananin burge ta da wajen yayi tace,mashaAllah....

    "Dan karamin wajen shakatawa ne da aka gyara shi da flowers da fruits iri iri sannan aka saka mishi kujerar lilo,yayi mutukar kayatuwa..
      Sbd yarda ya tafi da zuciyar juwairiya bata ma san lkcn da ta saka kafa ciki ba tana karewa wajen kallo cike da ban sha'awa..

**********
"Sarki jalal ne ya fito daga fada tare da magaji da turaki a gefensa..
Kallon su yayi a gajiyensa yace,ku karasa da sauran cases din kaina ke ciwo zan dan shiga na huta..
   Shamaki da sallama ne suka rufa masa baya suna masa kirari hade da gyara masa babbar rigar jikinsa..

"Rabi ba karamin nema tasha a dakin ba,a can karkashin gado ta hango layar da saurinta ta dauketa ta tura a cikin zani sannan ta fito..
   Ganin babu juwairiya a falon sai tayi tunanin ko har ta tafi ne..


_"'Kuyi hakuri da wannan zuwa anjima inshaAllah_

_RUMFAR BAYI give away,thanks for all d readers that participate in my next post i will ANNOUNCE the 2 winners"_



TEAM RUMFAR BAYI

[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:            *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 21
Wattpad @afreey101

_juma'at mubarak all may Allah forgive us our sins amin_

****************
"Washe gari"

   "Juwairiya na gani a zaune ta buga uban tagumi,yanzu menene mafita a gareta?

Ta shiga kallon yarda bayi ke ta wani rawar jiki  suna gyara jikinsu dan kawai su samu yarima ya zabe su a cikin sababbin masu mishi hidima asashen sa..

    Ita kuwa ya zatayi yanzu?tasan da cewa indai har tana ganin shi a kullum toh zuciyarta bazata taba samun sukuni ba,gashi kuma abun haushin ma yasan konewar fuskarta duk karya ce..

   Laure ce ta dafa kafadarta,a sanyaye ta dago ta kalleta,laure tace taso muje,juwairiya ta mike suka shige cikin dakin jakadiya..

   Hansai ta kalle ta tace, haba yar umma wannan hade rai har haka?
Juwairiya ta turo baki..
Jakadiya tace,ki kwantar da hankalinki juwairiya,na tabbata mai martaba bazai dauke ki ba ma,hansai tace,ni fa mamakin ma wadancan yaran nake da suke ta rawar jiki..

Laure tace ki kyele su duk so suke me martaba ya dauke su ko sunje su samu waje a can kinsan wasu da shegen kwadayin abun duniya suke...

   Jakadiya ta girgiza kai,matsalar dai itace,duk lkcn da sarki ya ga wata baiwa daga cikin su kuma ya kyasa ta har ya kuma kwana da ita toh daga ranar zata zama SA'DAKARSA,wasu ma a haka suke karatar rayuwar su bai sake waiwayen su ba,masu rabon haihuwa kawai ne ba'a mantawa dasu a tarihi,toh wannan rayuwar har wani abun kwadayi ce?

Juwairiya dake sauraren jakadiya taji jikinta duk yayi sanyi ,wato dai ita baiwa ba zata taba samun damar zama mata kamar kowacce mace ba?sai dai amatsayin kwakwara?

      Hayaniyar da sukaji ne daga waje yasa su duk mike duka,laure ta kalli juwairiya,
ki kwantar da hankalinki diyata,wannan tabon na fuskar ki kawai ya isa me martaba yaki zabar ki..
Juwairiya ta jinjina kai tana tausayin iyayen nata,
Wato su a nasu tunanin wannan tabon ne ze taimake ta?lallai da sun san da cewa jalal yasan komai da basu saka rai a kan shi ba..

"Suna fitowa suka tarar da bayi duk an ja layi,
kowaccen su na ta addu'ar samun nasara dan aiki a sashen sarki kamar wani garin girma ne suka samu..
   Du'bu ce tazo taja hannun juwairiya ta kai ta cikin layin itama..
  
****************
"A waje kuwa...

Sarki jalal ne tare dasu shamaki dakuma wasu fadawan ana ta kwararo masa kirari..

"Zaune yake a wata kujerar alfarma ga kuma lema (umbrella) an rike masa yana shan iskan inuwa abunsa..

Fuskarshi a daure tamau sai shan kamshi yakeyi abu ga jinin sarakai...

