Showing 21001 words to 24000 words out of 50448 words

Chapter 8 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

234

tunanin yana yin shine cikin zuciyar shi.


****
Abin duniya ya fara damun innah kulu komai da ta mallaka ta k'arar dashi wajen bin bokaye da malaman tsubbu Amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa, a hankali ta gano Laraba tana yi mata zagon k'asa domin ita kad'aice tasan sirrin ta Amma kuma duk wanda aka ce yau yazo gidan ta siyan abu zakaji ana yada Mata da magana kullum kuma cikin siyar da kadara take Amma babu ci gaba, ita dai Laraba kamar watan yin arzikin ta ne ya kama yanzu takai har gidaje gare ta abu ya ci gaba, hak'uri kawai innah kulu keyi kuma har yanzu bata fasa bata wasu kud'in ba duk dan ayiwa Bawan Allah Khalid asiri ya so y'arta, Amma duk a banza Kamar shuka dusa take shiru kake ji , ga y'ar Tata duk ta lalace tayi ba'ki cuta ta yau daban ta gobe daban tun lokacin da suka je wajen wani boka acan Zamfara yace zai yi rubutu a tsakanin cinyoyinta daga shi sai ita saboda rashin hankali irin na kulu da rud'un shaid'an matar nan tabar y'ar ta da shirgegen k'ato a d'aki d'aya, to tunda ga nan yarinya ta ke ciwo ga ciwon k'irji da kullum ta ke cewa yana yi mata.

*****

Ina shiga d'aki na, na tafi ko tsayawa banyi a ak'asa ba buri na naje naga Abinda ke cikin wannan kwalin, k'asan carpet na zauna harda mik'e k'afa ta kamar me shirin yin wani aiki sannan na bud'e, Abinda na gani shi ya kusa tarwatsa kwanyata.........









Comments Win ku shi yake bamu k'warin gwiwa masoya.


Share fi sabillillah=?O?=?O?=?O?=?O?

07049484066**IZINAA**

Store and writing
By
**Abeedatou Alhassan muosae** (oum inayah)


https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

**Mikiya writers association**



Sadaukarwa ga iyalan madugu


07049484066


Ina Masu so a tallata musu hajar su sai su tun tub'eni ta wannan number kai tsaye chat banda kira.


*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?


Page 28&29



Waya na gani sabuwa fill irin wadda ake yayi kampanin iPhone me kyau da ita, gefe guda ga Kud'i da bansan adadin su ba, sosai nayi mamaki harda wasik'a cikin envelope yayi mata rapen gwanin sha'awa.
Mik'ewa tsaye nayi na adana wasik'a sannan na ajiye kud'in had'e da wayar idan na sauka zanje na kaiwa Annah ta gani saboda ina tsoran yaya Haidar ya gani na shiga uku duk da cewa Annah da Abba sunyi na'am da Jabeer d'ari bisa d'ari Amma kuma dole na nuna musu amatsayin su na iyaye na, ga kuma Kud'i da bansan yaya zanyi dasu ba.
Kai tsaye tolet na shiga domin na d'auro alwala gabatowar sallar magriba, shaf shaf na kammala duk abinda zanyi har lokacin ban kunna wayar ba, kuma ban duba wasik'ar da ya aiko min da ita ba, har na juya zan fita na tuna kaina babu komai sakamakon ina idar da sallah na yadda hijabin daman ji nake kamar yana tsunkuli na, gudun naje ayimin fad'a sai kawai na juyo na d'auko wani d'an k'aramin d'an kwali na ya bud'a saman kaina sannan na fice da kaya a hannu.



