Showing 9001 words to 12000 words out of 83480 words

Chapter 4 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

973

uku...
Juwairiya ta jawo wani itace ta rike tana jira wanda ke bin nasu ya karaso wajen ta buge shi...

       Tafiya yake yi yana waige waige yan matan daya biyo daga wajen taro yake nema ina suka shiga ne?
     Baiyi aune ba sai dai yaji saukar itace a bayansa...

  Matse bakinsa yayi ya juyo yana musu kallon mamaki..
Gaba daya jikinsu rawa yakeyi..
Zainaba ce tayi saurin cewa..
Waye kai?meyasa kake bin mu?
Mustapha ya daga hannunsa irin surrender dinnan yace..
Kuyi hakuri yan mata dama zuciyata ce kuka taho da ita shine nake binku domin an amso ta..

Kallon juna sukayi,juwairiya ta shiga gaban zainaba wai ita nan tana kare tane..
Tace,malam kasan kuwa dawa kake mgn,gimbiya zainaba ce fa DIYAR SARKI kuma uwar dakin juwairiya...
Mustapha yace,madalla yanzu zan dan samu nutsuwa tunda na ji sunan masoyiyar tawa ZAINABA....yaja sunan yana lumshe idonsa..

Da kallo suka bishi..balle zainaba dake ta lekowa tana karewa fuskar shi kallo..
Kyakkyawa ne ,chocolate color kuma yana da tsayi sosai se de siririne..
    Juwairiya zatayi mgn zainaba ta dafa ta..

Mustapha yace,gimbiyata Allah yasa wani bai min shigar sauri ba ko,ya fada hade da karkace kansa..
Zainaba bata san lkcn da murmushi ya subuce mata ba sannan ta girgiza masa kai cike da kunya ta juya da gudu tayi gaba..
Juwairiya cike da mamaki tabi bayanta..

*************
'Da safe juwairiya na gani zaune laure na mata kwan'tar(tsifar)kai..

Laure tace,kedai yarinyar nan anyi kazama wlh kitso se ki barshi har kusan wata daya,gashi Allah ya baki gashi amma kwata kwata bakya kula dashi.. wai ni yaushe rabon ma da ki wanke shi ne?

Laure jin ita kadai keta zancenta yasa tadan kai mata duka..
Bakya jina ko?
Juwairiya ta kai hannu wajen da laure ta duke ta,ta turo baki haba goggo laure ina jinki fa wlh.
Laure tace karya kike,wai tunanin menene kikeyi ne haka?

Juwairiya tace babu komai,sai kuma ta mike da sauri tana kwace kanta daga hannun laure..
Goggo laure ina zuwa,ta shiga daki tayi shirin ta ta fito da gudu tayi hanyar sashen zainaba...

Tana shiga ta tarar da ita a tsaye,da sauri ta karasa wajenta lafiya ranki ya dade?..
  Zainaba ta sauke ajiyar zuciya yauwa dama ke nake ta jira,zauna..kiji....

Juwairiya ta zauna tana saurarenta.
Zainaba tace,dazu wannan saurayin ya turo min da wasika..

Juwairiya ta saki murmushi me yace ranki shi dade nasan dai da gani sonki yakeyi..ko?
Zainaba ta rufe fuska wai haka yace..

Juwairiya tayi dariya kasa'kasa dan ta lura uwar dakin tata ma ta fara zurmawa dayawa..
Zainaba ta gyara zamanta sannan ta buga tagumi,amma kinsan me yace?

Juwairiya ta gyara zaman itama ah ah se ranki ya dade ta fada min.
Zainaba ta turo baki..
Wai idan na amince masa toh naje da Fure (flower) na same sa a zaure na biyu yana jirana kafin su tafi..

   Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu ranki ya dade akwai wani fure me kyau dasu yasira ke cirowa zan samo miki shi..
Zainaba tayi murmushi, yauwa juwairiya yi maza kije toh..
Juwairiya na murmushi ta mike ta fita..

