Showing 27001 words to 30000 words out of 50448 words

Chapter 10 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

233

wallahi kinji na fad'a miki ki shiga hankalin ki tun wuri kisan abinda yake Miki ciwo, dan Ni babu wajen bokan da zani akan wani d'a namiji yaso y'ata , Abu d'aya zan fad'a miki shine duk wani abu da kika san yana so, to Kiyi saurin aiwatar da shi tun kafin ya sanar da ke , sannan ki ri?e mahaifiyar shi sosai Kiyi mata biyayya iya iyawar ki duk Wani abu da kika ga tana so to Kiyi mata shi cikin sauri , haka mahaifin shi duk da kema naki ne, hakan zai sa ko baya sonki idan yaga yadda kike a tare da iyayen shi to zaiji sha'awar ki kasance tare dasu kinji na fad'a miki yanzu ki tashi kije kiki kiran daya ke miki''. A hankali kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki taja hijabin ta tayi waje.

Tana zuwa a ciki mota ta same su shida Amira daga gani suna cikin nishad'i , tun da ta fito ya zuba mata ido kallon ta yake kamar wata Zahra cikin taurari duk da cewa ba kwalliya tayi ba Amma tayi kyau sosai hasken farar fatar ta da ya had'u da na rana sai ta bada wata irin kala abin gwanin ban sha'awa, har ta k'araso bai san tazo gaban shi ba Amma kuma tana yin magana ya wani had'e rai ya maze sannan yace '' sannu isashiya sai yanzu kika ga damar zuwa ko saboda ga driver kin ajiye tun d'azu nake jiran ki ina da abin yi Amma kinje kinyi zaman ki saboda kin rai nani '' ya fad'a yana wani tsare gida shi adole ga babban yaya, hak'uri kawai take bashi ganin yana ta yi mata fad'a duk da ita bata ga wani laifi anan ba Amma ya ta iya ance dur k'usawa, Wada ai ba gajiyawa bace, sai da yaga kamar zata yi kuka sannan a hankali kamar mai koyon magana ya juyo yace mata '' is okay Komai ya wuce, yanzu ki tashi kije kuyi sallama da Innah domin tafiya zamuyi, nima yanzu Zan shigo muyi sallamar'' ya fad'a yana mai bud'e motar ya fito daga ciki.
Bayan sunyi sallama da kowa suka kama hanyar koma wa gida tare da jibgin tsaraba da Innah ta had'a su da ita, Baffa har da cewa zai kawo musu masara da gyaWa idan suna so, shidai Haidar ganin ba'a kawo ba yace sun gode ma a hakan, cikin jin dad'i suka kama hanyar gida.


********************


Daga ni sai suhail da Babangida muka yi rakiyar Annah, lokacin da zasu tashi ji nayi inama tare zamu tafi sai dai ita kad'ai Allah ya kira babu ni, haka inaji ina gani jirgin su ya d'aga zuwa k'asa mai Tsarki, sai muce Allah ya sauke su lafiya ameen.

Muna dawo wa kitchen nayi domin na d'ora girki saboda yanzu nauyin y'an gida ya dawo kaina, gashi Honey jee yace yau zamuyi magana mai muhimmanci, duk da cewa nasan Humaira yau zata dawo Amma haka na zage nayi mana girki mai rai da lafiya daman ganin Humaira ne yasa na dena shiga kitchen Amma yanzu dole nayi ganin gidan babu kowa.
Bayan na kammala na zuba mana muka ci muka k'oshi sannan na jere wasu saman dining, kunna musu kayan kallo nayi sannan nace musu zanje nayi sallah idan sunji Abba ya dawo su hawo sama su fad'a min, ina gama yi musu bayanin na d'auki Abinda zan d'auka sannan na haye sama da gudu.


Duk wani fad'a da Daddy yake yi hak'uri kawai Jabeer yake bashi, kanshi a k'asa ko d'agowa bayayi , cikin bada umurni ya kuma cewa '' idan kaga ka auri yarinyar nan to ka k'addara bana numfashi adoron k'asa, kuma kar na k'arajin an tada maganar nan acikin gidan nan, ka tashi kaje ka fara shiri nan da 2 months za'a d'aura muku aure da Khadijah'' maganar k'arshe da Daddy yayi ita tayi sanadiyar d'aukewar numfashin Jabeer gaba d'aya........................







07049484066



Kuyi hak'uri da wannan babu yawa




Comments and share pisabilillahi=?O?=?O?=?O?*IZINAA*

Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan mousse* (oum Inayah)


https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

*Mikiya writers association*


07049484066


Page naki ne maman Gaicha gora taa>?p?>?p?>?p?


