Showing 66001 words to 69000 words out of 83480 words

Chapter 23 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

1132

ta murmusa..batace masa komai ba..
Shiru ne ya ratsa...
Se ji tayi yace...
Inaso a karshen watan nan ki tare ni a gidana..

juwairiya ta dan waro ido..
Da wuri haka..?
Jalal yadan langwabar da kai..
Nayi kokari ai..kinsan tun yaushe na fara mafarkin kasancewa dake ne?
juwairiya ta girgiza kai..
sai ka fada ranka ya dade..
Jalal ya daure fuska..
Bana son wannan "ranka shi dade"din fa..a tunani na mun wuce wurin..
Taja lumfashi..
Toh AMALE......
Ya saki murmushi ko ke fa..
Juwairiya tace,ina jinka toh..

Jalal yace tunda nayi gamo da gatar da fuskar ki nake mafarkin samun ki...
juwairiya dadi ya lallube ta..
Jalal ya mike cikin takun kasaita ya dawo kusa da ita zai zauna..

juwairiya tayi saurin matsawa tana kallo kofa..
Baka tsoron wani ya ganmu  a haka?
Jalal ya zauna yana fadin..
Sai me?
juwairiya ta tabe baki..
Ya kamo hannunta ta bishi da kallo..
Zoben sa ne ya gani a babban dan yatsan ta.
Mamaki ya kamashi..yace..

Ina kika samo wannan zoben nawa?
Tayi dariya tace ka manta? wajen MAI KIFI..?
Jalal ya jinjinar dakai yana dariya..
sannan ya cire zoben ya fito da wani a cikin alhujinsa ya saka mata shi..ya sumbaci hannun nata..

   Murmushi kawai takeyi..
Jalal ya kalleta..
Yanzu tunda kina da ikon sakawa shiyasa nazo miki dashi..
Tace..
Nagode Ranka..se kuma tayi shiru..tace auuu nagode AMALE ..
Jalal yace ni kuma fa me zaki bani?

juwairiya ta amshi zoben daya cire mata (nashi)
Ta maida masa a yatsansa..
Jalal ya kai hannunsa saitin bakin ta..
Dariya tayi dan ta gano me yake nufi..
Jalal ya langwabar dakai..
Kinsan abunda nake bukata a wajenki..
Juwairiya ta make kafada..
Kafin ta fakaice shi ta mike da sauri tabar falon tana masa dariya..
Murmushi ya sakar kafin ya mike shima yana fadin...
Zamu hadu ne yarinya...





*"Invitation"*
*Ana gayyatar duk fans din rumfar bayi zuwa daurin auren JALAL DA JUWAIRIYA gobe inshaAllahu...*😅😅

TEAM RUMFAR BAYI
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 38
Wattpad @afreey101

*BIKIN MANYA*
**************************

""Lkcn da su sarki jalal suka sauka a kasar daura..
Labari gaba daya ya gama ya'duwa acikin masarautar...
Sarki jalal zai kara aure,kuma diyar sarkin kanon dabo ce amaryar tasa..
Labarin babu inda baije ba,da masu murna da kuma masu bakinci duk yakai garesu..

"""Umayma na samun wannan danyen lbrn ta garzaya sashen gimbiya surayya da saurinta ta sanar da ita abunda ke wakana..

Wayyo hauka ne kawai surayya batayi ba....Jalal zai karo aure?
Duk ta susuce ta birkice a lkc daya..

"Umayma ta kalla da itama din ke taya ta bakin ciki sosai tace, yau na shiga uku!umayma..

idan itama wannan ta shigo ta samu nata cikin ai na gama yawo...kinsan tuni gimbiya kilishi zata saka jalal sakeni!
Umayma tace...
ni a ganina ranki ya dade wannan malamin tsabbun gsky aikinsa baya wani Ci..
Toh ace tun kwanakin da muka zubawa gimbiya khadija wannan maganin a kofar sashenta amma shiru kake ji ba wani lbr?
Ciki ma sai girma yakeyi..

