Showing 24001 words to 27000 words out of 50448 words

Chapter 9 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

243

kuma jikina duk babu dad'i sallar asuba ma sai da Annah tayi da gaske wajen tashi na, kasance War yanzu Ni da Humaira kowa d'akin shi daban, an raba mana d'aki.
Baayany na yi sallah , har zan d'auko Alkur'ani kawai sai naji wani b'acin rai ya taso min
Fasa d'auko wa nayi kawai na koma na kwanta ina tunanin mafarki da nayi jiya.

Shirye shiryen tafiyar Annah ya kan kama, yau ya rage saura 3days, su tashi addu'a Annah ta dage sosai musamman saboda yaran ta mata na Allah ya tsare mata su har taje ta dawo, a cewar ta babu inda zasu je, a gida zasu zauna tun da yaya Haidar yana nan sannan ga Abba sadiq ne yace shi dai gidan abokin Abba Alhaji Abubakar me sunan shi zashi, kuma tayi na'am da tafiyar tashi , yau tun safe ya tafi shi ya riga ta ma tafiya, mu dai munce asauka lafiya Malam Garba sunan da ya tsana duk duniya a kira shi, da shi,.

***

Har na fito daga d'aki na zan sauka k'asa naji ringing d'in waya ta, da sauri na juya na koma cikin d'akin, sai a yanzu na tuna ashe na kunna wayar tun jiya da daddare, sai da na nemi waje gefen gado na zauna sannan na d'auka tare da cewa '' Assalamu alaikum'' shiru naji, sakamakon wanda ya kira ta b'angaren shi bai yi magana ba, har zan a jiye sai naji wata murya me dad'i da karsashi anyi magana da ita ''wa'alakumssalam! Farin ciki na, da fatan kina cikin koshin lafiya?'' wani sanyi naji sakamakon jin dadad'an kalaman da yayi amfani dasu wajen yin magana, cikin sanyin murya danake da ita nayi amfani da ita nima nace ''ina wuni'' dasauri ya amsa da cewa '' lafiya k'alau ya gida dasu Amira,, ''duk suna lafiya'' na bashi amsa da yanayin rashin sabo, can kamar ba zai sake magana ba naji yace ''me yasa baki kunna wayar ba? Ko dai bata yi miki ba??'' gyara k'wanciya ta nayi kasancewar tun da muka fara wayar ban san lokacin da na kwanta saman gadon ba, sannan nace ''a'a ba haka bane'' ''to fad'a min menene'' ya fad'a yana me kwaikwayon murya ta, rufe fuska ta nayi kamar yana gani na ganin babba dashi yana Muryar yara kama ta, sai naji ya bani kunya ma, Amma dake namiji shi babu ruwan shi da jin kunya ko ajikin shi, haka yaci gaba da tsokana ta ta hanyar da yasan zai dad'a siye zuciya ta sai gashi ina dariya harda k'yalk'yalawa kamar ba nice me jin kunyarsa ba, kalamai kala kala haka na rink'a jin su abakinshi, bai kyale Ni ba sai daya ya tabbatar ya dasamin k'aunar shi cikin zuciya ta, Sannan ya ce shifa kamar yadda yayi min =?? Shima sai nayi masa, wata mashahuriyar kunya ce ta kamani Amma haka yace dole sai fa nayi haka babu yadda na iya haka nan sai da yasani nayi Abinda tunda uwata ta haife Ni ban tab'a kwtanta yi ba, ai kuwa da sauri na kashe kiran, ina jin shi yana farin ciki kamar wanda a kace an bashi kyautar aljanna, juyowar da zanyi naga Humaira na yin dariya har da rik'e ciki, sai ji nayi tana cewa'' gaskiya Aunty Hafsah kun iya love da yaya Jabeer, au na manta, Honey jee naji kince Wai gaskiya sunan yayi dad'i kamar ba a Nijeriya ba '' ta fad'a da yanayin xolaya irin Tata , murmushi nayi kawai na juya mata baya , da k'arfi nace ''idan kin gama tsokanar tawa ki jamin k'ofa, ko kuma wallahi kinji na rantse yau idan yaya Haidar ya dawo in fad'a masa ince kina son sa'' A0 ko tsayawa taji k'arshen zancen bata yi ba, ta arce a saba'in tana cewa '' Na wuce islamiyya tunda ke kin tsaya soyayya''

