Showing 9001 words to 12000 words out of 50448 words

Chapter 4 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

235

yanke sa?a,. To Amma dai ta wace hanyar zata samu ya sota kamar yadda itama take san shi, duk wannan amsar bata da ita se taje gidan aminiyarta Laraba idan ta samu mafita to shikenan yarta ta huta da auren ?auye!.
Cikin kwantar mata da hankali ta juyo ta dafa kafaWarta sannan tace"ki bar kukan nan ya isa haka! Indai wannan ce matsalar ki yarinya to share hawayen ki ta zo ?arshe kamar kin aure da kin gama, yanzu ki tashi kije kiyi abinda za kiyi min, Ni kuma idan na gama sanwar zanje gidan Aminiya ta Laraba musan abin yi tun kafin lokaci ya ?ure mana" ta ?a rashe tana mi ?ewa tayi waje.
Duk wannan maganar da take Ita dai Lanto gani take Khalid yayi mata nisa baze taSa auran ta ba tana 'yar ?auye mara gata, da wannan tunanin ta samu ta mi?e sannan ta tafi ta Webo ruwa da tunanin halin da take ciki na san maso wani.


***********

Bayan mun gama cin abincin Humaira ta dube ni sosae sannan tace "?awata yanzu da gaske tafiya zaki yi ki barni gaskiya zan cewa Baffah ya barni mu tafi tare idan naje can birnin asani a makaranta Ni na gaji da zaman jahilcin nan damukeyi a garin nan, in yaso idan na gama karatu na zan dawo nan, idan kuma na samu miji acan to shikenan" da dariya take duk wannan maganar kuma Nima naji daWi domin xan samu 'yar uwa kusa dani wadda zataa ?ebe min kewa tunda Amira bamu fiya zama inuwa Waya ba ita gaba Waya ba halin mu Waya daita ba, cikin kwantar mata da hankali nace " kin san da nafi kowa murna idan hakan ta kasan ce, Amma ki bar1 zan yiwa Annah magana yau duk yadda muka yi zan faWa miki, Ni kin san da ace yaya haidar ce Aure ki da nayi aunty me Sona domin wasu idan suka auri yayan ka sekiga anxo an rabaka da Wan uwan ka alhalin tare aka ganku" wani murmushi me kama da dariya Humaira tayi cikin zuciyar ta ta ce hum Dan bakisan Daman saboda shi zan biku ba Amma bazan nuna ba har se ya furta min da kanshi yace yana sona wai ranar da kowa se yasan ina cikin farin ciki "Mrs soyayya yanzu dai mu tashi muje muyi wanka tukun kinsan yayan nawa baya san ?azanta kuma wannan ha?ora naki da sukayi yellow kamar anyi Sarin Worawa zan baki abun gogewa kullum kina yi so biyu ko so Waya arana, kin ga idan yaga kina gyara wa da kansa zece inba keba se rijiya" na ?ara she ina dariya itama dariya ta yi sannan tace "ina sanki ?awata kuma 'yar uwa ta Allah Ya barmu tare" cikin zuciya ta na ce "Amin"

