Showing 33001 words to 36000 words out of 50448 words

Chapter 12 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

238

magana ita ta fara yi musu '' sannun ku da zuwa'' ta fad'a tana mai nuna musu b'angaren nasu, tare muka shiga ciki har yaya Haidar duk da bai so shiga ba amma ganin ummey tace ya shiga shima haka ya daure ya bisu a baya, ido na saman na Jabeer lokacin da muka d'aga labule yana kwance kamar yasan zamu shigo ya k'urawa k'ofar ido yana kallon ta tun bayan fitar k'awayen ummey bai koma cikin d'aki ba, Ammey ce tayi ciki domin ta kwanta ta huta yau tun safe suke samun bak'i, k'arasa shigowa muka yi yaya Haidar yaje kusa da kujerar da Jabeer yake sannan ya mik'a mai hannu sukayi musabiha cikin sakin fuska yake tsokanar shi, shima dariya yayi yana kallon tauraruwar tashi, Humaira ma ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska, sannan nima na gaisheshi da yanayin kunya duk da tsananin d'okin ganin shi da nake yi , Muryar Ammey muka ji a bayan mu, da sauri na sauko k'asa itama Humaira ta biyo baya na duk muka zube muka gaisheta , ta amsa da kulawa tana mai tambayar wacece surukar tata, to ganin na sunkuyar da kaina k'asa tun kafin a fad'a mata ta gano nice , adduo'in tayi mana na fatan alkhairi sannan aka cika mana gaban mu da kayan ciye ciye ,ruwa kawai nasha sannan muka yi sallama da su bayan ummey ta raka mu gaba Waya sauran b'angaren gidan nasu mun gaisa dasu har cikin part d'in Daddy ta raka mu yana ta sama na albarka, a kallon farko da yayi min yasan d'an na shi yayi dacen matar kwarai, muka fito bayan yaya Haidar ya ajiye musu kud'i masu yawa duk da Ammey na cewa mu tsaya amma haka muka kama hanyar waje sai ummey ce ta biyo mu da gudu da leda shak'e da kaya , har nace ta mayar yaya Haidar yace a'a ba'ayin haka , ta mik'o min wayar ta nasaka mata number ta sannan muka fito tana d'aga mana hannu.

A hanyar dawowa Annah tayi masa waya cewar gobe jirgin su zai sauka a Kano, kasancewar a handsfree wayar take duk abin da tace ina saurara wani dad'i naji da dawowar Annah , gashi shima yaya Khalid acikin satin nan zai dawo.
Bayan ya sauke mu ni dai sauka nayi na shige ciki su kuma na bar su a cikin mota.

Ina shiga na tarar Abba ya dawo d'aukar wani abu daya manta, anan yake sanar dani gobe Annah zata dawo kuma yau zasu yi magana da iyayen Jabeer domin ya buk'aci yau za su xo tare da y'an uwan shi, har ya bada sallahun idan mun tashi yin girki mud'an k'ara ko kad'an ne, a haka yana bayanin Humaira ta shigo sannan ta gaisheshi, itama ta juya tayi hanyar d'akin ta .
Duk bayanin da Abba yayimin a wunin ranar na aiwatar da shi kuma a zuwan da suka yi aka saka ranar auren mu da Jabeer wata biyar, hakan yayi wa Abba dad'i domin zai aurar da yarinyar shi tun kafin ta mallaki hankalin ta, shima Daddy abinda yake ta nanatawa kYnan domin sona so yayiwa Jabeer abinda zai goge masa tabon daya goga masa na Khadijah duk da yasan d'ane mai biyayya amma a wannan karon zai shayar da murja mamaki, da wannan zancen har yaje gida yana nanata shi cikin zuciyar shi.

Kyauta mai tsoka Daddy yayi wa malam audu mai aljan har da kujerar Makkah ya had'a mai, murna sosai malam yayi duk da shi komai yayi yayi ne dan Allah bawai dan kud'i ba amma an ce alkhairi dan k'one haka ya amsa yana mai sake godiya da k'ara ganin mutuncin Daddy.

