Showing 54001 words to 57000 words out of 83480 words
fito da saurin ta..
Juwairiya kam ba karamin tsarguwa tayi da irin kallon da marka ke mata ba..
"Suna nan a zaune shiru kusan minti goma..
Juwairiya taji wani irin kamshi ya daki hancinta..
Tayi saurin dago da kanta...
Sai caraf taci karo da fuskar AMMI..dake kokarin karasowa cikin falon cikin shiga ta alfarma..
ita kuwa Ammin gaba daya hankalinta na wajen khaleed ne dan bata ma lura da juwairiyar dake zaune a gefe ta tsare ta da ido ba...
cike da fara'a Ammi tace da khaleed...ah ah mutanen daura ne saukar yaushe?
Khaleed yayi murmushi yana gyara zamansa yace,jiya da daddare na dawo Ammi mun same ku lafiya?
Ammi tace lafiya kalau... ya kuma ka baro mana samirar?
Khaleed yace tana nan kalau ai da bakuwa ma nake tafe Ammi..ya nuna gefen da juwairiya take a daskare tana bin Ammi da kallo..
Ammi ta juya inda taga khaleed na kallo sai cin karo tayi da fuskar data tsorata ta sosai..
Kallon kallo suka shiga yiwa juna ita da juwairiya kamar idanuwansu zasu zazzago..
Khaleed dai gyara zaman sa ya sakeyi yana jira yaga yarda za'a karkare..
***********
*A masarautar daura kuwa*
"Jalal hankalinsa a kwance yake sosai dan yasan khaleed zai kula masa da juwairiyar sa..
tunda ya daukar masa alkawarin yin hakan.
Yaja lumfashi..
Allah yasa juwairiya ta gano asalinta...
shine kawai addu'ar sa a gareta dan kuwa yana so itama ta samu farin ciki a cikin zuciyarta..
A halin yanzu yana zaune ne a cikin wajen shakatawar sa...
Ba karamin kewar juwairiya yakeyi ba..
Surayya ce ta shigo da sallamarta...
ko kallon inda take bayyi ba..
Zama tayi a kusa dashi ta narkar murya tace..
Sarkina ka yafe min na san kana fushi dani,amma wlh bani da niyyar kai karar ka a wajen abba..
Jalal yaja tsaki yana mamakin halin surayya..
Ta sake kwantowa jikinsa..kaji sarkina kayi hkr..
Jalal a zuciyarsa yace..lallai wannan yarinyar yar rainin hankalin ce,dolene ya ho'ra ta da abunda yasan zai fi yi mata ciwo..
Murmushin mugunta yayi sannan ya kwalawa jakadiya kira..
Sai gata da sauri ta shigo wajen..tace gani ranka shi dade..
Jalal yace,inaso ki aika min sashen khadija a fada mata yau ina gayyatar ta kwana a sashena..
Dam!zuciyar surayya ta buga..lallai ma wato a gabanta yake gayyatar matarsa kwana?babu wani dan kawaici?
Jakadiya tayi murmushi sannan tace, An gama Amale..ta fice...
Surayya taja tsaki,ta mike rai a bace tabar sa awajen..
Jalal yayi dariya yace kadan ma kika gani Surayya...
*************
"""Zabba'u ce ta sanar ma zainaba tafiyar juwairiya..
Kuka sosai tayi na kewar ta tana jin haushin rashin zuwanta suyi bankwana..
wasiko kin da Mustapha ke aiko mata ne ta dauka sannan taja zabba'u suka fice zuwa lambu..
Zama tayi akan koren ciyayi dake wajen tana sake karanta wasikokinta dan ta samu damuwar tafiyar juwairiya tayi ta barta ya ragu acikin zuciyarta...
Kallon zabba'u tayi tace,kije ki samo min kayan marmari nasha..
Zabba'u tace toh ranki ya dade..
Zainaba na nan a zaune aka fara iska me karfin gaske ga kuma hadari daya hadu sosai..
Takardun data baje a wajen ne iska ya fara tafiya dasu..
Ta mike da sauri ta shiga kwashe su..
