Showing 42001 words to 45000 words out of 83480 words
karasa wajen yana fadin..
"Ya baki tafi ba?
Juwairiya tayi saurin mikewa..
Uhm dama dama uhm yauwa jakadiya ce tace na jira ta a nan..
Ya jinjina kai dan zuciyarsa ta gama basa shi take jira...
Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya nufi wajen shakatawar sa da ita..
Ya sake hannun nata sannan ya rufo kofar wajen.
Juwairiya gabanta ne ya shiga faduwa..
Jalal yace..
Yau zanyi tafiya...ya karashe mgnr cike da wani irin yanayi..
juwairiya ita kanta se dataji wani iri.. da murya me cike da sanyi ta samu kanta da fadin..
'Yaushe zaka dawo?
Ya kurawa kwayar idonta kallo..
Kwana biyune..
Juwairiya tayi murmushin yake tace..
Allah ya dawo dakai lfy ranka shi dade..
Jalal ya gyada kai..
Nagode..
Hayaniyar su shamaki ya jiyo daga waje..
Yaja lumfashi ni zan tafi..
Ta jinjina kai ta kasa furta komai..
Ya juya har ya kai bakin kofa ya sake juyowa..
Bai bata wani lkc ba ya janyo ta jikinsa..dan gaba daya kasa controlling zuciyarsa yayi..
Juwairiya taji gaba daya duniyar ta tsaya mata tsak...
Sai da suka shafe seconds talatin kafin yayi karfin halin sakinta ya juya da sauri ya fice........
*************
"Yana fitowa waje ya tarar da fadawa sun cika wajen gasu magaji da turaki suna ta jiransa suma..
Ya karasa wajen su cikin takon girma kafin suka nufi sashen gimbiya kilishi ga baki dayansu..
A nan suka tarar dasu surayya da khadija kowacce najin da kanta..
Sallama sukayi musu...sannan suka sake zuwa sashen mahaifinsu anan suka iske fulani sukayi musu sallamar suma kafin suka dau hanya..
"Sun isa kasar zazzau da yamma sosai..
Sarki ya saka aka kaisu masaukin su..
Abinci kala kala aka kawo musu suka ci sosai kafin duk suka bi lafiyar gado sbd sauke gajiya..
***************
Yau kwanan jalal daya da tafiya amma juwairiya duk ta rasa me ke mata dadi,
har fada take wa zuciyarta,ke wacece a wajensa da zaki damu dashi haka uhm?
Ta girgiza kai,yarima ka barni na huta!
Ta kalli zobensa data amso dazun wajen me siyar da kifi..ya zanyi da kai yarima?
Zabba'u ce ta shigo dakin ta sanar mata da sakon zainaba na son ganinta a sashen ta..
Tana fitowa daga rumfar bayi suka hade da umayma..
Umayma tace,sai ina haka juwairiya, ko saurayin naki zakije gani ne?
Gaban juwairiya ya fadi,ta ware ido tana dafe kirjinta..
Saurayi kuma?ta fada cike da faduwar gaba..
Umayma tayi dariya ke wasa fa nakeyi miki..
Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya,kee kuwa kin cika uwar zolaya..
Umayma ta jinjina kai sukayi sallama kowaccen su ta kama gabanta..
"A can kasar zazzau kuwa,sarki da kansa ne ya bukaci ganinsu da safe,suka shirya suka same sa a palace dinsa..
Sun fara mgnr yarda auren zai kasance sarki ya saka a kirawo masa dansa na fari wato mahaifin yarinyar da ake son hadawa da turaki..
yana shigowa fa'da ya kwashi gaisuwa wajen mahaifinsa sannan aka saka ranar biki..
Turaki dai kallonsu kawai yakeyi dan shikam dan dole ne zai yi wannan auren.
jalal ne ya sanar dashi sakon mai martaba dayaje yaga yarinyar can a gidansu aka hada shi da wani bawa..ba da son ranshi ba ya tafi..
"Jalal tare da magaji kuwa autan sarki khaleed ne ya shiga yawo dasu a cikin masarautar..