Ina sauka na tarar da su gaba d'ayan su sai hira suke yi abin gwanin sha'awa, gefe na samu Nima nabi ayari a ka cigaba da hirar tare, Anan naji Annah na cewa sunyi waya da innar su Humaira d'axu ta samu waya ta kira, gaba d'ayan su sai da suka gaisa Ni kad'ai ce banyi magana da ita ba, Amma tace tana gaishe Ni, bayan ta gama yimin wannan bayanin da ya gigita Ni, na cewa Humaira ta dawo k'auye anyi mata miji, cikin jin tausayin Humaira Annah taci gaba da cewa ''yarinya saboda anga tana cikin birni za'a takura mata! To wallahi bari Alhaji ya shigo babu ita Babu komawa k'auye da yardar Allah sai dai taje ziyara, kuma aure ba nufi ne Na Allah ba da za'a takura ace yarinya sai tayi aure, inshallah zasuyi mamakin mijin da zata aura, duk da ita ma suwaiba tasan zigace da hassada ake mata Amma ta kyek'ashe k'asa tace sai ta dawo tunda Baffa ya gama zartar da hukunci tuni'' da katawa tay1 sannan ta juya ta duba inda yaya Haidar yake, wayam ta gani babu shi babu alamar shi, ganin tana waiwaye sai sadiq yace tun d'axu ya fita, murmushi tayi tuna da Abinda zuciyar ta take kitsawa na alkhairi, jinta muka yi tana cewa ''ubangiji ka tabbatar da duk wani alkhairi acikin Rayuwar mu ameen'' da sauri mu ka had'a baki wajen cewa ''ameen Annah'' duk da bamu san me take k'ullawa cikin ranta ba Amma mun san bazata sak'a abin banza ba, ''yanzu to Annah ya kika ce ma innar?'' na fad'a ina duban bangaren da Annah take duk da cikin zuciya ta ina tsoron hukuncin da ta yanke domin Ni har ga Allah ina son zaman Humaira kusa dani musamman yanzu da ake shirin yimin Aure, ina cikin tunani naji Annah tace ''ai Ni ban bata goyon bayan tafiyar ba kawai nace ta bari idan Abba ya dawo zamuyi magana, ita kuma zuwa safiya zan kira ta, kinji yadda muka yi da ita'' Hamdala nayi cikin zuciya ta da godewa Allah da ba cewa ta yi ta yadda ba.
Ganin Babu kowa a parlon Humaira ta shiga cikin kitchen ita kuma Amira tayi wajen wasa, shiyasa ganin babu kowa na juyo na kalle ta ina wasa da yatsun hannuna sai ji nayi tace ''Hafsah'' da sauri na Wago ka na na dube ta sannan nace ''Na'am Annah'' na fad'a ina cigaba da wasa da yatsun hannuna, ''Daga ganin bakin ki akwai Magana, kike ta kallo na, ko surikin nawa ne yace zai turo?'' ta fad'a ta na kallon yanayi na, bangama jin kunyar ba ta k'ara yimin wani zancen da yasani jin kamar k'asa ta tsage nashige dan kunya ''to tunda Ni bazaki fad'a min ko mai nYnY ba, Bari Abba ya dawo sai ki fad'a mai'' ta fad'a tana yin murmushi Domin tasan hali na zan iya fasa yi mata zancen. Cikin magana ta me sanyi nace ''Annah daman sak'o ya bada a kawo min, to shine na kawo miki ki gani'' na fad'a ina me d'auko kwalin wayar da rafer kud'in da ya had'o ni da su. Amsa tayi tare da dubawa tana yaba kyau da tsarin wayar sannan tace ''Yaron nan yanzu har da hidima!to baza'a tab'a kud'in na, Amma wayar zakiyi amfani da ita, yanzu ki tashi kije ki adana kud'in a d'aki na, idan Alhaji ya dawo zan yi mai bayani, wannan Kud'i ai sunyi yawa daga zuwan farko zai k'undumo wannan uwar kyauta ya baki'' ta fad'a tana me kama bakin ta domin gaskiya kyautar tayi yawa. Mik'ewa nayi naje d'akin Annah na b'oye kud'in sannan na dawo parlon muka cigaba da hira, duk da wani b'arin na zuciya ta, ji nake kamar ana k'walamin kira da sautin da zan iya kira kai tsaye sautin yara k'anana, kunnuwa na, na toshe saboda yanzu har da kuka nake ji, suhail da ya kula da yanayi na shine ya tab'o Annah yace ''Annah duba kiga Abinda Aunty Hafsah take yi tun d'axu'' ya fad'a yana tab'o hannun ta domin shi kad'ai ya kula da yanayi na, abin mamaki juyowar da Annah zatayi sai na nemi gaba Waya abubuwan da nake ji na dena, ganin cewa Annah kamar suhail ya had'o da shirme yasa tace ''ni bari na tashi nashi ga daga ciki kafin a kira sallah, Hafsah idan Sad1q ya shigo ki ce yayimin magana da yayan ku'' tana gama magana ta shige d'akin ta, Nima ganin duk su sadiq nY cikin parlon yasa na tashi na haye sama.