"Magaji ne ya shigo lambun dan samun sukuni a cikin zuciyarsa, bayan yaji tafiyar juwairiya a bakin khadija ba karamin tashin hankali ya shiga ba,dan kuwa yasan har abada bazai sake ganinta ba...
Hango zainaba yayi tana ta faman kwasan gudu tana bin takardun da iska ke ta dauka..
Dariya sosai ta bashi..ai kuwa ya shiga kyalkyacewa da dariya..
Zainaba najin sautin dariya ta dago da sauri sai hango magaji tayi..
Ta tsaya tana kallonsa hade da rike kugunta..tace..
Yaya magaji ni kakewa dariya haka ko?
Magaji ya karasa wajenta..yana fadin..
Afuwa ranki ya dade...
Zainaba ta turo baki kawai taci gaba da abunda takeyi..
Magaji ya duka shima yana taya ta,sai da suka kusa gama kwashewa sai kuma ga ruwa kamar da bakin kwarya...
Zainaba duk ta rikice....gani tayi magaji ya cire babbar rigar sa yazo wajenta..
Da kallo kawai take binsa..
Daga jigar yayi sama yayi musu rumfa da ita..
Zainaba ta ware ido ta juyo tana kallonsa..
Magaji yace,yadai da kallo muje da sauri dan wannan rumfar ba mai dore wa bace....
Tafiya ya farayi tayi saurin binsa itama..
har sai da sukaje sashen ta sannan yaja burki ya tsaya yana dauke rigar daga kansu..
Zainaba ta kalleshi duk sun jike sharkaf..
Gani tayi yana kokarin juyawa ya tafi..
Tayi saurin kiransa..
Yaya magaji!!!
Ya tsaya yana kallonta..
Tace mu shiga daga ciki kadan sha ruwan dumi kada sanyi ya kama ka..
Magaji ya jinjinar kai dan kuwa yasan duk lkcn daya sha ruwa haka toh sai yayi mura..
Zainaba ta shige gaba yabi bayanta..
Wajen zama ta nuna masa sannan ta koma daki ta dauko masa bargo me nauyi ta fito..
Mika masa bargon tayi..
Magaji ya girgiza kai,da kin bar shi kanwata..
zainaba ta turo baki sannan da kanta ta jibga masa bargon a jikinsa..
Zayyi mgn ne sukaji shigowar zabba'u.
Zainaba ta kalleta,ke kuma a ina kika tsaya ne?
Zabba'u ta hau bata hkr..
Tace ya isa haka nan je ki kawo mana shayi mai zafi..
Zabba'u tace toh sannan ta fita..
Magaji ya kalli zainaba,yace..
"Kema baki san da tafiyar ta ba ko?
Zainaba tace,wacece?
Magaji yace,juwairiya..
Zainaba ta kura masa ido kafin tace,uhm se de tabar min sallahu,duk yarda muke da ita..
Magaji ya jinjina kai,lallai kam ko zainaba bata fadawa ba ashe?toh balle shi kuma...
Zabba'u ce ta shigo da tray din ruwan zafin su daya sha kayan kamshi..
Zainaba tace,har ruwan saman ya tsaya ne?
Zabba'u tace,eh ranki ya dade yayyafi kawai akeyi..
Zainaba ta dauki kofi daya ta mika wa magaji....
Magaji yasha ruwan zafin kadan sai mikewa yayi ya mata sallama ya tafi...
...............
"Nafisa ta kalli gimbiya kilishi dake zaune a kilisarta..
,umma dama uhm dama inaso ne naje gida a karshen satin nan dan muna da taron bikin yayana da za'ayi..
Kilishi ta kallii gefen da hamza yake zaune yana ta faman shan kankanar abunsa.
"Ta maido hankalin ta kan nafisa dake zaune kanta a kasa..tace..
Ina tunanin baki san a wane irin gida kikayi aure ba ko..
Ai duk macen da zatayi aure acikin gidan sarauta bazata iya fita kwana bakwai da daura auren ta ba..