Sun kawo sashen amaryar sarki khaleed ya hango ta tana kokarin fita da bayinta a zagaye da ita..
AMMI...!
Ya kira sunanta yana karasawa wajenta..
Jalal da mgaji ma suka bi bayansa..
Ammi ga surukan SAMIRA sunzo harda ma yayan mijin nata sarki JALALLUDEEN..
Wacce aka kira da Ammi jalal ya kura wa ido..
A ina yasan irin wannan fuskar?
Noo haba inaa...juwairiya?zuciyarsa ta raya masa..tabbas akwai kamanni a fuskokinsu..
Ya girgiza kai,amma basu da wani alaka da juna ai,mayb kawai kama ce daga Allah..
AMMI ta kallesu da kulawa suka gaisa,jalal kuwa ya kasa dauke idonsa daga kallonta yana mamakin yarda akayi matar take kama da juwairiya baiwar Rumfar bayi..
*************
"Badai kina nufin akwai wani da wannan me konannar fuskar take gani ba cikin masarautar nan?
Umayma ta gyada kai,na tabbata akwai ranki shi dade, dan danayi mata tambayar dazu wlh idanuwanta sun nuna tsoro tda fargaba..
Surayya ta jinjina kai,toh amma wane irin dolo ne banza da zai so wannan abun?fuska duk a kone..
Kuma tasan da cewa baiwa ce ita bazata taba iya aure ba,ba tare da an yanta ta ba.
Umayma ta gyada kai dole ne kuwa mu gano wanene take gani.
Surayya tace,ki saka mata ido dan akwai zargin da nakeyi...
*************
"Yau kwana biyu da tafiyar su yarima kuma a yau ne ake saka ran dawowar su..
Gimbiya kilishi da kanta ta saka ayi mata kiran du'bu dan ta sanar da ita duk shirye shiryen da za'ayi musu.
"A wajen juwairiya kuwa haka nan ta tsinci zuciyarta a cikin farin ciki sosai tun da ta lbrn..
Sai dai duk farin cikin ta bata kai ga na matan sarki ba..
Dan ba karamin shiri sukeyiwa dawowar mijin nasu ba..
Kowacce da irin kissar da take kullawa...
**************
Sai da yamma kilis su jalal suka shigo cikin masarautar,
sai da suka fara zuwa wajen sarki Abdul-Jabbar sukayi masa bayani akan amincewar sarkin zazzau acikin alliance din hada auren,kuma a take aka saka ranar biki rana daya dana hamza kamar yarda suka bukata..
Murna sosai fulani da mai martaba sukayi,sai dai shi gogan wato turaki,ko digon son yarinyar babu a cikin zuciyarsa...
"A gajiye jalal ya shigo sashen nasa,yana shiga dakinsa ya sauke ajiyar zuciya yana sakin murmushi kafin nan ya furta..
"Yau zan ganta...ya lumshe idonsa..
Kayan jikinsa ya cire sannan ya shige cikin toilet dan watsa ruwa..
"Yana fitowa ne kawai ya tarar da surayya a zaune tana jiransa..
Mikewa tayi da saurinta tazo gabansa tana amsar dan karamin towel din dake hannunsa..
Shidai da kallo kawai yake binta..
Surayya ta shiga goge masa ruwan dake jikinsa tana masa wani irin salo...
"Kirjinsa take goge masa tana yawo da hannunta a kai cikin kissa..
Yarima yayi saurin rike hannunta zayyi magana kenan kawai yaji ta fara kai masa sumbata a gaba daya jikinsa..
"Jikinsa ne yayi lakwas, surayya na ganin haka tayi murmushin samun nasara....
Dan dama tasha alwashin a yau sai yarima ya kwana da ita tun kafin khadija tama saka shi a ido..
Gashi kuma tasha maganin da yakumbo ta aiko mata dashi na daukar ciki da wuri...addu'ar kawai Allah yasa ciki ya shiga...
***************
"Juwairiya ce zaune a cikin RUMFAR BAYI tana jin haushin hanata zuwa sashen jalal da jakadiya tayi..
