Showing 63001 words to 66000 words out of 83480 words
dai kai fa sarki ne ni kuwa diyar sarkin ce kaga har yanzu umurnin ka dole yayi tasiri a kaina..
Jalal yaja lumfashi...sannan ya samu kansa da furta abunda ke cikin zuciyarsa..
"Nayi kewarki rashin ki a sashena....
Juwairiya tayi mutuwar tsaye...
Dan kalaman shi sunyi wa zuciyarta shigar mamaki..
Yadai da kallon kina mamaki ne?
juwairiya ta gyada kai cike da kunyarsa..
Yayi dariya yana daga kafadar sa..
Ina jiran sakon ki anjima...
yayi gaba cike da tsantsar farin ciki acikin zuciyarsa..
"Taro ya tashi lafiya?baki duk sun wuce masaukinsu...
Jalal da magaji tare da sauran bayin da sukazo daga kasar daura duk suna sashen bakin inda aka sauke su..
Magaji sai mamakin jalal yakeyi..
Ganin yarda ya wani saki rai sai faman fitar da murmushi yakeyi tun dazun.
Magajin ya dawo kusa dashi yana fadin..
Ni kuwa AMALE dazu kaga diyar sarkin kanon nan?
Ni sai nake gani kamar nasan fuskarta a wani wajen amma na kasa tunawa...
Jalal yayi saurin kallonsa..
Magaji yace,ko da yake ma me yasa zan tamabayeka kai da kayi tafiyar ka..
Jalal ya mike yana fadin..
Bari na shiga na watsa ruwa...
Magaji ya girgiza kai wani abun sai AMALE..
"Juwairiya ta dauko wasu kaya ta saka bayan ta fito daga wanka..
Sai data gama shirinta tsab sannan ta kira hanne...
Tace..
Hanne aiken ki zanyi dan Allah..
Hanne tace toh ranki ya dade inaji..
Juwairiya tayi dan jim kafin tace..
Kije sashen da aka sauki bakin mai martaba inaso ki sanar da sarki jalal ya same ni a bayan sashena yanzu..
Hanne ta kura mata ido..
Juwairiya tayi saurin cewa..
Gaisawa kawai zamuyi dashi..
kuma ki fada masa sakon a cikin sirri kinji?
Hanne tayi dariya na gane ranki ya dade kada ki damu..
Hanne na fita juwairiya ta fada kan gadonta tana murmushin murna..
Yau dai zata kasance da jalal dinta..
Allah yasa ya sanar da ita amsar da ta dade tana son ji daga bakinsa...
"Lkcn da hanne ta shigo sashen bakin wani bawa ta tarar ta fada masa tana son ganin sarki jalal..
Bawan yayi sallama a cikin falo a lkcn jalal da magaji na zaune suna fira..
Bawan yace wata baiwa ce tazo yanzun wai tana son ganin ka ranka shi dade..
Jalal ya mike da saurinsa..
Ya kalli magaji..yace
Ina zuwa..
Magaji yabi sa da kallon tuhuma..
Jalal ya fice da saurin sa...yana ji wani irin farin ciki na ratsa sa..
"A tsaye ya tarar da ita ta juya bayanta..
Jalal ya saki murmushi sannan ya karasa wajenta da sallama..
Ta juyo suka hada ido dashi..
A tare suka sakarwa junan su murmushi..
Jalal ya bita da kallo up n down..
Tana sanye ne da doguwa riga kalar ja da baki sai mayafinta kalar fari da digon baki..sai kamshi take bazawa..
Jalal yace..
Kin canza..
Ta kalli jikinta da sauri..
Amma kinfi kyau a haka..
Ta lumshe ido ta bude kafin tace nagode..
Jalal ya gyara tsayuwarsa yace..
kamar yarda nayi miki alkawari zan fada miki amsar tambayar ki duk lkcn da muka sake haduwa..
Ya shafa sajen fuskarsa yana fadin..
Tun a baya ban gama fahimtar abunda yasa nake kyautatamin miki ba,sai bayan wani lkc da zuciyata ta shaku dake...
Juwairiya ta kura masa ido..
Jalal ya kalleta cikin ido yace..
Juwairiya....