Duk bayanin da Baffa yayi wa Annah akan muhimmanci auren da suke so yaran su suyi na zumunci bata Musa mishi ba cikin girmama wa da dattako irin nata tace" se nake gani ka bari idan mun koma gida saboda yanzu shi Khalid yayi min bayanin ze koma ?aro karatu kuma kasan bazeyi aure yabar matar sa a Nijeriya ba shi kuma yana wata ?asar ba Amma duk yadda ka gani Ni shawara nake badawa ba umarni ba a matsayi na, na mahaifiyar su" suna cikin magana suka ji an ban kaWo labule an shigo Wakin babu ko sallama, wa zasu gani, yakunbo Amina ce ?anwar Baffa cikin masifa tace" Eh naji duk abinda kika ce toni ban yarda ba Sai dai su mutu dan ba?in ciki Itama wannan me kama da Turawan salele na waje na jiya da yazo ya ganta kuma yace ita yake so ya aura yaga matar aure a gida kuma kamar anyi an gama kinji na faWa miki" cikin fusata Baffa yace mata "ke yimin shiru na faWa miki ke wai me yasa har yau bazakiyi hankali ba kullum da kalar haukan da zakiyi duk abinda kike yi ina sane kyale ki nayi bawai dan ina tsoron ki bane yasa nayi shiru to kar na kuskura na ?ara jin kin Wagawa Hadiza hankali, inbanda rashin tunani mata tazo muku ziyara Amma kullum se kinzo kin yi mata rashin mutunci to ranar da kika zo kika yi ma ta bana nan suwaiba ta faWa min kuma naso zuwa har gida naja miki kunne se wani uzuri ya rikeni amma zanyi Miki last worning karki kuskura ki kuma zuwar min gida da tashin hankali, ke yanzu salele har namiji ne da zaki ce wai yana san Hafsah to karna kuma ji tun muna mu biyu yaron da ko kwana a gida bayayi bayan haka gurgu kuma me hannu Waya shi zaki ce ta aura saboda ?iyayyar da kike wa uwar ta toni a tsari na mata su bana yi musu dole saboda ?iyayyar mace bata taSa dena ta shi namiji wataran ko baya sanki wataran kina yimishi ladabi da biyayya ze soki ya manta ya taSa ma rashin sanki to shikenan na gama magana ki tashi ki koma Wakin ki goben Kya dawo yi musu sallama da wuri za su tafi" ya ?arashe yana nuna yakunbo Amina da ta tsaya kamar wacce aka dasa atsaye tayi poster, wani ?ululun ba?in ciki ne ya tokare mata a ma?oshi ba?in ciki hassada kyashi duk suka zo suka dabaibaye ta wai yau ita ce aka yiwa wannan cin mutuncin agaban ma?iyiyarta tab aekuwa zata ga wanda ze auri Hafsah idan ba salelenn ta ba.


Bayan fitar ta yaji yo yace wa Annah "Hadiza kiyi ha?uri nasan abinda Amina tayi miki ba kiji daWi ba to dan Allah kibar komi a wajena zan Wau mataki, fatana dai Allah yasa yaran nan kar su bamu kunya musamman na wajan ki tunda sune ban san halin su sosai kamar su Jamila ba, yanzu duk inda ya kamata kuje duk kunje an rarraka ku ko?" ya faWa yana duban Annah " eh duk mun je jiya Amma wani wurin sedai suyi hak'uri tunda yanxu yamma tayi baze yiwuba mu fita" "To maashaa Allah haka ake so yanxu zan fita se gobe idan Allah ya kai mu duk wani abu da yakamata ku tafi da shi duk an tana da se fatan Allah ya kaiku lafiya" Malam mun gode da Wawainiya Allah yaji?an mahaifa ya k'ara muku lafiya da nisan kwana " ameen ameen" ya faWa sannan ya mi?e ya fita.



**********************

"Sallaman ku dai masu gida "
Lale marhabin da ?awar arzik'i yanzu kike tafe sannu da zuwa". Bayan ta yi mmata shinfiWa a tsakar gida sannan ta juyo ta kalleta tace "wata sabon gani kamar kinyi Satan hanya yau kece agidana".
"Hum dai Bari Laraba zuwan ne ba na lafiya ba"
"To naji zuwan to menene?"
Laraba ta tambaya cikin za?uwa da san jin labari.
"Wallahi ina zaman zamana yarinyar nan ta tsiri shigewa Waki ita ?aWai ko kuma ki ganta cikin tunani abubuwa dai gasunan bar katai babu daWin ji, in faWa miki da abun ya ishe Ni ranar nan dai na rutsa ta a Waki na tambaye ta , anan duk ta zayyane mata abun da tasani da Lanto ta faWa mata" tana ganin cewa kamar tasamu biyan bu?atar ta indai ' Laraba ce .
"To ke yanzu me kike so ayi ko kina so ayi masa asirin da ze sota Ko kuma zuwa kika yi na baki shawara zaSi ya rage naki" da sauri ta juyo sannan tace" komi ma ayi indai ze sota ya aure ta ina so'' ta faWa tana jin wani karfin gyiwa atare da ita" to yanzu akwai wani boka yana aiki kamar yankan wu?a zaki samu kuWi kizo muke na rakaki duk wani damuwar ku tazo ?arshe indai boka na kan tudu ne".