  Surayya tace,gskyr kine umayma tunda ga aikin da yayi mana akan wannan baiwar har yanzu babu wani ci gaba a har wajen yariman ma..
Gashi yakumbo tayi tafiya..

Umayma tace,kada ki damu ranki ya dade mu koma can yanzu mu same shi ya fada mana dalilin da ya saka aikin da yake mana baya CI...duk dukiyar da muke bashi..

Ai kuwa shiryawa sukayi suka koma wajen malam na Sandamu..
Yana ganin su ya kwashe da dariya..
Umayma tace, hattara!
Malam yace,nasan ai zaku dawo ne..
Surayya tace,ban gane ba?wato da saninka kenan kake mana aiki baya Ci ?
Malam ya buga kasa yace,ai abunda yasa aikin ki baya ci sbd wannan asirin ne da kika yiwa wannan baiwar..

Surayya tace ban fahimce ka ba?
Malam yace,aljani daya ne kawai yake min aiki a yanzu bazan boye muku ba..
Toh na riga na tura shi da sunanki akan wannan baiwar,dan haka duk aikin da zan basa da sunanki bazai yi sa ba..
Surayya ta gyara zamanta,toh miye abunyi yanzu?dan ina damuwa sosai wlh..

Malam yace,sai mun warware wancan asirin kafin wani aikin Ya yiwu.
Umayma ta kalli surayya..
Surayya tace,toh me muke jira?ai tuni na manta da lbrn wannan baiwar malam,tunda ta bace tabar masarautar mu ai ni a yanzu na gama da shafin ta..
Malam yace toh angama..
A take ya warware asirin da sukayi wa juwairiya...
Ya sake kallon surayya..
Yanzu me kike so ayi miki?
Umayma ta dawo kusa da surayya tace..
Ranki ya dade me kike so ayi yanzu?
Surayya tace cike da tsantsar kishi,a hana auren sarki JALAL..

   Umayma ta girgiza mata kai,ranki shi dade yanzu ke kenan haka zaki ta zama ba ciki bare goyo?
A tunanina haihuwar da kike nema tafi miki komai mahimmanci a wurinki yanzu?
Idan amaryar ta shigo basai mu san abunyi ba a lkcn..
yanzu kawai ya taimaka miki kema ki samu naki cikin ko ba haka ba?
Surayya ta jinjina kai cike da gamsuwa da shawarar umayma..
sannan ta kalli malam tace..
So nakeyi nima na samu ciki malam,ka taimaka min..dan ni kadai nake so na haifar wa sarki magajin sa..

Malam yace babu damuwa an gama ranki shi dade ..
Ya bata wani garin magani yace,kin ga wannan ki samu kiyi amfani dashi kamar sau biyu..zaki dawo kiyi min godiya..
Surayya da umayma murna ta kashe su..
Suka biya malam da dukiya me yawa suka tafi..

"Samira ta kalli turaki..
Yanzu me kake gani zamu iya yiwa yaya jalal na auren sa..
Turaki ya mike daga kwanciyar da yayi..
Ni a tunanina kawai mu hada masa liyafa ta gani ta fada..
Samira tadan muskuta tace ah ah ba wannan ba..ni nafi son muyi masa abun da zai bashi mamaki ko ya kika ce zainaba?
Zainaba data buga tagumi ta dago a sanyaye ta kallesu, ni kam bani da wani abun cewa duk abunda kukayi yayi min..
Nafisa ta dafa ta,kanwar mu kamar fa akwai abunda ke damun ki kwanan nan?
Hamza ya jaa hancinta yace,ai nafisa ki bar tambayar ta ma..
indai wannan ce yanzu haka fada tayi da wani..
Zainaba ta turo baki,haba ya hamza ni ka maida uwar fada ko?
Magaji ya kai wa hamza duka..
Wai me yasa kake matsa wa yar kanwarmu ne?
Turaki yace,wai ni fa wlh mamaki nakeyi,wai ya jalal ne da kansa ya samo wacce yake so....

Zainaba tace ai shine,mutum sai shegen girman kai da kasaita,ko fa matan sa naji ance hakuri sukeyi da shi..
Magaji yace, ai wlh dan baku ga wannan yarinyar nan bane ba,ta hadu karshe ne,amma duk da haka nayi mamaki nima dan Amale bai ma tsaya ganin ta ba ko a ina kuma suka hade oho?..