Gashi kuma Zuciyarta na mutukar son ganin fuskarsa..
"Rabi ce ta zauna a gefenta tana dafa kafadarta..tace..
Wai ni lafiyarki kuwa juwairiya? Kwana biyun nan kin cika zama ke kadai wlh..
Juwairiya zatayi mgn sai ga umayma ta karaso wajensu tana washe baki kamar gonar auduga..
Rabi taja tsaki..ke kuma fa?
Umayma ta dalla mata harara..da akayi me?
Rabi tace,naga se wani washe baki kikeyi sai kace baiwar da aka yan'ta ta..
Umayma ta rangwadar da kai..
Ba dole nayi murna ba tunda dai a wannan lkcn ina kyautata tsanmanin uwar dakina na can akan shinfidar sarki JALALLUDEEN....
"Ba rabi ba har juwairiya dake sauraren su sai da zuciyarta ta buga..
Tayi saurim dafe kirjinta..
Me ke shirin faruwa da ita..."kishi"
Ah ah me yasa zatayi kishin sarki da matarsa...
Ta dafe kirjinta..
Rabi taja dogon tsaki sannan ta mike da gudu tabar wajen dan zuwa sanarwa khadija..
Umayma tahau gu'da...sai can ta hango yarda juwairiya dafe kirji..
Yanayinta ta karanta kawai kafin tace..
Yadai juwairiya lafiya?
Juwairiya ta kakaro murmushi sannan ta mike da sauri ta shige dakinsu...
Kwanciya tayi tana sauke lumfashi me dumi..
Ya kamata kisan abunda ya dace dake juwairiya ta fadawa kanta..
"Take taji jikinta ya dau rawa dan dama tana jin signs din zazzabi ajikinta tun satin daya wuce..
"Hansai ce ta shigo da fitilar kwai a hannunta cikin dakin..
Har ta fara mitar kwanciyar wuri da juwairiya ta tsira..
Sai hango ta tayi tana rawar sanyi..
Ai da sauri tayi kanta..
Juwairiya ke miye ke damunki haka?
juwairiya ta kasa mgn dan harcenta yayi mata nauyi..
Hansai ta fita da gudu tayi kiran du'bu da laure..
Laure na taba jikin juwairiya tace,zazzabi ne mai zafi ya rufe ta..
Du'bu tace subhanallahi..
Hansai ta girgiza kai,ai dama dole ne zazzabi ya kama juwairiya tunda ta maida gaban kogi wajen zamanta duk iskar duniya ya kare akanta..
Du'bu tace bari naje na hado mata magani....
******************
"Da safe jakadiya ta shiga dakinsu juwairiya, ta ganta a kwance jiki kam sai a hankali..
Hansai ta kalla tace,Allah ya bata lfy ni bari na karasa wajen aikina,zan saka wasu bayin suyi mata (covering)aikinta..
Hansai ta jinjina kai dan itama in ba dan dole ba bazata iya fita tabar diyar ta acikin wannan halin ba..
***************
Tunda sassafe jalal ya farka yayi wa surayya kora da hali..
Ya zauna yana ta jiran shigowar juwairiya..
Amma shiru shiru har ya gaji da jiran ta bata shigo ba..
Jakadiya ce ta rangwada sallama ta shigo dakin..
Jalal dake zaune ya amsa ta ciki ciki..
Allah ya kara maka yawan rai ayi min afuwa na shigo ne dan nunawa wannan baiwar aikinta..
Sai lkcn jalal ya hango baiwar dake bayan jakadiya..
Jiyai tace,ki shiga ki hada masa ruwan wankan sa sannan ki dawo dakin ki gyara shi..
Jalal gaba daya wutarsa ta dauke,me yasa jakadiya zata kawo masa wata baiwar ba juwairiya ba ta gyara masa daki?ina ita juwairiyar take?me yasa aka canza masa ita?
"Wasa wasa dai har ranar ta ka're jalal bai sa juwairiya a ido ba..