Yarda ya furta sunan sai da tsikar jikinta ya tashi..
*INA SONKI.........*
Wani irin yanayi taji wanda bazata iya fassara shi ba...
Zuciyarta nata harbawa..dum!dum!dum!
Jalal ya dawo daf da ita ya tsaya..
Kece mace ta farko da zuciyata ta fara kamuwa da sonta..
Bansan dalilin da yasa nake sonki ba..
Amma tunda idanuwana suka ga wannan kyakkyawar fuskar ta ki a wancan lkcn na kasa sukuni...
Na rasa meke damuna..
Bani da tunani sai naki..
Ina mutukar jin dadin kasancewa dake....
Juwairiya.....
Ina kuma fata kema zuciyar ki ta kamu da son JALAL ko?
Wani irin kunya ne ya lullube ta..
Tayi saurin juyawa zata gudu..
Ya cafko ta da karfi yana rungume me a jikinsa...
A cikin kunnenta taji yace..
Ko bakya son MIJI me mata biyu ne?
juwairiya taji wani iri har cikin zuciyarta a take kuma ta tuna da irin wulakancin da surayya tayi mata..
Sai Ta samu kanta da turo masa baki ta kwace jikinta daga rikon sa..
Jalal yabi ta da kallo..
Ta kalleshi..tace
Kasan dai yanzu ba da bane ba ko?dan ina yancina..!
Jalal dai kallonta yake..cikin mamakin canzawarta farat daya(but he like ha courage)..
Taci gaba..
Toh kada ka kara tuna min da wadan nan matan naka..
Jalal ya rike kugu..yana fadin..
Eyyyeeeeh duk kishin ne haka?
Juwairiya tadan harare shi..
Ba wani kishi so nake kawai ka bari dan bana so..
Jalal yace,toh ina dai jiran amsata zuwa gobe kafin na tafi..
Juwairiya tace wace amsar?
Jalal ya rike baki,lallai yarinyar nan haka kika koma?
Juwairiya tayi murmushi tace eh din..
Jalal yasa hannu ya fisgo ta zuwa jikinsa..
Kallon cikin idonta yayi..yace..
Ina ganin SONA da kishina a cikin wadan nan kwayar idanuwan naki...
Dan haka ina jiran amsata sbd bana son wani yayi min shigar sauri kin gane?ya kashe mata ido daya..
Juwairiya ta samu kanta da gyada masa kai..
Yace yauwa ko ke fa..
Muje na maida ke sashen naki..
"Hannayensu sarke dana juna har suka iso kofar sashen nata..
Ya sakar mata hannun sannan ya matso zuwa gabanta..
Ji tayi kawai ya kai wa goshin ta sumba (peck)
Ta runtse idonta ta budesu ahankali tana jin wani irin abu ya na tsirga mata..
Jalal harde hannayensa yayi yana kallonta...
ki shiga se da safe..
Ta gyada kai amma ta kasa motsawa ta tafi..
Jalal ya kamo hannunta..
Ko baki gaji da kallona bane..
Juwairiya ta samu kanta da sake gyada masa kai..
Murmushin murna yayi..
Ya sa hannu a habar ta ya dago da fuskarta..
Suna kallon junan su..
Yace,kada ki damu akwai ranar da zaki gaji da kallon wannan fuskar tawa..
juwairiya tayi murmushi..
Hannunta yakai kan kirjinsa tana jin yarda zuciyarsa ke bugawa..
"Juwairiya kina jin bugun zuciyata?
Ta kyafta masa ido..
Idan ban same ki ba..
ban san yarda rayuwata zata kasance ba...
juwairiya tayi saurin saka hunnu saman lebensa...
Tace..
Shiiiish
Jalal yayi dariya..
Toh shiga kije ki kwanta...
Tace toh sai da safe...
ta juya ta shige ciki cike da farin ciki marar misaltuwa...
TEAM RUMFAR BAYI....
[9/25, 7:53 AM] 0mer Farouk: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 37
Wattpad @afreey101
*********************
""""Har jalal ya koma masaukinsa bai bar sakin murmushi me kayatarwa ba..
Magaji kam har ya fara gyangyadi yaji dawowarsa..