Page 34&35


____________________
Dai dai lokacin da ya yi wannan k'arar ita kuma Ammey ta kawo kai kenan zata shigo Wakin, da gudu tayi kanshi tana jijjashi Amma ina Jabeer yayi nisa ta yadda babu kiran da zai amsa , Duk hak'uri da kawaici irin na Ammey Amma wannan karon tsabar ya kaita bango, da kallon da yasan tun da suke shekara Ashirin da tara da Aure bata taSa yi mai irin shi ba ta juyo ta fara magana '' Babu abinda zance maka yanxu Amma ka k'addara idan ka kashe min yaro to wallahi hukuma ce zata raba mu da kai sannan ka jira dawo wata'' ta fad'a tana mai juyawa da saurin ta tayi bakin get, Malam Garba ta gani dan haka da sauri ta k'arasa sannan cikin yanayin da kana kallon ta zaka gane ba a hayyacin taa take ba, kafin tayi magana yace ''hajiya lafiya kika fito haka,, kafin ya k'ara sa magana tace masa ''kayi sauri ka biyo NI cikin gida'' Habu! Ta kwalawa Habu Kira, Habu daya ke zaune gefe yanajin rediyo da sauri ya kashe ya k'araso, kafin ya k'ara so har sun fito da Jabeer da yake a sank'ame, rubos kawai yayi yaje ya bud'e mota sannan suka kama suka shigar da shi ciki, Habu driving yake kamar zai tashi sama saboda kukan da yaji Ammey tana yi, tafiyar mintuna k'alilan ta kawo su asibitin.
Da gudu suka nufi ciki domin a zo a d'auke shi a shiga da shi, sun yi Sa'a kuwa, a kwai likitoci biyu da basu tafi, anan aka Wauko shi kamar matacce suka shiga da shi ciki, likitoci sun iya k'ok'arin su Amma numfashin shi bai dawo ba, nan hankalin su, suma ya tashi sosai, ganin babu amfanin su b'oye yasa d'aya daga cikin su ya fito yana share gumi, Ammey dake zaune ta haWa kai da gwiwa da sauri ta d'ago jim takun tafiya a gaban, ganin Dr Ammar yasa tun kafin yayi magana ta riga shi ''Dr ! Ya jikin my son?, Ya farfaWo ko , dan Allah kayi magana'' ta fad'a tana me tsare shi da idanu, ganin kamar ba'a hayyacin taa take ba yasa Dr Ammar kallon ta cikin nutsuwa da kalami mai dad'i ya ce '' Hajiya ki kwantar da hankalin ki inshallah zai tashi ya samu heart attach ne sakamakon an sanar dashi wani abu mara dad'i Amma Yanzu muna kan aiki zuwa anjima zai farka'' ita dai Ammey bata yadda ba gani take kamar b'oye mata yayi, a hankali cikin Muryar kuka tace '' Allah ya baka lafiya Jabeer ubangiji ya tashi kafad'ar ka ya Allah ka dube Ni da idon rahama kar ka d'ora min abinda yafi k'arfin zuciya ta'' ta k'arashe tana mai share hawayen ta, shi dai Dr Ammar juyawa yayi ya koma d'akin yabarta a wajan, ko kafin mintuna asibitin ya cika da y'an uwa da abokan arziki kowa ka gani fuskar shi babu annashuwa, gaba d'aya y'an gidan duk sun hallara ana jira likitoci su fito suyi bayani , Daddy shi kad'ai ne bai zo ba yana gida yayi kwanciyar shi , haka umma ganin hankalin jama'a baya kansu take bawa Ammey labarainn yadda suka yi da Daddy tace har ciki da zasu tawo ta lek'a bedroom d'in shi tace me yasa ta ganshi a gida ba Jabeer a ka kai ba Amma bawan Allah nan bud'ar bakin shi Sai cewa yayi ina ruwan shi babu inda zashi ya mutu man kanshi yayi wa asara ba shi ba , tunda bazai ji maganar shi ba ya rai na shi , to ita ma anan ta baro shi ko tsayawa taji k'arshen zancen da yake yi bata yi ba saboda haushi taji sosai duk da cewa ba tasan halin da ake ciki ba game da kai Jabeer asibiti kawai ummey ce taje take fad'awa Mama an kai Jabeer asibiti tun d'azu , wani kuka ya kwacewa Ammey jin Bayan k'iyayyar da Daddy yake yiwa Jabeer ashe har fatan mutuwa yake yi mai ''innalillahi waina ilaihi rajiun wannan wace irin masifa ce ace uba na kwarai ke yiwa d'an shi fatan mutuwa Allah ka kawo min d'auki ni Maryam'' Ammey ta fad'a tana me share hawayen fuskar ta, kasancewar Ummah tasan irin tsananin k'aunar da Daddy yake yiwa Jabeer yasa itama tasawa abun alamar tambaya, hak'uri kawai take bawa Ammey kasancewar su basa yin kishin jahilci abunsu kullum cikin tsabta suke yi ta ciki na ciki Amma yanzu ganin cewa dole ne a tausaya wa Ammey halin da suka tsinci kansu itama mama hak'urin dai take bata , sosai ta samu nutsuwar zuciya Amma idan ta tuna da har yanzu babu wani likita da ya fito yayi musu bayanin halin da Jabeer yake ciki sai gaba d'aya hankalin ta ya k'ara tashi, jugum jugum sukayi gaba d'ayansu bakajin hirar kowa sai y'an koke koke da yake tashi daban daban, ummey tsabar kuka ko Muryar ta bata fito sosai saboda idan ta tuna d'an uwan ta mafi soyuwa a gare ta yana kwance rai a hannun Allah bata san lokacin da wani kukan yake sake tawo wa ba.
****************