Samira tace,yanzu dai mu koma kan shawarar mu dan inaso idan su goggo Amina sunzo kawo amarya su sha mamaki..ko ba haka bane?
Nafisa tace, hakane kam..
amma ke baki san amaryar tamu bane samira?naji ance goggo ce matar sarkin kanon..
Samira ta girgiza kai,gsky ban san taba nima...
A haka dai sukayi ta shan fitar su cike da nishadi...

"Jalal kuwa tunda ya dawo yake ta faman shirye shiryen sa,sashen dake kusa da na nasa ya saka ake ta faman gyarawa..dan yana so sosai ya burge juwairiyyar tasa..
    
********************
*biki ya matso*

"Shirye shirye kawai akeyi babu kama hannu yaro...
Masarautun biyu duka basu zauna ba..
Ana ta gayyace gayyacen mutane..

Gimbiya kilishi da fulani sune a kan gaba wajen shirya bikin dan kuwa matan sarki kowacce langwabe wa tayi akan basa jin dadin jikinsu..

Khadija kanta taji saukin laulayin cikin nata,amma kishi ne kawai ya sake kwantar da ita dan har a cikin zuciyarta bata so wannan karin auren da yarima yake shirin yi ba.
gashi sai rawar jiki yake yi musu ita abun ma tsoro yake bata kada wannan amaryar ta sa ta shigo ta dauke masa hankali daga gare su..
Lallai suna da aiki jaa a gabansu..

*"Masarautar kanon dabo...*

      AMMI da sauran yan uwa daga kasar zazzau har sun sauka..
Yan biyu ne tare da juwairiya a can sashen nata inda gimbiya jamila ta dauko mata wata me gyaran jiki daga can kasar chadi tun ana saura sati uku daurin aure..

Gyara dai kam ba'a mgn dan kuwa fatar juwairiya kamar ta jajirai ta koma..
ga maganguna ana ta dirka mata ita har abun ma ya fara fita kanta..

"Ko yanzu ma Ammi ce ta shigo dakin nata da wani tsumin cikin kofi ta mika mata..
Yatsine fuska tayi,ammi tace amsa mana ki shnaye..

juwairiya ta amshi kofin tana fadin..
Wlh ammi na gaji ne da shan wadan nan magagungunan..ga daci wasu ke garesu..
Ammi tayi murmushi,shanye kedai bana son gardama..
Juwairiya ta daga kofin sama ta shanye shi duka tana yastine fuska..
Ammi tace ko ke fa?
Yan biyu ne suka dakin tare da yarimaADO..

   Ammi tace toj sarakan yawo se yanzu?
Hassana tace,kai ammi yarima ne fa yadan fita damu siyayya a waje..
Ammi ta mike zata fice take fadin..
Nidai kada ku riga jan hankalin juwairiya dan bana son tana yawan yawace yawacen nan..

Ammi na fita yan biyu suka haye kan gadon da juwairiya take a zaune..
YarimaADO yace,yaya kinga..
Ya nuna mata wata wasika..
juwairiya tace menene hakan?
hussaina tace,wasika ce daga angonki yarinya..
Hassana tace,lallai wannan sarki da iya soyayya yake..
Juwairiya ta saki murmushi..cikin kunya..
Yarima yace,yanzu ya za'ayi kenan yaya?tunda ba karatun kika gama iyawa ba..
Yan biyu suka kwashe da dariya kawai karanta kowa yaji Ado..ai mu iyayenta ne..

Juwairiya tayi saurin mikewa tayi wajen ado ta fisge wasikar daga hannunsa tana boyewa a bayanta...
Dariya sosai suka shigayi mata kafin duk suka fice daga dakin..

Juwairiya ta koma ta zauna a gefen gadon tana ji wani irin dadi na ratsa ta..Amalen ta ya aiko mata da wasika?wasikar soyayya....

