Showing 3001 words to 6000 words out of 83480 words
can kasuwar bayi ki siyo da kanki..
Zainaba tayi saurin cewa ah ah RUMFAR BAYI zaku kaini umma..
Cike da mamaki bayin dake wajen suke kallonta dan kuwa babban kaskanci ne ace jinin sarauta ya shiga rumfar bayi..
Kina da hankali kuwa!
Fulani ta fada cike da daga murya..
Zainaba ta turo baki,umma ni wacce nake so tana can a RUMFAR BAYI..
Laure ta hadiye yawu kut amma sanin kuma juwairiya bata fita ko ina.. da wuyane a san da ita a cikin masarautar ma,sai ta sauke ajiyar zuciya tace,ranki shi dade wacece ita yanzun nan na kawo miki ita?
Zainaba ta langwabar da kai..
Sannan tace..
Wata yarinya ce kamar ni haka..
Laure taji kafafunta sunyi sanyi..
Fulani tace,me kike fada haka,kin taba jin a Rumfar bayi akwai yara ne?
Zainaba tace wlh umma da bakinta tace mana a Rumfar bayi take..kima tambayi yaya..
Fulani zatayi magana sukaji ana sanar da shigowar turaki..
Sai daya zauna ya gaisar da fulani sannan tace..
Wai turaki wane shirme ne zainaba ke fada,tace min akwai yarinya baiwa dake rumfar bayi kuma ita take so a matsayin baiwar ta ..
Laure ta cije baki...a ina zainaba ta gano juwairiya kuma?
Turaki ya kalli zainaba, ke dama da gaske kike?
Zainaba ta gyada kai ni ita nake so ta zama BAIWA ta ..
Ya kalli fulani eh mun hadu da wata yarinya dazu tace mana a Rumfar bayi take..
Fulani cike da tsananin mamaki ta kalli laure..
Wai haka?
Laure ta kakalo murmushi..
A...eh..eh....kam..anyi haka..akwai diyar hansai ina tunanin itace suka gani din...
Fulani ta ce cike da kasaita a kawo min ita nan!
Laure ta mike da sauri tace toh ranki ya dade..
Laure na fita ta shiga buga sauri bata zarce ko ina ba se sashen gimbiya kilishi tayi tsaye tana tunanin yarda zata samu mgn da hansai...
Can ta hango wata baiwa ta fito da tire a hannunta,laure ta tare ta da sauri..
ke Yimin mgn da hansai kice mata ina mata neman gaggawa..
Laure na nan jingine da kango sai ga hansai kamar an jeho ta, ta kalli laure ya akayine laure?
Laure tace ina jakadiya?
Hansai tace tana can fadar mai martaba ,laure taja lumfashi sannan ta sanar ma hansai yarda ake ciki,hansai ta dafe kirji yau mun shiga uku yaushe juwairiya ta fito daga rumfar bayi?
Laure tace ba wannan ba yanzu ya zamuyi?dan fulani ta nemi dana kawo ta..
Hansai tace a gaskiya bana son juwairiya ko kadan tayi irin rayuwar da muke ciki,bamu san asalinta ba bamu san daga wace duniyar ta fito ba amma laure wlh bana son ganin juwairiya cikin damuwa ko kadan,kuma kinsan halinta kwarai bata ji kada taje tayi wani laifin...... kuka ne yaci karfin ta..
Laure ta dafa ta bari na saka wani bafaden yayi mana kiran jakadiya se mu san nayi.
Cikin tashin hankali jakadiya ta karaso wajen su,lafiya naji kira haka,shamaki yake ce sanar min ana nema na bayan kunsan yau ina fa'da ne da kyal na samu waziri yamin alfarmar tahowa..
Hansai na hawaye ta sanar mata da komai,jakadiya taja lumfashi toh miye a ciki?dole ne kun san watarana hakan zata faru,laure tace bari dai na je na kai ta wajen fulani nasan dole ne a gobe zata fara aikinta na BAUTA...
Laure ce ta shigo rumfar bayi can ta hango juwairiya tana ta tsalle tsalle tana zolayar du'bu dake zaune tana linkin kaya..
Laure ce ta karasa ta zauna kusa da du'bu tana sanar mata umurnin fulani na son ganin juwairiya..
Du'bu ta gyara zamanta tana murmushin murna dan ita kam ta hannun damar fulani ce sosai sam bata son komai daya danganci gimbiya kilishi..
Tace Allahu akbar ai zainaba ba kadan ta biyo mahaifiyar ta fulani ba,na tabbata juwairiya zataji dadin zama da ita.
