Showing 30001 words to 33000 words out of 50448 words

Chapter 11 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

244

bane, sai dai Dr Ammar ya fad'a musu za'a fitar da shi waje, ni kuma zanyi wa wani mai magani magana daga Nijar yake zuwa Kano kuma inshallah za'a dace''' ya fad'a yana mai nuna tausayawa a fili ganin irin wahalar da yaron yake sha abin ya bashi tausayi . Jim nayi kamar wata mutum mutumi har bansan adadin zaman da nayi cikin parlon ba, sannan bansan lokacin da yaya Haidar ya sulale yay1 b'angaren shi ba, duniyar naji gaba d'aya tana juya min, daga wannan lokacin bank'ara sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi naganni a hospital, bud'e idanu nayi a hankali da suka yimin nauyi ina k'arewa d'akin kallo nan idanu na ya sauka a na Humaira da tayi nisa cikin tunani, Amira itace ta kula da motsin da nake yi domin tun da aka kawo ni banko juya ba ganin yanzu ina yin motsi shine ta tabbatar da cewa na motsa ai kuwa da murnar ta, ta tab'o Humaira tana cewa ''la kalli Aunty Hafsah ta farka kinji Aunty Humaira'' ta fad'a tana mai tab'o Humaira da tayi zurfi cikin tunani, hamdala tayi cikin ranta sannan ta mik'e domin kiran likita.
Office d'in Dr Haidar taje sannan tayi noking k'ofar '' Yes come in'' taji yace bayan ta kwankwasa, a hankali ta bud'e k'ofar cikin takun ta mai nutsuwa tayi sallama ta shiga
Da murya mai sanyi yaji tace masa ''yaya Aunty Hafsah ta farka yanzu'' tana gama faWa mai ta juya tayi hanyar waje '' Na sallame kine?" Taji yace kamar Kuma Ba shi yayi magana ba ya had'e rai, ita dai bata ce uffan ba har yagama yangar shi sannan ta ga ya mi?e ya d'auki kayan aiki yace '' biyo ni man, ko gadin office d'in zaki yimin?" Yanzu ma ba ta tanka Shiba, kamar yadda yake tunani tabi bayan shi suka tafi d'akin da Hafsah take, lokacin da suka shigo a xaune suka taraddani ina kallon Amira kamar na samu TV, sosai yaji dad'i ganin na farka lafiya k'alau babu wata matsala daya gama duba ni sai hamdala yakeyi cikin zuciyar shi tare da godewa Allah, kallon gefen da Humaira take yayi sannan yace taje ta had'a min ruwan wanka nayi sai naci abinci' anjima kad'an sai mu tafi gida tunda abin ya zo da sauk'i, duk abinda ya fad'a mata an aiwatar sannan nayi sallolin da suke kaina na, nayiwa masoyi na addu'ar samun lafiya da kariyar ubangiji sannan na mik'e a hankali na koma saman gadon , har ana kwanta naji Muryar yara daban daban suna kuka cikin kunnuwa na, da farko abun kaWan nake jin shi amma daga baya sai naji yana k'aruwa, addu'a na kama yi cikin zuciya ta har naji nade na ji, sannan wani bacci mai dad'i yayi awon gaba dani. Bayan na farka naji kwarin jiki na sannan Abba yazo ya k'ara gani jiki na bayan yaje d'akin da aka kwantar da Jabeer ya duba shi kasancewar yaya Haidar ya fad'a masa komai kuma ya tausaya mai ganin har zuwa wannan lokaci ko motsi bayayi, ganin mun fito zamu tafi banji ancemin naje na duba shi ba, kawai munxo sai tin da naga ummey k'anwar shi Allah ya taimaka ya tab'a nuna min pictures d'in ta Kuma na ganeta, da sauri nayi wuff nazo inda take duk da banajin dad'in jiki na amma haka na daure naje na sameta duk basu lura naje ba, sallama nayi mata itama tana d'ago kanta ta ganeni cikin fara'a da sakin fuska duk da halin da ake ciki na rashin lafiyar yayanta amma ta saki ranta muka gaisa a mutum ce, nace ina d'akin mara lafiyar, tashi tayi tace ''muje na kai ki'' ni kuma nabi bayan ta a hankali ganin har yanzu jiki na babu kwari, fitowar Dr Ammar kenan daga d'akin mukuma muka shiga, ai kuwa ya bini da kallo harda bigewa da k'ofa, sai da wata mata zata wuce ta ankarar da shi sannan yakama cewa '' subhanahi'' ni dai bansan Yana yiba hango abun k'auna ta kwance kamar gawa, da gudu na k'arasa bakin gadon har zan fad'a kanshi sai Kuma naji wata murya tana min gargad'i akan kar na kuskura na tab'a shi in ba haka ba kuwa yanzu za'a k'arasa shi , cak na tsaya ban k'arasa ba kuma ban dawo baya, sai a sannan naji wani kuka ya kwace min har ban san lokacin da na durk'ushe a wajan ba, a wannan lokaci nayi danasanin yin zurfin ciki yanzu gashi na saka bawan Allah acikin Matsala duk da babu wanda yasan ta sanadi na yake kwance haka tsawon lokaci bai ko motsa ba '' ya Allah ga bawan ka nan yana buk'atar taimakon ka ubangiji ka bashi lafiya alfarma sayyiduna Rasulullah =?O?'' na fad'a murya ta ko fitowa ba tayi tsabar kukan da nakeyi, hannun ummey nagani tana d'ago ni ita ma Muryar ta ta ,ko fitowa batayi da yawa ta hau lallashi na da bani baki anan naji cewa yau kwanan shi biyar a haka kuma tunda ya fara jinyar ko motsi baiyi ba, ''innalillahi waina ilaihi rajiun wannan wace irin masifa ce ace mutum ya shafe Kwana ki har biyar bai san wanda yake kanshi ba Ubangiji ka kawo mana d'auki ya Allah'' na fad'a ina mai sake rushewa da wani kukan kamar ancemin Annah ko Abba wani ya mutu a cikin su, Muryar Humaira naji tana cewa '' ki taso mutafi tun d'azu ake neman ki sai da Dr Ammar yace yaga shigowar ki nan, kuma gasu Abba can a waje'' jiki a sanyaye na mik'e ina sake kallon b'angaren da Jabeer yake bai ma san nazo ba ''kaico rayuwa '' na fad'a ina mai sake rushewa da kuka, a haka na bi bayan Humaira muka fito sannan na bawa Abba hak'uri, ganin ko juyowa bai yi ba hankali na ya kwanta , muka shiga motoci aka kama hanyar gida.
Muna zuwa gida duk muka fito ashe yaya Haidar biyo mu yayi domin yana so suyi magana da Abba, d'akin Annah na bud'e na shiga domin wata kewar ta ce ta dawo min, inajin sauran yayyena su Babangida suna min sannu amma ban iya tsayawa ba saboda saurin da nake naje na kwanta, Humaira girki ta tafi d'ora wa ganin kowa na gidan yana nan sadiq ma yana hanya zai zo dubiya, ina shigowa d'akin Annah ta kira waya ta domin muna shigowa Humaira tabani wayar hannu na rawa na d'aga sannan na gaishe ta ''ya jikin naki Hafsah?'' '' da sauk'i Annah , yaushe zaki dawo?'' nan muka cigaba da hira cikin kwanciyar hankali duk da wani abun batasan da shiba a tare dani amma tace tana yimin addu'a kullum idan sunje harami, ''sannan ki rin?a yin azkar d'in ki nasan ki da shiririta ki kula sosai kinji yarinyar Abba'' dariya nayi har cikin raina naji dad'in wayar da muka yi yanxu, mun yi sallama tana cewa na gaida mata da autar ta nace zataji tana parlor na ajiye ina jin kewarta tana ratsa ni.