***


Abin duniya yayi wa innah kulu yawa, Domin dai yanzu Jikin Lanto kullum k'ara gaba yake ya zamto sai an kwantar an tayar da ita, a hankali kuma innah ta gano shigar ciki a jikin ta, hankalin ta ba k'aramin Tashi yayi ba, Kuma tasan babu shakka acikin yawan gidajen bokaye wani d'an iskan yayi mata, tasan tun da abin nan ya faru Lanto ko k'ofar gida bata zuwa Daga d'aki sai ko idan zasu je wajen wani bokan. Ranar da baza ta tab'a mantawa da ita ba itace ranar da taje gidan k'awar ta Laraba domin ta fad'a mata halin da y'ar Tata take ciki, Amma matar nan da halin d'an Adam sai ta murtsuke idan ta tayi mata tatas da duk wani shiri da take yi a kanta, sumewa ce kad'ai innah kulu bata yi ba saboda tsabar shok d'in da ta shiga, bata gama dawo wa dai ' dai ba ta sake jin wani abin da ya kusa kai ta lahira kai tsaye ''kiji in dad'a Miki da babbar murya kar ki kuskura ki sake zuwar min gida na, saboda kin raina mutane yarinya taje tayo iskan cinta awaje sai kizo kice wai boka ne yayi mata cikin! to wallahi duk ranar da kika sake takomin k'ofar gida na sai nasa y'an iskan unguwa sunyi miki duka, kuma yanzu zanje na sanar da me gari halin da ake ciki, da irin bad'alar da kike aikatawa keda shegiyar y'ar ki, waya sani ma ko kece kika kashe mijin naki ma, Allah Sarki malam Sule Allah ya jik'an ka yasa ka huta'' ta fad'a tana me yi mata wani duba, duban da kai tsaye za'a kira shi da cewa gargad'i ne take yi mata da babbar murya da kuma cewa zaki sani ne baki san wacece Laraba ba.

Innah dai ko ganin gaban ta ba tayi, haka ta kama hanyar gida tana tafe tana hawaye, sai yau tasan cewa tayi gangancin saurin yarda da Laraba tun farko ma, yanzu ya zata yi idan y'an gari suka san Abinda ta aikata, ita duk ba wannan ba ta lafiyar y'ar take yi kafin azo kan y'an gari tukunna, tana tafe kamar mahaukaciyar da ta baro gidan mahaukata duk inda ta gifta zakaji yara na shewa da darairaku irin na yaran k'auye da basu da tarbiyya ko kad'an, da haka ta k'arasa gida tana tunanin ta yarda zata fita da Lanto domin zuwa asibiti, Amma ta yanke shawarar idan dare yayi zata d'auke ta suje asibitin.


*****

Duk bayanin da Jabeer yayi wa Ammey bata ce masa komai ba, tadai ce masa ''Allah ya tabbatar da alkhairi'' cikin zuciya shi yace ''Ameen'' ta lura da yanayin shi kamar bai yi na'am da Abinda ta ce ba sai kawai tace ''Ka dai san halin mahaifin ku yanzu idan naje masa da wannan zancen kasan idan zancen ya fito nice zan dad'a yin bak'in jini cikin dangin ku! Amma ka kwantar da hankalin ka inshallah idan yarinyar nan matar ka ce, to ka k'addara ka Aure ta ka gama, kawai dai kabi komai a sannu Ni kasan bana san tashin hankali'' ya gamsu sosai Da bayanan ta cikin nuna girmamawa da dattako yace '' Bani da bakin yi miki godiya Ammey ubangiji ya k'ara tsare ki ya kuma sa a gama da duniya lafiya'' ya fad'a yana me tashi yayi mata sallama da fita, dai ' dai lokacin da umme ta bud'e k'ofar ta shigo, ganin yayan nata sai ta russuna tace ''barka da gida yaya '' juyowa yayi ya amsa da fara'a a fuskar shi sannan ya ce ''yarinyar Ammey kinyi kasuwa fa'' ya fad'a da yanayin fara'a kwance saman kyakkyawar fuskar shi, sunne kai tayi da gudu tayi d'aki tana dariya, shima dariyar yayi Sannan ya fice yana me cewa '' zamu had'u ne bari a gama da tawa matsalar tukun nan ''.