"Sashen hamza ta nufa dan anan ne yasira ke aiki,ta jawo ta waje ta tambayeta ina ne take ciro furen?
Yasira tadan waro ido,juwairiya yaushe rabon da ki ganni da wannan furen?yanzu fa kinsan an tare sashen..

Juwairiya tace,wai dama sashen waye?
Yasira tace,sabon sashen matar yarima jalal ne..
Juwairiya hakanan taji gabanta ya fadi,ta juya kawai tayi gaba..

Tsaye tayi a kofar shiga sashen,tunani takeyi ko ta shiga ko kada ta shiga,bata son ko kadan ta hadu da wannan yariman...
   Leke tayi karaf ta hango itaciyar furen kuma akwai dayawa a jiki...
  Taja lumfashi sannan kai tsaye tayi wajen tana waiwayen bayanta..
  
*************
Yarima jalal ne na gani a tsaye gaban surayya dake ta kwasar baccinta a takure.
Ya kura mata ido ko tunanin me yakeyi oho..
Haske ya gani yana ratsuwa dakin daga window yana taba fuskarta..

  Juyawa yayi yazo gaban window din yana kokarin rufe labulen ya hango ta..

  Dauke kai yayi da sauri dan kuwa konannen sashen fuskarta yaci karo dashi ,zuciyarshi yaji ta baci,ya tsani yarinyar can baya son ganin irritating face dinta ko kadan,duk da ze iya kirga ganin ta da yayi a masarautar..

   Ya juya kawai ya fito a fusace dan bai ga me ya kawo ta sashen ba..
   Yana fitowa bayin dake tsaye bakin kofar suka shiga gaisar dashi..
Bai amsa musu ba kawai yayi waje abunsa..

******
Juwairiya ta ciro furen daya mai kyau sosai..
takai hancinta tana shakar kamshinsa me sanyi..
Ta tabbata dole ne zainaba ta yaba mata idan taga turen..
Har ta juya zata fice taji ance..

    Me ya kawo ki nan!

Da sauri ta tsaya tsak..
Cikin kasaita ya karasa gaban ta yana yatsine fuska..
Juwairiya ta zube kasa tana sunne kanta dan tasan babu abunda ya tsana kamar ganin fuskarta..

Dama...dama..uhm..na...
Yarima ya daka mata tsawa..
Ki bude baki kiyi min mgn!
Bana hane ki da nuna wannan fuskar taki a inda kika san ina nan ba?

Juwairiya tace,afuwa zanka shi dade uwar dakina zainaba ce ta umurceni da samo mata wannan furen ta nuna masa furen dake hannunta..
   Yarima ya tabe baki,ki ba'ce min daga gani...
yana gama fadar haka ya juya yai tafiyar shi..
Juwairiya tabi bayansa da harara sannan ta mike ta kakkabe jikinta tayi gaba.......

***********************
Pls share
Comments
And
Vote
[9/18, 3:13 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
NA Afrah bhai
Page 8
Wattpad @Afreey101

*************************

'Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita a tsaye sai safa da marwa takeyi.
Juwairiya ta mi'ka mata furen dake hannunta, ta amsa tana sakin murmushi me kayatarwa,gaskiya furen nan yayi min kyau sosai,se de akwai wata matsalar kuma juwairiya.. ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..

     Juwairiya tace,matsalar me kuma ranki ya dade ba dai har sun tafi din ba?

'Zainaba ta girgiza kai,dazun ne fulani ta aiko min da sakon cewa kada na fita ko ina  zata aiko min da wata mai magani ta dubani akan yawan ciwon cikin nan da nake fama  dashi ,kin kuma san halin fulani, har fa wani bawa ta ajiye a kofata wai dan kada na gudu sbd bana son magani..yanzu ya za'ayi na fita kenan?

