Showing 15001 words to 18000 words out of 83480 words
can ana yi muku kallon baku isa ba..dan ni burina a kullum shine ku samu girgimawa a wajen mutane..
Magaji yayi murmushi, godiya muke umma..
Hamza yace,abun mamaki wai yau yayane da kansa yake son tafiya da bayi mata...
ba'cin kullum fada yakeyi min idan na dauke su..
Yarima ya banka masa harara. .
Kilishi tace ina ruwanka toh?ka manta jiya ba yau bace?duk suka saka dariya..
Suna cikin mgn sai ga jakadiya da du'bu sun shigo suna sanar dasu an tara bayin suna waje..
Yarima gaban shi ne ya fadi,idan ya ganta a cikin bayin can ya zayyi?addu'a kawai yakeyi Allah yasa bata cikinsu wata zuciyar kuma na addu'ar Allah yasa ya kanta..
Cikin wannan tunanin ne ya karasa waje shima yana baza idanuwansa ta ko ina...
Kilishi ta kallesu cikin kasaita tace,yarima....je ka duba wadan da sukayi maka,ta mika masa wata sanda kamar yadda al'adar su take idan yaga wacce tayi masa zai sa sandar ne ya nuna ta dashi...
Cikin tafiyarsa me daukar hankali ya karasa gaban bayin dake jere kowacce ta sunkuyar dakanta cike da ladabi...
************
"A wajen juwairiya kuwa tana jin ance yarima...gabanta ya fadi..ras!
Ta sake sunne kanta kasa tana matse hannayenta duk da tasan ita dai ba daukarta ma zayyi ba amma hakanan bata son ya sake wulakanta ta kamar yadda ya saba..
Yarima na tafe har ya kusa kai wa karshen layin kawai ya hango side view dinta,
bai gama tantance ko wacce yake tunani bace kawai kai tsaye ya saka sandar cikin saurinsa ya dauke mayafin data lulluba akan ta..
Jikin juwairiya ne ya hau rawa,miye hakan?
Ita ya zaba?
Kodai bai gane ta bane?
Yau ta shiga uku...runtse ido tayi kawai.....tana ji kilishi na cewa KE!! Fito...!
**********
Shi kam yarima wani irin yamutse fuska yakeyi ganin wacce ya canko,me yasa wannan me konannar fuskar ta cika bibiyar rayuwar shine?
Tsaki yaja ya koma gefen su kilishi ya tsaya dan gaba daya ranshi ya baci..
A sanyaye juwairiya ta fito ta tsaya kamar ta rusa ihu takeji..
Kilishi ta yamutse fuska tana mamakin duk a cikin bayin nan wannan ce yarima zai dauka?ko da yake tasan dan nata,komai nashi na daban ne..
Kilishi tayi gyaran murya tace,toh sai kije ki shirya kayanki dan tafiyar tasu cikin nan da minti talatin ce...
Ta juya wajen magaji,kai ka koma ka zabar muku sauran dan naga ra'ayin abokin naka sai a hankali...tana gama fadar haka ta shige ciki abunta..
Du'bu da jakadiya duk ransu bai so aka zabi juwairiya ba ko kadan,toh balle hansai da laure dake gefe suna hawayen bakin ciki...
Yarima ya banka wa juwairiya harara kafin ya wuce magaji da hamza suka bi bayan sa..
Ai suna watsewa bayin duk sukayi kan juwairiya dake kuka,hansai ta kamo hannunta suka karasa rumfar bayi..
Suna kuka suna hada mata yan kayan ta..
Laure tace,kada ki damu juwairiya babu abunda zai faru dake se alkairi..
Hansai ma sauke lumfashi tayi,ta riko hannun ta..
Hankalina yadan kwanta jin tafiyar tasu yarima da magaji ne,na tabbata babu wani abunda zai faru dake dan kuwa yarana ne da suka san abunda sukeyi,ki kwantar da hankalinki kinji?duka kwana uku zakuyi zuwa biyar,kada ki manta da tabon fuskar ki shine kariya a gareki kinji?
Juwairiya ta gyada kai kafin ta dau kullin kayanta ta fice..
**********
Tana fitowa ta hango zainaba can gefe a tsaye tana jiran shigowar ta..
Da sauri ta goge hawayen ta tayi wajen ta..
Zainaba na ganinta ta fara hawayen itama a shagwabe tace..
Yanzu fi sabilillahi dauke min ke yaya jalal zayyi..
Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu zanki ya dade babu me dauke miki ni,tafiya kawai zamuyi mu dawo kinji..
Zainaba ta gyada kai,muje kiyi sallama dasu fulani...