Yau dai cikin farin ciki da annashuwa kowa a cikin wannan a hali na mu yake sakamakon tafiya da zamuyi gida, tun safe ake neman Humaira agida annemeta sama ko ?asa babu ita Babu alamun ta wannan karon a motar yaya haidar nace zan koma, sadiq dai yace yaji daWin zuwa wannan karon hum su babban yaya kamar a Kan ?aya dama suke ko bacci ba suyi ba har gari ya waye, lokacin da aka kai musu abin kari ko kallo be ishe su ba a cewar su yau abincin gida zasu ci.
Ni dai bana ce ga yanayin da nake ciki ba nasan dai bana jin daWin jikina tunda na tashi yau sallah ma Da asuba da Annah ta tasheni da k'yar na tashi nayi ta.

Bayan duk mun shirya duk 'yan gidan suka fito rakiya Baffa ya cika mana Boot da tsaraba abin dai se san Barka Waya bayan Waya Annah ta yi sallama da kowa na gidan sannan duk muka shiga cikin mota suna Waga mana hannu.

Tafiyar awa uku ta kawo mu cikin garin Kano wannan karon ko bacci banyi ba Amira dai ansha bacci har Muka zo. Hon kawai suke danna wa ba kaWan ba. Dasauri me gadi ya tawo domin yasan da dawowar masu gidan yana buWewa suka shiga da motocin wai Alhamdulillah kawai kake ji tana tashi kowa ya fito yana hamma, me gadi da gudu ya tawo yana cewa"barkan ku da zuwa sannunku da hanya" yaje ze buWe Boot kawai yana buWewa yaga mutun akwance kamar matacce a kwance ya haWa kai da gyiwa me zeyi inba gudu ba yana cewa "gawa a mota hajiya, gawa" , duk muka jiyo mukayi inda yake nuna wa , wa, zamu gani.................

Kubawa kanku amsa. .


Labarin akwai darussa acikin sa kudai kubiyo ni

Comments and share=?O?=?O?=?O?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?**IZINAA**

Story and writing
By Abeedah Alhassan( mrs bt)


Mikiya writers association






Sadaukarwa ga iyalan madugu.



Page naki ne Abeedatou (Namecyna)