Nafisa bataji dadi ko kadan ba,ita dai taso ace taje bikin yayanta,gashi kuma mijin nata sai dai yace mata ta nemi izinin mahaifiyar sa...
A sanyaye ta mike tace,toh umma ai babu komai bari na koma sashena..
Hamza ya mike shima..
Umma zamu tafi,kilishi ta sakar masa murmushi toh shikenan Allah yayi maka albarka..
Suna fitowa nafisa taja burki ta tsaya tana yiwa hamza kallon bataji dadin hana ta fita da kilishi tayi ba..
Hamzan yayi saurin jawo hannunta yana fadin..
Haba matas kema fa kinsan fitarki yayi wuri dayawa,ki bari kawai ko wata dayane kika cika nayi miki alkawarin kai ki har gidan ku da kaina..
Nafisa ta kwace hannunta,bana so! Tayi gaba tabar shi a wajen..
Hamza yayi kwafa shima ya bi bayanta...
****************
*masarautar zazzau*
"AMMI ahankali ta shiga tafiya har ta iso gaban juwairiya..
Juwairiya tayi saurin mikewa itama suna karewa juna kallo..
Ammi a take taji kuka yazo mata sosai,ya akai haka ta faru?
Ta juya ta kalli khaleed..tace
Khaleed!!!babu tantama wannan JININ FATIMA ZARAH (didi😉)CE,babu tantama wannan Diyar ZARAH'U na ce!!!
Ta janyo juwairiya jikinta ta kankame ta tsam,Allah na gode maka daka sa'da ni da JININ FATIMA,Allah nagode maka daka bayyanar min dasu!!!..
Juwairiya dai jin abun take banbara kwai,Wacece kuma FATIMA?kuma meye hadin ta da wannan matar da suke mutukar kama da juna?
Ammi ta dago ta tana kallonta cike da tsantsar kauna..
Tace..
Ina fatimar take ita?ina fata a tare kuka zo nan?ina fata fatima ta yafe mana shiyasa ta dawo garemu...
dan Allah ki sanar dani ina mahaifiyar ki take?
Juwairiya kai tsaye tace tana RUMFAR BAYI.....
Ammi ta tsaya cak tana kallonta..
Rumfar bayi? Ta maimaita sunan..
Khaleed ne yayi saurin mikewa ganin juwairiya ko kadan bata fahimci me ammin take fada ba..
Hannun Ammi yaja suka shige uwar da'ka..
Ammi ta kalleshi,khaleed ka sanar dani meke faruwa ne haka?a ina ka gano mana ZARAH'U?
Khaleed yace,ammi ki tsaya ki saurare ni..
Ammi ta girgirza kai tana kamo hannunsa ka fada min..
A ina ka hadu da yarinyar can da babu tantanma diyar fatima na ce,kuma me yasa tace min fatima na rumfar bayi? bacin fatima bata da wani hadi da bauta a rayuwarta! !!...
Khaleed yaja lumfashi yana damke hannun Ammi..yace
Amim yarinyar can da kika gani,a jiya aka yantar da ita a MASARAUTAR DAURA, baiwa ce...
Ammi ta dafe kirjinta tana fashewa da kuka,yau na shiga uku!
Dama halin da fatima ta fa'da kenan?
Khaleed yace,ammi ki nutsu kiji labarin da zan fada miki..
Ammi na kuka shabe shabe ta gyada masa kai..
Khaleed ya sanar wa Ammi dan takaitaccen lbrn juwairiya kamar yarda jakadiya da kuma jalal suka sanar masa..
Mutuwar zaune Ammi tayi..
Tabbas Fatima ce,ZARAH'U ce wannan matar data haihu a cikin RUMFAR BAYI, DIYATA wacce ta dade da bacewa kuma YAYARKA ce da muka dade muna nema....
Khaleed ya waro ido yana fadin..
Ina nufin Juwairiya diyar yaya zarah'u ce?zarah'u da nake jin mai martaba yana yawan fa'dar ta?wacce kuka saka yan farauta su nemo muku ita?wacce ta AURI SARKIN KANON DABO?SARKI ABU-TURAB?