Suna shiga sashen fulani diyya,juwairiya ta zube kasa tana kwasar gaisuwa..
Fulani a sake ta amsa mata tana fadin,ashe dake zasuyi tafiyar?
Juwairiya tace uhm,fulani tace,toh Allah ya dawo daku lfy,gaba daya falon suka amsa da amin..
Suna fitowa waje suka ci da turaki..
Yana ganinsu ya sauke idonsa kan juwairiya,a take ya fahimci hankalinta a tashe yake..
Gaida shi sukayi,yayi murmushi yace,ah ah yan matah ana ta bankwanar ne?
Zainaba ta shagwabe fuska,yaya harda kai zolayar ko?
Turaki yayi dariya,naga ai kwana uku ne kawai miye abun damuwa?ya karashe mgnr yana kallon gefen juwairiya..
Juwairiya tadan murmusa kawai..
Turaki yace,addu'a kawai zakuyi abunda akaje nema a samo shi lafiya,yana gama fadar haka ya shige ciki cikin takunsa...
Zainaba ta ja juwairiya zuwa sashen ta..
Wani kulli ta miko mata..
Gashi ki ringa ci ahankali a hanya kinji..
Juwairiya cike da murna tace nagode ranki ya dade...
Wani bawa ne yazo yana sanar dasu ana neman juwairiya...
*************
Motace irin ta da dinnan,sai wata bus..
Juwairiya da gudunta ta karasa wajen..
Yarima da magaji na tsaye da sauran bayin duka an gama saka kayansu a cikin motocin..
Tana zuwa duk suka maida kallonsu gareta..
Yarima yaja tsaki...lallai ya gama kufsawa kansa yanzu haka zai tafi da waccan yarinyar yana kallon konannar fuskar sa,mtsw ..
Surayya ce ta karaso wajen tare da baiwa a bayanta..
Wajen yarima taje ta mika masa kullin dake hannunta..
Se daya kalle ta sannan ya maida kallonsa kan kullin yace,menene?
Tadan karkace kai,
Ka amsa mana kaga fa akwai mutane a wajen,yadan yi yake sannan ya amsa ya shige mota,surayya tabi bayin dake wajen da kallon wulakanci balle ma juwairiya data gani duk a tsorace...
Suna shiga mota shamaki da galadima sukayi musu addu'ar suka lafiya sannan suka hau hanya...
"Toh ya kuke ganin wannan tafiyar zata kasance?"
Keep following rumfar bayi
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 12
Wattpad @afreey101
*****************
"Sunyi tafiya mai nesan gaske kafin suka iso Daular borno..
"Yarima dake zaune a bayan mota yace wa bawan dake tu'ka su,idan muka shiga borno sai mu a tsaya a masarautar su mu kwana zuwa gobe sai mu karasa chadin..
'Magaji ne ya gyara zamansa yace,ai mun shigo Daular borno tun dazu yarima tunanin me kake ne haka?ba dai har ka fara kewar surayyar taka ba..yayi mgnr cike da zolaya..
Yarima yaja tsaki kawai yana kallon window..
'A can cikin bus kuwa su juwairiya ne,tunda aka shigo kasar borno ta maida hankalinta akan kallon window tana karewa tsarin garin kallo...har taga sun shiga wata katowar kofa sai gasu acikin masarautar ta borno..
'Ido ta ware tana kallon mutane dake ta zurga'zurgar su duk da dare ne amma harkar gabansu kawai sukeyi..
Rabi ce ta dan tabo ta ganin motar su ta tsaya,muje juwairiya....
'A sanyaye ta fito daga motar jikinta duk a gajiye tana rungume da kullin kayanta..
Daidai lkcn ne shima yarima ya fito yana wani shan kamshin sa.
Har fadar mai martaba aka kai su suka kwashi gaisuwa sannan aka saka wasu matah su kaisu masaukin da zasu kwana zuwa goben..
Masaukinsu ya hadu sosai dan komai an wadata su,tunda Takawa (mahaifin jalal)ya riga ya turawa sarkin borkon sakon zuwan su.
daki daya aka ware wa su juwairiya ,sai daki daya na yarima, daya kuma na mazan bayi sai dakin magaji...
Suna shiga kowaccen su ta kwanta cike da gajiya,basu dade da shigowa ba sai ga sakon magaji ya iso musu daga wajen wani bawa,wai a cikin su ukun wata taje ta hadawa yarima ruwan wankan sa..
'Rabi ta marairaice ta kalli juwairiya,waye zai je a cikin ku dan ni kam wlh bazan iya zuwa ba jikina ciwo yakeyi sosai..
