Showing 12001 words to 15000 words out of 83480 words

Chapter 5 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

971

masa rai wata rana ki yi kokari ki gabatar masa da ita ina tabbatar miki da zai ji dadi sosai..

Surayya tace,Allah umma?ai kuwa zan gwada inshaAllah..
    Suna cikin yar firar su sukaji ana sanar da shigowar da yarima da hamza...

     'cike da kasaita suka shigo..
Sunsha gayun su cikin tufafi mai tsadan gaske..
Surayya tabi yarima da kallo..
Har cikin zuciyarta tasan sbd kyawu da tsari irin nasa ne yasa ta amince da mgnr auren su ...dan yarima jalal yayi ne babu karya...

'Zama sukayi sannan a tare suka gaisar da mahaifiyar su..
Kilishi cike da murnar ganin yaran nata tace,har kun dawo daga rakiyar mai martabar ne?.

Hamza ya amsa da eh umma ai tun dazu ma muka dawo a gidan waziri muka tsaya...
  Yarima yayi shiru sai sauraren su da yakeyi...

   Surayya ce ta mike duk suka bi ta da kallo..
Tiren kayan kwayam din ne ta dauka ta ajiye a gaban yarima...
Da kallo ya bita kawai yana mamakin karfin hali irin na yarinyar,dan kuwa lbrn karyar da tayi na daren farkon su yazo har kunnen sa lallai ya jinjina mata.

Alawan madarar ta dauko ta mika masa tana murmushi. .
Yanzu umma ta gama sanar min da cewa kana sha'awar alawar nan sosai..
  Yarima ya dauke kai gefe..
Sannan yayi kasa da murya yarda itace kawai zataji yace..
Ba'a fada miki idan har ya fito daga hannu irin naki ba bazai taba burge ni ba?

'Surayya tayi murmushin ya'ke,sannan dan da'ga murya tace ai ban san cewa azumi kakeyi yau din ba...watarana zan samu damar gabatar maka dashi,ta mike ta maida tiren inda yake..

Kilishi da mamaki tace,azumi kakeyi a yau din?
Na dauka ai se litinin kakeyi ai?

Yarima yadai jinjinar dakai kawai,lallai wannan yarinyar muguwar yar rainin wayo ce..

Kilishi ta kalli surayya,ki tashi ki koma sashen ki gobe da yamma yarima zai zagaya dake cikin masarautar, surayya ta mike cike da yanga tayi sallama da kilishi tayi waje a kufule da irin hali na yarima.

********
'Washe gari  juwairiya ta nemi izinin tafiya da yamma dan tana da wankin ta take so tayi musu ita da ummanta..
Zainaba ba wani bata lkc ta amince mata,cikin jin dadi ta taho zuwa rumfar bayi...

'Koda ta kusa isowa sai hango su yarima tayi da amaryarsa surayya tare da bayi a bayansu suna tafiya cikin nutsuwa sai dai ba wani mgn sukeyi ba,amma ko waye ya kalle su sai sun burge sa dan dukkanin su ba baya ba wajen tsara ga'yu..
   
Surayya ta kalli yarima dake tafiya cike da kasaita sai shan kamshi yakeyi,tunda suka fito ko A bai ce mata ba..
Yarima can fa inane?ta nuna saitin Rumfar bayi..
Yarima yabi inda hannunta ya nuna da kallo..

Karaf idonsa yakai juwairiya dake kokarin shigewa cikin saurinta...
    Da sauri ya kauda kansa tsikar jikinsa na tashi..yaars..

"Surayya jin yayi mata shiru kuma a gaban bayin ta ne wanda ita hakan raini take gani zai jawo mata,sai ce mai tayi kace me?banji ka ba,(wato dai ta maida abun kamar yayi mgn ne itace bata ji shi ba)

    Yarima yadan matse baki kafin yace RUMFAR BAYI  kenan...
Ta sake maimata sunan,tana jin lbrn wajen daga wasu bayi a can masarautar su amma bata taba tsanmanin haka wajen yake ba...