Ihun Ameerah shi ya sa na tabbatar da dawowar su, tashi nayi na sauka k'asa domin nayiwa yaya Haidar sannu da zuwa duk da tun lokacin da na hawo sama nake jin fad'uwar gaba, dauriya kawai nakeyi gashi na kira number Honey jee sau babu adadi bata shiga ba Amma ina kyautata zaton cewa ko wani aiki ne ya rik'e shi shiyasa bai tawo da wuri ba, da wannan tunanin na k'ara sa sauka k'asa ina fara'a ta Kamar babu komai cikin raina, da Humaira na ci karo zata hawo sama ganina da tayi yasa ta koma da baya, tun kafin tayi magana na riga ta ''sannun ku mutanen kt kunsha hanya gaskiya , ya nagan ki ke kad'ai ina yaya'' na fad'a ina mai duban parlon ko yana ciki , dawo da kallo na nayi gare ta domin naji amsar da zata bani ''to yanzu Aunty Hafsah wace tambaya zan amsa miki'' ''ko wacce ina jira na sani ko kin barmin babban yaya na a k'auye ko wata tayi wuff dashi '' na faWa da yanayin da tana ji tasan xolaya ta ce duk da ana cewa sai nayi magana ake gane cewa Ni bahaushiya ce Amma na iya abubuwan Hausawa da dama '' To yaya Haidar yana sauke mu ya juya wai yana da aiki a asibiti yau baki ga sauri da yake yi ba a hanya'' ta fad'a tana Me dariya saboda anyi mata zancen masoyin ta abin k'aunar ta, kallon ta nayi sannan nace '' Yanzu ki je Kiyi wanka da sallaloli, sai ki sauko k'asa ga abinci nan ki tawo ki ci , Ni yanzu girki zan d'ora Kinga yamma ya fara yi'' na faWa ina mai k'arasawa na shige cikin kitchen.

****************

Sai da suka kwashe sama da 1 hours sannan Dr Ammar ya k'ara fito wa, wannan karon ba Ammey ce ta tashi ba da ido Dr Ammar yayi wa Hameed babban yayan su magana shine ya tashi yabi bayan likitan office d'in su , ganin haka ita ma Ammey ta tashi da sauri tabi bayan su, suna tsaka da magana suka ji bugowar k'ofar ta , babu yadda ya iya haka yace mata ta zauna ga wuri nan, sannan ya juyo ya kalle su d'aya bayan d'aya yana tsoron abinda zai sanar da su Amma babu yadda ya iya haka ya fara bayani ''A sakamakon abinda muka gani a tare da marar lafiyar nan gaskiya a yanzu yana cikin step na kusan k'arshe, mun yi iya yin mu dan ganin wace kalar cuta ce a tare da shi da tasa yayi wannan doguwar sumewar Amma Allah bai bamu ikon ganin komai ba kawai gashi nan kamar me rai ko akasin haka, gashi munyi iya yin mu dan ganin ya tashi Amma har yanzu bai ko motsa ba, Abu d'aya zan sanar da ku idan har ya kai gobe bai farka ba to zaku iya fitar dashi waje domin akwai wani asibiti a Germany da suke da k'ararrun likitoci da kowani irin ciwo ne suna iya bakin k'okari su wajen ganin an samu lafiya , duk da yanzu ma bazamu fitar da rai da farfaWo Warshi ba, yanzu zaku iya shiga ku ganshi Amma banda hayaniya dan Allah , xan yiwa abokin aiki na magana Dr Haidar ya barku ku shiga''. Ya k'ara she Yana Mai share zufar da ta taru cikin fuskar shi.
Ajiyar zuwa yaya Hameed yayi bayan sun gama saurar duk bayanan Dr Ammar to shi duk ba haka ba suna ina duk wannan matsala ta samu d'an k'aramin k'anin nasu, da har ake tunanin fitar dashi waje, kallo Dr Ammar yayi cikin nutsuwa irin ta shi ya fara magana '' munji duk bayanan ka fatan mu ubangiji ya bashi lafiya ameen'' ita dai Ammey duk bayanan da Dr Ammar yake yi babu abin da ta gane illa zuciyar ta na bata Jabeer mutuwa kawai yayi ana dai b'oye mata ne , mikewa tsaye tayi tana bin bango har ta koma waje da su Ummah suke, Hameed kiran ta kawai yake Amma ko juyowa bata yi ba tunani take kodai wajen Daddy zata ya fara jin halin da yasa ka Jabeer tukun kafin ma tasan abinyi, sallama Hameed yayi wa Dr Ammar ya fito domin yaje yaga halin da d'an uwan sa yake ciki.