******************

A gurguje bayan wasu watanni abubuwa da dama sun faru ciki har da dawowar Annah da Khalid gida, basu da matsalar komai a yanzu sai bikin Hafsah da Jabeer da ake ta shirye-shirye ko ta ina ka gani zuciyoyin su cikin nishad'i yake, a wannan tsakanin Haidar ya kasa ha?uri har yaje ya samu Annah da zancen auren shi da Humaira, ta yi murna sosai duk da tasan za'a rina dama amma dan ta k'ara gwada shi sai tace yaje ya nemi yardar ta tukun kafin a san abinyi, haka dai ya tashi sukuku ganin kamar so take ta gwarashi sai ya kama shirin tafiya Katsina wajen Baffa.
Babu wanda yasan ya tafi sai ganin shi sukayi rana tsaka da Baffa a gida har yaje ya d'auko shi, sunyi mai tarba ta musamman sannan da Abba ya dawo yake sanar dashi halin da ake ciki na Haidar na son Indo, kallon Annah Abba yayi bai san da zancen ma gaba d'aya ba, itama sunkuyar da kai tayi ganin tasirin idanun shi cikin nata bazata iya jurewa ba, ganin kowa bai ce komai ba sai Baffa ya katse shurun da cewa '' yanxu dai ni ba tone tone nace ayi ba kawai tunda bikin y'ar uwar tashi da saura sai kawai a had'e ayi tare, da fatan hukunci da na yanke zai yi wa kowa dad'i'' hamdala Haidar yayi cikin zuciyar shi jin cewa Humaira ta kusa zama mallakar shi shi kad'ai, suma iyayen babu wanda ya musa duk suka saka albarka sannan yace shi ba kwana zai yi ba yanxu zai koma gida, sai da aka kai ruwa rana Sannan ya yadda sai gobe amma da wuri zai tafi.
Da sassafe Haidar ya kama hanyar mayar da shi gida zuciya yoyin kowa fal da farin ciki.

Lefe na gani na fad'a aka kawo wa Hafsah daga gidan su Jabeer akwati set uku tare da mukullin mota da Daddy ya saka, Alhamdulillah komai yayi babu ce kawai babu aciki, itama Humaira Annah da kanta taje waje ta haWa mata lefe na gani na fad'a, banbanci da aka samu ita Hafsah da mukullin mota ita kuma Humaira babu, komai dai sai san barka da fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuriya d'ayyiba.

Kuma har wannan lokacin ban kuma mafarkin wannan abun ba da nake gani, kasancewar Annah ta dage a kaina da adduo'i, kuma Alhamdulillah nima nasan yanzu ina jin dad'in jiki na sosai ba kamar da ba, ashe lumbu lumbu yayi musu ba wai ya tafi ne ba gaba d'aya yana nan ya shirya ranar dawo wa ya d'au fansa.

Biki' za'a yi na gani na fad'a, amare biyu a gida d'aya ango d'aya, can Kuma gidan su Jabeer ango d'aya sai amarya Khadijah k'anwar Jabeer, ko ina shiri ake, musamman Annah ta d'auko mai gyaran jiki daga Nijar, y'an uwan Annah na Agadez gaba d'ayan su kwansu da kwarkwata suka kamo hanyar zuwa, ga y'an Katsina suma ba'a bar su abaya ba, abindai sai san barka.

*********
Ranar wata juma'a dubban jama'a suka shaida d'aurin auren Jabeer Ibrahim da amaryar shi Hafsah Muhammad akan sadaki dubu d'ari lakadan ba ajalan ba, sai kuma Aliyu Haidar Muhammad da amaryar shi A'ishatul Humaira Usman akan sadaki dubu hamsin, ina kwance kamar mai zazzaSi message ya shigo waya ta, bud'ewa nayi domin nasan bazai wuce Honey jee bane, Ina bud'awa naga an rubuta ''alhamdulillah''ko ba'a fad'a ba nasan nazama matar shi daga yanzu, haka nan naji gaba na ya fad'i ban san dalili ba sai kawai nayi addu'a na koma na kwanta duk da sai da aka sani nayi kwalliya, kuma nayi kyau sosai kowa kallo na yake musamman y'an k'auyen DUGUL, innar su Lanto har da ita a zuwa biki, Humaira ita take kula da komai saboda ita babu wani irin jin kunyar nan atare da ita.

Daga nan aka zarce da wuni, babu wani b'ata lokacin Yamma nayi aka turo motoci daga gidan su Jabeer domin d'aukar amarya, kuka dai nasha shi lokacin da za'a rabamu da Annah dakyar suka jani akayi mota dani kasancewar ita Humaira babu nisa sosai daga gidan mu zuwa gidan ta.

Haka aka kaini tank'amemen gida na daya tsaru fiye da zaton mai tunani, bayan kowa ya watse aka barni daga ni sai hali na, ya shigo bayan abokan shi sun rako shi duk abinda ango da amarya Yakamata suyi mun gabatar amma bai tab'a niba haka ya kyale ni nasha bacci na. B'angaren ango Haidar a wannan ranar ya maida Humaira cikakkiyar mace duk rakin da kukan bai sa ya kyaleta ba sai da ya samu nutsuwa sannan ya koma aikin lallashi, komai shi yayi saboda yayi aiki ba kad'an ba, wanka ma shiyayi mata yana ta aikin ce mata sannu ita dai Humaira hawaye kawai take wata kunyar shi tak'ara kama ta, tare da soyayyar shi.