********************

Da taimakon Allah da na Haidar aka samu komai ya na tafiya yadda ya kamata Alhamdulillah sunje yayiwa Ammey bayanin malamin addinin Muslunci da yake bada magunguna na cutar junnu shiyasa aka sallame su zuwa gida bayan ya shafe Kwana ki bakwai babu wani cigaba a cikin asibitin, zuwa na farko yayi yabada rubutu da adduo'i dazaa yimai yana sha ana yi masa wanka, kuma Alhamdulillah sauk'i ya fara samu, a irin zuwan dayake yaga halin da Daddy yake ciki na halin ko inkula dayake yiwa d'an nashi, nan ya k'udirta cikin ranshi na inshallah sai ya kawo k'arshen wannan mugun domin ko ba'a fad'a mai ba yasan bayin kanshi bane wannan al'amari ba kowa ne zai iya tarar wannan mugun aljanin ba. Tun lokacin da Khadijah da uwar ta suka ga halin da Jabeer yake shikenan tayi tsalle ta dure tace ita tafasa auren shi kuma ta kama gabanta ta koma Abuja ko zuwa ta duba shi batayi ba, Daddy har gida yaje akan zancen bikin, saboda tsabar rashin ta ido bataji kunyar Daddy' ba ta fututtuke ita y'ar ta bazataje zaman jinya ba tunda ance ba lallai idan ya tashi ya iya ko tafiya ba, haka jiki a sab'ule ya hawo jirgi ya dawo garin Kano babu wanda yayi wa zancen a gidan duk da Ummah taso yasan me yakai shi Abuja gidan y'ar uwar tashi, amma ganin yanuna ba komai sai ta hak'ura ta kyale zancen, ita dama Ammey tunda abin ya faru ko girki ta sallamawa y'an gida ko b'angaren ta yadena zuwa, bare yaje ya ga halin da d'anshi yake ciki........................
'?
'?
'?
'?
'?
'?
'?
'?







