Showing 81001 words to 83480 words out of 83480 words

Chapter 28 - Rumfar Bayi Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

991

ta kike ko?
juwairiya ta make kafada ni na isa nayi wa baban SARAKI zolaya?
Jalal ya mike yana fadin..
Toh bari naje wajen khadija tunda ita har addu'a takeyi danta/yarta yayi kama da ni..

Juwairiya tayi saurin mikewa tana fadin..
Nima ai na yarda..
Jalal ya kwashe da dariya yana sake rungume ta ciki da tsantsar farin ciki da nishadi...




Team RUMFAR BAYI
             *RUMFAR BAYI*
          (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 43

*KARSHE.........*

ONELOVE😘

********************

      "Washe gari...
Sai ga mai magani ta dira a cikin sashen sarki jalal..
Jalal ya saka jakadiya taje tayi masa kiran surayya da kuma juwairiya..

   Ai kuwa sai gasu sun shigo..
Surayya gaba daya jikinta babu wani karfi duk tayi laushi..
Jalal ya kalleta yace,surayya tunda kin ki sanar dani meke damunki yanzu dole ne ki tsaya me magani ta duba mana ke dan mu san halin da kike ciki..bakya ganin duk yarda kika koma ne?

Surayya ta shiga girgirza masa kai tana zubar da hawaye...tace
Sarkina nasha fada maka babu abunda ya ke damuna kada ka damu dani duk laifin da nayi muku....am...kuka yaci karfin ta..
Juwairiya ta dafa ta..a sanyaye tace..
Ah ah surayya ki bari kawai a duba ki dan hankalin mu bazai taba kwanciya ba idan har bamu san meke damun ki ba...

  Da kyal su juwairiya suka samu surayya ta yarda me magani ta duba ta..
   A firgice me magani ta kalli jalal tana fadin..
Mai martaba ai guba ce a jinin ta....

GU'BA!!!!!!
Jalal da juwairiya suka hada baki wajen fada cike da tsananin fargaba..
Ita kanta surayya sai da lumfashin ta ya dauke na wasu yan dakikai..

    Mai magani ta saka surayya ta kwanta flat a kasa,sannan ta saka wasu allulori ta tsaka su a saman ciki ta  sake fitowa dasu..
Sai ga wani bakin jini ya fito bakikkirin dashi..
Ta sake kallon jalal tace, Guba ce me tattare da bakin asiri,kuma tabbas da baku kawo ni nan yau din nan ba ina tabbatar muku da cewa a cikin watan nan zata iya rasa rayuwar dan bakin asirin dake jikinta ya gama gurbata jinin dake jikinta..

Jalal tashin hankali sosai ya shiga..
Juwairiya ma duk ta rude ta kama hannun surayya dake kuka sosai tace..
Dan Allah surayya ki sanar damu meya same ki?waye yake son kashe ki?
A ina kika ci wannan bakar Gubar?

Surayya duk a rikice take jin abunda me maganin nan ta fada..
Ta rirrike  juwairiya tana wani irin matsanan cin kuka...
Sannan ta sanar dasu duk abunda ya faru..
maganin neman haihuwa  ne da sukaje amsa a wajen wani malam can Sandamu,tunda tasha maganin ta rasa sukuni...

  Jalal  kam takaici duk ya ishe shi..
sbd neman haihuwa gashi nan  taje zata kashe kanta a banza..
Mai maganin tace..
Ni abunda ban gane ba a nan shine..
Shi me yasa malamin zai nemi ya kashe ki da bakar guda?
Bacin da kudin ki kika je wajen sa neman taimako..
Juwairiya tace nima shine na gani ai..
Ta kalli jalal tace..
Amale dan Allah ka saka aje a dauko mana wannan malamin ya fadi dalilinsa na son kashe surayya da bakar guba..
Jalal ya kalli jakadiya yace..
Kije ki sanar dasu shamaki aje can sandamun a dauko min wannan bokan malamin!!!..

"Malam sandamu a gaban sarki Jalal da sauran(royal family)...