Ta bude wasikar da sauri ta kura mata ido..
DAGA SARKI JALALLUDEEN zuwa SARAUNIYA JUWAIRIYYA haka ta gani a saman takardai..

  Murmushi ta saki,Allah ya sota ta dage wajen koyan karatun ta..
Kwanciya tayi shame shame kan gadon ta shiga karanta wasikar da kyal kyal tana hada(words)din....

Ta dauki kusan awa hudu...tana krnt wasikar..
Sai ga Hanne ta shigo tace,ki fito ranki ya dade me gyaran jiki na jiran ki..
juwairiya ta turo baki,nifa wlh na gaji da wannan gyaran..
Hanne tayi dariya,amma ai baki ga yarda kika canza bane?
Taso muje dan Allah..
Da kyal hanne taja ta suka tafi...

""""Sarki abu-turab sashe guda ya gyara dan saukar manyan bakinsa..
(ni kuwa ina yan RUMFAR BAYI grp,ko BQ ne ma a tanadar musu😅)

An kira mawaka da masu ki'da daga kowane yanki na nigeria, ga yan busa algaita da masu hawan doki sunzo daga kasashe daban daban..

   Masarautar kano ta cika ta batse,gobe kawai suke jira...dan shafa fatiha..

Mai martaba sarkin zazzau ma ya shigo da mutanen sa,su khaleed da sauran yaransa...
An shirya babbar kilisa a filin hawa...
Sannan a cikin gidan kuma mata na can ta hada'hadar KAMUN amarya...

"Tunda ga kasar Sudan gimbiya amina tayi odar kayan da juwairiya zata saka a wannan ranar..

Wayyo Allah zanso kuga irin kyau da kwarjinin da juwairiya tayi,tasha gwalagwalai har ta gaji,ga jan lalle da akayi mata ya fito da ita shar...

    Wajen KAMU kansa jakadiya ce da kanta da sauran bayin dake masarautar suka gyara shi...gwanin ban sha'awa..

   Abinci kam da kayan kwalam ba'a mgn dan sai anci an ture..ga masu gashin nama a gefe an yanka shanu bila adadin,farfesu dai na kowane dabba a kwashi a nan wajen..

  A can na hango muku yan Team rumfar bayi groups anja layi wajen rabon abinci...
Yan pherty novels anci anko din lace sai baza ido akeyi..
Yan WATTPADIANS kuwa har da su gayyar Sodi irinsu 😅😅 deejaaat,ceecyblack,haliemahtou 530_khadeejat da sauran su..
,sai ga kuma jama'ar Taskar marubuta suma sun shigo..
Kai waje dai ya cika ya batse da mutane..

Ammi na hango rike da hannun amarya juwairiya,sai PHERTY a dayan gefen(su babbar kawa manya😉)manya..
Wajen da aka tanadar domin ta suka zaunar da ita..
Juwairiya kanta na kasa dan gani takeyi kamar mafarki ne takeyi,wai yau itace zata auri sarki jalal..?

Pherty ce ta kamo hannunta..
Juwairiya ta kalleta tace,anty faty se nake ganin kamar mafarki ne nakeyi wlh?

Pherty ta girgirza mata kai,ba mafarki kike ba juwairiya ,me yasa bazaki yarda da CANJIN kaddarar da Allah yayi miki bane?
Muna bayanki dari bisa dari kada ki damu kinji?
Juwairiya ta saki murmushin murna nagode anty faty,sannan ki tayani mika godiyata a wajen anty Afrah,wadan nan bakin da sukazo domin Ni Allah ya biyasu da gidan aljanna.......
  

*********

A masarautar daura.....
An kammala komai da komai..
Jakadiya ta tara su hansai da laure a cikin daki ta warware musu zari da abawa..

   Suma ne kawai basuyi ba sbd tsananin mamaki..
Hansai harda kwallar farin ciki..
Shiyasa naga babanta ya dawo da yancinsa?oh shine ko ya sanar min..
Laure tace,amma naji dadi wlh,kice diyarmu zata dawo garemu..
Jakadiya tace,kwarai kuwa zata dawo amma a matsayin matar Sarki jalal..
   Wani sabon farin cikine suka sake shiga..
Allah me iko....
Ai gaba daya wani karfi ne yazo musu suka ci gaba da shirye shiryen da aka saka su na tarbar bakin gobe...