*=???TEEMERH COOL*=???
Special DATA

*GARA?ASA Kar ku bari ayi ba ku=؃?
MTN
500 MB 150
1GB 280
2GB 550
3GB 840
4GB 1,100
5GB 1,380

AIRTEL
500 MB 160
1GB 290
2GB 580
3GB 870
4GB 1,150
5GB 1,450

GLO
500MB 170
1GB 300
2GB 600
3GB 900
4GB ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????1,200
5GB 1,500

9MOBILE
500 MB 130
1GB 250
2GB 500
3GB 750
4GB 1,000
5GB 1,250
........................................

Account No: 9048703453

Account Name: Fatima muhammad Aliyu

Bank Name : Opay Bank

WhatsApp Number or Call: 09039340545

Sai Kun Taho>?s?>?s?>?s?







Comments and share fisabilillahi=?O?=?O?=?O?*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan muosae* ( Oum inayah)


*mikiya writers association*

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1


Page d'in nan gaba d'ayan shi naku ne.

Y'an makarantar GGSS KURNA
One love.

Mom twince
Dr Nusaiba
Mom Zahra
Maman Fatima
A&H for ever
Fatima Abdullah
Nana khadija076
Ummin ummah
Ummin su ummahani

Ina godiya sosai da k'auna Allah ya barmu tared'?>???>???

07049484066



Page 38&39


________________________
Rana tsaka Ammey na shafawa Jabeer rubutu ajikin shi kawai sai gani tayi hannun shi na motsi, a 'a sai taga kamar idanun ta ne yake yi mata gizo, '' ummey!" kawai sai ta kwalawa ummey kira dan tazo taga ikon Allah itama, ummey da ta zo a guje jin kiran da Ammey tayi mata, hannun itama taga ya kuma motsawa abin al'ajabi kuma sai suka ga idanun na shirin bud'ewa ,ai da sauri Ammey ta juya tayi sujjadar shukur ganin Allah ya amshi adduo'in su, wani abin k'arin jin dad'in sai ganin Daddy sukayi ya yi sallama ya shigo, a kuma dai dai lokacin ne idanun Jabeer ya k'ara sa bud'ewa gaba d'aya ya sauke saman fuskar Daddy, Ammey jira take taji Daddy ya daka masa tsawa sai kuma taji akasin haka domin da sassarfa ya k'araso bakin gadon da Jabeer yake idanun shi na zubar da hawaye gani kalar ramar da Jabeer yayi, bai yi wata wata ba kawai ya rungume shi tare da fashewa da kuka ''Alhamdulillah da Allah ya dawo da hankalina tun ba'a je ko ina ba'' cewar Daddy bayan ya rungume d'an nashi cikin k'irjin shi, sai kuma ya jiyo ya fuskanci Ammey da ta ke murmushi tun bayan da ta gano Daddy ya dawo hankalin shi, ''dan Allah Maryama ki yafe min nasan nayi miki laifi kuma nasan ke mai hak'uri ce duk cikin mata na, kuma ina fatan ki cigaba da hak'uri kamar yadda nasan ki ubangiji ya k'ara kare mu inshallah addu'a yanxu muka fara yinta, yanzu kafin kowa ya shigo ki kama shi ki kai shi torlet yayi wanka kafin ya ci abinci ko ruwan tee ne'' ya fad'a Yana mai d'ago Jabeer sai kuma yaga ya tashi da kanshi ya zauna , gaba d'aya hamdala suka yi har ummey dake tsaye taji daWin ganin hankalin Daddy daya dawo jikin shi.
Bayan yayi wanka ummey taje kitchen ta had'o tee ta kawo, har Ammey ta d'auko zata bashi dakan ta kamar yadda ta saba, sai gani tayi ya amsa dakan shi ya fara kurb'a hankalin shi kwance alamun lafiya ta samu, da kanshi ya sha sannan aka d'auko mai kaya ya saka, nan ya fito fes dashi kamar ba shine ya share sama da kwana bakwai a sume ba, nan gidan ya fara d'auka jama'a sai shigowa suke sashin Ammey domin yi mata barka da arziki na samun lafiyar Jabeer, matan yayyen su suma duk wanda yake cikin garin Kano a ranar suka zo ganin shi, abokan aikin shi har baya gane wasu. Gida dai Alhamdulillah haka akayi ta shiga da fita abinci ma ad'ora wannan a sauke wannan domin dai sadaka a ka wuni badawa agidan na murnar samun lafiyar Jabeer,
har garin Allah ya waye mutane basu dai na shiga da fita ba a cikin gidan.