Yayi saurin mikewa yana kallonsa..cikin mamakin yace
Allah ja zamanka wai ina kaje ne haka..naji shiru tun dazu..
Jalal ya dafa kafadarsa kawai yana sakar masa murmushi..
ya shige cikin daki yana ji inama daya kulle idonsa ya bude yaga har safiya tayi..
"A wajen juwairiya ma tana shiga sashen nata sukaci karo da hanne tana kokarin fita neman ta jin har lkcn shiru bata dawo ba..
Sai gani tayi juwairiya ta wuce ta bata ko lura da ita ba..tana rungume da hannayenta se murmushi takeyi...
Tayi saurin bin bayanta tace,uwar dakina!
Juwairiya tayi firgigit ta juyo ta kalleta..
Hanne ta kyalkyace da dariya..
Juwairiya ta turo baki tayi ciki da gudun ta
har ta kwanta a kan gadonta me laushi murmushi ne ke fita daga bakinta..
Ta jawo filo ta rungume sa tsam tana tunano fuskar jalal da yarda yake lumshe idanuwansa idan yana mgn..
Lallai Allah me yarda yaso,wai ace sarki kamar jalal mai ji da kyau da farin jini a wajen mata shine ya so Baiwar kamar ta?a wancan lkcn..
Idonta ta murza,tabbas tayi dacen masoyi...
Wanda ya sota batan mulki ko wani abu data mallaka ba..
Tunani sosai ta zurma har barci mai dadin gasken yayi awon gaba da ita.
**********
"Washe gari..
"Da sassafe jalal ya tashi yayi shirinsa tsab..
dan ba karamin kagara yayi garin ya waye ba..
Koda magaji ya farka se ya tarar dashi har ya kammala komai shi kawai yake jira..
Magaji ya mike cikin mamaki yana fadin..
AMALE badai duk zangin komawa iyalin bane haka?
Jalal ya harare sa..yace
Kayi ka shirya bani lkcn batawa malam.
Magaji yace,toh ranka ya dade...an gama..
"A wajen Juwairiya kuwa..
Har makara tayi sallar asuba sbd irin dadin da barcin yayi mata..
har tayi wanka ta shirya amma ta rasa hanyar da zata samu haduwa da jalal dan ta fada masa amsar sa..
Tasan ko tace bata jinsa a ranta toh karya ne takeyi..
Hanne ce ta shigo dakin tace da ita..
Uwar dakina yanzu nan gimbiya amina ta aiko wai kije sashen ta ku karya a can tare..
Juwairiya ta jinjinar da kai sannan ta mike ta saka alkyabba a saman kayan jikinta suka fito daga cikin sashen..
Har sun fara tafiya juwairiya ta kalli hanne..tace..
Wai ni hanne Ta ina ne sashen bakin yake?
Wata hanya hanne ta nuna mata..
Juwairiya tace,muje ki rakani toh..
Hanne tayi saurin shan gabanta..
Ah ah ranki ya dade ba girman bane ace kinje har can don neman sa ba..
Juwairiya taji kunya ta kamata,tace toh ya zanyi?hanne
Ina so ne na fada wani abu kuma kinga babu yarda zamu hadu dashi yau sbd komawa zayyi kasar su.
Hanne taja hannunta zuwa bayan wani gini tace,jirani a nan ranki ya dade ina zuwa...da gudu tabar wajen juwairiya tabi ta da kallo..
"""" Juwairiya na nan a tsaye tana jiran dawowar hanne sai ji tayi an kamo hannunta daga baya..
Kamshin sane kawai ya daki hancinta..
Ta saki murmushi babu shiri..
Jalal ya rankwafo da kansa wajen kafadarta yace cikin(husky voice)..
Yanzu har kina da ikon sakawa a kira miki sarki kamar ni ko..
Juwairiya ta juyo da sauri suka hada ido dashi..
Jalal se da gabansa ya fadi ganin irin kyan da tayi....
Yace...
Fadi inajin ki..da gani bakin nan naki akwai mgn ko..?
juwairiya ta rufe fuskarta da tafin hannunta..
tace toh ni me zance?.
Jalal yayi dariya..
Kunya ta kikeji ne haka?