Koda ya shiga fa'da ma ba wani abun kirki yayi ba magaji ne ya taimaka masa yayi masa rabin aikinsa..
"a Kwana na biyu yarima ya rasa mafita,kullum a falonsa yake wuni dan ganin ko zai hadu da ita amma shiru.
gashi baya son ya tambayi jakadiya dan bai san wane irin kallo zatayi masa ba..
"Dan haka ne ya shirya dan zuwa sashen kanwarsa zainaba yasan koma miyene zata sani tunda tana kaunar juwairiya sosai..
"Koda zainaba taji sallama na sanar da isowar jalal sashen ta ba karamin mamaki tayi ba..
Ta mike tsaye har ya shigo ya zauna kafin itama ta samu wuri ta zauna fuskarta dauke ta da tsantsar mamakin ganinsa..
"Jalal ya sakar mata murmushi..
Yadai?wannan kallon fa?
Zainaba tace,wlh mamaki nakeyi wai ya jalal da kansa ne a sashena..
Jalal ya murmusa,nazo bada hkr ne nasan kanwata tayi fushi da yayanta ko?
Zainaba ta shagwabe fuska, ni na isa nayi fushi da Sarki?
Jalal ya shafa sa'jen sa,gashi har umma ma fushin da ake dani ya shafe ta,tunda ta fada min kin daina zuwa gaishe ta ko?
Zainaba ta turo baki..
Jalal yayi dariya..toh ya ake ciki ne menene lbr..?
Zainaba a take yanayin ta ya canza,damuwar dake ta cinta a rai ta rasa kuma dawa zatayi sharing yasa kwalla sulalowa akan kumatun ta..
Jalal yaji hankalinsa yadan tashi,kodai wani abu ne ya samu juwairiya?dan a ganinsa zainaba bata tare da wani damuwa..
Cikin kulawa yace,haba zainaba menene kuma na zubar da kwalla..
Zainaba ta kallesa tana nazari,maybe Allah ya turo mata ya jalal ne dan ya taimake ta..
Gyara zama tayi sannan ta fada masa komai a tsakanin ta da Mustapha..
Jalal ya kura mata ido kawai yana fadi a zuciyarsa TIRKASHI..
Zainaba ta katse shi da cewa,wlh yaya bana son ayimin wani auren hadi kamar yarda akeyi muku,ni Mustapha nake so kuma shi nake son na aura..
Jalal a take zufa ta shiga ke'to masa..
Lallai akwai chakwakiya nan gaba...
Dan kuwa ya samu lbr a wajen gimbiya kilishi....
Tun ZAINABA na yar jaririyar ta mai martaba ya bawa MAGAJI ita,duk da shima magajin bashi da wani masaniya akan hakan...................
Toh fa........
Muje zuwa 👇
TEAM RUMFAR BAYI
[9/18, 3:22 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
( A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 27
Wattpad @afreey101
**********************
"Jalal ya gyara zamansa yana kallon zainaba cike da tausayin irin tata kaddarar ..
"Ki kwantar da hankalinki kanwata kawai kici gaba da addu'a Allah ya zaba miki abunda yafi alheri kinji,ke da ma ko fara mgnr auren ki abba bayyi ba..
Zainaba tace,ah ah yaya dan Allah nidai ka taimake ni,nasan idan kayi wa abba bayani bazai ki amincewa ba..
Jalal ya rasa me zai ce mata,sbd dai magajin nan amininsa ne kuma yasan waziri ma bazai taba aminta ba ace an bawa dansa zainaba kuma taje ta auri wani can daban..
"Zabba'u ce ta shigo falon da sallama..
Zainaba tace,yadai zabba'u ya na ganki ke kadai?ina juwairiyar?
Zabba'u tayi fuskar tausayi..
Ranki ya dade juwairiya fa bata jin dadi tun kwana biyu da suka wuce..
Hankalin zainaba e ya tashi mutuka,a take ta mike tsaye tana fadin,shine baki sanar min ba?
Zabba'u tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma itace tace min kada na fada miki dan tasan hankalinki ne zai tashi..