Jalal ya kalli sarkin dorina dake tsaye yana ta bude hanci..
Yace..
idan har bai fada mana gsky ba akan dalilinsa na son kashe gimbiyar daura surayya.. toh na baka izinin lugwigwita shi a nan wajen..
   Malam na Sandamu ya hau wiki wiki da ido tsoro ya shige sa sosai..
Hamza yace..
Kayi mgn malam!!!!ko kaga tsararrakin ka a nan ne?

Malam ya zube kasa yana neman gafara yace..
Wlh tallahi babu ruwana a ciki..
Sarkin dorina ya kai masa duka mai shiga jiki..
Malam ya hau ihun azaba sannan yace..
Wallahi BAIWARTA ce,baiwarta ce wlh babu ruwana a ciki !!!!..

Jalal yace baiwarta ce?
Gaba daya wajen suka cika da al'ajabi da kuma tsananin mamaki!..

Surayya da kyal take iya bude ido ta kalleshi..
UMAYMA ta gama cutar  da ita..
har abada ba zata taba yafe mata ba..
Yanzu dama kashe ta dake da niyyar yi?
Lallai mutum abun yarda bane..

    Turaki yace,me baiwar tayi?
Malam yace,watarana ne tazo har wajena da makodan kudi sosai..
tace min..
zasu zo tare da uwar dakin ta akan tana neman haihuwa...
Shine ta biyani akan tana so na taimaka mata mu cuce ta mu bata wannan Gubar a matsayin maganin daukar cikin..
   Shine na ni kuma na hada ta da wanj bakin aljani shiyasa take ta fama da wannan ciwon ciki duk dare,aljanin ne yake zuwa yana lalata jinin ta da wannan gubar..

      Gaba daya wajen aka hau sallalami...
Nan suka tsare shi sai ya karya wannan asirin da yayi mata..
  Malam yasha bugu kamar ba gobe sannan ya karya asirin dake jikin surayya..duk ya gama tsorata..
  A Take surayya ta sume a wajen kilishi ta saka bayi suka dauke ta zuwa sashen ta..

""""""A cikin kankanin lkc labarin duk bazu a cikin masarautar...
juwairiya kam ta tausayawa surayya sosai...
Mutum ba abun yarda bane ashe dai cutar ta kawai umayma takeyi..
oh rayuwa kenan se ka rantse da Allah umayma tafi kowa san surayya...
ALLAH dai ya tsare gaba..
Amin

****************
""""A haka rayuwa taci gaba da tafiya a cikin masarautar ta daure...

Dan A yanzu kam surayya ta murmure sosai jikinta ya dawo..
dan kuwa tana samun kulawa sosai daga wajen yan gidan..
Duk da dai da farko sun ji haushin ta sosai na bin malamai da takeyi..
Sai kuma daga baya suka gane dai cewa abunda ta shuka ne ta garbe yanzu duniya tayi mata hankali..

"Wasa wasa cikin juwairiya ya fara girma gashi yanzu har yayi wata shidda...
Jalal kam na mugun son cikin nan dan kullum sai shiga sashen ta ya duba ta..
Duk kuma abunda da take so sai ya saka ayi mata shi..
khadija kam a watan nan ake saka ran haihuwar ta..

"Yau dai shirye shirye kawai akeyi a cikin masarautar dan yau ne daurin auren MAGAJI DA ZAINABA..

    Juwairiya ce uwar biki dan kuwa duk ita aka bar wa duk wani shirye shirye na bikin..
hakan kuwa ba karamin bata wa jalal rai yayi ba dan shi kam yafi so a bar masa giwar sa ta huta...

"An daura auren ne da karfe biyu na ranar asabar..

Dun'bim jama'ar kasar daura suka halarci daurin auren MAGAJI dan gidan WAZIRI da kuma gimbiya ZAINABA diyar mai martaba tsohon sarki Abdul-Jabbar..