         'Juwairiya tadanyi tunani kadan sannan tace inda ranki ya dade ba zata damu ba ina da shawara..
Zainaba tace da gaske?
Juwairiya ta gyada kai ..
Zainaba tace fadi muji..
Juwairiya tace ko naje na sanar dashi bazaki iya fitowa se shi din yazo nan..

Zainaba ta ware ido...
Ah ah bana so yazo nan juwairiya..ta karashe mgnr a shagwabe tana kallon juwairiyar..
Can kuma tace,yauwa! Tasa hannu taja juwairiya zuwa dakinta...

'Cire.....ta fada kai tsaye..
Ciki da mamaki juwairiya ke kallonta..me zan cire ranki shi dade ?
Zainaba ta nuna kayan dake jikin juwairiya..cire kayanki ki bani..
A tsorace juwairiya tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma.....

Zainaba tayi dariya,ba ina nufin ki tu'be min ba dan naga jikin ki ba..
Ah ah ina so ne muyi canjen kayane kawai kin ga babu wanda zai san ni ce na fita bake ba ko?

    Juwairiya ta gyada kai,wato wayo zakiyi wa fulani ko?amma idan aka kama mu fa?ni gsky tsoro nakeji..
Zainaba ta murmusa kada ki damu bazan jima ba zan dawo,kedai kawai cire kayan ki bani..

Juwairiya a sanyaye ta cire kayanta,zainaba ma ta cire nata ta bata..
Juwairiya tabi kayan da kallo,ina zata iya saka wadan nan kayan?
Ta girgiza kanta,ranki shi dade bani da matsayin da san saka wadan nan kayan..
Zainaba ta harare ta,amsa!
Kuma umurni nake baki daki saka su yanzun nan!
Juwairiya ta amsa a tsorace..
Tana kallon zainaba bata nuna wani kyama ba ta saka nata kayan tana dariya tace,lallai ke kam wannan kayan naki ashe walawa kike yi sosai..(ta fada tana jujjuyawa cikin katoton rigar juwairiya )

Juwairiya dai da kallo kawai take bin ta,a sanyeye ta saka kayan itama atamfa ce riga da zani sai wata alkyabba ja da ruwan madara,ita kanta tayi mamakin yarda kayan suka amshe ta....
Zainaba tabi ta da kallo,lallai juwairiya Allah yayi mata baiwa dayawa,se de kawai yanayin data tsinci rayuwarta ne...
     Zainaba tace,toh ni na tafi,ta dauki furen ta tana sake fadin,babu wanda zai gane ni ce,ta saki murmushi tayi gaba..

juwairiya ta zauna a takure tana tunanin idan wani ya shigo fa yanzu tasan tabbas kashin seya bushe..
    Motsin dataji ne a waje ana sanar da shigowar turaki yasa ta saurin komawa shinfidar zainaba ta kwanta hade da juya bayanta ta rufe rabin fuskarta..

   A tsanake ya shigo falon cike da takonsa yana mamakin rashin ganin juwairiya da bayyi ba..
    Yan matan fulani naji mun kusa hutawa da jinyar ciki ko?dazu fulani ke sanar min an kawo me magani daga cikin katsina..

     Juwairiya tayi wiki wiki da ido,bata so ko kwakwaran motsi tayi turaki ya gano ita ce..
Turaki ya zauna yana mamakin shirun da zainaba tayi masa..
To wai ko barci take ne ?
Yana wannan tunanin ya mike har ya kai bakin kofa yace, ko ina kawarta ta tayi yau oho..

   Juwairiya najin fitar sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike zaune,se a lkcn ta nuna da inda take zaune(wato akan kilisar zainaba ),ta mike da sauri tana sake kallon shigarta,tabbas bata taba saka kaya irin wannan ba,ta dan murmusa zataso ummanta dasu jakadiya su ganta a cikin irin wannan shigar..
Wani tunani ne yazo mata..
Da sauri naga ta shige dakin zainaba ta dauko mirror tana kallon kanta..