Juwairiya ta gyada masa kai..
Yasa hannunsa ya cire hannayenta daga kan fuskar ta yace..
Toh bari na taimake ki..
KINA SONA?
juwairiya ta kura masa ido kafin tayi kasa da kanta da sauri tana murmushi..
Jalal ya sauke ajiyar zuciya..
Naji dadi sosai..sai ki shirya komawa KASAR DAURA cikin yan kwanankin nan..
juwairiya ta dago da sauri..
Yanzu fa idan ta aure shi dole ta koma masarautar su,masarautar da tayi rayuwa a matsayin BAIWARSU..
Jalal ya kamo hannunta..
Kada ki damu...ina tare dake..
juwairiya tayi shiru...kafin tace..
Ka gaida min da zainaba sannan ka fadawa jakadiya halin da nake ciki a yanzu dan ta sanarwa su umma nasan hankalin su a tashe yake..
Jalal ya gyada kai,toh ranki ya dade..
Dariya sosai ya bata..
Jalal ya kura mata ido yana kallon fararen hakoranta..
Zan tafi yanzu..
Juwairiya taji wani iri har cikin zuciyarta..
Kai ta gyada masa..
Jalal yace,zan shiga fa'dar abbanki muyi sallama dashi..
Ta sake gyada masa kai..
Shi kanshi ji yake kamar kada ya tafi..
Juyawa yayi ya fara tafiya..
Juwairiya tabi bayan da kallo tana ji kamar taje ta rungume sa..
Dauke kanta tayi jin hawaye na niyyar tarowa a cikin idonta..
Bata ankara ba taji dumin mutum a jikinta..
A tsorace ta dago..
Sai ganin jalal tayi rungume da ita..
Ta sauke ajiyar zuciya me nauyi..
Cikin murya me sanyi tace..
Ranka ya dade kada kuyi rana fa?
Jalal ya dago daga jikinta..yace
Indai dan na kasance dake ne muyi dare ma ba rana ba..
Sakin baki tayi tana kallonshi..
Ta lura yanzu fa bayajin kunyar fada mata wasu kalaman..
Jalal yayi dariya ya saka hannu ya rufe mata bakin kafin yayi gaba da saurinsa..
""""A fa'dar sarki abu-turab....
Sarakuna ne ke bankwana dashi dan komawa kasar su..
Sarkin GWANDU ne ya samu shamaki yayi masa rada a kunne..
Shamaki ya bude baki sosai yace..
Allah ya karawa Sarki lafiya..
Sarkin Gwandu yace a gaya maka..
Sun ga SARAUNIYA JUWAIRIYA a jiya kuma suna son hada zumunci me karfi dakai..
Wato dai ana nemar wa YARIMA FAHAD auren SARAUNIYA JUWAIRIYA...
"Caraf kalaman shamaki suka riske Sarki Jalal dake kokarin shigowa cikin FADAR...
Gabansa ne yaji ya fadi..rass,aure!!!!juwairiya! !innalillahi wa'inna ilaihir raji'una"kalmar da yake ta ambato kenan...
Ya karaso ciki da saurinsa..
Ji yayi Sarki abu-turab yana fadin..
Bana cikin wadan nan sarakan dake yiwa ya'yansu auren dole..
Dan haka duk YARIMAN dake son DIYATA yazo nan da karshen watan nan zan hada taro na musamman ga masu neman ta dan ta zabi wanda yayi mata..ina tunanin hakane adalcin da zanyi mata..
Wata irin ajiyar zuciya jalal ya sauke,lallai ya jinjinawa sarki abu-turab tabbas yana kaunar diyar sa sosai...
Dole ne ya tashi tsaye..
In ba haka ba juwairiya na dab da subuce masa...
******************
"Lkcn dasu jalal suka iso masarautar daura..
Sashen gimbiya kilishi ya zarce dan yasan ita kadai ce zayyi wa dadin baki ta shige masa gaba a wajen auren da yake son yi...
Hansai ce ta gabatar masa da abinci kala kala...
ya tausaya mata sosai dan ganin yarda duk ta rame sbd tunanin juwairiya..
Sai daya ci abinci ya koshi sannan ya maida hankalinsa kan gimbiya kilishi..