"Zabba'u itace karama a cikinsu,dan haka tace,ni wlh tsoro nakeji kuma ni ban ma iya hada ruwan wankan ba tunda ni a madafa nake dama..
"Juwairiya tadan hararesu,kawai ku fito fili kuce ni naje mana..
Dariya sukayi sannan a tare sukace..
Dan Allah juwairiya ke kije..
"Juwairiya zatayi mgn bawan dake waje ya sake cewa, baku ji bane? !ba a barin yarima yana jira,juwairiya ta zunboru baki sannan ta mike tana sake gyara kayan dake jikinta kafin ta fito..
Bawan na gaba tana binsa a baya har suka shiga bangaren su yarima..
Magaji ne kawai a falon zaune..
Yabi juwairiya da kallo, shiga ga dakin can ya nuna mata wata kofa..
Toh tace kawai jiki a sanyaye ta shiga kofar..
Yarima ta hango a zaune kan dago ya jingina bayansa a kan gadon ya lumshe idonsa..
Ta rasa me zatace masa, wace irin gaisuwa zatayi masa..
Dan haka se ta lallaba zata shige kofar data ke tunanin ta ban dakin ce..
'Haka aka koyar dake!!!?
Muryar yarima ta da'ki dodon kunnenta..
Da sauri ta juyo ta hango shi yana kallonta fuska a daure..
Dawowa tayi baya tace,afuwa zanka shi dade na dauka barci kake ne...
Ya yamutse fuska yayi sannan ya maida idonsa ya lumshe..
Juwairiya ta shiga toilet din ta hada ruwan wankan sannan ta fito ta tarar dashi a tsaye..tace..
Na gama...ta sunkuyar dakai..
Tsaki ya danyi haushin kansa kawai yakeji daya za'bi ta a tafiyar....ya kasa gane meyasa wannan yarinyar take shiga rayuwar sa..
tsaki ya dan'yi kafin yace,Zaki iya tafiya,ya mike a natse yana cire alkyabbar dake jikinsa..
Toh tace kawai ta fice..
Tana fitowa falon ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi..
Magaji ne yayi dariya...
Tayi saurin kallonsa dan ta manta ma akwai mutum a falon..
Yace duk tsoron yariman ne?
Juwairiya tayi dan murmushi sannan ta fice tana jin kunya sosai..
Da asuba suka hau shiri,wannan lkcn rabi ce taje ta hada masa ruwan wankan dan juwairiya kekeme tace itama ta gaji..
Da sassafe kuwa sai ga kayan karin kumallo an kawo musu me rai da lafiya,suka ci sosai kafin suka hau hanya..
*************
"Sun sake shan wata tafiyar mai nisan gaske kafin suka shigo kasar chadi...
Ba karamin mamakin nisan garin juwairiya tayi ba...
A wani wajen saukar da baki ne suka yi masaukin su..
Su juwairiya na tsaye gaban kofar dakin da aka basu suna jira a bude musu magaji ya karaso wajen...
Ya kalli juwairiya yace, yarima yace kije ki hada masa ruwan wankan sa..
Juwairiya ta gyada kai kawai amma can cikin zuciyarta haushi ne kawai takeji,ko ya dan bari ma su dan huta,koda yake su bayinsa ne bai damu da samun hutun su ba,shi kullum se shegen son wanka kamar wani kifi mtsww...
'Kullin kayanta ta mikawa rabi sannan ta juya tabi bayan magaji tana mamakin wai ita yarima da kansa ya kira bayan kullum se ya mata gargadin zuwa inda yake mtsww...
**************
'Ta same sa ne a cikin wani makeken falo..
Da sallama ta shiga ya amsa mata ciki ciki idonsa na kan wata takarda..
Barka da hutawa ranka shi dade..
Yayi banza da ita,se hannu daya sa ya nuna mata kofar toilet kawai..
Tadan ja lumfashi kafin ta shiga ban dakin...
Da kallo ta bi toilet din ganin irin nasa tsarin..
Toh fa ina zan samu ruwan a nan?ta fadi tana rike kugu...
Ganin bata da masaniyar hakan ne yasa ta leko tana kallon yarima amma ta kasa magana..
Yarima naji a jikinsa kallon sa akeyi amma ya da'ke ya share ta...
Juwairiya tadan ja tsaki kadan,sannan ta koma cikin toilet din tayi tsaye...
Yarima ya mike tunawa da yayi famfo ne a cikin toilet din kuma tabbas da wuyane ta san shi tunda can masarautar su, mai martaba da matan sa ne kawai ke dashi a ban dakin su..