Sai da muka yi kwana bakwai da Aure awannan lokacin sannan Jabeer ya samu kusanta ta ashe lokacin ciwo na ya dawo ba musani ba.

Kwan kwasa k'ofar da ake yi ita ta dawo dani duniyar tunanin da na fad'a wannan shine asalin labari na da irin bad'ak'alar da akasha wajen aure na kuma har yanzu momy murja bata hak'ura ba ganin y'ar ta har yanzu bata yi aure ba a cewar ta Jabeer zata aura. Jiki a sanyaye babu kwari naje na bud'e k'ofar, ganin ummey ce da murna naje na rungume ta muka ranka yo muka dawo farlor, duk aikin gidan ita ce tayi shi amma duk in da tayi ina biye da ita a baya, har dare muna tare, ko daya dawo cewa nayi babu in da ummey zata har sai tayi sati sannan in ba haka ba kuma ya kaini gidan mu, babu yadda ya iya haka ya hak'ura bayan ya kira Ammey awaya ya sanar da ita anan ummey zata kwana amma bai gaya mata matsalar tasu ba ya dai ce Hafsah bata da lafiya kawai ummey zata taya ta wasu ayyukan na gida.............................



*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB 1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?






IZINAA

Story and writing
By
Abeedatou Alhassan muosae ( Oum Inayah)

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1


Mikiya writers association


Ina yiwa kowa barka da zagayowar watan da aka haifi shugaban halitta baki Waya

HAPPY MAULLUD


Page 40&41


Haka muka kwana bacci ko kaWan bai ga idona ba, ganin shi ya samu bacci sai nayi shiru kamar nima yi nake, har garin Allah ya waye ban rintsa ba sannan kuma ban dai na tunanin mafita, haka shima Sangaren ango Jabeer da ya fara bacci sai ya bud'e ido yaga ko na samu bacci haka dai har aka kira assalatu, shima bai wani yi baccin kirki ba, da tunanin samun mafitar shima ya kwanta amma bai samu ko d'aya ba, ya yanke shawarar kawai yaje gidan Haidar ya fad'a mai halin da suke ciki, tun da bazasu iya fad'a a gida ba, lallab'a wa yayi saitin kunne na ya hura min iska, duk a tunaninshi bacci nake, sai dai wata gantsarewa da nayi ita ce ta tabbatar mai da idona biyu ba bacci nake ba, cikin wata kalar murya da ni kad'ai nasan da ita yace '' ki tashi muje muyi wanka da alwala kar mu makara'' ya faWa yana mai shafo in da yafi so ajikina, da sauri na bud'e ido ina mai tashi na duro daga saman gado sakamakon wani shok da naji tamkar wutar lantarki aka jona, ko sauraren shi ban tsaya yiba nayi hanyar toilet ina tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, bayana ya biyo sannan yayimin wanka kamar y'ar beby haka ya saSeni tass sannan yace nayi alwala, shima ya samu yayi wankan da sauri saboda yaji ana tada sallah a masallaci, a cikin toilet d'in ya barni shi kuma ya tafi masallaci bayan ya shimfiWa min abin sallah da hijabi a gefe, bayan na kammala na fito na fara Wauko kaya na saka marasa nauyi sannan na tada sallah cikin nutsuwa irin tawa da ta zzamemin jiki akoda yaushe, ina idarwa na d'an kishingiWa maimakon na nemi Alkur'ani na karanta, har zuwa lokacin da gari ya fara haske, ban ji shigowarsa ba sannan ban ankara ba naji ana shafa duk wani sassa dake jikina kafin nayi wata magana har ya haWe bakina da nashi yana wata iriyar tsotsa kamar wani mayunwacin zaki, sai jinayi yayi sama dani ina mamakin wannan abu daya ?i bari mu haWa ido dashi,, ganin lafiya ya fita ya barni bai wani nuna cewa yana bu?atata ba, duk wani abu dayake yi bana wani jindaWi shi kaWai yake kiWansa da budirinsa, sai kuma da aka zo mai gaba Waya labari yasha bambam sakamakon wani azababben zafi daya ziyarceni bansan lokacin dana ?walla wata gigitacciyar ?ara ba, dai dai lokacin shigowar Jabeer kenan daga masallaci yaji wannan ?arar, ai asukwane ya yi jifa da carbin hannunsa ya shiga cikin Wakin, a san?ame ya tarar da ita babu numfashi a tare da ita ko kaWan, maimakon ya yi kitchen samo ruwa ya zuba mata sai kawai ya yi toilet yaWebo da yawa ya she?a mata, amma ko gezau bata motsaba, to ganin cewa zai Sata lokaci kawai ya sungumeta ya yi asibiti ganin kamar babu rai a tare da ita.