"Amarya zainaba ba karamin  gyara tasha ba..
Dan tun sati daya kafin bikin me gyaran jiki tazo daga kasar borno ta shiga gyara ta a can sashen juwairiya.. dan nan ta dawo da zama ko su samira sai dai su leko su..

"Yau kuwa fulani ce ta aiko mata da kaya na alfarma data  saka ayi mata na musamman..
Gimbiya kilishi ma dai ba'a bar ta a baya ba dan kuwa sai data aikowa zainaba zinari me kyan gaske..

  Samira itama da tsohon cikin ta,nafisa kuwa cikin ta karamine shiyasa duk  tafi su karfi a wajen hidimar da akeyi da ita da surayya..

Dan itama Surayya dai har a wannan lkcn shiru bata samu cikin ba,sai dai a yanzu ta bar wa Allah komai ta rungumi kaddarar ta..

  Magaji ango ansha babbar riga sai washe baki akeyi...
jalal ne babban abokinsa kuma babban yayar amarya,hidima kam a ranar ba a magana..

"Karfe shidda na yamma aka fara shirin kai amarya..
Khadija dama ita tana can gidansu tunda sune dangin ango da katoton cikin ta haihuwa yau ko gobe..

An kai amarya dakin ta lafiya a can kusa da gidan Waziri magaji yayi ginin gidansa babban gaske..
taro ya watse lafiya aka bar amarya da halinta..

  Magaji kam yayi farin ciki sosai da kasancewa da zainabar sa dan kuwa a daren farkon su ba karamin faranta masa tayi ba..

Kwana biyu da auren su da zainaba..
Khadija ta sullubo yarta mai kama da ita sosai..
Jalal yayi murna sosai hakama sauran yan uwa..
Yarinya taci sunan kakar su jalal wato SHAFA'ATU

******************
Bayan wata uku..

"A yau juwairiya ta tashi da nakuda sosai..
Hansai da laure sukayi kiran jakadiya aka sanarwa sarki da kuma su gimbiya kilishi..

    Addu'a sosai aka shiga yi mata dan ta haihu lafiya dan ba karamar wahala take sha ba.

Surayya kam na gefen ta tana rike da hannunta tana tayi mata sannu..
Jalal kam ya kasa zaune ya kasa tsaye..
Turaki da hamza ne ke ta basa baki dan ya kwantar da hankalin sa..

Bayan wucewar awanni uku sai ga kukan jarirai ya cika sashen..
Nan aka hau murna bayi nata wakokinsu na nuna murna da farin ciki..
  Hansai ta kalli laure duk sunyi zufa tace..
Allahu akbar....
Yan biyu ne kuma duka maza.....!!!!!!!
Gu'da du'bu ta hau yi jakadiya kuwa tayi waje da gudun ta...

Sai sashen Sarki jalal..
Yana ganinta ya mike tsaye da saurinsa... ya taro ta hankalinsa a tashe..
Ta shiga rangwada guda tana rangwado wa jalal kirari cike da tsantsar farin cikin ta..
"Ga toya matsafa,babban Bajimi Babban Bako,Ga magajin Rumfa!
Ga........
Jalal yayi sauri tsayar da ita cike da kagara yaji da mai ta zo....dan kuwa hankalinsa ya kasa kwanciya ko kadan.....bai san halin da juwairiyar sa take ciki ba...
Jakadiya taja lumfashi kafin tace
Allah ya sauki GIWAR AMALE lafiya sumul..
ta haifa mana samari har biyu kyakkyawa kamar ka Sarkin mu..,Allah ya kawo mana TAGWAYEN SARAKAI..jinin JALALLUDEEN sarkin da ba kamar sa...!

Murna sosai Jalal yayi...
Ya rasa me zai ce sai godiya da yake ta zuba wa Allah...
turaki da hamza ne suka zo suka rungume sa suna taya sa murna sosai suma..

Sati na zagayo wa akasha bikin sunar yan tagwaye..
ba karamin kudi jalal ya kashe ba..
Mai martaba tsohon sarki ne ya radawa yaran suna..
Hassan shi yaci sunan ABDULSAMAD na biyu...
Shi hussaini kuwa yaci sunan kakansa ABDUL-JABBAR na biyu..