Page 12&13


_______Humairah ce tayi wujiga wujiga ina banda gumi babu Abinda take gani ma suka yi kamar ta suma, kallo Waya yaya haidar yayi mata ya Wauke kansa cikin zuciyar sa cewa yayi, wannan anyi mayya wato ma biyo mu tayo tsabar maita ai kuwa da ?afarki zaki koma ?auye ku yarinya, ya juya yayi cikin gida yana mita shikaWai, su ma saurar duk suka bi bayan sa waje ya koma daga Hafsah se Annah da Ameerah cikin sauri Annah ta kira me gadi ya temaka mata su shigar da Indo, domin tasan wa incan masu kafaffiyar zuciyar kota kira su bazasu dawo ba , ganin za'a ce me gadi ya taSa jikin 'yar uwa ta yasa na yi sauri na shiga cikin parlor na Wauko ruwa me sanyi, na bawa Annah nace ta yayyafa mata, ko minti Waya ba'a yiba ta farfaWo tana ware idanunta a kaina, ganin ta farko yasa Annah cewa''tunda kin farka ai sai ku shigo ciki asan abinyi '' ita ma taja hannun Wiyar ta ta ?ara gaba, na jiyo ina dariya nace wa Humaira'' gaskiya mun iya tsara abu cikin sau?i babu wanda ya gano shiri ne'' ta kalleni tace ''kedai bari yadda nake jin labarin birni tun ina ?arama idan kunzo na keso na biyo ku Amma innah bata so yanzu ai idan taga nayi mata hakan sai ta ha?ura, tunda nayi mata nisa'' tana yi tana dariya jin daWi, '' kin ga tawo mu shiga ciki kowa ya huce gajiya banda mu'' da sauri ita ma ta biyo baya na tana cewa ''tsaya Ni kar na Saci a hanya' kai Humaira da abin dariya take ko ina haraba ina cikin farlor da zata Sata, ko jiyowa banyi ba na ci gaba da tafiya ta, ina shiga daret sama nayi domin ruwa nake so na watsa na kwanta, duk inda nasa ?afa itama nan take sawa babu kowa a parlor kowa nasan yayi Wakin sa wasu ma hadda masu bacci ba za'a rasa ba, muna shiga Waki na juyo nace '' ki tsaya nayi wanka idan nafito kema sai kiyi'' kafin na rufe baki tace min ''nayi wanka fa jiya Kinga yau basai nayi ba'' wata dariya nayi nace mata '''lallai ma Humaira yanzu ke wankan ne dan kinyi jiya baza kiyi yau ba?" To in dai kina Kano kuma cikin gidan nan wanka in bakiyi sau biyu ba to kyayi so Waya a rana'' nayi cikin torlet na barta da tunanin wannan rayuwa data kawo kanta.




*************



Bayan na fito daga wanka na juyo nayi Wa Humaira magana itama ta shiga kawai gani nayi tayi WaWWaya a saman gado se munshari take yi, kyaleta nayi naje na shirya jikina cikin wasu riga da wando iya gwiwa sannan na Wauko hijabi ta da nakeyin sallah na feshe jikina da turaruka masu ?amshi, sannan naje na tada Humaira nace ta shiga torlet tayi wanka da alwala tazo tayi sallah, da magagin bacci a idon ta tashi ta shiga torlet, Ni kuma na tada sallah.
Tun da nayi raka'a ta farko naji ihun ta, na cigaba da Sallah ta ban katse ba har na idar azahar da la'asar sannan nayi adduo'in da nake yi na shafa har lokacin ban dena jin ihun ta ba acikin torlet Win, yun ?ura wa nayi na cire hijabi na lunke ta sannan nayi hanyar torlet Win hhhhhhh wata dariya ce ta suSuce min ganin Humaira a zaune a ?asan torlet Win tana ta kuka ga kumfa ta game jikin ta da ita hanci duk majina kamar ?aramar yarinya , cikin sauri na shiga ciki naje na kunna famfo na ruwa na ce mata taje ta Wauraye jikin nata sannan na fita ina mata dariya, a ?alla sau uku ina cema ta ''wai har yanzu baki gama ba ko sai na zo nayi miki da kaina, sai da ta shafe sama da minti talatin sannan ta fito Ni har bacci ya fara Wauka ta naji ta saman kaina tana cewa ''bani hijabi nayi sallah'' ta faWa tana Waukar dadduma ta shimfiWa a tsakar Wakin, da ?yar na yin ?ura na bata hijabi sannan nace mata '' idan kin idar nayi bacci karki tadani indai ba Abba kika ji ance ya dawo ba'' na faWa ina me sake mi?ewa saman gado na na yi kwanciya ta, ita kuma ta tada sallah, bansan lokacin da ta idar ba domin bacci na yayi ?arfi.






?AUYEN DUGUL.


Hankali Baffa be kwanta ba har sai da aka yi masa waya aka tabbatar da cewa Indo fa tana birni kuma lafiyar ta ?alau sannan kowa yayi hamdala innah suwaiba kuwa kullum cikin yiwa Wiyar ta addu'a take na Allah yakare mata ita 'yan gidan kuwa wasu cewa suka yi kwaWayi ne yasa taba da 'yar ta a tafi da ita har birni, ita dai ta toshe kunne ta illa kawai bata fasa yimata addu'a ba koma dai me zasu ce suyi ta faWa tunda gidan ?anin uban ta ta tafi ba wajan wani ba.