****

Da wata kalar murya yayi amfani da ita wajen yi mata tsawa Abinda tunda suke bai tab'a yi mata ba shine tsawa Amma yau jin Abinda take fad'awa bil'adama yasa duk ya rud'e ya rasa nutsuwar shi, ''idan kika kuskura kikayi soyayya da wani bil'adama ki tabbata kwanan shi ya k'are kuma kar ki tuhumi kowa Ni ne nan na kashe shi'' ya fad'a da wata murya da gaba d'aya dajin sai da ya amsa, kallon gefen shi tayi ganin yarinyar ta d'aya kwance kamar mara lafiya ya ta tambayeshi meya samu hulwa, nan ya kuma jin wani haushi ganin ta banzatar da su shi da yaran ta, gashi daman kwana biyu idan yaje inda take yana shan wahala kafin ta bashi hakk'in shi, Ni ko nace kiji k'arfin hali daman tsakanin mutum da aljan akwai mu'amala ma bare harda hakk'i?=??, Kuka kawai take tana bashi hak'uri da k'yar ta samu ya hak'ura, ganin masoyiyarsa cikin wani hali, sosse yayi mata gargad'i akan kar ta kuskura taci amanar shi tukun suka lula duniyar gajimare.
Firgigit na farka daga baccin da ya kwashe Ni bayan fitar Humaira, cikin Muryar kuka na d'aga hannu na sama nake cewa ''innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah gani gareka ka kawo min mafita cikin al'amura na, ubangiji na rok'e ka ka kare min masoyina aduk inda yake, Allah kar kaba shi ikon cutar da bawan ka, ya samadu ya hayyu ya k'ayyum ka yimin tsakani da wannan mugun , Allah kabani ikon sanar da iyaye na halin da nake ciki, ya zuljalalu wal ikram'', mi k'ewa nayi naje nayi wanka sannan na d'auro alwala nazo na shinfid'a sallaya duk da lokacin Sallah da saura Amma haka nayi tayin nafila, har sai da naji k'afa ta na neman gagarar d'auka ta tukun na zauna na cigaba da adduo'i, har sai da aka kira sallah magriba Sannan na mik'e nayi, ina jin dawowar Abba kamar na sauka sai kuma na share na kwanta gefen sallaya, saboda gaba d'aya jiki na ciwo yake min, ina kwance naji Amira ta shigo da gudu, bata ma kula da ina k'asa akwance ba tayi tuntub'e da k'afa ta sai cewa take '' Kiyi hak'uri Aunty Hafsah tun d'azu Annah take Kiran ki Kuma so biyu ina shigowa kina bacci, shine yanzu tace nazo na tadaki kiyi sallah'' kallon ta nayi kamar na samu TV ganin ita batasan komai na rayuwa ba nishadi kawai takeyi, ahankali na ce mata '' kice nayi sallah t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?un d'axu'' na maida kaina na koma yadda nake, da gudun ta kuma fita yanzu ma inajin sautin saukar ta kamar bibbiyu take had'awa ma, Ni dai ban san lokacin da bacci ya kuma awan gaba dani ba.


*****

Kuka take sosai sakamakon jin wata irin shak'uwa da take yi tun d'azu ,gashi gida babu kowa daga sai Lanto a gidan tun bayan mutuwar mijin ta kasancewar ita kad'ai Allah ya bata, yau tun safe da suka tashi jikin ya dad'a rikicewa ga cikin ya dad'ad'a girma kuma tun da abin ya faru ko asibiti bata tab'a Kaita ba, sai jik'e jik'e su take bata=?? rungume ta ta sake yi ajikin ta duk da nauyin da ta k'ara yi Amma haka ta ke rungume ta ajikin ta, haka suka kasance tun safe tana shan wahala sai abin ya lafa sai kuma da an jima kad'an ya dawo, ita kanta innah kulu ranar babu abinda ya shiga cikin ta, bacci ma rabi da rabi ta yi shi, nadama da danasani babu wanda bata yi shi ba awannan dare tausayin y'ar Tata ya cika mata zuciya, fatan samun lafiya kawai take mata.

Cikin bacci taji kamar Muryar Lanto na magana, da sauri ta mik'e tana jijjigata , ''innah ki yafemin mutuwa zanyi , inajin ciwo sosse na biyewa San zuciya ta Saboda gashi yanzu Ban samu komai ba sai zunubi ! Innaii idan kin had'u da Indo kice mata ta nemamin yafiya a wajen Khalid, sannan tace masa da soyayyar shi na koma ga Allah, ina sonshi! Ina sonshi!! Inaaa anan rai yayi halin sa, kullu nafsin zaikatil mau, Allah ya jik'an ki lantana, abinda Innah take ta Nana tawa kenan , bayan ta tabbatar da cewa Lanto ta riga mu gidan gaskiya, Idan Allah ya tsara abu to babu wanda ya isa ya dakatar da ikon shi, gadai Lanto yadda Allah yayi da ita duk burin da aka ci be tabbata ba sai dai aje lahira da tarin burika, Yanzu gashi an tafi tafiya ta har abada babu dawowa.