    Tabi wajen da kallo...
Yarima ya juyo yana fadin, a nan zamu tsaya?
Surayya ta saki murmushi, ah ah yarima bazamu je kogin mai martaba bane?na ji lbrn cewa kogin mai martaba ya kayatu sosai..
Yarima yadan ja tsaki kafin yace,muje....

********
"Juwairiya na shiga rumfar bayi taga wayam kamar anyi shara,taja lumfashi su kenan kullum basu da lkcn kansu..

Dakin jakadiya ta shiga ta kwaso wankin su ita da laure,sannan ta shiga nasu dakin ta kwaso nasu suma wankin,can daga bayan rumfar bayi akwai wani ruwa mai gudana daga can kogin mai martaba ruwan ke fitowa,toh a nan ne suke wankin kayansu..

'Juwairiya ta samu dutse ta zauna a kai sannan ta zube kayan wankin a kasa tana kallon dajin dake gabanta...

Lumfashi taja,ko yaushe zatayi rayuwa kamar kowane dan Adam me daraja?
Ta girgiza kai, ki daina irin wannan tunanin juwairiya, haka rayuwar ki zata kare a bautawa uwar dakin ki zainaba...ta gyada kai sannan ta hau yin wankinta...

Ba karamin wanki tasha ba,ganin garin da sauran haske ga iska na ta kadawa hadari ya taso.. sai tsinci kanta cikin wani irin nishadi...

    Hadari ne sosai har an fara yayyafi,murmushi tayi tunawa da tayi babu kowa a cikin RUMFAR BAYI sai ita..
'Ta karasa gaban ruwan tana kallon reflection din fuskarta a ciki,hannu tasa ta dinga  dibar ruwa kadan kadan tana watsa wa fuskarta har ta wanke tabon dake jiki..
  Ta mike tana tsalle tana jin dadin yarda ruwan saman ke sauka akan fuskar ta data daga sama cike da nishadi.........


Pls
Comments
Share
Vote
[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Page 10
Wattpad @afeey101

_Notice-thanks for all the love *TEAM RUMFAR BAYI*,ur comments always gives me straight,pls keep on supporting me n add rumfar on wattpad my what'sApp fans,i need ur votes too pls...much love_


****************
"Surayya ta bude baki tana kallon irin tsarin kogin na mai martaba, ta juya bangaren da yarima yake a tsaye yana shan kamshi,gaskiya wajen nan ya hadu sosai,watarana nima zan zo nayi wanka a nan,dan ina masifar son shiga ruwa balle mai dumi haka,kasan ko a gi.....kallon da ya watsa mata ne yasa taja bakin ta tayi shiru..

     Yayyafi ne aka farayi..
Yarima yace muje ko?
Surayya ta make kafada sannan ta karasa cikin kogin tana wasa da ruwan cike da nishadi..

"Takaici ne yasa yarima karasawa wajen a fusace ya daka mata tsawa..
Baki ji ni bane!

A tsorace tayi losing balance dinta ta fada cikin kogin..
Ihu ta saka tana kallon yarima..(irin ka taimaka min dinnan)
Tsaki yaja ya shiga ruwan shima yana kokarin jawota..

Tazo fita ne hannunsu na sarke dana juna,ta jawo dan yatsansa da karfi...
ai kuwa zoben azurfan dake hannun yarima ya sullube cikin kogin ruwa yayi gaba dashi..

Cikin tsananin tashin hankali yace..
"Zobena..."baki da hankali ne!?

Surayya tace,toh miye ?
Ba zobe bane kawai...
Ko fa a yau dinnan kace a yi maka wani sabo a cikin daren nan za'a kawo maka shi,toh miye na wani tashin hankalinka,ta karashe mgnr tana kallonsa (giving him i dnt care look)...