"""Gimbiya kilishi da fulani ne tsohon sarki Abdul-Jabbar yayi kiran su.
Yace,ina son gobe zainaba,turaki da matarsa sannan da magaji suka bi mu zuwa daurin auren  can kanon..
Fulani tace hakan ma yayi..
Gimbiya kilishi tace,nafisa da hamza se su tsaya a nan dan tayamu tarar bakin kenan?.
Abba ya jinjina kai..
Eh haka za'ayi...

"Umayma ce ta kalli surayya,ranki ya dade ya jikin naki?
Surayya ta dake dafe da cikinta tace,anya kuwa wannan maganin na malam bazai kashe ni ba umayma?.
Kinji azabar da nake sha kuwa?cikina tun jiya ko barcin kirki ban samu ba..

Umayma ta girgiza kai,kici gaba da daurewa uwar dakina..
  Surayya zatayi mgn sai ji sukayi ana sanar da shigowar jalal....
Ai da sauri surayya ta lulluba bargo a kanta tana wani sakin lumfashi kamar wata me shan jiki sosai da sosai din na..

  Jalal ya shigo ciki umayma ta gaishe shi ta fice..
Ya zauna a gefen gado yana kurawa surayya ido..
Ya jikin naki?
Ta bude ido ta kalleshi cike da kissa tace,da sauki sarkina ya shirin bikin kuma?
Jalal ya jinjina kai,muna tayi,yanzu ma nazo ne nayi miki sallama dan gobe da sassafe zamu tafi can kanon..
Surayya kamar ta fasa ihu..
Amma ta daure..
Ai da ace lfy ta kalau da dani za'aje na dauko kanwata..
Jalal ya saki murmushi har cikin zuciyarsa yana tausayawa matansa,tunda aka fara mgnr aurensa duk suka kwanta ciwo....

Ya mike yana ajiye mata wani kulli..
Ga wannan sarka ce ta gwal da na siya muku keda khadija na cin biki..
Surayya ta washe baki,mun gode sarkina Allah ya dawo mana daku lfy..
Ya duka ya sumbaci goshinta,nagode sosai surayya....sannan ya fice tani bayan sa da kallon takaici..

*RANA BATA KARYA***

Masarautar kano ta cika ta batse da mutane daga kowane lungu da sa'ko na nigeria...
      Sarki abu-turab ba karamin farin ciki yake ciki ba zai aurar da diyarsa..

Karfe sha daya na safe sai ga yan DAURA..sun dira..
Tsohon sarki Abdul-Jabbar suka hade da mai martaba sarkin zazzau fira ta dinke a tsakanin su..

Su Jalal kuwa sarki abu-turab ya saka yarimaADO da shamaki su kaisu can masaukin su dan hutawa kafin lkcn daurin auren yayi..

Su zainaba kuwa samira ce taja su zuwa cikin gidan nan dan ita kam masarautar ba bakuwar ta bace ba...

Suna shiga sashen gimbiya amina samira ta fa'da jikinta cike da murna..
Amina ta dago ta,ashe har kun iso?
Samira tace,goggo wai ina su Ammi ne?
Amina tace suna can sashen yar uwar taki.
Zainaba ta duka ta gaishe da amina..
Amina tace,sannunki da zuwa yan mata ku karasa can din mana bari na saka a kaiku..

Ai kuwa gimbiya amina ta saka wata baiwa ta kaisu can sashen juwairiya..

   Suna shiga a falo suka iske yan biyu da firdausi suna ta hidimar su..
   Samira na yin sallama yan biyu suka mike cike da murnar ganinta suka rungume ta..
Zainaba kuwa da kallo take binsu,ita addu'ar ta daya Allah yasa ta hadu Mustapha taji dalilin da ya saka ya daina aiko mata da wasikun sa..