    Ita kanta wani lkcn idan taga fuskar ta a haka tsoro take bata..
Hannu tasa a hankali ta fara goge tabon har kyakkyawar fuskarta ta bayyana..

    Ta kurawa fuskarta ido..
Motsi taji daga falon..
Da sauri ta mike jiki na ba'ri ta fito zuwa falon tana leke...
Sai ji tayi bawan dake waje yana daukar izinin zainaba  dan zagawa bayan gida..
  TOh!
Kawai ta fada a da'ke sannan tace,wai ina zainaba ta tsaya ne?(tayi mgnr kamar ta fashe da kuka)
Gani nayi Tadan jawo hular alkyabbar ta rufe rabin fuskarta tana fadin,dole ne naje na dawo da ita tun kafin asirin mu ya tonu,ba tare da wani tunani ba tayi waje da saurinta..

**************
'Surayya na tashi daga barci taga wayam babu yarima a dakin.
tsaki taja cike da takaici,wai yau itace gimbiya surayya ake wulakantawa har haka,wulakancin ma wai daga namiji..

Ta juyar da kwayar idonta tana tuna irin  samarin dake tururuwa a wajen neman aurenta,amma gashi sbd wata tsohuwar abokantaka dake tsakanin mahaifinta da mahaifin yarima jalal an kawo ta nan se wulakanta ta akeyi..

      Ta kalli shinfidar gadonsu cike da takaici,ta tabbata duk bayin da zasu shigo da kuma yan uwanta da zasu zo mata bankwana toh gulma ce zata kawo su dan  ganin  yarda daren farkon ta da yarima ya kasance...

Abu daya data tsana a rayuwarta shine a ga kamar bata isa ba (she hates pple downgrading ha),bata son ko kadan a raina ta,sbd ta mallaki komai a rayuwarta, tana da kyau,gata diyar sarki,yanzu kuma matar yarima me jiran kujerar mulki...

Wani tunani ne yazo mata..
Ai da sauri Ta mike da ta tube duka kayan dake jikinta tas..
Sannan tasa hannu ta hargitsa shinfidar gadon,ta dauko yar karamar wuka dake cikin tiren fruits ta hawo kan gadon tasa wukar a finger dinta tana runtse ido ta tsakawa kanta wukar kadan'sannan ta samu jinin ta dake ta di'qa ta shiga shafawa a wani bangaren gadon....

       Yamutsa gashin kanta tayi dayasha gyara sannan ta ja bargo ta rufe kanta tana kuka kasa kasa..(yarima yayi kadan ya jawo mata raini,dolene ta nuna masa wacece SURAYYA)

   'Bayi ne tare da yakumbon ta suka shigo dakin da jakadiya a bayansu..
   Ganin halin da take ciki yasa duk suka saki murmushin murya suna gyada kai cike da gamsuwa..

Yakumbo ta karasa wajenta tana dago da ita zuwa jikinta..
Sannu surayya,sannu UWAR GIDAN YARIMA JALALLUDEEN...
ai duk mace idan tayi aure dolene ta fuskanci wannan  daren farin cikin,amma daurewa zakiyi kinji?
Surayya dake sunne kai ta gyada kai,yakumbo ta ciro zanin shinfidar  ta mikawa jakadiya dake ta gyada kai cike da farin ciki,lallai yarima an  girma...

     Jakadiya na amsar zanin da saurinta ta karasa sashen gimbiya  kilishi dan aiwatar da umurninta..

    Uwar soro na ganin jakadiya ta karaso sai washe baki takeyi..
yasa tayi sauri wajen fadin isowarta cikin kirarinta masu tsada...

    'Gimbiya kilishi na a kishin'gi'de jakadiya ta shigo tana bayyana mata zanin dake hannunta..
Wani irin murmushi ta saki..