A haka bayin suka ringa fitowa set by set.
duk wacce tayi masa kalar tsabta sai yayi wa shamaki kwatancen ta a kunne shi kuma shamakin yaje ya sanar wa uwar soro itake zuwa ta dauko su ta kai gefe...

Set dinsu juwairiya ne zasu fita yanzu,gabanta nata faduwa,zuciyarta ta kasu kashi biyu.
Kallo daya zakayi mata ka fahimci a tsorace take sosai ..

   Fitowar ta yayi daidai da saukar da idanuwanta  akan fuskar yarima..
  Ji tayi duk karfin ta yana so ya kare..
Ta dauke kai da sauri taja kafarta taje ta tsaya akan layin.

   Shamaki ne ya dan duka wajen kunnen yarima yace..
Allah ya kara maka yawan rai ga wasu nan sun sake fitowa suma..
   Jalal kamar bayaso ya dago da kansa..

Caraf ya kyallo ta a cikin su..
   Ya lumshe ido ya bude su ahankali,se yanzu ne yake jin dadin wannan selection din.
bai wani bata lkc ba ya sanar ma shamaki wacce yake so acikinsu..
Shamaki ba karamin mamaki yayi ba dan kuwa sai yarima ya dauki kusan minti sha biyar bai zaba ko daya ba, amma ji yanzu ko minti daya bai dauka  ba ya zabo wancan..

Shamaki ya fadawa uwar soro..
Juwairiya kuwa kanta na kasa ta damke hannayenta..
Ji tayi kawai an dafa ta..
Ta dago a tsorace tana kallon uwar soro..
Uwar soron ta gyada mata kai,kware  kuwa yarinya mai martaba ke ya zaba a duk cikin wannan layin!
Dum dum dum kake ji kirjin juwairiya nata bugawa..

Tadan kallo sa kasa'kasa...
taga yarda ya wani hade rai,tadan ja tsaki a cikin zuciyarta toh me yasa zai zabe ta?
ji yarda ya wani dauke fuskarsa...wata zuciyar kuma dadi takeji dan zata ringa samun ganin sa a kullum..
   Cikin rumfar bayi ta koma,ta tarar da lbr har yaje kunnensu hansai,rungume ta kawai sukayi suka fada cikin daki..

****************
"Umayma ce na gani  a zaune tana lillasafo wa surayya bayin da yarima duk ya zaba jiyan..
Tana kaiwa kan juwairiya surayya tayi saurin mikewa daga kwancen da take..
"Kina nufin harda wannan yarinyar me konannar fuskar?

Umayma tace kin san tane ranki ya dade?
Surayya taja tsaki,dole ne kuwa mu saka ido a cikin sashen sarki..

umayma kin gane,inaso ki samo min baiwa da zamu aminta da ita kina jina?
Umayma tace an gama ranki shi dade..

******************
"Da safe jakadiya da kanta ta kawo wa juwairiya kayan da ringa kasawa (kamar matsayin uniform kenan)
  Sai da ta gama shiryawa sannan suka fito dan tafiya..

  Juwairiya ta kalli jakadiya,kiyi gaba inna bari na dan shiga wajen zainaba ,jakadiya tace,toh amma kiyi sauri dai,juwairiya tayi murmushi sannan da gudu tayi gaba..

"Tun kafin ta idasa shiga sashen take jin ihun zainaba, hankalinta a tashe ta shige  da saurinta...

   "Laure ta iske a tsaye tare da zabba'u a gefenta ,zainaba sai zazzaga masifa takeyi..

Ni wlh babu wata baiwa da za'a canza min,ni juwairiya nake so!
Laure kamar ta fashe da kuka tace,Allah ya huci zuciyar ki,jiya fa mai martaba da kansa ya zabe ta a matsayin sabowar baiwarsa,dole ne kiyi hakuri a canza miki da wata..

Zainaba zatayi mgn juwairiya tayi saurin karasa wajenta..
Dan Allah ranki shi dade kiyi hakuri..
Zainaba ta damko hannunta muje wajen fulani dolene ya jalal ya barmin ke...

"Haka zainaba tayi ta jan juwairiya har sashen fulani diyya..
Turaki da fulani na zaune suna gaisawa sai ganin su kawai sukeyi kamar daga sama.

Zainaba ta fashe da kuka tana fadin..
Ni dai wlh fulani kije ki fadawa abba ya jalal ya barmin baiwa ta bazan bawa kowa ita ba!
Fulani ta mike tana fadin,haba zainaba kinsan fa a yanzu jalal shine mai wuka da nama acikin masarautar nan..