Ammi tace kwarai kuwa..itace...
Khaleed ya jinjina kai cike da al'ajabi..
Ammi tace,da alama yarinyar nan bata san ASALINTA BA kuma ya kamata ta san ko ita wacece....ya kamata mu sanar da ita mu danginta ne..
Mikewa ammi tayi ta fito falon inda juwairiya take zaune gaba daya tambayoyi ne acikin zuciyarta..
Ammi ta zauna a gabanta tace..
Ya sunanki?
Juwairiya tace sunana JUWAIRIYA..
Ammi tayi murmushi ta shafa gefen fuskarta..
Juwairiya kada kiyi mamakin abunda zamu fada miki yanzu kinji?,nasan dai da idonki kin ga irin kamannin da mukeyi ni dake ko?
juwairiya ta gyada kai dan shi yafi damunta,menene hadin ta da wannan matar..
AMMI tace toh ke JIKATA ce diyar DIYATA fatima data ba'ce shekaru masu yawa da suka gabata...
Gaban juwairiya ne ya fadi ras!!!!
Muryar na rawa tace..
Am am amma ai ni iyayena na can DAURA,kuma mu bayi ne..
Ammi ta girgirza kai..
Ta kalli khaleed tace,yanzun nan khaleed ya sanar dani yarda iyayen naki na can sukayi sanadiyyar samun ki...
juwairiya ta waro ido cike da tsantsar mamaki tace,suka same ni!ban gane suka same ni ba,ta shiga girgirza kai,ni ummana ba samu na tayi ba ,haihuwa ta tayi da kanta!!!!
Ammi ta kamo hannunta,ki kwantar da hankalinki,ammi tayi kiran Marka..
Se gata ta shigo..
Shiga ki dauko min zanen (painting )din zarah'u a ciki..
Marka tace toh uwar dakina..
Marka ta shiga ta fito da wata takarda ta mikawa ammi ita..
Ammi ta amsa ta bude ta mikawa juwairiya...
Jikin juwairiya ne ya hau rawa..
Ta amshi takardar ta kurawa zanen matar dake jiki ido..
Wani irin abu ne takeji har cikin zuciyarta, tabbas wannan matar tana da alaka da ita,tabbas su hansai samun ta sukayi ba haihuwar ta sukayi ba,me yasa suka boye mata?
"sai ta tuna wani lkc da ummanta ta samu wani sabani da laure,taji lauren na cewa..
"Kin manta ba ke kadai bace me iko da ita?idan baki so asirin da muka dade muna boyewa ya tonu toh ki daina nuna min iyaka ta akan juwairiya tunda dai mu duka suka same ta bake kadai ba"
Kuka sosai ta shiga yi,tana tuna duk wani lkc da tayi dasu hansai,wayyo Allah ashe basune iyayenta na usuli ba...
Ammi ta rungume ta itama tana kukan sosai,tana jin bakin cikin hukuncin da suka yankewa FATIMA gashi yanzu ta tafi ta bar su har abada,diyarta kuma ta ka're a matsayin BAIWA...
Sai da suka sha kuka me isar su kafin Ammi cike da tausayawa rayuwar da juwairiya ta shiga tace,ki zauna a sashena har zuwa gobe kakan ki mai martaba ya dawo daga tafiya,zamu sanar dake labarin iyayenki...
Juwairiya ta jinjinar dakai kawai dan ita gani ma takeyi mafarki takeyi...
***
Saida ammi ta bata lkc sosai tasha kuka mai isarta sannan ta kamo hannunta suka shige uwar da'ka..
Marka ce tare da wata baiwa..
Ammi tace,ina fata kin hada min ruwan?
Marka tace,anyi yarda kika ce ranki ya dade..
Ammi ta kalli juwairiya daga sama har kasanta kafin tace..
Tube kayanki..
Juwairiya tayi saurin kallonta da jajayen idanuwanta..
Ammi tace,tube mu shiga ban daki kiyi wanka..
juwairiya tace a sanyaye,ai nayi wanka dazun..
