Showing 18001 words to 21000 words out of 50448 words

Chapter 7 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

232

zaki ji amsarki inshallah'' ya fad'a yana mik'e wa yayi hanyar waje , suma duk suka mik'e kowa tayi b'angaren ta daman murja b'angaren Ummah take Ammey ce kad'ai tayi nata sashen ita kad'ai sukuma suka tafi tare. ** *****
Yunwa naji sosse bayan na fito daga wanka nayi sallah, a lokacin na tuna rabona da abinci tun safe gashi yanzu wajen biyar na yamma, yunk'urawa nayi na mik'e na sauko daga gado saboda nasan Bacci zai iya d'auka ta yanzu 'yar wannan kwanciyar da nayi, shiyasa na sauko k'asa naci abinci'.
Ina saukowa nayi ido biyu da dodon namu yana kallon matattakalar benen daman Ni yake jira na sauko ya tambaye Ni inda muka tsaya har ya riga mu dawo wa gida, wani ts'orone ya cikani kamar na koma sai kawai nayi shahada na k'arasa saukowa, daga gani dai ansan bani da gaskiya, salin alin ya kyaleni naje kitchen na d'ebo abinci duk a tunani na babu abinda zai ce min, na zo zan wuce ta gaban shi da kwano a hannuna, har na gota naji ance ''ke'' ''innalillahi shikenan tawa ta k'are yau na kad'e har hanji na'' Iya abinda na furtawa kenan cikin zuciya ta saura kad'an kwanon dake hannu na ya fad'i.................





Ina sane da masuyimin comment



Comment and share fisabillahi=?O?=?O?=?O?**IZINAA**


By.
**ABEEDAH ALHASSAN (oum inayah)**

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

**Mikiya writers association**



Sadaukarwa ga iyalan madugu.
Gaisheku 'yan uwa na rabin jiki Allah ya k'rasa had'a kawunan m?.


Godiya ta musamman.
Surayya b. Abdul d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a gudummawar da kike bani ubangiji yaraya zuri'arkii


Page 24&25



----------Hafsat gudawa ce kad'ai ba tayi, a tsaye ba, cikin tsare gida da ya saba yi musu yace ''ina d'an kwalin ki? Sannan kuma dubi kayan jikin ki, kamar ba y'ar musulmi ba! Kwana biyu kin ga bana zama a cikin gidan shiyasa kika dad'a lalacewa, yanxu dan Allah sai abu ya samu Aceh kuma me?' Yanzu haka nasan haka kika fita kamar y'ar arna kina yawo, kai babu komi kayan jikin ki ko rufe ki basayi, Ke ba kya tausayin kanki ko?, kin san ba Lafiya ce ta ishe ki ba, Hafsah ki tausaya mana muma 'yan uwan ki dan Allah kidena wannan banzar shigar ko dan lafiyar ki, ba sanki ne Bama yi ba, A'a duk duniya babu wanda zai soki kamar yadda muke sanki m? y'an uwan ki!'' Ya sassauta murya cikin kwanciyar hankali yake min magana kamar ba yayan da nasani ba, ban gama jin bayanin da zuciya ta take yi ba na tsinkayi muryar Yaya yana magana ''ki nutsu dan Allah kidena wannan abubuwan da kike yi kinji y'ar k'anwata'' ya fad'a da murmushi a fuskar shi kamar ba shi ba, ''to yaya inshallah zaka same Ni me jin maganar ka'' ''yauwa tashi kije ki ci abincin kinji saura idan Abba ya dawo kice nayi miki fad'a'' sum sum na tashi na haye sama da gudu, sai jiyo dariyar su Amira nayi saitin d'akin Annah, ashe suna wajen suji ko duka na yaya zai yi basusan nasiha yayi min ba ''munafukan banza'' na fad'a ina me k'arasa shiga d'aki na.