Yarima ya banka mata harara kafin cikin sauri yabi inda zoben ya tafi...surayya se kwala masa kira takeyi yayi banza da ita..

'Tafiya kawai yakeyi ga ruwa ya fara yawa a lkcn...
  Bai taba zaton kogin yana tsawo haka ba...

   Wata murya ce yaji ana ta rera waka cike da nishadi..
Ya dago kansa cike da mamaki...

  caraf sai Hango ta yayi tana ta tsalle tsallen ta tana rera wakarta hankalinta akwance....
Har zai dauke kansa'kawai idonsa ya sauka akan fuskar ta...

   Wani irin ware ido yayi yana mamakin ganinta a wajen...
Wai wacece wannan yarinyar?
Gabansa nata faduwa kallonta kawai yakeyi ya kasa dauke idonsa..

Ita kuwa juwairiya bata ma lura dashi ba a wajen,tana gama tsalle tsallen ta ta kwashe wankinta dan dama batayi shanya ba ganin hadari,ta dauki kwal'lar ta tayi gaba...

      Yarima yaja lumfashi, ina ne can din data shiga?me yasa wai ya damu da sanin wacece ita?me yasa bazai mance fuskarta ba?meke damunsa haka?

      Ganin tunani na neman yi masa yawa ne ya dauke kansa da sauri yaci gaba da neman roben sa,da kyal ya ganshi wani dutse ya tare shi ya dauka yayi gaba yana waiwayen hanyar da ta bi...

*********
"Bayan kwana biyu yarima ne yayi kiran magaji zuwa sashen sa_(magaji yaron waziri ne kuma babban aminin jalal ne)_

  Magaji daya gaji da jiran yarima yayi masa mgn'yayi gyaran murya yace..
Yadai ranka shi ya dade?ka kirani kuma naji kayi shiru..da fatan dai lafiya ko?

  Yarima yaja lumfashi kafin gyara zaman sa yace,magaji ko kasan iya inda ruwan kogin mai martaba yake kaiwa?

Magaji yadan yi tunani sannan yace idan bazan manta ba naji ance ruwan har fa RUMFAR BAYI  yake kai wa..da wani abun ne?

Yarima yadan girgiza kai "rumfar bayi fa kace?
Magaji yace kwarai kuwa..
Yarima yadan yi shiru,amma shi fuskar da yake gani batayi kama da wata baiwa ba sannan ma ranar ai da kayan alfarma sosai ya ganta..
      Magaji ne ya katse masa tunanin sa..
Wai yarima meke damun ka ne? Ka sanar dani mana ko zan iya taimaka maka..

Yarima ya kalleshi,babu komai magaji tashi ka tafi..
Magaji ya jinjina kai sannan ya mike ya fice..

Yarima ya mike shima,bawansa ya kira ya fada masa yaje ya sanarwa surayya a dakinta zai kwana yau...

Bawan na fita kuyangi suka shigo dan hada mishi ruwan wanka..
Suna hadawa yace dasu zasu iya tafiya..
  Kayan jikinsa ya rage sannan ya shige cikin bahon wankan yana lumshe idanuwansa..

***************
  "Surayya na cikin cin abinci ne bawan yazo ya isar da sakon yarima..

Zo kuga Murna a wajen surayya tu're abincin dake gaban ta tayi dan a take taji ta koshi,bayinta ta kalla sannan tace dasu su shiga su sake gyara mata dakinta...

   "Ba karamin gyara suka sha ba,surayya jiki na rawa ta shiga ban daki da wasu bayin aka wanke ta tas sannan ta fito ta turare jikin ta ta saka rigarta mai santsi ta barci sannan ta zauna jiran yarima..

Shiru shiru babu yarima ,surayya taja tsaki,wannan kuma wane irin salon wulakancin ne?
Har sha dayan dare babu shi.. surayya na nan zaman jiran sa sai gyangyadi takeyi..can taji ana sanar da zuwansa..