Toilet din nufa cikin tafiyar sa a sanyaye..
Ita kuwa juwairiya tabe tabe ta shiga yi dan gano inda zata samu ruwan..
Sai ji tayi an bude kofar toilet din..
Ta juyo da sauri tana kallonshi..
Yarima bai ko kalleta ba ya shiga tafiya yana kusanto inda take a tsaye..
A tunanin juwairiya kashin ta ne ya gama bushewa tunda ta bata masa lkc har haka tasan bazai barta ba tsoro ne ya dirar mata..
Yarima kuwa wajen fanfom dake kusa da ita yake son zuwa ya kunna...
Tana jin yazo kusa da ita sosai sai ta zube a kasa tana shirin mgn kawai taji saukar ruwa a jikinta dan dama fanfom bayanta yake a karkashin sa ta du'ka ..
Yarima ya harde hannayensa yana kallon yarda ruwa yake wanke juwairiya tas...
Ita kuwa a tsorace take sosai daga ina zuwan nan ya fitowa haka?
Ta dago fuskar ta da ruwa ke sauka a kai...
Yarima yaji gabansa ya buga,bum! Bum!
Minene haka?
Ya fada cikin tsananin mamakin ganin tabon dake jikin fuskar juwairiya yana wankewa a hankali ahankali ..
Kura mata ido yayi kawai yana kallon ikon Allah..
Ita kuwa juwairiya jin ruwa ya cika mata ido yasa ta mike da sauri tasa hannunta tana goge ruwan daga idonta..
"Sauke hannunta daga fuskarta yayi daidai da bugawar zuciyar yarima cikin tashin hankali...
Me zai gani haka?
I...TA...CE !!!!!
Ya furta da karfi....
Juwairiya ta tsorata sosai jin yarda yake ta furta itace itace kuma yana nuna ta..
Yarima ya karasa gabanta....
kawai ji tayi yasa hannunsa me taushi yana shafa fuskarta...
Idanuwanta kawai ta zazzaro tana kallonsa..
Lafiyarsa kalau?
Taja baya da sauri a firgice ...
Hakan yasa hankalin yarima ya dawo jikinsa..
"Haushin kansa yadan ji..
Ya daure fuska kamar ba shi ba yace kiyi sauri ki hada min ruwan..ya juya da saurin sa ya fito daga toilet din..
Daki ya shiga yana dafe kirjin sa..
Mamaki tsantsa a cikin zuciyarsa..
Dama itace?
Amma me yasa take boye fuskarta ne da wannan tabon?
Lallai kuwa itace me wannan fuskar da ya dade yana son gani,ya shiga tuna duk haduwar da sukayi a baya..
Murmushi yayi kawai cike da farin ciki..
Wata zuciyar tace masa,yanzu tunda ka ganta se kuma me?
Sonta kake ne?
Ah ah ya girgiza kai da sauri ni nayi soyayya da wata baiwa?Allah ya tsare ni..
Dolene ya saita kansa kada yaja wo wa kansa raini a wajenta..
Haka nan yayi ta murmushi shi kansa ya rasa dalilin hakan...
***********
Juwairiya kuwa shaf ta manta da wani tabo a fuskata ,tana gama hada ruwan ta fito ta tarar da baya cikin falon..
Ta kalli kofar dakin..
Ko ta shiga ta sanar dashi ne?
Tadan girgiza kai,kada kije ya kuma ci mutumcin ki a banza..
Ta samu wuri ta rakube a gefe dan jiransa..
Sai jin fitowar shi tayi..
Yana ta wani kallonta bai ce mata komai ba ya shige toilet din..
Tadan ja tsaki,ko yace min zan iya tafiya ma mtsw..
Haka tayi ta zama har ya fito daga shi se dan wani yadi daya daura a kugunsa..
Juwairiya tayi saurin dauke ido tana jin gabanta na faduwa......
Please
Vote
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 13
Wattpad @afreey101
********************
'kallon ta yayi Ya dan saki murmushi, kafin nan ya daure fuska yace,ke!...
Ta dago da kanta a tsorace amma bata kalli in da yake ba..
'Yarima ya shafi sumar kansa Yace,ki biyoni.....sannan yayi cikin dakinsa..
A sanyeye jikinta na rawa ta bi bayansa a tsorace...
Tana shiga dakin ta iske shi a tsaye yana goge jikinsa cike da nutsuwa..
Tayi kasa da kanta da sauri..
Yarima yace,har yanzu baki san aikin ki ba ne?
A cikin sarkewar murya tace na sani?
Ya karasa gabanta ya mika mata dan karamin kyallen dake hannunsa..