***

Bayan wasu watanni abubuwa da dama sun faru ciki hadda kammala karatun Hafsah na ssce Alhamdulillah nasa mu kyaututuka da dama ciki har da kujerar Makkah da wani bawan Allah yazo taron yaye d'aliban ya ji irin k'ok'arin da nayi, b'angaren Islam ma ba'a barni abaya ba Masha Allah dai dai gwargwado ina ganewa yanzu haka sauran y'an watanni nayi saukar Alkur'ani mai girma, b'angaren rashin lafiya ta yanzu abu yafi na da saboda sai na kwanta xanyi mafarki kamar namiji na amfani da Ni ko nayi mafarki yara k'anana sun zagaye Ni abubuwa dai gasunan barkatai Kuma na kasa sanar da kowa kullum cikin tunani na ke, k'awa ta kullum cikin tambaya ta take me yake damuna amsa Waya nake bata ita ce, babu komai' shiyasa ta ha?ura da tambaya ta.

Bayan mun dawo gida Abba ya ke tambayata ya za'ayi da kujerar, cikin ladabi nace ''Abbah Ni bazan iya tafiya ba yanzu saboda muna cikin tsaka Da karatun sauka sai dai ko Annah ita ta tafi idan ina da rabon zuwa Ni ma watarana zanje''
''maasha Allah haka ake san y'ar albarka Allah ya nuna min sauka taki dakai na zan biya miki kije inshallah'' Abba ya fad'a tana me shigewa b'angaren shi.
Annah taji dad'i sosai saboda tayi shekara rabon da taje k'asa me tsarki, tayi alfahari da samun y'a kamar Hafsah, yanzu sai shirin komawa karatu na addini da zanyi kodan matsala ta.


****

Tun da Daddy yayi zance fito da miji umme ta ke tunanin wa zata ce shi ne zab'in ta, duk ta rame tak'i cin abinci daga gado sai torlet shima saboda wanka da sallaloli ,da k'yar Ammyn ta lallab'a Daddy' ya yadda banda umme a maganar auren Amma yace nan da shekara biyu ko d'aya idan bata fito da shi ba to kowane zai had'a ta da shi, Khadijah dai tayi magana da saurayin ta Abubakar kuma yayi na'am har ya turo iyayen shi sunyi magana da Daddy' an tsayar da lokaci k'arshen shekara yakama wata hud'u masu zuwa idan Allah ya kai mu, biki biyu xa'a yi kenan, Jabeer da Khadijah Sannan Abubakar da Khadijah , kowane b'angare ana farin ciki Amma banda ango Jabeer idan ya tuna wacece zai aura sai yaji kamar ya had'iyi zuciya ya mutu, kullum tunanin ya'r buzuwar shi yake yi da komi nata burgeshi yake, ko wajen aiki baya zuwa idan ma ya fita zuwa yake yasamu saitin layin su Hafsah yayi parking na motar shi ya k'urawa gidan su ido har sai lokacin da yaga rana ta take sannan zai bar layin.


''Mommy yau baki kawo min chacolate d'in nan me dad'i ba! Kuma Daddy' yace zaki kawo min, gashi kuma kinzo babu'' cewar wata yarinya da kallo d'aya zaka gane ba kalar yaran mutane bace duba da irin halitta da take dashi idanunta wani launi mara kyan gani kan ta yayi wani girma da ko cikin jin sin aljanu babu kyan gani, nayi iya yina dan na gano kalar siffofin jikin ta amma na kasa saboda tsoron abin da wannan da ta ambata da sunan Daddy' zai min idan ya gane d'aukar rahoto nazo yi masa.

''Innalillahi wainna ilaihi rajiun'' Abinda na furta kenan bayan na farka daga wannan mummunan mafarki da nayi, duk da bashi ne karan farko da nayi irin shi ba. I

Yunk'urawa nayi ina layi na shige torlet kaina babu ko d'an kwali Amma haka na shige idanuna ko ganin gaba na ba nayi.


Yau ya k'udur ce cikin zuciyar shi,sai ya je gidan su Hafsah kuma yau da k'warin gwiwa zai tafi, shirya wa yayi cikin had'ad'd'iyar shadda shi, sai walwali take yi, ya d'auko agogon sa, k'irar Gucci, maashaa Allah ab1n da na furta saboda kyan da yayi kamar a k'asar larabawa, dama shi Jabeer kaf gidan yafi su kyau da tsarin halitta ga farin jini tun yana yaro shiyasa komi nashi ya bambanta da na sauran ya'yan,
A hankali ya fito daga b'angaren shi, taku yake dai'dai kamar ba zai taka k'asa ba, dai' dai lokacin Khadijah ta fito zata aiki drever ya siyo mata kati ta ganshi ya shiga mota, wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare mata mak'oshi kishi tuni ya tun k'ureta, babu shiri tayi cikin gida da gudu ko aiken kasa tsayawa tayi ta bada.