  Ta mike da sauri ta zauna tana daure fuskarta..
   Yarima na shigowa dakin kamshi ya daki hancinsa..
Ya lumshe ido hade da saukesu akan surayya data harde hannayenta ta juya masa keya..

    Tabe baki yayi kafin yace..
Badai ni ake jira ba har aka kai wannan lkcn ba'a kwanta ba?
Ta juyo tana kallonsa shima ita din yake kallo..

   Cike da masifa tace,wai me yasa kake jin dadin wulakanta ni ne uhm?
Yarima ya cire alkyabbar jikinsa..yace,
Menene wulakanci a ciki?
"Sanar dake na yi zuwana?ko kuwa zuwan nawa sashen ki bayan shudewar kwanaki biyar..

"Surayya ta turo baki,sannan tazo ta haye saman gado tana tunanin yarda zata aiwatar da shawarar yakambo data aiko mata da wasika jiya..

    Gadon shima ya hau sannan a natse ya jawo bargo ya rufe jikinsa..
  Surayya ta runtse ido sannan ta shige cikin bargon itama ta matsa daf dashi ta sa hannu ta rungume sa ta baya..

  Yarima najinta a jikinsa yaji wani abu ya tsarga masa a gaba daya jikinsa...
Surayya ta na fitar da lumfashi ta kai bakinta saitin wuyan sa ta sumbata,cak yarima yaji wutar sa ta dauke,a take ya juyo suna kallon junansu dan akwai dan hasken fitila a dakin..

   Me kikeyi hakan....ya fada da muryarsa da ta canza amo (sauti)
Surayya ta kura masa ido batace kome ba..

Yace ko bakya jina ne eyeh?..
Ta sake motsawa kusa dashi,wai yarima ni ba matarka bace ba?meyasa ne kake min haka...ta karashe mgnr a shagwabe..
Yarima ya kamo hannunta...me nake miki?
Surayya ta zunburo baki,kaima ka sani ai wulakan.....bai bari ta karasa ba ya hade bakinsa da nata yana sumbatarta cikin salon sa..
   A wannan daren ne yarima da surayya suka san minene aure...

***********

"Juwairiya ta kalli khadija da zainaba dake ta muhawara akan zuwansu sashen matar yarima..

    Zainaba ta rike kugu tace,kedai kawai khadija ki ce kishi ne ke damun ki kuma duk tsiyar ki se naje ganin matar yayana ehe..

Khadija ta banka mata harara, ai dama nasan duk abotar karya kike dani..
Zainaba tayi dariya tana rungume ta,haba kawalli kema miye naki dan Allah ba gwara kije ma ki ga yarda take ba ma dan kisan inda kika dosa..

Khadija tace kuma fa haka ne,duk da dai naji ana ta wani fifita kyawun ta..
Zainaba tace yanzu dai muje mu ganewa idonmu ko?...

  Shiryawa sukayi juwairiya dai jinsu kawai takeyi....
   Suna kai wa sashen juwairiya taja ta tsaya a waje,zainaba ta juya tana kallonta muje mana?

Juwairiya ta girgiza kai ku shiga kawai ranki ya dade zan jiraki anan..
Khadija ta harare ta ai gwara ki tsaya a nan din kam tun kafin ganin ki ya jawo mana wani rainin..

Ko tanka ta juwairiya batayi ba ta samu wani dan dutse ta zauna a kai...
*********
Bayan anyi musu iso ciki ne suka shiga suka zauna a falonta suna jiran fitowarta..
Khadija tabi kwalliyar falon da kallo tana yatsina fuska lallai kam an kashe kudi a nan ...

'A wajen Surayya kuwa kwana biyun nan cikin wani irin farin ciki take,ganin yarda yarima yake dan kula ta ba karamin dadi hakan ke saka taba..