Kwantar da ita tayi sannan taja lullub'i ta yafa mata , ita ma taja gefe tana kuka a haka har gari ya waye, sannan taje ta sanar da y'an uwan baban Lanto da megari da wanda ya kamata yasani.
Duk wani abu da Yakamata ayi anyi mata , jama'a ko ta ina cikin k'auyen nasu sunzo wajen jana'izar, wasu ma wucewa suka zo yi suka gani haka aka d'unguma bayan ance innah tazo tayi mata addu'a, aka kaita gidanta na gaskiya, Allah Sarki rayuwa ubangiji kasa muyi kyakyawan k'arshe duniya da lahira.

Nan fa Gulma kala kala ta cigaba da tashi a gidan mutuwar.
Gidan su Indo mazan gidan duk dasu akayi jana'izar Lanto shiyasa suna komawa Baffa ya sanar da Innah suwaiba zancen mutuwar, anan yake cewa '' ya kamata a sanar da Indo rasuwar k'awar Tata'' ''Haka ne malam nima abinda nake tunani kenan Amma bari na aika isuhu d'an wajen salame ya aro min waya wajen Ramatu na kira Hajiyar na sanar da ita ya kamata tazo gaisuwa'' ta fad'a tana me share guntuwar k'wallar da ta zubo mata cikin idanunta.

Kuka sosai Humaira tayi bayan ta samu sak'on rasuwar Aminiyarta Lanto Amma babu yadda ta iya haka ta share hawayen ta, tana fatan Allah yasa Abba yace zasu je je gaisuwa, ilai kuwa da daddare suna zaune a farlon gaba d'ayan su, Abba ya dubi b'angaren da yaya Haidar yake sannan yace ''Ka shirya gobe za kuje Katsina wajen addu'ar uku da wuri kusamu ku dawo da wuri zaka kai su Hafsah'' ya fad'a da yanayin bada umurni ba shawara ba, dasauuri na d'aga kai na na dubi Abba jin yace hadda Ni za'a sannan nace '' Abba bani da lafiya kuma kaga gobe Annah zasu ta shi ina so na raka ta eaport'' ta fad'a da Muryar da kana ji kasan bata da cikakkiyar lafiyar, ''to shikenan suje da Amira '' Abba ya fad'a Yana kallon yaya Haidar da yayi kicin kicin dashi , murya babu amo ko kaWan muka ji yace ''shikenan Abba Allah yakai m? goben''' yana gama magana ya tashi yayi d'aki zuciyar shi cunkushe kamar yayi kuka dan dai Abba ne yayi magana amma wallahi da babu inda zashi da wannan y'ar k'auyen, daga haka kowa ya tashi yayi d'akin shi, kasancewar ankawo k'arshen firar.


******

Da safe suka kama hanyar Katsina da tarin tsarabar da Abba da Annah suka had'a mata takai wa Baffa da mutan gida, sunyi sallama da Annah kasancewar kafin su dawo ita kuma ta d'aga k'asa mai tsarki, murna awajen Humaira ba'a maganar ta gefe guda kuma tana alhinin rashin k'awar ta da tayi, tafiyar kurame ita ce ta wakana tsakanin oga Haidar da Madam Humaira, i, Amira dai tayi bacci tun kafin su wuce gidan mutum d'aya, sai can kamar me jin bacci yace ''wai ke mayya ce tun d'azu kike kallona'' ya fad'a yana kuma tsare ta da ido, sai yaga kamar ba ita ba ganin wani kyau da tak'ara yi kamar ba ita ce wannan me yellow d'in ha?oran ba da suka zo da ita aboot d'in mota, ko dan baya kallon ta , shiyasa yaga kamar an canza ta, da wannan tunanin suka shiga cikin jihar Katsina, anan ya samu wani wajen cin abinci me kyau ya fita yaje ya siyo ya dawo, saboda yasan bazai iya cin abincin k'auyen ba.
Tafiyar 30 minutes ita ta kawo su cikin k'auyen DUGUL, a hankali har ya shigo layin gidan Baffa kasantuwar yasan gidan sosse , ko tsayawa ya gama parking Bata yiba ta bud'e da gudu tayi cikin gida tana k'alawa innah kira ''Innaaaaa'', tsayawa yayi yana kallon ta tana gudu shi gani yayi kamar ma ba gudu take yi ba, Muryar Amira yaji tana cewa ''yaya har munxo?'' firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya fad'a sannan ya rok'e hannunta duka shiga suma cikin gidan.................