    Gabanta ne ya yanke ya fadi..
Ganin juwairiya ta fito tare da ammi daga wata kofa...
Ware ido tayi tana tsananin mamaki sosai..
Wuce su samira tayi da gudu taje ta rungume juwairiya tana kuka sosai..

  Juwairiya kanta sai data tsorata da ganin zainaba..
Amma jin zainaba a jikinta tana kuka sai ta shiga shafa mata baya..
Samira kuwa mutuwar tsaye tayi..
Ammi ce tazo ta riko hannun tana fadin saukar yaushe? ..

Juwairiya tasa hannu ta dago zainaba suna kallon junansu..
Tace,haba uwar dakina wannan kuka haka?
Zainaba takai mata duka,ai nayi fushi dake..
Ammi ta jawo hannun zainaba din itama ta shige dasu daki ta fayyace musu komai.
Murna sosai sukayi.
Da saurinsu suka fito falon suka sake rungume juwairiya suna taya ta murna..

Zainaba tace,ni dama na zargi ya jalal wlh,ace farat daya mutum ya canza?ta kalli samira.. sai fa kinga yarda ya tsane ta a baya ,amma lkc guda ya koma me taimakon ta ya dauke min ita daga sashena..

Hassana tayi dariya,ke baki san soyayya ake ta sha ba?
Zainaba tace ina kuwa zan sani?dan na lura ita juwairiyar ma bata dauke ni a matsayin kawar taba..
Juwairiya tayi murmushi tana sake rungume ta..
Haba kawalli ta,kinsan fa a duniyar bani da kamar ki..
Duk suka saka dariya...

"Magaji ne ya kalli jalal da bayi ke ta faman shiryasa..cikin kayan sa na alfarma..

AMALE ka fada min gsky mana?kasan dai baka da kamar ni ko?

Jalal ya juyo yana kallonsa..
Wace gaskiyar kika son ji ne Anaci?
Magaji ya zauna a kusa dashi..
Ni na san ranar hawan nan baka tsaya ganin diyar sarki abu-turab ba,toh a ina ka hadu da ita har kuka kulla soyayya haka?

Jalal ya kwashe da dariya..
Kai fa ka cika tambayar tsiya kamar wani alkali..
Toh bari kaji in fada maka.......
A nan jalal ya kwashe komai ya fadawa magaji..
Magaji ya dafe kirjinsa..
Kai amma kayiwa maza dayawa shigar sauri..
Wato a yarda nake ganin ka saida kaji saida kaji..
Jalal ya amshe..toh saida rakum'ma ne ni...fadi da kyau..!

Magaji yace,ahh lallai...wlh ni kaina naso wannan yarinyar a baya..
Jalal ya daure fuska,yace..
hattara dai magaji mallakin  AMALE ce..
Magaji ya daga hannu cikin surrender yace,ai na dade da janyewa ma...

Su Turaki ne ya shigo tare da khaleed..
Turaki Ya kallesu..
Wai har yanzu ango bai gama shirin nasa bane?jama'a na waje suna jira..

Magaji yace kasan fa yau AMALE jin sa yake kamar wanda akayi wa albishir da aljanna, gayunsa ma na daban ne Yau!
   Khaleed yayi dariya..yace
Kuma duk diyata ce sanadi ba..
Turaki yace ban gane ba?
Khaleed yace ai bazaka gane bane abokina muje na warware maka kan zaren..
Yaja turaki suka fice...

"Karfe biyu da zabi na ranar JUMA'A  ASHIRIN DA TARA GA WATAN DISAMBA..
Aka daura auren SARKI JALALLUDEEN ABDUL-JABBAR,da kuma amaryar sa SARAUNIYA JUWAIRIYYA ABU-TURAB..akan sadaki mai tsokar gaske............



@TEAM RUMFAR BAYI...
_Godiya ta musamman ga duk wacce ta samu halartar wannan bikin..
Kada ku damu akwai sauran event idan mun koma can masarautar Daura..
Dan haka ku ci gaba da kasancewa da ni AFRAH bhai.._


XOXO😘😘😘
*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 39
Wattpad @afreey101

**********************


""Bayan an gama daura aure sai kuma aka fara shirin daukar amarya zuwa can masarautar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login