Yace
Umma mgn nake so muyi dake..
Kilishi ta gyara zaman ta tace ina jinka jalal...
Jalal yaja lumfashi kafin yace..
Umma aure nake so na kara..!
Kilishi ta tsare shi da ido..
Jalal yace,umma dan Allah ki shige min gaba wajen abba dan ya amince..
Kilishi tace,ban ki ba jalal dan nima nayi tunanin hakan sai dai har yanzu ban samu wacce nake ganin ta kai zama matar ka ba..
Jalal ya shafa gefen fuskarsa..
Umma jiya na hadu da wata a can kasar kano..
Kilishi ta gyara zamanta..
Diyar wacece ita?yar wacce (family)din ce?
Jalal(with full confidence)yace..
DIYAR SARKIN KANO ce umma..
Wani irin dadi ne ya lullube kilishi..tace da kyau AMALE haka nake so..
Nidai indai ta ni ne na amince dari bisa dari kuma zanyi kokari na shawo kan mahaifinka kada ka damu..kaji?
Jalal yayi murna sosai sannan ya mike ya fice..
Sai daya shiga sashen khadija ya duba jikinta kafin ya fito zuwa sashen sa..
Umayma dake lebe ta ciji yatsa..
Lallai dole ta sanarwa uwar dakin nan wannan zance..
"Sashen sa ya koma cikin tsantsar farin ciki..
Jakadiya ce ta shigo tare da kuyangi dan hada masa ruwan wankan sa..
Ganin yarda yake cikin farin ciki jakadiya ta kasa hkr tace..
Allah ja zamaninka wannan farin ciki da kake ciki Allah yasa ya dore har karshen rayuwar ka..
Jalal yayi dariya amin jakadiya,kema ina da mgn dake ai jakadiya..
Jakadiya ta kalli kuyangin dake fita daga dakin sun gama aikin su..
Tace ranka shi dade ina jin ka..
Jalal ya dawo kusa da ita yana kasa da muryar sa sannan ya fayyace mata komai kamar yarda juwairiya ta sanar mishi..
Jakadiya zubewa tayi kasa dan kafafunta ma kasa daukar ta sukayi..
Yanzu dama diyar sarki ce juwairiya? Lallai idan kama raye zaka sha mamaki..
Jalal yace,jakadiya inaso mu boye wannan sirrin har sai ranar da ta dawo gidan nan a matsayin matata..
Jakadiya ta sake kallon jalal cike da murnar ta,tace ALLAH ya nuna mana wannan ranar AMALE...
************
Juwairiya na sashen ta suna tare da yarimaADO ne yana koyar da ita karatu..
Hanne ce ta shigo ciki tace da ita wai wani mutum na son ganinta yana waje..
Juwairiya cikin mamaki ta mike ta fito..
Ga mugun mamakin ta BABANTA ne ta gani a tsaye..
Ihun murna ta saka taje wajen sa tana fadin..
Baba ashe ka dawo?
Se dana tambayeka aka cemin mai martaba ya aike ka can kasar MALI.
Babanta juwairiya yayi murmushi yana kare mata kallo dama zuciyarsa sai data bashi juwairiyar suce ake mgn..
Allah mai iko ashe asalinta na nan kasar kano inda yake rayuwa..
Yayi murna kwarai da ganinta a haka..
Juwairiya a take tayi sashen gimbiya amina dashi ta gabatar mata dashi..
Sannan ta saka sarki abu-turab ya yantar dashi..
Zo kuga murna wajen bawan Allah nan..
Washe gari da sassafe kuma ya shirya sai kasar daura wajen yan uwan sa..
*************
"Karshen wata yazo sarki abu-turab da gimbiya amina suna ta shirye shiryen taron zabar mijin juwairiya da za'ayi.
ita kuwa tunda aka sanar da ita sai taji wani iri dan kuwa ita ta riga ta san wanda take so ...
"Ranar gabatar da taron gimbiya amina da jamila sune gaba wajen shirya juwairiya..
Kai kace wata amarya ce dan ba karamin kyau tayi ba,ga kaya masu tsada da sarkar gwal data sha..
"Kilishi ta shigewa jalal gaba a wajen abbansa har ya amince da mgnr..