Sai dai gimbiya kilishi ta samo musu sunan banza kamar haka..
Hasssan wato abdulsamad zasu ringa kiran sa da YARIMA SARAKI..
Shi kuma hussaini Abdul-Jabbar SADAUKI zasu ringa kiransa dashi..

Bayan sati biyu itama samira santalo nata dan shima namiji ne,ranar suna yaci sunan JALALLUDEEN na biyu wato kawun sa sarki Amale kenan..

  Nafisa kuwa sai da yan biyu sukayi kusan wata uku sannan ta haifo yarta mace wacce taci sunan kilishi wato MAIMUNA kenan..
  Surayya baiwar Allah se dai ta zama uwar ya'ya dan kullum hanne sai ta kai mata yan biyu dan su dan debe mata kewa..
Hakan kuwa ba karamin dadi yakeyi mata ba,kullum sai tasha kukan bakin cikin yarda ta mayar da rayuwar ta a baya gashi yanzu ta cuci kanta...

Jalal kuwa har tausayin ta ya fara ji dan kullum bata da mgn sai ta Sadauki da saraki..

************
Bayan shekaru sha tara 19yrs..

"A cikin wadan nan shekarun  da suka gaba ta...
juwairiya ta sake haihuwar yan matan ta har biyu..
akwai me sunan mahaifiyar ta wato ZARAH'U fatima kenan suna kiranta da BATOOL sai kuma JAHAWIR itace karama kuma autar su a ciki..
Zainaba da magaji nada yaran su biyu suma mace da namiji..
Akwai IBRAHIM KHALEEL da RASHIDA..
Samira ma ta sake haihuwar ZEENATU...
nafisa kuwa yaranta uku yanzu itama maimuna,Ramla da halimatu..
Khadija ta sake haihuwar ABUBAKAR  da FADILA..

Masarautar daura kam ta cika da yara masu albarka da shiga rai..

"Juwairiya ce na hango ta kara girmanta tayi jiki ta kara haske ga wani irin kwarjini da ta kara....

Zaune take a sashenta..ta hakimce akan kilisar..
  ta kalli hanne tace wai ina yarima saraki ya shiga ne?
  Hanne ta buga uban tagumi tace..
Ai ranki ya dade ni na rasa me yarima saraki yake nema a cikin *RUMFAR BAYI*.... nan kullum fa sai ya matsa min akan wai shi sai ya shiga har ciki yaga irin tsarin wajen....
Nasha fada mishi Kanskanci ne ace dan Sarki kamar sa ya shiga RUMFAR BAYI  amma gaba daya ya kasa fahimta..

Juwairiya tayi murmushi tace,Saraki kenan yanzu...
Yanzu dai jeki ki kira min shi sannan ki biya sashen khadija ki kira min su BATOOL da JAWAHIR suma tunda shi sarkin yawo Sadauki yabi babansa ziyara gidan magaji..
Hanne ta mike ta fice tana fadin toh ranki ya dade ....

"Tana shiga sashen khadija ta iske yaran gaba daya yan matan sai wasa sukeyi amma banda JAWAHIR ta na can a zaune abunta tana kallonsu..
Hanne da rabi sukayi murmushi dan ba karamin burge su halayen jawahir yake ba kullum a natse zaka same ta..ga fara'a da son mutane sam bata da wata damuwa ba kamar Batool ba..
 
"YARIMA SARAKI  kuwa yana can kogin mai martaba a zaune tare da bawan sa Cigari suna shan iska abunsu..

Ya hakimce yana kallon yarda ruwa ke gudana a wajen ga iska me sanyi yana kadasa sai lumshe ido yakeyi..

  Hanne ce ta shigo wajen da sallama..
Ta jinjina kai tana mamakin irin kasaita da girman kai na yarima saraki...
Sam shi ko mgn ma wahala take masa in ba da babansa sarki  JALAL suke mgn ba toh da kyal ne kaji muryasa a wani waje..