   Cikin tafiyarta ta yanga ta shigo falon..
Sannunku kawai tace musu ta zauna..
Zainaba tace,nayi fushi dake matar yaya..
Surayya ta danyi murmushi dan ta fahimci kanwar yarima ce zainaba diyar fulani diyya..

   Haba kanwar mu ni ce ai ya kamata nayi fushin,tunda nazo baki ko leko ni ba..
Zainaba tayi murmushi hakane kuma gsky,kinsan halin mijin naki ne sai muna bi a hankali..

Surayya tayi dariya jin ance mijinta..
Khadija kuwa se kare wa surayya kallo takeyi..
Can dai tace,matar yaya nidai nasan baki sanni ba,sunana khadija kawar zainaba ce sannan diyar waziri..
Surayya tace,kanwar magaji kenan ko?
Khadija tadan murmusa kawai..
Surayya ta kalli baiwarta,ya baki kawo musu abun tabawa bane?
Baiwar tayi kasa kai sannan ta mike ta fita..

************
"A can wa'je kuwa juwairiya na nan a zaune tana wasa da kananun duwatsu kanta a sunkuye,tana rera yar wakarta dan debe mata kewa..
       
      Magaji ya kalli yarima 'lkcn suna tafiya ne dan zuwa sashen surayya'
   Lallai ango ka ganka kuwa?wannan hasken da kake ta yi lallai gimbiya surayya ta iya ki'yo..

Yarima ya tabe baki,ta iya ki'yo fa kace?wa'to ni din wani dabba ne ma kenan da har ake ki'yona ko?

Magaji ya kwashe da dariya..maida wukar abokina..
Yarima yace,ba wannan ba,ya kake gani zamu bul'lowa mgnr da mai martaba ya fada mana dazu?
Magaji ya lumfasa gsky al'amarin kamar da girma kaga fa se munje har can chadin mun hadu da wannan mutumin..

Yarima ya jinjina kai yana shirin mgn ne kawai yaji wannan muryar da ko a mafarki yaji ta sai gabansa ya fadi...(muryar juwairiya dake dawainiya da zuciyar yarima)

    'Da sauri yabi inda sautin muryar ke fitowa da kallo..
Hango ta yayi can gefe a zaune tana wasa da duwatsu kanta a sunkuye..
   Cikin saurinsa ya karasa gabanta...

   Bai tsaya wani tunani ba yasa hannu a ha'bar ta(chin) ya dago da fuskarta....idanuwansa kamar zasu zazzago kasa..

*********
Juwairiya a tsorace take kallonsa dan kuwa ji kawai tayi an dago da fuskarta..
   Yarima na ganin fuskarta ya ture ta gefe da karfi cikin zafin rai..

"Ba ita bace"
Ya fada a zuciyarsa, ya runtse ido cike da takaicin ganin fuskar juwairiya dake saka tsikar jikinsa tashi..
ya juya bai ce komai ba yayi gaba..fuuuu
  Juwairiya tabi bayansa da kallo cikin mamaki tace,miye kuma hakan?

********
  "Ko gama sanar da isowarsa bai bari anyi ba ya shige ciki abunsa,magaji dake biye dashi yana tambayar sa miye hadin sa waccan baiwar ya tsaya yana bin bayan sa da kallon mamaki ...

   cike da tunanin abunda yarima yayi yanzun nan magaji yace,a ina kuwa nasan waccan fuskar?
Girgiza kai yayi,kai ba ita bace gsky,dan waccan fuskarta ba haka take ba..
Yana cikin wannan tunanin shima ya shige ciki..

***********
Surayya na ganin yarima ya shigo ta mike tsaye itama cikin zumudi dan baya zuwa sashen ta da rana haka..

  Ko kallon inda suke bayyi ba ya shige cikin daki abunsa..
   Zainaba ta tabe baki ko ma ya tsaya su dan gaishe shi..