Laure tace uhm,sannan taje ta kamo hannun juwairiya, juwairiya tace,goggo laure ina zamuje?laure tace badai ke yawo ba ai gashi nan jin jawo wa kanki aikin BAUTA..
"A kofar sashen fulani akayi musu iso..
Laure taja hannun juwairiya dake ta kalle kalle suka shiga ciki..
Baki sosai juwairiya ta bude ganin kyau da tsarin falon ,can ta hango fulani hakimce akan kilisar ta..
Tayi kasa da kanta,zainaba ce ta mike tana fadin,itace wannan umma kin ga ta nan..
Fulani tayi murmushi tana kallon juwairiya a ranta tace,yarinyar kyakkyawa, ta kalli laure toh kinji laure ita zainaba take so a matsayin kuyangar ta dan haka daga gobe zata fara yiwa zainaba hidima...
Juwairiya tayi saurin kallo zainaba dake kallonta dauke da murmushi, sannan ta kalli turaki dake zaune shiru yana saurarensu..
Laure tace an gama ran fulani ya dade,zainaba ta kalli juwairiya sai mun hadu gobe ko?juwairiya ta gyada kai sannan suka juya suka fice..
"A daren ranar raba dare su jakadiya,laure da hansai sukayi suna fahimtar da juwairiya yanayin rayuwar da zata shiga..
Suka fara da gaya mata matsayin ta,ke ba kowa bace fa'ce BAIWA,
yanzu gimbiya zainaba itace uwar dakinki wacce zakiyi wa hidima..
komai takeso shi zakiyi mata babu gardama,
ko me tace dole ki amince dashi,
duk abunda take so shi zaki so,
duk abunda bataso kada kiyi,
ki guji bata mata rai,
kome zakiyi se kin nemi izinin ta,
ki bauta mata dan a halin yanzu rayuwarki kamar tana hannunta ne..
Juwairiya taji abun banbara kwai,tace amma umma jakadiya rayuwa tana ga Allah ne ai ko?laure tace hakane amma rayuwarki da zakiyi a wannan masarautar tana hannun gimbiya zainaba ne,dan a kowane lkcn zata iya ba'tar dake...
Juwairiya ta tsorata sosai,jakadiya ta shiga nuna mata yarda duk zata kula da gimbiya zaOneloveuk wata hidima da akeyiwa ya'yan sarauta an koyar da ita,sai cikin dare sosai suka samu rintsawa sbd tambayoyi da juwairiya ta rufe su dashi....
" Wannan kenan "
Share pls n pls vote on wattpad @afreey101
#Onelove
[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 4
Wattpad @afreey101
************************
"Washe gari da sassafe,hansai ce ta shirya juwairiya cikin irin shigar tasu ta bayi, kayane irin na Sa'ki' dinnan riga da zani(blue color kayan fulani dinnan ),laure ta shigo taja hannunta suka fice..
"Tafiya sukeyi juwairiya na ta kalle kalle tana tsallenta cike da nishadi..
' can ta hango wani yaro dauke da kwando a kansa aciki kuwa su mangoro ne da gwaba gashi tana mugun son mangoro sosai,nan ta kura mai ido tana tafiya tana waiwayen sa,yana dago da kai ya hango ta,ganin yarda take bin kwandon dake kansa da kallone sai ta bashi dariya har sai daya murmusa..
Laure ce ta hadu da wata baiwa suka tsaya gaisawa,juwairiya ta tsaya tana tunanin irin girman masarautar dan sun sha tafiya sosai ga gine gine masu yawa ga shukoki masu kayatarwa..
" Amsa.."
Taji ance daga bayanta,tayi saurin juyowa..
Sukayi ido hudu da wannan yaron..yana mika mata mangoro biyu fuskarsa dauke da murmushi..
Ta kalleshi ta saki wani irin murmushin murna,ji tayi laure tace,muje muje juwairiya....
Da sauri ta amshe mangoron ta furta ngd da sauri tayi gaba...
Suna isa sashen zainaba ayi musu iso ciki..
Zainaba na hakimce a zaune ana ta mata fifita...
Juwairiya ta saki baki ganin kyawun dakin ya burge ta sosai..
Zainaba ta saki fuska sannan tace,wai ya sunan ki ne ma?
Sauke kanta tayi kasa tuna mgnr su yaha ta jiya da sukace banda hada ido da uwar daki,a sanyaye tace sunana JUWAIRIYA..
Zainaba tace toh muje makewayi (toilet ) dan ina son nayi wankana yanzu..