Zainaba ta kalli turaki dake ta kallonsu yana jin abun wani banbara kwai,me yasa ya jalal zai dauke juwairiya? Haka nan yaji wani irin abu a cikin zuciyarsa...

   Ya turaki dan Allah muje ka tayani rokonsa?
Turaki ya mike a sanyaye,ki yi hakuri zainaba kinji?
Zainaba ta kalli juwairiya dake gefenta tana yan hawayen rabuwa da uwar dakin tata.
Allah ya gani ba karamin shakuwa tayi da ita ba..

   Naji zan bar masa ita...amma da sharadi idan har ita ce ta amince zata zauna acan din..
Juwairiya taji gabanta ya fadi..
Fulani tace wane irin sakarci ne haka?

Zainaba bata tanka ta ba ta sake jan juwairiya suka fice turaki na bayansu yana faman kwalawa zainaba kira..

"A sashen sarki jalal taja burki,jakadiya ta fito da sauri ta tare su,zainaba tace,jakadiya ina ya jalal?inason ganinsa dan Allah..

Jakadiya zatayi mgn sai ga yarima ya fito cikin shigar alfarma se baza kamshi yakeyi..khadija ce a gefensa tana wani yanga sai faman gyara masa alkyabbar jikinsa takeyi..
     Zainaba ce ta karasa gabansa tana kuka..

  Jalal ya tsaya yana kallonta da mamaki..
Cikin muryar tausayi tace,dan Allah ya jalal kabar min baiwata ta nuna gefen da juwairiya take..
Sai a lkcn ya lura da juwairiya dake gefen zainaba tana goge hawayen ta..

   Ji yayi zuciyarsa ta buga,ya sake kallon zainaba yace cike da kasaita,sarki baya mgn biyu kanwata..

Zainaba tace,nidai yaya bazan iya bar maka ita ba sai dai idan itace tace min zata iya zama a nan din..
Khadija dake faman hararar juwairiya tace,ya jalal kawai ka bar mata ita mana me zakayi da wannan me konannar fuskar..

Har cikin ransa yaji kalamanta..
    Zainaba ta kalli juwairiya, ki fada min gsky na barki a nan kinaso?zaki iya rayuwa a inda ake kyamatarki?
   Juwairiya gabanta ya hau faduwa zuciyarta ta kasu kashi biyu...

  ga Idanu duk a kanta...
bakinta ne ya soma rawa tana shirin mgn ne.. sai ganin turaki sukayi ya karaso wajen..
Bai tsaya wata'wata ba ya fisgo hannun zainaba sannan ya kalli jalal yace..kayi hakuri yaya......ya shiga jan zainaba sukayi waje...
   Khadija taja dogon tsaki itama kafin tabi bayansa tana wurgawa juwairiya harara...

Yarima dake tsaye ya maida kallonsa kan juwairiya dake ta sharar kwalla..
   Karasawa yayi gabanta yana rungume hannayensa a kirjinsa kafin nan taji yace a takaice..

  "Ki saka a zuciyarki bazan taba bari ki subuce min ba......"

Yana gama fadar haka yayi tafiyarsa...
  "Juwairiya tabi bayansa da kallon mamaki..
Bazai bari ta subuce masa ba?
Me hakan yake nufi?
Ta dafe kanta, lallai idan batayi a hankali ba yarima yana gab da rikita mata lissafinta...

*************
"Jakadiya ce da kanta ta shiga da juwairiya wajen shakatawar yarima,tace nan ne wajen aikin ki juwairiya,nan ne kawai nake ganin zai nisantaki daga duk wani rikicin gidan sarauta..
  Juwairiya ta murmusa tace,nagode da kulawarki inna jakadiya..

"Da daddare duk sun gama aikinsu suna tsaye suna jiran jakadiya ta fito ta sallame su,sai ga surayya ta shigo tare da umayma a bayanta..
Taci gayu kamar zata kasar sarauniyar kyau (yau ne kwananta)
  Ko kallon inda su juwairiya suke batayi ba..
Umayma kam harda zuwa ta gaisa dasu tana karewa juwairiya kallo..

************
"A daki surayya ta iske shi ya kwanta ya lumshe idanuwansa..

A tunaninta ko barci yakeyi,dan haka tadan ja tsaki,ba haka taso ba ko kadan...amma ya ta iya..

  Kayan jikinta ta dan rage sannan ta haye kan gadon tana matsawa kusa da shi..
  Duk abunda takeyi yarima yana jinta amma yayi mata shiru..