Jakadiya tace, gimbiya uwar gidan mai martaba, ina miki albishir da a daren jiya yarima ya zama cikakken namiji....
   Kilishi ta gyada kai cike da gamsuwa tace,wannan albishir naki jakadiya ba karamin farin ciki ya saka ni ba,dan haka ina so ki samu shamaki a baki azurfa goma a matsayin Tu'kwicin ki.......
   Gu'da jakadiya ta saki hansai dake zaune kusa da kilishi na tayata sai murna sukeyi..ni kuwa afrah nace 'Oh"

***********

"Mustapha ya dade tsaye a babban zaure yana jiran zuwan zainaba..
Shiru har sai da abokinsa yazo ya sake sanar dashi  cewa shi kadai ake jira su tafi rana keyi...

  Ya cire rai kwarai da zuwanta har ya juya zai fito ya hango wata ta tunkaro wajen..se de shigarta kawai ya nuna masa ba ita bace ba..
     Yana fitowa tana karasowa wajen..
Ta yaye lullubin dake kanta tana sauke lumfashi sosai sbd tsabar gudun data sha..

Mustapha cike da mamaki yana bin ta da kallo,wai dama kice haka?
Zainaba ta gyada masa kai sannan ta fito da furen data boye cikin riga ta mika masa..

   Wani irin farin cikine ya lullube sa..
Yasa hannu ya amsa sannan yace..
Nagode kwarai da kika amshi tayin soyayyata,ina miki alkawari akan bazakiyi dana sani ba gimbiyata..

"Zainaba ta rufe fuskarta cike da kunya tana murmushi..
Mustapha yace,duk da baki damu da sanin sunana ba bari ni nayi karanbanin fada miki..

Zainaba ta bude fuskarta tana kallonsa kafin tace,kawai ka riga ni fada ne amma nima yanzu nake shirin tambayarka..

Mustapha ya gyara tsayuwarsa, kice ma har tunanin mu iri daya ne kenan ko?
Zainaba ta murmusa kawai..
Yace,toh sunana Mustapha dan gidan WAMBAN kano..ina fata matsayina yakai da yin soyyaya da diyar sarkin daura...
   Zainaba tace,kwarai kuwa..
Yace toh nagode....
A nan suka hau yar firar su sama sama...

*********
'A wajen juwairiya kuwa sauri kawai take bugawa,har tazo hanyar da zata kaita inda su zainaban suke amma sai ganin jama'a tayi sunyi yawa a wajen sosai..

Ta cije yatsan ta,yanzu ta ina zata bi kenan?
Hanya da'yace kawai zata iya kaita kuma sai ta bi ta sashen samarin gidan,wato sashen su turaki kenan..
Kafada ta daga lkcn data karasa sashen taga babu kowa a wajen,ta saki lumfashi tace, ina tunanin duk suna fa'da ne...

   Tafiya take cikin sauri kanta a kasa..
Batayi au'ne ne kawai taji taci karo da mutum..
  A tsorace ta dago da kanta.....

'HAMZA....
ta furta a cikin zuciyarta....
A take tsoro ya mamaye ta.
dan ba sau daya ba,ba sau biyu ba tana jin bayin dake aiki a sashen sa suna yawan fadar halayensa na mugunta idan har akayi masa ba daidai ba toh lalle a ranar kashin ka ya bushe ne..

    Fitsari ne kawai bai fito mata ba..
Amma mai?
Gani tayi hamza ya tsaya kamar an shuka shi a wajen...
Kallonta kawai yakeyi baya ko kyafta idonsa..

  Ta'ke tabi inda kwayar idonsa dan gano inda yake kallo ajikinta dan ita a tunaninta ko kayan dake jikinta ya gane na zainaba ne su..
Amma se gani tayi fuskarta kawai ya kura wa ido..

'A Take ta fahimci ta sake tafka kuskuren fitowa ba tare da tabon fuskarta ba..
   Hamza yaja lumfashi...yace,
Baiwar Allah kin samu batar hanya ne...?