Magaji ne ya shigo yana fadin , ah ah ashe yan matan suna nan suma..
Surayya tayi murmushi,ai kuwa dai sunzo ganin yayarsu ba..

Magaji yace ai sun kyauta,nima bari na karasa wajen umma babba,ya fice..
   Surayya duk ta kagu su khadija su tashi su tafi dan ta shiga wajen mijin nata,tayi tsaye ita taba bi yarima dakin ba ita kuma  bata zauna ba..

  Zainaba ce ta fahimci kamar su take jira su wa're..,dan haka ta zunguri khadija dake ta tabe baki,tashi muje khadija nasan fulani na can na jiran mu tunda fada mata zamuje sashen ta ko?

Khadija tadan harareta kasa'kasa,sannan ta mike,surayya kuwa ba karamin dadin hakan taji ba,murmushi tayi ta kalli zainaba tace,nagode sosai da ziyara kanwar mu,ko amsar su bata jira ba ta shige cikin daki da saurin ta....


Wattpadians/what'sApp fans lets know our status...
Who r d..
Team yarima's?
Team juwairiya?
Team surayya?

#rumfar bayi...

[9/18, 3:14 PM] Aysha Galadima: *RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 11
Wattpad @afreey101

******************
'juyi kawai yakeyi a gadon barci ya'ki daukarsa,ya kalli gefen da surayya take a kwance tana ta sharar barcinta hankali kwance..

"gobe ne zam'to tafiyar su kasar chadi,ga tunanin wannan yarinyar gaba daya yaki barin kwakwal'warsa,ya mike ya zauna yana dafe kansa,ya za'ayi ya nemo ta a cikin dubban bayin dake cikin rumfar bayi,wata zuciyar kuma tana gasgata masa cewa wannan yarinyar ba baiwa bace..
Ya koma ya kwanta yana sauke lumfashi bayan ya yanke wata shawara wacce kila ta amfane shi(ni ko afrah nace ko wacce shawarar ce? )...

****************
"Da safe juwairiya ta gama shirinta tsaf,tana fitowa daga dakinsu taga an jera bayi layi layi kamar ana asambili..

"Mamaki ne ya kamata sosai ta karasa wajen ummanta dake ta kokarin jera wasu fuskar nan a daure kam..
   Lafiya umma?ya naga duk sun ja layi?haka

  Hansai ta dan girgiza kanta cike da jimami tace, kema shiga layi ki bi mu..

Juwairiya a tsorace tace harda nima umma?ina zamuje ne haka?
Laure dake karasowa wajensu tace, sashen gimbiya kilishi zamuje,dan haka inaso ki nutsu da kyau nasan dai ko hauka sukeyi bazasu dauke ki cikin yan tafiyarsu ba..

  "Hansai ma kallon diyar tata kawai takeyi,a tsorace take sosai dan kuwa idan har za'ayi tafiya irin wannan kuma aka bukaci daukar bayi mata dan a tafi dasu,toh duk akasari dawowa sukeyi da ciki wasu kuma ace an sayar dasu ga mutanen can garin,wasu a lalatasu,wasu kuwa a maida su SA'DAKA..

   "Juwairiya ta dafa ummanta,kada ki damu umma na fahimci duk tsoron da kikaji sbd ni ne ko...
Hansai ta dan kamo hannunta, idan mukaje kada ki kuskura ki dago da kanki kina jina?duk da ma nasan da wuya ne a zabe ki,juwairiya tayi dariya tana nuna mata tabon fuskarta,tunda inada wannan umma ba inda zani je..
A sanyaye hansai ta gyada kai,hakane ..
Yanzu shiga layin mu tafi..

*****************
"A sashen gimbiya kilishi kuwa,yarima ne tare da magaji da hamza a zaune gabanta..

Kilishi tace,na saka duk a kawo muku bayin dake masarautar nan,ku zabi wacce tayi muku dan bana so kuje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login