Sauri take suyi fitar wuri domin Laraba tace mata idan ba'a je da wuri ba koro mutane yakeyi, akuya Waya ta siyar ta har haWa da 'yan kuWaWen ta na hannun ta kuWi suka haWu se fatan nasara kawai.
Kafin goma na safe harta kammala 'yan ayyukan daza tayi, sannan tayi wa Lanto sallama ta kama hanyar gidan Aminiyarta Laraba.
Tana sallama ta tarar ita ma ta shirya ko zama batayi ba suka Wunguma sai wajan boka na kan tudu me aiki kamar yankan wu?a a faWar su masu zuwa Satattu, sun tarar wajen da layi sosse mutane sun fi ashirin masu jiran shi Amma saboda rashin tsoron Allah haka suka nemi waje suka zauna suma, wasu ma ba 'yan gari ne ba daga garuruwa ake zuwa da matan manya masu san duniya Allah ya kyauta.






********************


Abun duniya fa yayiwa yakunbo Amina yawa ganin Hadiza da iyalanta sun bar garin ba'a yi maganar salele da Hafsah ba, Gashi Baffa yace kar ta kuma zuwar masa gida indai ba alkhairi ne ya kawo ta ba. Yau ma tun safe ya ?i cin abinci sai kuka yake wai shi akai shi ya gano abar ?aunar sa, ta yi lallashi tayi banbakin duk abanza, har sai da tayi mishi dabara tace masa '' kayi shiru salele na zan aura maka Hafsah na kawo maka ita har gida, kabari tunda ance baka da lafiya to shikenan zan je har birni na auro maka ita wajan baban ta, shi ai yana da tausayi ze baka idan na faWa masa halin da kake ciki'' ta ?ara she tana daWa bashi baki, wani irin hangame baki yayi wai nan dariya zeyi wai waya ga shantu riders Ashe haka bakin salele yake wai ?ofar shadda kenan wawakin uban can, dawata ?atuwar halitta murya ya buWe baki yace '' kyale su innah ae dama temaka musu zanyi na auri 'yar tasu tunda since basaso to shikenan na fasa 'yar tasu ma sauran aljanu ai Ni yanzu ko a ?afa aka ?ulla mun ita da gudu zan kunce suje su ji?a ta su shanye babu me auren ta da aljanu gari guda akanta'' ya faWa yana wani buWe wa kamar wani horo, shi adole yayi abin arzi?i cikin jin daWin abin da ya aikata ya tashi ya fita har yana cewa'' innah yau zan siyo miki tsiren haladu me nama Kar kiyi bacci da wuri''
''Kai yaro dai yaro ne yanzu ya gama Waga min hankali Amma dubi abin da yake cewa'' cewar uwar salele angon Hafsah me rundunar aljanu .










Cikin Bacci naji hayaniyar Amira tana tashi na '' Aunty ki tashi Abba ya dawo tun Wazu yana neman ki'' ta faWa tana nunamin abinda ya bata yanxu, babu shiri na sauko daga gado nayi torlet da gudu, wajen Humaira ta koma itama ta tashe ta sannan tace'' Abba yana neman ku gaba Wayan ku yanzu yace kuxo ke da Aunty Hafsah'' tana gama faWa tayi ?asa da gudu.


Kowa ya hallara cikin babban parlon gidan, Annah tayi masa bayanin yadda akayi Humaira ta biyo su da kuma shawara da ta yanke na cigaba da ri?on ta har Allah ya bata miji tayi aure, duk wannan jawabi da take yi kowa yana jin ta babu wanda yace komi har ta gama sannan na tashi naje gaban Abba nace '' Abba ina wuni wallahi nayi missing Winka sosai daman kai kaWai ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login