Juwairiya tayi saurin kallon laure,laure ta gyada kai sannan taje kusa da ita tace,kada ki manta da maganar mu ta jiya,tana gama fadin haka tayi gaba..
Juwairiya kanta a kasa tace ina ne ban dakin ranki shi dade?
Zainaba ta dan murmusa sannan ta kalli baiwar dake kusa da ita tana mata fifita tace,kai ta ban dakina sannan ki nuna mata yarda nake son ruwan wanka na..
"toh ranki shi dade ta mike hade da kiran juwairiya suka shiga wata kofa data sada su da wani makeken toilet sai kamshin sabulai yakeyi ga wani bahon wanka na silver a ciki, baiwar ta kalli juwairiya tace,kingani ruwan zafin kadan zaki saka dan zainaba bata son ruwan wankanta yafiya zafi da yayi dumi ya isa'
,ta dauko wasu ganyayya'ki masu fitar da wani sanyin kamshi,tasa hannu ta damka kadan tace kinga haka?juwairiya ta gyada kai,toh haka zaki ringa sakawa duk lkcn da zaki hada mata ruwankan ta,juwairiya duk ta fahimta dan kuwa akwai ta da kaifin basira.
'Se data taimakawa zainaba ta cire kayanta sannan suka shiga ban dakin.
'zainaba ta shige cikin bahon wanka da dan shimin dake jikinta,ta kalli juwairiya,tace..
"cu'da min bayana"
juwairiya ta dauko soso mai taushi tazo ta fara cu'ta mata bayan a hankali sbd dai an sanar mata yarda akeyi.
Sai da zainaba ta wanko sosai sannan suka dawo daki,ta kalli juwairiya dauko min wancan akushin,ta dauko tazo gabanta ta ajiye,zainaba ta bude kayan kwalliyarta ne a ciki.
Ta kalli juwairiya......
miko mi'ni jan bakin can,juwairiya tayi sakatoto tana kallonta dan bata ma san minene shi jan bakin ba,zainaba taji shiru tace lah baki san shi ba ne?
"Ta gyada kai tana fadin,Allah ya huci zuciyar ranki ya dade bani da masaniyar me kike bukata idan har ranki ya dade baza ta damu ba ina so ta ganar dani minene shi,zainaba tayi dariya sannan ta dauko jan bakin da kwalli da hoda duk ta nuna mata su'sannan ta tsara yar kwalliyarta da kanta,juwairiya cike da mamaki take kallonta ta saki baki ganin yarda zainaba tayi kyau abunta.
sai da ta taimaka mata ta saka kaya sannan suka dawo cikin falo...
cikinta ne ya hau rurin yunwa ganin irin delicious din dake jere a gaban zainaba tana ci tana wani yatsina.
Tunawa tayi da mangoron ta na dazu data ajiye akan ta'ga (window)lkcn shigowar su.
Tadan sadda kai kasa,ranki shi dade zan iya fita yanzu yanzun nan na dawo?
Zainaba ta kalleta da mamaki ina zakije?
Juwairiya ta dan dafe cikinta sannan tace wata ajiya nayi a waje zan dauko.
Zainaba ta gyada kai zaki iya tafiya..
Da gudu ta fito neman mangoron ta,sai ko ta gansu a inda ta ajiye su din.
cikin murna ta dauka ta shiga shansa kamar an aikota duk tayi kaca kaca da bakinta..
"Ashe ke kazama ce?
Taji an fada daga gefen ta,da sauri ta kallo wajen,turaki ne ta gani da bawan sa a bayansa..
Ta dan sude hannunta sannan tayi kasa da kai,barka da zuwa ranka ya dade..
Cike da mamaki yake binta da kallo wato yanzu ta fara sanin dokokin gidan kenan?
Yauwa kawai ya fada sannan ya shige wajen kanwar sa..
'Yana shiga zainaba ta mike cike da murna,yaya ashe zaka zo?
Ya dan daure fuska miye na kirana da sassafen nan haka?
Zainaba ta shagwabe fuska,dama fa zan tuna maka ne yau nakeso muje na hau do'ki nima..
Turaki ya lumfasa wato bazaki bar wannan zancen ba ko?
Daure fuska tayi,amma ai har fulani na fadawa kuma ta amince naje na da'na dokin nima..
'Turaki ya girgiza kai sanin halin kafiya irin ta zainaba,juwairiya ce ta shigo kamar munafuka se goge bakinta takeyi..
Zainaba ta kalleta ki shirya zamuje hawan doki,juwairiya tace toh ranki ya dade.
Tsaye suke a cikin wajen ajiyar dawakan sarki.