*****


Sallamar da naji Humaira nayi daga bakin k'ofa ita ce ta ankarar dani daga tunanin da na fad'a, da sauri nayi abinda zanyi duk da zuciya ta babu dad'i haka na daure nayi wanka na d'auro alwala na fito, yanzu da tangad'i na fito, da sauri Humaira ta kamo Ni sannan ta zaunar dani bakin gado tana ta jeramin sannu, da kai na nake amsawa saboda baki na wani irin nauyi yayi min, ganin yanayin da nake ciki yasa ta fara karanta min adduo'in da ta iya, duk da babu laifi yanzu ta iya wasu abubuwa saboda tana fahimta sosai, Alhamdulillah wata nutsuwa naji tana shiga ta Saboda adduo'in da take min, fuska na bud'e ina kallon Humaira Sannan nace ''yaushe kuka dawo daga islamiyya'' yau ban ji d'uriyar Amira ba shiyasa na tambayeta ''d'azu muka dawo, na shigo kina Bacci har Annah tace yanzu kika kwanta! Yanzu ma bak'o kika yi, yana sittin room, Annah tace ki sauko yanzu'' ta fad'a tana me mik'ewa tasaye tayi wajen kayana.

Komai da xansa itace ta d'auko min ina zaune Kamar mutum mutumi, doguwar riga kawai nace ta bani nasa ko mai ban shafa ba,turare na mutsuka sannan na mik'e na fito dan naga wanda yake kira na................




Ina sane da masuyimin comments






Comments and share fi sabillillah**IZINAA**



By.

**Abeedatou Alhassan mousse (oum inayah)**



**Mikiya writers association**



https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1



Ina masu san a tallata musu hajar su, sai su tun tube Ni a wannan number akan farashi me sauk'i.
07049484066


A guji satar fasaha da masu yin audio babu izini da masu haWa da comment ko baka ce komai ba Allah yana kallo wahala tane dan haka a kiyaye.



*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?.



Page 26&27


______Da sallama na shiga a baki na, karon farko da nayi mai kallon tsaf domin ya juya bayan shi, dogo ne irin wanda da an kalle shi za'a kira shi dogo, ban samu damar kallon face na shi ba saboda ya juya baya, Jabeer tun lokacin da ta shigo yaji a jikin shi a kwai mutum a bayan shi, amma bai jiyo ba har sai da ta sake yin sallama a karo na biyu sannan ya juyo, ya nemi d'aya daga cikin kujerun farlon, yana me kallon b'angaren da nake, cikin jin nauyi nace ''ina wuni'' duk da bana jin daWin jiki na Amma haka zan daure kar yaga gazawata, kallo d'aya nayi mashi naga ya tafi da zuciya ta Saboda a gaskiya guy d'in ya had'u babu k'arya irin haWuwar da kallo d'aya za'a kira shi kai tsaye kyakyawa ajin farko, kamani yayi ina kallon shi, da sauri na sunkuyar da kai na ina wasa da yatsun hannuna, ''Hafsah'' kin san irin son dana Ke miki kuwa, mafarki na da komi tunanin ki na ke tun lokacin da na fara ganin ki, naji duk duniya babu wata 'ya mace da nake burin ta zamo uwar 'ya'ya na idan bake ba, ya rarrafo dai dai saitin k'afafuna ya sunkuya, da sauri nace masa ''dan Allah ka tashi kar wani ya shigo ya tarar da kai a haka'' ''yess in dai a kan son kine bana jin komi dan anzo an sameni a haka nidai fata na ki amshi k'ok'on bara na ki soni har fiye da yadda nake son ki! Suna na Jabeer dafatan zaki karb'i soyayya ta da hannu biyu, kuma Ni ba wai dad'e wa xamuyi ba muyi aure ba, saboda Ni ba yaro bane kaf gidan mu Ni kad'ai ne banyi aure ba, a yanzu idan kin amincewa zan sami iyayen ki mu gaisa na haWa da neman iri'' ya fad'a yana me kallon yanayin da nake ko nayi na'am da buqatarsa, sai dai ko kad'an bazan yi wannan gangancin ba saboda yaya Haidar,ban tab'a yin saurayi ba tun da nake, har na kammala school d'ina shiyasa na ke tsoro duk da cewa nasan Abba yana nan babu abin da zai min, kuma nima ina son shi tunda bashi da matsala, ina so na tambaye shi ko yana da mata Amma ina jin nauyi,na dai bar abin sai tafiya tayi nisa kar yace daga zuwan shi na fiya tambaya, sosai yayi min kawai irin abun nan da mata keyi sai cewa nayi ''ka bari zan yi shawara'' kallon baki da wayo yayi min sannan yace ''dawa zaki yi shawara? Sannan ta yaya zan sani idan kin gama ko kina da waya?" Ya fad'a yana tsare Ni da idanunsa masu haske da sanya mutum kasala, cikin haka sai ga Ameerah da abinci tayi sallama sannan ta gaisheshi ta ajiye kwanuka.
Sun kuyawa nayi na d'auko cup na zuba masa ruwa sannan na mik'a mai cikin girmamawa ya amsa, Bayan na bashi ruwa na d'auko plate na zuba masa hadaddiyar masah da miyar taushe da taji kayan lambu, sannan na zuba masa zob'o me sanyi na mik'a mai, tashi nayi zan gudu domin ya samu yaci abinci, sai kawai naji nayi baya zan fad'i daman jiki na babu kwari ko kad'an, har na sadak'ar nasha k'asa sai jinayi na fad'a jikin mutum, ''ki Dena tashi da gaggawa gashi yanzu da tuni kin fad'i kinyi min asara Ni daman ina kula dake tunda kika zauna kamar baki da lafiya'' ya fad'a yana me kallon face d'ina, cikin wata irin murya da Ni ban san ina da irin ta ba nayi masa magana, ''lafiya ta k'alau kawai ciki zan shiga kafin ka kammala sai nazo kuma sai nayi tuntub'e da carpet''
Nasan jina kawai yayi ba wai lalle ya yadda ba kawai ya gyad'a min kai sannan ya ajiye Ni saman kujera, shi kuma ya zauna ya fara cin abinci hankali kwance kamar irin mata da miji haka na kalla.