Ammi tace,ba wannan wankan zakiyi ba yanzu..
wanka ne zan miki dan na goge duk wani dattin bauta dake jikin ki dan a yanzu kin dawo mahaifarki..
Juwairiya tayi kasa'ke tana kallon Ammi..
Marka ce ta murmusa tace..
Ina tunanin kunyar mu takeji ne uwar dakina bari mu baku waje..
Marka ta jawo dayar baiwar sukayi waje..
Ammi da kanta ta shiga cirewa juwairiya kayan jikinta..
Juwairiya ta runtse idonta gam tana mamakin abunda ammi ke aikata mata babu ko kunya ta tube ta tas ta barta da yar shimin dake jikinta..
Ban daki suka shiga,ammi ta umurce ta data shiga cikin bahon wankan dake cike da ruwa me dumi sai kamshi yakeyi..
Juwairiya gaba daya girman/kunyar ammi takeji kuma har zuciyarta tana jin kaunar matar..
Batayi mata musu ba ta shige ciki..
Ammi da kanta da shiga wanke juwairiya tana bata labarai da suka danganci masarautar su..
Juwairiya gaba daya ji takeyi kamar mafarki takeyi...
Tasha mamaki sosai ganin Anyi mata wanka yafi kala biyar..
Data fito daga wannan ruwan ammi ta fita ta kirawo su marka su hada wani..
Ta wanko iya wankowa..
A take kuwa fatar jikinta ta canza..
Tayi wani irin fes da ita..
fatar ta tayi wani irin haske,gashin kanta sai baza kamshi yakeyi..
Tana fitowa daga baton ammi ta nade ta cikin bargo mai kauri ta saka marka ta dauke ta cak dama ita ba wani nauyi ba..
A saman gadon ammi marka ta ajiyeta..
Ammi ta kalli marka..
Kije can MA'DINKA(wajen tailors)ki fada musu inaso suyiwa juwairiya kaya yanzun nan ki kawo min,marka tace toh ranki ya dade sannan ta fice..
Ammi ta zauna a gefen juwairiya tana hada mayuka masu shegen kamshi tace..
Ina so ki daina jin kunyata juwairiya,ni kakar kice babu wata kunya a tsakanin mu kinji?..
Juwairiya ta gyada kai tana murmushi..
Sallamar wasu yan mata guda biyu ne ya katse su..
Ammi na jin muryar su tace..
Ku shigo ciki yan matana har an taso daga makarantar ne?
Yan matan suka shigo ciki...Ammi kin san ko...
Mgnr ce ta tsaya musu a makoshi ganin juwairiya da sukayi akan gadon ammin su..
Kallon kallo suka shigayi wa juna..
A tare sukace..
Ammi a ina kika samo me kamar dake haka (her look alike)
Ammi tayi dariya, diyarku ce..
Cikin murna suka haye kan gadon suma suna saka juwairiya a tsakiyar su..
juwairiya dai da kallo kawai take bin su..
farare ne kamar ammi amma da ganin su zaka gane yan biyu ne da suna kama da juna..
Ammi na dariya tace..
Juwairiya wadan nan sune Autaye na,ga hassana ga kuma hussaina..
Juwairiya tabi su da kallo..
Hassana ta shafa fuskar juwairiya, diyar mu na kama da Ammi sosai..
Husssaina tace,sosai ma kuwa..
Ammi ta mike tana fadin,toh ku shirya min Jikata na bar muku wuka da nama a hannunku.
Murna sosai suka shiga yi ....
Ammi ta fice tana sanar musu marka zaka kawo kayan juwairiya..
"Sun gama shirya juwairiya cikin kaya na alfarma ba karamin kyau tayi ba,zan iya ce muku kamar an canzo mana juwairiya ne dan gaba daya (transforming)tayi..kamar ba juwairiya BAIWAR RUMFAR BAYI ba..
"Jama'ar gidan ne suka shiga shigowa ganin ta,ana ta taya ammi da murna..
Ammi kam baki bar kunne..
Hassana da hussaina kuwa suna makale da ita..
Khaleed ma sai da ya shigo,ya wara ido yana kallon juwairiya yace..