Zainaba se zumudi takeyi,ta kalli bawan dake tsaye wajen tace,wancan dokin nakeso na hau,ta nuna wani farin doki dayaji kayan ado sosai..
Zubewa kasa bawan yayi yace,kiyi min rai ranki shi dade wannan dokin musamman YARIMA yasa aka shirya masa shi yau din nan..
Zainaba a take ta daure fuska ta kalli turaki dake gefenta,yaya kaji wai na ya jalal ne ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..
Turaki yace,kiyi hkr ki zabi wani mana?
Zainaba ta zunburo baki,zatayi mgn suka hango yarima yana tahowa cikin kasaitar sa bayi na biye dashi a baya.
Yana karasowa wajen duk suka tsaya kallonsa bayin dake wajen kuwa suka zube suna kwasar gaisuwa..
Bai ko kallon inda su turaki ke tsaye bayyi ba..
idanunsa ne suka sauka akan juwairiya dake tsaye a bayan zainaba bata da ko niyyar dukawa ta gaishe shi..
Ke!
Ya fada yana yastine fuska..
Juwairiya ta dago suka hada ido,dauke kansa yayi..
"Na lura har yanzu baki san matsayin ki ba ko?
Sake dukar da kanta tayi tace'barka da fitowa ranka shi dade..
Yarima ya tabe baki sannan ya maida kallonsa kansu turaki..
Zainaba ta daure fuska Allah ya gani bata son girman kai da isa da ikon da ya jalal yake ji dashi..
Lafiya?...yarima ya fada yana musu kallon me kuke a nan?..
Turaki ya murmusa babu komai dama wucewa muka zo yi..
Yarima ya tabe baki ya karasa wajen do'kin sa wani bawa ya taimaka masa ya haye sama abunsa....
Zainaba kuwa ta banka wa turaki harara sannan ta juya a fusace tayi gaba,juwairiya tayi saurin bin bayanta ..
"Fulani ce a zaune saman kilisar ta laure na mata tausar kafa suka shigo bayan anyi musu iso..
Zainaba ta fada jikin fulani tana kukan shagwaba,fulani wai me yasa a gidan nan ne akafi girmama su UMMA babba (gimbiya kilishi kenan) da su yaya YARIMA?akan mu?
Naga ai mu ma baban mu daya dasu ko?tunda duk mai martaba ne ya haife mu..
Fulani ta sa hannu ta dago fuskarta'da ta fara ji'kewa da ruwan hawaye..
girgiza mata kai tayi,zainaba nasha fada miki ke jinin sarauta ce ba'a san'mu da zubar da hawaye haka ba kaskancine a garemu....
Zainaba ta goge fuskarta..
Toh umma na daina..
Juwairiya dake tsaye fulani ta kalla,sannan ta maida kallonta ga zainaba..
Ya baiwar taki?
Zainaba tayi murmushi,tana kula dani sosai umma sannan ta iya aikinta tana da kokari ..
Laure dake zaune ta saki lumfashi..
*********
'Sai da daddare bayan uwar dakin tata ta samu barci sannan a gajiye ta fito daga sashen tana hamma..cike da gajiya dan zainaba akwai shegen son yawo..
Tafiya takeyi cikin duhu sai dan hasken farin wata dake haska mata hanyar kadan..
Maganganu ta fara jiyowa a tsorace ta shiga kalle kalle..
Can ta hango inuwar mutane biyu dake can wani lungu..
Da sauri ta karawa tafiyar tata sauri amma me sai taji kamar muryar TALATU wata sabowar baiwa da'a kawo shekaran jiya..
A hankali ta shiga labewa tana karasawa wajen duk da zuciyarta cike take da tsoro..
Ware ido tayi ta dafe kirjinta ganin wani katon gardi yana neman ya'ge rigar dake jikin talatu dai fisgiwa takeyi amma ina.... yafi karfinta..
Juwairiya ta rasa yadda zatayi gashi mutunen ya juya baya sai dai tufafin dake jikinsa ya nuna mata dan gidan masu dashi ne..
Har ta juya zata wuce sai kuma ta tuna mgnr mahaifiyarta inda take ce mata idan har taga mutum cikin bukatar taimako toh lallai ta taimaka masa ..
Sauke ajiyar zuciyar tayi kafin tayi saurin karasawa wajen wasu fadawa dake tsaron kofar babban zaure..
Dan Allah ku taimaka min wata baiwa na cikin neman taimakon ku, da sauri suka bi bayanta,sai dai suna kawowa wajen suka ja suka tsaya,juwairiya ta kalle su,daya daga cikinsu yace yarinya kiyi hakuri amma nan ba hurumin mu bane ba kema idan har kina son rayuwarki tayi tsawo acikin masarautar nan toh ki kama hanyar gaban ki..