Bayan ya kammala na kira Ameerah ta kwashe kayan sannan yace na rakashi ya gaida Annah, muka jera abin sha'awa duk da banjin dad'1 amma haka na ke daurewa muka shiga farlon, har k'asa ya sunkuya ya kwashi gaisuwa wajen Annah sannan tace Ameerah ta kira Abba su gaisa yanzu ya dawo, shima dai cikin girmamawa suka gaisa anan Abba yake tambayar shi, kamar yasan fuskar shi, nan yake cewa, ai shi d'an gidan Alhaji Ibrahim wakili ne, Abba cewa yake ''maashaa Allah tunda na kalle ka nake tunanin kamar nasan fuskar ashe d'ana ne domin ko yau mun had'u da baban ka wajen taro lalle haka ake so Allah yayi muku albarka ameen'' gaba Wayan mu muka amsa da ''ameen''.
Lokacin da zai tafi ya ajiye wa su Abba rafer na y'an d'ari biyar yace babu yawa, Abba na kira ya zo sun gode Amma ko waiwaye be yiba ya bud'e k'ofar farlor ya fita, Ni kuma nayi tsuru a cikin su har sai da Annah ta juyo sannan tace ''ke bazaki je ki rakashi ko bakin get'' mik'ewa nayi kamar marar gaskiya na fice ina jin dariyar Humaira k'asa k'asa Amma ban jiyo ba.
Ko kafin Naje har me gadi ya bud'e mai get ya tafi, sai sak'on da ya barmin wajen me gadi, amsa nayi na juya nayi cikin gida ina tunanin Honey jee cikin zuciya ta, sunan da na lak'a masa.


***

Yana tafe ya na NishaWi karon farko yasan ya gama da y'ar buzuwa duba da yadda yaga tana kallon shi, yasan ta fad'a kogin k'aunar shi, matsala d'aya itace Daddy gaba Waya ya manta da baikon da ke kanshi na Khadijah, soyayyar Hafsah buzuwa itace ta rufe mai ido Amma yasan babu Abinda yafi k'arfin Allah zai dage da addu'a inshallah komi zai dai dai ta, a yau zai sanar da Ammyn shi ta san da maganar da ya koma gida, duk wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login