Zainaba jiki na rawa tace,muje na ganta..
Da sauri zabba'u ta shiga gabanta, ranki shi dade kin manta bazaki iya shiga rumfar bayi ba..
Zainaba taja tsaki ta koma ta zauna cikin takaici..
Jalal kuwa duk yana saurarensu,hankalinsa ba karamin tashi yayi ba shima..
Dama bata da lafiya ne?
Toh Meya same ta?
A wane hali take ciki yanzu?
Mikewa yayi kawai ba shiri yayi sallama da zainaba sama sama ya fice..
"Gaba daya a ranar jalal tunanin yarda zai saka juwairiya a idonsa yakeyi..yana son yaji ko ya jikinta da sauki ko yayi tsanani?amma bashi da me bashi wannan amsar..
Da yamma magaji ne yazo yaja shi da kyal suka je yin wasan doki..(Polo )
Lkcn daya dawo sashen sa sai ya tarar da khadija a dakinsa tana zaman jiransa...
Tsaki yadan ja yana mamakin nacin wadan nan matan nasa..kullum sai sun kawo kansu wajen miji..mtsw..
"Khadija kuwa tana ganinsa ta saki murmushi, ya jalal sannu da shigowa..
Jalal yace,yauwa a takaice..
Khadija taje ta kamo hannunsa ya jalal wai nayi maka laifi ne?
Jalal ya kalleta,laifin me zakiyi min khadija..?
Ta shagwabe fuskarta..
toh ba naga ne daga ganina da kayi ba sai ka wani daure fusaka,kamar bakayi wani farin cikin ganina ba..
Jalal yayi murmushi ya shafa gefen fuskarta yace..
ba haka bane..kawai dai abubuwa ne sukayi min yawa..
Khadija ta rungume sa,kada ka damu komai zaizo maka da sauki idan akayi sabon na'din (palace counsel)...
*********
"Wasa wasa juwairiya jiki sai daya kai ta har kusan kwanaki biyar bata fita daga cikin rumfar bayi ba tana ta jinya...
Sai dai tana samun sako daga wajen zainaba dan har fulani kanta ta saka aka kawo me magani ta shiga har cikin rumfar bayi ta duba ta..
"Yau kam ta tashi jikinta da sauki sosai tana zaune ne kwanon abinci a gabanta tana ta faman tsakurar sa kamar bataso..
Tunani kawai takeyi yarda take jin zuciyarta kamar tayi tsuntsuwa ne taje sashen yarima ta dan gan sa..
hansai ce ta kalleta duk ta rame tace,juwairiya kodai sai na nemo miki maganin cin abincin ne?
Juwairiya tayi murmushi kada ki damu umma,kawai bakina din ne babu wani dadi shiyasa..hansai ta jinjina kai kawai..
"Mai martaba ina tunanin kawai a kai mutanen nan gidan yari..
"Magaji dake zaune gefen jalal suna cikin fada ya fada..
Ji yayi jalal bai ce masa komai ba,dan haka ya dago yana kallonsa..
Ya rasa meke damun abokin na sa kwana biyu haka bashi da wani nutsuwar kirki kullum se dai ya zauna shiru..
A hankali ya karasa gaban throne din jalal ya dafa shi..
Jalal ya kalleshi da sauri lafiya?
Magaji yace,dan Allah ka fada min abunda yake damun ka..
Jalal yasa hannunsa ya janye hannun magaji daga kafadar shi..yace
Na sha fada maka babu komai dake damuna wai meyasa ka cika naci ne?..
Magaji ya jinjina kai yana bin shi da kallo..
ko yaushe jalal ya daina fada masa sirrin sa?oho...
Kodai ya daina daukarsa amininsa ne?
*********************
"Da yamma juwairiya ta fito can bayan rumfar bayi gaban kogi inda suke wankin kayansu ta tsaya..
Iskan dake kadawa ta shaka...
Murmushi ta saki tana murnar samun lafiyarta,gobe dai inshaAllah zata saka jalal a idonta..