Likitoci biyu suka rufu a kanta da kyar da suWin goshi suka samu numfashin ta ya dawo, amma kuma wani abin tashin hankali bayan ta farko daga bacci ta kasa yin magana gaba Waya sai dai tabi mutane da ido babu baki a tare da ita.

Ganin haka sai ya yanke shawarar faWawa Ammey halin da ake ciki, bayan ya kira number tata ringing biyu tayi Ammey ta Wauka tare da sallama '' Ammey ina kwana'' jin Muryarsa wata kala da sauri tace ''lafiya ?alau Jabeer! ya Hafsah da jiki?'' kamar ta sani abinda ke faruwa ta tambayi jikin Hafsan, kafin ta k'ara magana yace '' Ammey daman jikin Hafsah ne yashi, yanzu haka muna asibiti tun safe,, ''subhanallahi yanzu jikin har yakai haka! bari yanzu naje na sanar wa Daddy halin da ake ciki'' ta faWa tare da mi?ewa tayi Sangaren Daddy', suna gama waya da Ammey ya kira Annah itama kamar yadda ya yi wa Ammey bayani itama cikin girmamawa ya sanar da ita tare da faWa mata asibitin da suke.


Ummey da sassafe ta tashi ta Wora breakfass, ba wani girki mai wahala ta yi ba, amma tayi iya ?o?arin ta wajen ganin mutane gidan ta burgesu, sai da ta kammala komai sannan taje ta watsa ruwa, sannan ta zo ta Webi nata su kuma ta bar musu nasu saman dining table, har wajen tara bata ji alamun sun tashi ba, a cikin zuciyarta take tunanin yau wani irin bacci sukeyi, haka ta mi?e taje ta ?ara kimtsa wajen da ta Sata , sannan ta dawo Waki, ringing Win wayarta shi ya dawo da ita duniyar tunanin da takeyi tun Wazu, da sauri ganin number yayanta ne yake kira ta Waga tare da cewa ''yaya'' shima ya amsa da ''na'am UmmeyUmmey! Kinga na kira ki daman Auntyn ki ce babu lafiya, muna asibiti tun safe'' ''wayyo yaya mai ya sameta?'' ta faWa tare da tashi kamar ance mata mutuwa tayi, ganin itama kamar ta ruWe sai ya sassauta murya cikin kwanciyar hankali yayi mata bayani tare da ce mata drever ya kawo ta, sannan ta shiga Wakin Hafsan ta Webo kaya kala biyu, tare da abinci idan ta girka, sai da ta shiga tayi wanka sannan tayi duk abinda yasa kata, sannan ta fito tare da rufe ko'ina na gidan, taje ta samu Malam Garba tayi mai bayanin asibitin da zai kaita sannan suka tafi.


Humaira amarci akesha babu kama hannun yaro, tayi kyau tamkar ba'a Nijeriya take ba, kallo Waya zaka yi mata ka gano tana da shigar ciki atare da ita, idan ka kalli Haidar duk wannan jan ajin babu shi yanzu, tarairayar y'ar matarsa kawai ne aikin shi kullum da kalar shagwaba da zata tsiro mai duk yayi wani iri kamar cikin ajikinsa yake, abu kaWan tace wai bayana, ta fanni Waya yake morewa itama cikin nata wata kalar jaraba yake sakata, duk kunya irin ta 'ya'yan fulani yanzu babu wannan tsakaninsu da mijinta, dai dai gwargwadon iyawarta tana mishi biyayya sai dai abinda ba'a rasa ba, yau ma suna kwance ta tada kai da saman cikinsa, shi kuma yana wasa da gashin kanta, hira sukeyi cikin nishad'i da annashuwa, kasancewar yau weekend ne babu kuma ina da ya je tun safe, sai jin ringing ya yi wayarshi, yun?urawa tayi zata Wauko mai wayar , da sauri ya ri?o hannunta yana mata wani irin kallo na musamman, da ita kaWai tasan ma'anar shi, ido Waya ta kanne mai sannan ta dawo ta kwanta saman doguwar kujera, shi kuma ya shiga Waki amsa wayar kasancewar yasa ta cikin caji tun Wazu, tana nan akwance sai ganin dawowarsa tayi yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login