>?p?>?p?Comments and share fi sabillillah=?O?=?O?=?O?*IZINAA*


Story and writing

By.

*Abeedatou Alhassan mousse* (oum inayah)


Mikiya writers association


https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1


Wannan page d'in sadaukarwa ne ga duk masu suna Hafsat.


*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?




Page 32&33


____________________
Da tunanin sauyawar da Humaira tayi ya k'arasa cikin gidan. Murna sosai innah tayi na zuwan d'iyar Tata , ganin tana cikin kwanciyar hankali babu wata matsala a tare da ita, nan fa y'an bak'in ciki aka rasa yadda za'a yi ganin ba 'yay'an su bane suke hutawa yasa wasu a cikin gidan ko da ta je gaishe su ba duka ne suka amsa ba, sai kuma da suka ga Haidar da tsarabar da ake ta shigo wa da ita nan fa akayi ta fara'a ana yak'e wanda aka ce yafi kuka ciwo, har cikin d'akin innah suwaiba wannan karon Haidar ya shiga ya gaisheta da mutuntawa, kamar ba shi bane lokacin da aka zo ko tsayawa su gaisa bayayi, Itama innah tayi farin ciki da sauyin da aka samu.
A gurguje ganin lokaci yana ta tafiya, bayan sun ci abinci sun huta sannan ta tafi taje tayiwa inna kulu ta'aziyya, anan innah ta yiwa Indo bayanin gaba Waya halin da suka shiga da irin wahalar da Lanto ta sha alokacin da suka san da cikin, kuka kawai Humaira keyi tunda ta fara yi mata bayani, wani tsoran Allah ne ya sake shigar ta lokaci guda domin duk halin da k'awarta ta shiga itama ta shige shi, banbanci ita ba taje wurin boka ba, a hankali ta juyo ta kalli innah kulu wadda gaba Waya tun mutuwar Lanto ta zabge ta rame babu ko rabin ta, cikin yanayin tausawa tace ''Yanzu innah ke kad'ai zaki cigaba da zama cikin gidan nan?'' dariya tayi kamar babu Abinda yake damun ta sannan tace '' uhm ke banda abinki Indo wanene yanxu zai yadda ya bani yaron shi bayan ansan duk Abinda Ya samu Lanto da sa hannu na'' ita dai Humaira tausayi innah kulu take bata sosai fiye da tunanin mai tunani a hakan dai suka rabu tayi wa innah sallama bayan ta aje mata kayan abinci da y'an kud'ad'e, godiya tayi har da kukan ta tunawa da d'iyar ta ta da tayi.

Bayan ta koma gida gaba Waya ta kwashe labarin da Innah kulu ta bata ta fad'awa innar ta, nan ita ma har da kukan ta na tausayin Lanto, cikin kuka Humaira ke cewa '' Innah! Inshallah zan ringa yiwa Lanto sadaka ubangiji ya yafe mata duk kan kura kuranta, duk da cewa rabin abin innar su ce mai laifi, Tun farko da bata ce mata suje wajen boka ba to ita bazata kawo haka cikin ranta ba, duk da shi Allah gafurirrahim ne, fatan mu dai ubangiji ka yafe mata'' ta fad'a tana mai share hawayen da suka gangaro mata saman kun cinta, suna cikin wannan tattaunawa Amira dake wajen yaya Haidar ta shigo tana cewa '' Aunty Humaira kizo inji yaya yana waje'' tun farkon ambatar sunan shi da tayi taji wata iri yar fad'uwar gaba Amma haka ta dake kamar babu komai saboda kar innah ta fahimci akwai wani abu, cikin sakin fuska tace '' yauwa y'ar autar Annah kije kice masa sallah nake yi'' jin wannan shahararriyar k'aryar da ta shirga tasa da sauri inna tace ''ki ce ga tanan zuwa'' ta fad'a tana mata wani kallon baki da hankali, bayan fitar Amira innah ta juyo ta kalleta da wata kalar harara da bata tab'a ganin innar Tata tayi mata ita ba Amma yau saboda tace a cewa Haidar tana sallah shine innah duk ta tada hankalin ta, cikin maganar da kana ji kasan hadda fad'a aciki innah tace mata '' ki zauna sakarai yaje waje ya nemi mata tunda ke baki da hankali, in banda ke wawiya ce yaushe yanxu ake yiwa maza wula?anci bayan neman su ake ido rufe, kina kallo tunda kuka zo gidan nan ake dama dama dani , Domin su gani suke yi auran shi zakiyi, Amma ke kamar ba Birni kika je ba inda wata ce har sai ta zauna ya kirata sannan ma zata tafi, to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login