Yarda yayi zancen cikin wata kaukausar murya ne yasa ta sake jin hanjin cikinta sun motsa..
   Da kyal ta iya furta.....
Eh..ka.. kayi hakuri...tayi kasa da kai tana shirin wucesa ne taji murya a bayansu..
Hamza me ya tsayar dakai haka?bana fada maka sauri nakeyi ba...
Yarima ne......( ta fada ba tare data kalleshi ba,dan ta gane muryarsa ce )...

'Yarima kuwa dake fitowa daga cikin falo ya tsaya yana kallon hamza kafin yakai dubansa kan budurwar dake kusa dashi...
  Ware ido yayi a take yaji kirjinsa ya buga..bum!
Itace.....ya furta a zuciyarsa. ..
  
Juwairiya kuwa najin fitowarsa tayi saurin guduwa daga wajen tana dafe kirjinta....
     Da sauri yarima ya karasa gaban hamza dake ta sakin murmushi. .
Hamza dama kasan ta ne?

Hamza ya kalle sa' wa fa?
Yarima yace yarinyar data bar wajen nan yanzu..
Hamza ya sosa keyarsa..

Ah ah yaya kawai dai yanzu na kanta nima,ina tunanin ko tayi batar hanya ne..
Dan daga gani ma tana cikin yan uwan surayya ne da suka zo jiya,sbd ni dai ban ma taba ganin irin fuskarta a wannan masarautar ba..

  Yarima yaja lumfashi tabbas hakane yar uwar matarsa ce ita, toh amma kuma jiya ai idan bazai manta ba daya ganta lkcn ma su surayya basu iso garin ba?ya juya zuciyarsa cike da damuwa da tunane tunane kala'kala....lallai yana kyautata zaton GA'MO ne yayi.....

*********
Vote n comments
N pls share too

    
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 9
Wattpad @afreey101


*******************
"Juwairiya na komawa sashen zainaba tayi saurin dauko kayan kwalliyarta ta maida makeup din tabon ta duk da beyi daidai ba amma da wuya ne mutum yayi ssurin gane hakan.
Tana kammalawa zainaba na shigowa sai faman tsalle takeyi tana murna abu ga sabon shiga.

*************
  Juwairiya na shiga rumfar bayi taji labari da dumi duminsa..

A Lkcn ma tana zaune ne a dakin du'bu suna cin dan wake jakadiya suka shigo da hansai da laure..

    'Nan jakadiya ke kwashe musu lavarin duk abunda ya faro tsakanin yarima da amaryarsa,kunya ce ta lullube juwairiya, ta mike zata fice dan lbrn nasu yafi karfin kunnenta..
' can tajiyo jakadiya na fada musu irin kyautar da gimbiya kilishi tayi mata sai murna sukeyi..

**********
Bayan sati.....

  'Surayya ce zaune a gaban gimbiya kilishi..
     Hansai tayi sallama ta shigo dauke da tire dake cike da kayan kwalama..
Ta ajiye musu a gefe sannan ta koma wajen zamanta ta zauna..

   'Gimbiya kilishi tadan lumfasa..tace,
Ina fata babu wata matsala? ko akwai wani abu dake kike bukata ne?

Surayya tayi kasa da kanta..ita kuwa ke da matsala,kullum sai dai miji ya shigo mata daki yayi kwanciyarsa ko kallon arziki baya yi mata mtsw...

  a fili kuwa cewa tayi,Babu komai umma..ta fada a kunyace..
Kilishi ta murmusa..
Nasan zaman kadaici ya fara gundurar ki,saboda tun zuwanki kina sashen ki ba wani dan fita,amma kada ki damu za nsa yarima da kansa ya fita dake  cikin masarautar tamu dan ki bude ido..

Murmushi surayya tayi tace,godiya nake umma..
    Kilishi ta dauko alawar madara daga cikin tiren da hansai ta ajiye..
Kinga wannan alawar?itace mafi soyowa a wajen yarima...dan haka idan kinason faranta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login