Har dare suna asibitin ganin haka sai Ammey tace ummey ta koma gida ta d'auko mata abubuwan buk'ata sannan kuma ta d'auko kayan sawa kala d'aya , drever ne ya kai ta duk abubuwan da Ammey ta lissafo mata d'auko har abinci suka bata su umma saboda su tun yamma suka koma gida, addu'a dai haka Ammey ta zauna tana yiwa Jabeer yana kwance kamar gawa duk mai imani idan yaga halin da Jabeer yake ciki sai ya zubar mai da hawaye, har garin Allah ya waye babu wani cigaba da aka samu sauk'i dai sai wajen Allah kawai za'a ce.

*********

Dariya kawai yake yi babu dad'in ji cikin dokar dajin Ni kuma a hakan da naga yau yana farin ciki sai gaba d'aya naji wani bak'in ciki cikin rai na, ko kallon shi ban yiba har ya gama dariyar shi sannan ya juyo ya kalleni da wata murya babu dad'in ji ko kad'an ya fara magana '' Ba na fad'a miki ki fita sabgar wani bil'adama ba kin k'i jin magana ta ko to yanzu gashinan sai Kiyi soyayyar da matacce dan yanzugaba d'aya na tura a cigaba da bashi wahala ta yadda ko anyi magani bazai tab'a warkewa ba, sannan mahaifin shi Ni nake zuwa ina juya tunanin shi da komi nashi ta yadda zai ta k'untata mai tunda baya jin magana nayi mai kashe di ya k'iji shiyasa na biyo ta wannan hanyar, domin ke tawa ce! Nace ke tawa ce!!'' ya fad'i haka har sau uku.
Da sauri na bud'e idanu na sakamakon baccin da ya kwashe Ni yanzu bayan na idar da sallar magriba, tare da k'allah wata mahaukaciyar k'ara na mik'e da gudu nayi k'asa kamar mahaukaciya.......................





*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?





Wallahi rashin comments yasa na dakatar da posting kwana biyu>?7?
@&?>?7?
@&?>?7?
@&?>?7?
@&?>?7?
@&?




>?p?>?p?Comments and share fisabilillahi=?O?=?O?*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedah Alhassan mousse* (Oum Inayah)

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

*Mikiya writers association*



Sadaukarwa ga ni karan kaina marubuciyar littafin=?L?=?L?


07049484066



Page 36&37

______________________
Shigowar yaya Haidar kenan yaga na fito kamar mahaukaciya abin ya bashi mamaki kuma ina kuka, tsawa ya daka min sannan yace na nemi waje na zauna, sai da na samu nutsuwar zuciya da ta fili sannan ya fara magana cikin kwantar da hankali '' yanzu ke ina zakije haka da kika fito ko wani abu aka yi miki, kin san Annah bata nan yanzu dole sai ana taka tsantsan wajen ganin mutane basu gane cewar babu mace agidan ba Amma kin fito kai ko d'an kwali babu kalli shigar jikin ki dan Allah'' ya fad'a yana mai nuna kayan da suke jikina, kafin na bashi amsa ya cigaba '' yanzu daga asibiti nake ankawo wani naga kamar saurayin ki wanda ya tab'a zuwa har muka gaisa dashi, amma na lura kamar ciwon ba na asibiti

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login