Ranar tafiya kuwa da kansa yace wa jakadiya ta shirya da ita za'a tafi,sannan ya dauki hamza dan a lkcn magaji yayi tafiya tare da waziri baya gari...
Lkcn da suka isa kasar kano,masarautar har ta fara cika da yaran sarakuna daga kasashe daban daban..
Jalal kuwa kallonsu kawai yakeyi dan kuwa yasan yayi musu zarra... ya siye zuciyar wacce suka zo neman soyayyar ta..
Abu-turab da kansa ya saka aka shigo da juwairiya cikin Fadar..bayi na biye da ita a baya ..
Wajen zama na musamman aka ware mata,jakadiya da su gimbiya amina na gefenta suma..
Lkcn da aka fara kiran sunayen (princes)din juwairiya addu'a kawai takeyi Allah yasa sarki jalal ya zo yau shima..
Duk wanda ya shigo idan jakadiya ta tambayeta se tace ah ah bai mata ba..
Gimbiya amina tadan rankwafo wajenta tace..
Juwairiya ki kwantar da hankalinki ki zabi wanda kika ji ya kwanta miki.
Ta gyada kai tana fidda ran zuwan jalal...
"Kamshinsa kawai taji ya daki hancinta..
Ta kurawa kofar shigowa ido..
Ai kuwa sai ga hamza a gaba jalal na bayansa jakadiya na biye dasu a baya..
Wani irin lumfashi ta saki da karfi..
Jalal kuwa kura mata ido yayi ji yake kamar yaje ya dauke ta daga inda take zaune..
Ganin yarda duk mazan dake wajen sai wani faman kallonta suke..
Shamaki na gabatar da sarki jalal jakadiya ta tambayi juwairiya (opinion ) dinta akan sa..
juwairiya ta saki murmushi sannan ta gyada kanta cike da tsananin kunya..
Ai a take fada ta hau kida aka hau busa algaita..matan bayi na ta ku'da wajen duk ya karade da kide kide..
Sarki abu-turab ya mike cike da kasaita da murna sosai..ya sanarwa jama'arsa shi Sarki abu-turab ya bawa sarkin daura JALALLUDEEN auran diyarsa sarauniya JUWAIRIYA ...
Ihu da shewa aka hau yi..
Gimbiya amina ta rungume juwairiya tana murna sosai..
Jalal baki yaki rufuwa zuciyarshi yaji wasai,sai gaisawa ake dashi ana shi murna..
"Da Yamma mai martaba Abu-turab ya saka aka gyara can sashen da karamin falonsa yake dansu juwairiya su kebence su fahimci junansu(date)
Gimbiya jamila taja juwairiya zuwa sashen ta..
Ta shiga bata shawarwari akan yarda ake fitar da lafazi me dadi da kuma yarda mace zata kama kanta a gaban (suitor)dinta..
Ta shiryata cikin kayan alfarma kafin hanne tazo suka fice..
"Juwairiya na kawowa gaban kofar falon jakadiya tayi saurin tarar ta..
Murna sosai sukayi da ganin junan su,juwairiyata rungume jakadiya tana tambayar ta ko ya su ummanta suke..
Jakadiya tace,kowa na nan kalau,ai babanki ma ya dawo..
Juwairiya tayi murmushi tace,nayi kewar su dayawa..
Jakadiya tace,ai kin kusa komawa garesu,yanzu ki shiga ciki yallabai yana jiran ki..
"Lkcn data shiga falon jalal na zaune a saman kujera cushion...
Ya dago ya zuba mata ido har ta samu waje itama ta zauna a kujera me fuskantarsa..
Irin fadin farin cikin dake mamaye a cikin zukatansu bata lkc ne..
Jalal yayi gyaran murya..
Ta dago ta kalleshi..
Jitai yace
Nagode....juwairiya
Tayi murmushi..
Kafin tace itama...
Nima haka...ranka ya dade
Jalal yayi murmushi..
Kafin ya sake fadin..
Kinyi kyau..
Ta dukar dakai se yayi tace...
Kaima haka...
Amma kin fi ni ai tunda kika siye zuciyar mazaje dayawa..
juwairiya