*********************
"Washe gari tun da asuba take ta shirinta..
Jakadiya na lekowa tayi saurin mikewa tace,inna muje na shirya..
Jakadiya tabi ta da kallo kin tabbata jikin naki ya warware?
Juwairiya tace kwarai kuwa inna..
Jakadiya tace toh muje dama nayi kewar ki...
"Suna shiga sashen juwairiya taji zuciyarta tayi wasai..
Da saurinta ta fada cikin dakin..dan jakadiya ta sanar mata ta shiga kawai matan sarki basa ciki..
"Can kan gado ta hangosa a kwance..
Tayi saurin karasawa tana kurawa fuskarsa ido...kamar yadan rame shima..
Gani tayi yana motsa bakinsa..
Bata ankara ba kawai taji yana kokarin furta sunanta..
Juwai....
Tayi saurin kai kunnenta kusa dashi dan ta tabbatar ko sunan ta din yake son furtawa..
Aikuwa dai juwairiya yake ta furtawa..
Washe baki tayi kafin tace a hankali..
Na'am ranka shi dade...
Ga babban mamkinta sai ta ga ya bude idanunsa tangaren ya sauke su akanta..
Ai a tsorace taja baya tana jin kirjinta na bugawa..
Shi kuwa jalal da sauri ya mike ya sauko daga kan gadon ya tsaya a gabanta..yana mamakin ganinta..
Murna sosai ya ziyarci zuciyarsa har baisan sanda yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa ba..
A tare duk suka sauke ajiyar zuciya mai nauyi...
Acikin kunnenta taji yace..
Ina kika shige uhm?
Juwairiya tayi murmushi tana shakar kamshin sa..
Bani da lfy ne..
Jalal ya dago ta daga jikinsa yana kare mata kallo duk ta rame tayi wani irin haske..
_"A Take ya tuna da amaryar sarkin zazzau AMMI,tabbas suna mutukar kama da juwairiya, amma taya hakan ya faru?wata zuciyar tace masa kana mamakin da ikon Allah ne?jalal ya girgiza kai da sauri,tabbas kamanni ne kawai daga da Allah..tunda dai bai ga wata alakar da zata hada matar sarki da kuma baiwar Rumfar bayi ba"_
Lumfashi yaja kamin yace..
Ya jikin naki yanzu?
Zatayi mgn ya sake cewa, ah ah ina zuwa ma dai...
Fita yayi bai dade ba sai gashi ya sake dawowa..
Juwairiya zatayi mgn sai ji tayi jakadiya na sanar da shigowar me magani..
Da sauri ta kalle shi..
Kafin tace..
Mai martaba naji sauki fa..
Jalal ya zauna a gefen gado yana fadin..
Ina so ne kawai na tabbatar....
Me magani ya shigo jalal ya nuna masa juwairiya yace..
ka duba min ita.
Me magani yace..
Na duba ta?ya nuna juwairiya cikin mamakinsa..
Jalal bai tanka masa ba..
Me maganin ya bukaci data zo ta zauna..
A sanyaye taje ta zauna ya duba tan..
Sannan ya tabbatar wa jalal ta samu lafiya...ya amshi kudinsa ya fice..
Jalal ya dawo kusa da ita yace..
Kinga Yanzu na yarda..
Juwairiya ta gyada masa kai sannan ta nufi hanyar toilet..
"Jalal na tsaye yana sakin murmushi sai ji yayi ana sanarwa surayya zata shigo ciki..
Daure fuska yayi a take..
Surayya kuwa na shigowa ta rungume sa cike da murnar ta..tana fadin..
Sarkina kasan kasan yanzun nan na samu wasika daga masarautar mu matar yayana ZAID ta haihu..
Jalal ya tabe baki yace,toh shine zaki fado min daki da sassafe haka?
Surayya ta sake matse shi ajikinta..
Wa nake dashi a duk fadin masarautar nan da zan(sharing)farin cikina dashi idan ba kai ba..
Jalal na shirin mgn sai ga juwairiya ta fito daga cikin toilet idanuwanta