Shiyasa take tausayawa cigari kullum sai dai suyi zaune babu uhm bare uhm uhm..
   Kirari kawai ta shiga yi masa...

Lafiya jinjirin wata sha kallo..
Lafiya sukukun bakaka..
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa.
Lafiya Gar'kami wandon karfe
Lafiya Toron Giwa SARKIN GOBE..

Kai kawai ya jinjina mata kafin a kasalance yace..
Meke tafe dake inna hanne?
Ta kalli Cigari daya tsare ta da ido..
Tace,dama GIMBIYA GIWAR AMALE  ce take son ganinka..
  Ya mike cike da nutsuwa ya kalli Cigari yace muje..
Sukayi gaba aka bar hanne tana ta sakin murmushi..

"A falon ta ya iske ta saman kilisarta..
Ya zauna yana yankwashe kafafunsa..
juwairiya ta kurawa dan nata ido tabbas dolene ta gode wa Allah daya bata ya'ya nagari masu so da kaunarta..

   "SARAKI inaso ka fada min miye dalilin ka na son shiga cikin RUMFAR BAYI?
Ya dago suka hada ido da ita..
Yace umma.....
Kawai so nake naga a inda mahaifiyata tayi Rayuwa a baya...
Juwairiya tayi murmushi..tace
Saraki kenan...
Ya dan dukar da kai yace,ki bani izinin ki gobe na shiga cikin RUMFAR BAYI..
MUMA haka UMMA...!
Sukaji muryar JAWAHIR da BATOOL  a bayansu..
Juwairiya tayi murmushi kawai kafin tace dasu...
kada ku damu yarana gobe nayi muku alkawarin zamu shiga  cikin RUMFAR BAYI..daku
Zamu canza DOKAR wannan masarautar..
Dan babu wani Kanskanci aciki..
dan kawai Jinin sarauta ya shiga muhallin Bayinsa.....
Nayi rayuwa a cikin RUMFAR BAYI kuma tabbas yana da babban tahiri a kaina..

********
"A Lkcn da jalal ya dawo tare da SADAUKI a sashen juwairiya suka sauka nan suka hade da yaran duka aka hau fira cike da kaunar juna..
Kafin saga bisani jalal ya janye matarsa sukayi sashen sa..

"Suna shiga ya jawo ta jikinsa ya Rungume ta yana fadin..
Maman yara nayi kewar ki dayawa..
Juwairiya tayi murmushi tace..
nima haka Amalena..
Ya shafa gefen fuskarta yace...
a kullum bazan bar shi miki albarka ba dan kuwa nasha fada miki KE Din TA DABAN CE a cikin zuciyar JALALLUDEEN...
Juwairiya tayi murmushin farin ciki tace..
Nagode sosai da soyayyarka ALLAH YA KUMA BARMU TARE har abada..
Jalal ya janyo ta jikinsa kafin ya amsa da..
AMEEEEN....GIWATA...

                            Karshe...

Tammat...
A yau na kawo muku karshen littafin RUMFAR BAYI...
"Idan nayi laifi ko wani sa'bo a rashin sani ina neman gafarar ka Allah...

Godiya ta musamman ga...
"Duk Fans din RUMFAR BAYI nagode sosai da Kaunar ku,na kuma gode da duk addu’o'in ku Allah yabar zumunci..

"Godiya ga dukkan RUMFAR BAYI whatsapp Groups..
"Godiya ga PHERTY NOVELS group.
"Godiya ga FATIMERH XARAH didi i love you😘
"Godiya ga WATTPADIANS u guys r just d best..
"Godiya ga TASKAR MARUBUTA group.
" godiya ga RASH KARDAM HAUSA NOVELS.
"Godiya ga QUEEN MEEMI Fans..


AFRAH BHAI LOVE YOU ALL...😘😘

Watch out for my new novel inshaAllah...
                        Coming Sooon....

And👇

Dnt forget to follow me on instagram @khadi_nana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login