*******

Bayan Abba ya dawo Annah ta bari ya ci abinci tukun ya huta, sannan ta kawo zancen Humaira ta fad'a mai, jim yayi sannan ya dube ta cikin kulawa da mutum tawa sannan yace ''Babu wanda zai mai da yarinyar nan k'auye sai dai idan bana raye ko kuma ita ce ta buk'ata da kanta to alokacin da kai na zan Kaita gaban iyayen ta Amma ki kwantar da hankalin ki ban amince ba, sannan kar ki bari yarinyar tasan da zancen ko kad'an'' ''ai Alhaji magana ta k'are tunda a gaban ta nayi waya da mahaifiyar ta d'axu'' ''to ba damuwa yanzu Abinda za'a to ki kwantar mata da hankaln ta Babu Me maida ta cikin duhun jahilci tunda ita ta nuna tun farko tana san zuwa, dad'i sosai Annah taji ganin cewa Abba ya goyi bayan su. To ganin sun gama da wannan matsala sai ta sako mai zancen Hafsah, bai wani nuna damuwa ba kasan cewar yasan Jabeer sosai bazai tab'a cutar mai da yarinya ba, illah dai yace ''abinda nake so dake shine kinsan Hafsah yarinya ce qarama kawai dan ta gama makaranta da wuri ne, dududu yanzu bata wuce 17 years ba Amma ace aure za'a yi mata, zancen da nake miki nasamu mahaifin nashi munyi magana, Ashe anyi masa baiko da yarinyar k'anwar baban nashi, kuma na ga alamu sun nuna kamar baya so d'an shi ya had'a mata biyu, kawai Abinda nake so Da ke shine abikomai a sannu idan matar shi ce sai kiga ya aureta', yanzu ki tashi ki had'a min ruwa nayi wanka yau naga ji da wuri nake so na kwanta, au na manta tafiyar ku fa wannan satin ce inshallah Visa ki ta fito '' ya fad'a yana kallon fuskar abar k'aunar shi wadda akullum gani yake dad'a kyau take yi domin bata tsufa ko kad'an, . Mik'ewa Annah tayi taje ta haWa mai Ruwan wanka da yaji turaruka kala kala na wanka sannan ta fito tayi mai magana ''to ko zaki zo kiyi min wankan'' ya fad'a yana mai jawo ta jikin shi, murmushi kawai Annah tayi masa cikin zuciyar ta cewa ta ke ''gaskiya Alhaji baka girma da wasu abubuwa''. Har yaje yayi wanka tana d'akin nashi , komai ita tayi mai har da shafa mai da saka kaya ta feshe shi da turare sannan ta mi?e zata tafi, ai kuwa ya ce'' baki isaba wallahi tunda kika tadamin sha'awar ki, yau anan zaki kwana '' ya fad'a yana mai jawo ta jikin shi.................. ..





Comments and share fi sabillillah=?O?=?O?=?O?





Littafin IZINAA free ne, fatana ubangiji yasa a amfana da Abinda zan rubuta, duk abinda na rubuta ba dai dai ba Ubangiji ka yafemin.




Comments Win ku shike k'ara mana ?warin gwiwa wajen rubutu >?p?*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan mousse* (oum inayah)



*Mikiya writers association*


https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1


Sadaukarwa ga iyalan madugu Abarshi.


Labarin IZINAA akwai tausayi da soyayya cin amana sannan akwai fad'akarwa, Allah ka bani ikon rubuta abinda al'umma zasu amfana dashi.
=?O?=?O?=?O?=?O?


07049484066

Ina masu so a tallata musu hajar su nesa tazo kusa ku tuntub'e Ni akan wannan number chat banda kira.


*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?


Page 30&31



______washe gari lafiya k'alau na ta shi, Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login