Ammi wacece wannan haka?
Ammi tayi dariya,diyarka ce mana..
Hassana tace,ya khaleed kaga yarda juwairiya ke kama da ammin mu ko?
Khaleed yayi dariya na gani sarkin surutu..
Juwairiya ta dago tana kallon khaleed, wai dama wannan mutumin kawun tane?
Khaleed ne ya kashe mata ido..
Yadai kina mamaki ko?
juwairiya tace ni gani nakeyi ma kamar mafarki nakeyi..
Ammi ta kamo hannunta tace..
ba mafarki kikeyi ba juwairiya duk abunda ke faruwa dake a yanzun GASKE NE.....
Juwairiya ta saki murmushi me cike da farin ciki...
Lallai dole ta gode wa Allah daya bayyanar mata da ASALINTA.....
Team RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 33
Wattpad @afreey101
***************
"Washe gari...
"Mai martaba sarkin zazzau ya dawo daga tafiyar sada zumuncin daya tafi..
Labari ne mai dadi ris'ke sa na bayyanar diyar zarah'u...
Bai ma san wane irin farin ciki zayyi ba, bai bata wani lkc ba ya saka akayi masa Ammi..
Ammi da kanta ta saka su hassana su shirya juwairiya tsab sannan suka nufi bangaren na mai martaba..
Juwairiya har cikin zuciyarta take jin dadi sosai zata ga kakanta kuma mahaifin ummanta ta gaskiya..
"Sun tarar dashi a zaune saman kujerar sa ta karfe a cikin dakinsa..
Tsoho ne da zaikai shekaru kusan tamanin haka,amma ba zaka taba cewa mijin Ammi bane dan kuwa ta fishi jikin yarinta sosai..tunda dai ya girme mata nesa ba kusa ba..
"Tunda suka cikin shigo dakin sarki ya kurawa juwairiya ido yana kallonta cike da al'ajabi...
Tabbas wannan jinin diyar sa ce zarah'u ..
Da hannu yayi mata alama dataje garesa..
Ammi juwairiya ta kalla..
ta gyada mata kai tace kije juwairiya..
Ta taka har zuwa gabansa sannan ta duka kasa ta gaishe sa cike da girmamawa..
Hawaye ne suka cika masa ido..
Sai yanzu yake mugun dana sanin abunda ya aikawa diyar sa..
Ya shiga shafa kanta hannayensa na rawa haka ma lebensa...
Yace...
Asma'u (AMMI)
Ina godewa Allah daya bayyana mana jinin fatima muka ganta tun muna da sauran lumfashi a duniyar nan.
ina farin ciki sosai dana samu ganawa da ke...
ya fadi yana dago dakan juwairiya, hawaye itama takeyi sosai..
Ammi ta zauna tana fadin..
.. (note an sanarma sarki lbrn juwairiya duka)
Ba lkcn zubar da hawaye bane wannan,lkcn farin ciki ne da gode wa Allah...
Sannan kuma lkcne da zamu sanar ma juwairiya labarin mahaifiyar ta..
Mai martaba ya gyada kai,cike takaicin rashin zarah'u da sukayi yace,hakane dole ne mu sanar dake Wacece FATIMA wato ZARAH'U mahaifiyar ki....
*******************
*Masarautar zazzau A shekarun baya da suka gabata*..
"Zarah'u itace diya ta farko da Ammi ta fara haifa tun bayan auren su da mai martaba..
yarinya ce mai saukin kai da tausayin gaske gashi bata da wani hayaniya ko kadan,bazaka tabajin tayi fada ko gardama da wani ba..
Ta taso ne cikin so da kaunar mutanen dake cikin masarautar nan..
Dan Ko ina a cikin masarautar nan shiga takeyi tun tana yar karamar ta dan haka babu wanda bai santa ba..
"Zarah'u na da shekara sha bakwai mane ma aurenta sukayi mana caaaa..
Tunda ga yayan yan uwanmu zuwa masu kudin kasar mu..
"hakan kuwa ba karamin tashin hankali ya saka mu