   Rungume sa tayi tana daura kanta a kan kirjinsa me fadi..
Taja lumfashi kafin nan ta runtse idanunta..
"Yarima gaba daya yaji kamar ya ture ta daga jikinsa..

Ga tunani duk ya gama cika zuciyarsa, dazu da zainaba tayi wa juwairiya wannan tambayar yaso yaji amsar ta kwarai da gaske..amma bai san irin halin da zai shiga ba idan har ta fadi abunda zuciyarsa bazata so taji ba..

_zakuji update anjima inshaAllah_

Team RUMFAR BAYI
  
  
[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima:           *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 22
Wattpad @afreey101

_gaskiya ina godiya sosai,my wattpad fans are rlly d best,hakama fans din rumfar bayi na whatsapp duk ina jin comments dinku wlh Allah bar zumunci amin_



"Ahankali ya bude idanuwansa...

ya kalli fuskar surayya da barci me nauyi ya dauke ta,
sannan ya saka hannu ahankali ya janyeta daga jikinsa ya sauko da kafafun sa kasa ya zauna a gefen gadon yana dafe kansa da duka hannayensa...

   Muryar jakadiya ce yaji yana sallamar bayin dake waje....
    Haka nan ya samu kansa da mikewa ya zura kaya a jikinsa..sannan ya saka takalmansa ya fito daga dakin..

Jakadiya da tsananin mamaki take kalle sa dan a duk tunaninta ya dade da yin barci.
tace,da fatan dai lafiya ko ranka ya dade?
Jalal yadan murmusa mata sannan yace,
lafiya kalau jakadiya zan dan fita ne na dawo ba da dadewa ba.
Ya sake yin kasa da muryarsa yace.. fitar sirri ce wannan dan haka ki rufa min asiri kinji?dan yasan jakadiya na iya sanar wa kilishi..

Jakadiya tayi murmushi, toh amma bari na saka a kira maka shamaki se yayi maka rakiyar ko?
Jalal ya girgiza kai,ah ah ki barshi kawai ni kadai zan fita,bana son ma kowa ya san fitar kin gane?
jakadiya ta jinjina kai kafin ta karasa ta bude masa kofa ya fice..

************
"Tunda suka ba'ro sashen sarki suke ta buga sauri...
kasancewar dare ne babu wani isasshen haske a hanyar..
  Juwairiya da aka baro can baya ta daga murya tace..
Wai baza ku jirani bane..?
Wata baiwa dake cikinsu tace,kema ki daga kafa dan Allah kina tafiya kamar wata me tausayin kasar kinsan dai dare ne atooh..

  Juwairiya kamar zatayi kuka ta karawa tafiyar ta ta sauri,dan ita kam tana tsoron duhun nan sosai..

     Sun sha kwana kenan kawai taji an damko hannunta da karfi....
A mutukar tsorace ta kware baki zata saka ihu..sai ji tayi wani abu me shegen taushi ya rufe mata baki,sannan aka shiga janta da karfi...
    Fitsari ne kawai batayi ba sbd tsananin tsoron da fargabar data shuga...

   Can bayan wani kango aka sake ta duhu ne sosai a wajen dan haka tayi yunkurin guduwa tana laluben hanya...

Sai ji tayi kawai taci taro da mutum bum!
Lumfashi me tsayi taja dan ko ba'a fada mata ba tasan waye...
Kamshin sa kawai data ji yasa ta gane YARIMA NE....

Jalal ya sake kama hannunta suka dawo saitin da kawai dan haske a wajen..
  Yana sakin hannunta ta dago da sauri suka hada ido dashi..

  Jalal ya harde hannayensa yana kara matsawa gabanta..
  Tadan ja baya kadan..tana fadin..
Ka ka kayi hakuri ranka shi dade..
  Yarima yaja burki yana fadin,hakurin me zanyi?

Juwairiya ta girgirza masa kai..
Jalal yace,"nazo ne dan ki fada min amsar ki ta dazun?
  Ta dan ware ido,amsata wace kenan?ranka shi dade..?

Yarima ya gyada kai yana matse lebensa na kasa..
Dariya yaso ya bata,wato dan kawai yaji amsatar ta ne.. shine ya fito da a cikin daren nan?sannan kuma har ya baro matarsa a daki?ya biyo ta ita baiwa?.

  Ina jinki?ya fada yana gyara tsayuwarsa...
Juwairiya ta rasa me zata ce masa,bakinta ya shiga rawa....
Ni ni ai babu wani zabi a gare ni,duk inda kuka kaini ai dolene naje nayi aikina..

    Mgnr da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login