Jiki na rawa ta amsa..
Ya koma ya zauna yana juya mata bayansa,kawai be ce da ita komi ba..
'Juwairiya ta karasa ta tsaya a bayansa da kyallen a hannunta..
Se data ja lumfashi sannan ta runtse ido ta shiga goge masa jikinsa..
Tana gamawa taja gefe da saurinta..ta runtse idonta kirjinta na bugawa..
'Yarima ya saki murmushi sannan ya mike ya karasa wajen kayansa ya dauki man shafawar sa .
yana shafa man yana kallon juwairiya dake rakube a gefe idanuwanta a kulle gam! haka kawai sai ya tsinci kansa a cikin wani irin nishadi..
"Zo ki taimaka min ya fada kai tsaye yana mika mata alkyabbar dake hannunsa..
Ta bude ido taga ya gama shirin sa tsaf cikin wani farin yadi mai sauki ,ta karasa ta amsa alkyabbar sannan ta taimaka masa ya saka..
Maganar wani bawa sukaji daga can cikin falon...
Yarima ya fito tana biye a bayansa..
Abincine kala kala aka kawo masa..
Bawan ya du'ka har kasa yace,ranka shi dade sun ce na baka hakuri akan kayi hakuri da wannan ya nuna abincin daya shigo dashi,saboda dare yayi ne basu samu damar gaba tar maka da abinci masu yawa ba..
Yarima yace banu komi zaka iya tafiya..
Juwairiya ta dan tabe baki duk wannan kayan dadin shine harda wani bashi hakuri..tab lallai ta yarda yarima babban mutum ne..
'Yarima ya kalleta yaga idanuwanta kyam akan abincin..
Zama yayi kawai yana lankwashe kafafunsa..
Juwairiya ta dan hada karfin da gareta tace..
Ranka shi dade zan iya tafiya?
Yarima ya girgiza kai...
Juwairiya tace na shiga uku wai meke damun mutumin nan ne?(a cikin zuciyarta)..
Yarima ya lumshe ido ya bude,kafin yace,zo ki bani abincin..
Juwairiya a sanyaye ta duka ta zuba masa abincin a cikin plate sannan ta ajiye a gabansa tana kokarin mikewa yace..
A ba'ki zaki bani...dan na gaji dayawa..
Juwairiya gabanta ya fadi,...
'A baki'?ta fada a tunaninta cikin zuciyarta tayi mgnr se ji tayi yace..
Da a hanci zaki bani?
Ta girgiza kai,ai ko zainaba bata zama a bata abinci a baki..
Tsokali ta dauka ta debo abincin kadan a ciki sannan ta mika masa..
Yarima na kallon fuskarta ya bude baki ta saka masa abincin aciki..
Cike da takura take basa abincin har yayi mata nuni da ya koshi..
Dadi taji sosai dan ta san yanzu dolene ya sallameta tunda dai ba ita zatayi masa barcin ba..
Ji tayi kawai yace..
'Saura ke ki ci'
Ta dago da mamaki tace,Ni?
Yarima fuska ya daure yace ban sani ba..
Juwairiya ta rasa yarda zatayi wai "saura ke ki ci"kodai kunnenta ne yaji mata badai dai ba..?
Yarima ya mike kawai yace,idan kin gama zaki iya tafiya...
Yana shiga daki juwairiya ta sake kallon delicacies din dake wajen ko kwatan abincin yarima bai ci ba..
Gyara zamanta tayi a wajen tana fadin..
'Gwara naci dan kada ma ayi asarar abincin nan da mutane dayawa basu da halin kamar shi...
Cin'yar kaza ta dauka tana yashe lebenta,se yau Allah yayi zata dandana irin wadan nan abincin oh"dama su ummanta na nan suci tare..
Yarima dake labe a bakin kofa ya saki murmushi yana ta kallon yarda take cin abincin da gani ta kwaso yunwa sosai, tausayinta ne yaji ya kamasa..
Juwairiya taci tasha sosai sannan ta kwashe sauran tayi gaba dashi dan ta kai wa su rabi suma su sa wa bakin salati.
Tana shiga dakin ta tarar basu a ciki ko ina sukaje oho,sallolinta tayi sannan ta zauna ta sake maida tabon fuskarta shaf bata kawo ya wanke bane a toilet din yarima duk a tunaninta a wajen alwala ne ta wanke sa.
"A daren yarima yayi barcin farin ciki sosai dan har mamakin kansa yakeyi,duk da baisan matsayin yarinyar a cikin zuciyarsa ba amma zayyi kokarin kyautata mata tunda dai ko ganin ta ma kawai a kusa dashi