Juwairiya na kallonsu suka fice,ta dafe kanta yau ta shiga uku yanzu ya zatayi kenan?
Dubara ce tazo mata,se data je saitin inda suke har mutumen yayi nasarar kwantar da talatu a kasa ta daga murya sosai tana fadin..
Talatu ! Talatu wai ina kika shigane haka!
Jin an ambaci sunan talatu kuma tabbas wajen da suke ne aka nufo,sai ya mike da saurin sa yabar wajen..
Da sauri juwairiya ta karasa wajen tana kallon talatu dake kuka kamar ranta zai fita..
Tasa hannu ta dago ta tana rarrashin ta..
Suna shiga rumfar bayi hansai da du'bu dake zaune gaban wuta sukayi kansu..
Lafiya juwairiya ina kika tsaya haka?juwairiya ta kalli talatu dake bayanta tana goge kwallar bakin ciki..
Umma dama...
Ta sanar musu komai,nan matan bayi sukayi kan talatu cike da tausayawa suka shiga tambayar ta ko yayi sa'ar yi mata fyaden?ta girgiza musu kai nan aka shiga hamdala dan kuwa a wajen su bayi sun dade suna fuskantar irin wannan kalubalen sosai,ayi musu fyade a banzatar dasu kamar kayan wanki..
Lamarin nan ba karamin tashin hankalin hansai yayi ba,ta jawo juwairiya har daki ta tsaya tana kare wa jikinta kallo daga sama har kasa.. yarinya yar shekara goma amma duk halittun girma sun fara bayyanar mata,bata so kadan a ba'ta rayuwar diyarta dan kuwa a yanzu ji takeyi juwairiya kyauta ce daga Allah a garesu..
Ki zauna ki jirani ga abincin ki can a cikin dan chinan can..
Hansai na fita juwairiya ta jawo dan chinan tana kare ma tuwon dawar dake gabanta kallo,ta tuna da irin abincin da zainaba ta gama ci dazun,dafaffiyar kaza ce,miyar naman shanu ne,dambu dayaji zogaye da kayan lambu,ga juice din inibi ne da aka matse shi aka saka mazarkwaila aciki..
Ta girgiza kanta da sauri dan ganin ta fara hadiyar yawu,oh haka rayuwa take"ta saka hannu ta fara kai wa towun ta loma..
Hansai dakin jakadiya ta shiga suna zaune da laure suna yar firar su..
Hansai ta zauna tana saka tagumi.
Jakadiya tace lafiya hansa'u?
Hansai ta kallesu,ni fa hankalina a tashe yake wlh,kunfi kowa sanin irin rayuwar da BAYI mata suke fuskanta a wannan masarautar, ina tsoron wani abu ya faru da juwairiya ganin yarda yanzu ko wane dare ake samun matsalar fyaden nan..
Laure tace toh yanzu ya zamuyi?dan wannan yarinyar juwairiya da gani ba karamar mace za'ayi ba..
Jakadiya tace nima wlh ina cikin wannan tunanin amma miye abunyi?
Hansai tace,ga shawara duk suka kalleta..
TABO (scar )
Tabo kuma?duk suka tambayeta cike da rashin fahimtar abunda take nufi..
Hansai ta murmusa TABO zamuyiwa fuskarta dan babu abinda maza suka fi kyamata kamar TABO ajikin mace..duk wani basarake ko mai mulki da dukiya babu abunda ke saka shi kyamatar mace kamar TABO ...
Laure ta kwashe da dariya kuma fa hakane,dan ko kadan idan bayin dake kula dasu ko SA'DAKA ce suka samu wani dan Tabo ko Konewa a jikinsu toh fa a ranar ake canza musu su..
Jakadiya tace wannan hakane,hansai ta mike tace kuzo muje..
Juwairiya na faman sude kwano suka shigo,ta gaida su tana fadin,goggo laure ina alkawarina yake?
Laure tace ke fa yar nan baki mantuwa..
Hansai ce ta zauna a kusa da ita tace,juwairiya kina jina.....
Wattpad @afreey101
[9/18, 3:10 PM] Aysha Galadima: 🏕 *RUMFAR BAYI* 🏕
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 5
Wattpad @afreey101
************************
"Bayani sosai sukayi mata,a tsorace tace, ummana kada ki damu zanyi kokarin rike mutumcina insha Allahu..
'Jakadiya ta fita ta dawo da wani tire ta ajiye a