**********************

Dr Ammar ne yake sanar da Haidar a waya na samun lafiyar Jabeer kasancewar shi kusan kullum sai ya je gidan a cewar shi ya ga matar aure tun lokacin da ya k'ella ido akan ummey yaji duk duniya babu wata mata da ta burge shi sai ita, to bayan samuwar lafiyar Jabeer d'in zuwan shi biyu gidan sake duba shi, to ganin kamar Haidar bai sani ba , yau ke sanar da shi awaya, shima Haidar yaji dad'in samuwar lafiyar Jabeer d'in domin shima yana ganin idan y'ar uwar shi ta samu labari zata fi kowa jin dad'i, da haka ya k'udirta daya gama shirya wa zai sameta ya sanar da ita wannan labari mai daWin ji, to sai da ya gama komai yayi wanka ya shirya cikin shigar da tafi d'aukar kalar fatar shi ya shirya yana ta zuba k'amshi, sannan ya fito yana taku d'ad'aya kamar wani basarake , lokacin da ya sauko duk muna farlor muna hira duk da cewa sun girme ni gaba d'aya mazan gidan a mata ne nake babba amma kasancewar yanzu Annah bata nan sai naxama nice yanzu babba, shiyasa suka zagaye ni ana ta hira duk da jikin nawa sai a hankali tun bayan da na kwanta a asibiti har yanzu saboda ban kuma komawa duba Jabeer ba, yanzu ma rabi tunanin halin daya ke ciki nake yi kawai ina saurar sune amma hankalina yana can wajen tunanin masoyi na, a haka ya same mu duk muka gaisheshi sannan ya nemi kujera ya zauna, kallon Babangida yayi ai kuwa ya san kwanan zancen sai gani mukayi ya mik'e ya bar farlon shima d'ayan a hankali ya tashi, sai muka rage mu uku saboda Amira yau an tafi school, daga ni sai Humaira yayi saura ina lura da kallon da suke yiwa junansu amma tsabar miskilan ci daga shi har ita sunk'i bawa kansu damar kasance wa tare, gyaran murya yayi kowa ya dawo hankalin shi sannan ya fara magana '' ke Hafsah!" ya nuna ni da hannun shi sannan ya cigaba '' abinda yasa na tsaya ban tafi ba saboda ina so muyi magana dake, d'azu ina kwance abokin aikina kin san shi ma Dr Ammar yayi min waya cewar Jabeer ya samu lafiya'' wata ajiyar zuciya ce ta kwace min da bansan da ita ba sannan acikin rai na nace ''alhamdulillah'' kallo na yayi sai yaji yana tausaya min har cikin ranshi ganin daga faWa min haka naji dad'i ina ga ya ce nazo muje a ganshi, ban zataba sannan ban yi tsammani ba naji ya sake cewa '' ku tashi ku d'auko hijaban ku kafin na wuce office na fara kai ku gidan ku duba shi'' ''d'an uwa mai dad'i'' na fad'a cikin rai na sannan na mik'e da sauri nayi sama tun kafin yace ya fasa kai mu, kallon Humaira yayi ganin bata tashi ba sannan ko motsi bata yiba yace mata '' Madam sai a tashi ko sai na zo na d'aga ki da kaina?'' ya fad'a yana mai tashi kamar zai zo in da take, da gudu ta tashi itama tabi bayan Hafsah tun da taga shi baya jin kunya ko kad'an asalima a gaban mutane yanzu sai yace zai yi mata magana alhali da baya ko kallon in da take, shima dariya yayi sannan cikin zuciyar shi yake ayyana Annah na dawowa zai sanar da ita shifa yanzu a shirye yake domin ya zauna da Humaira ko da dayake gudun ta k'azanta ce da rashin wanka yasa yake gudun ta amma yanzu ko y'an matan Kano baza su nuna mata gayu ba, yana wannan tunanin suka sauko a cikin shigar dogayen riguna iri d'aya sak har kala, ko banbance su bazaka iyayi ba domin gaba d'ayan su farare ne tsayi ne Hafsah tafi Humaira amma ko a siffar jikinsu kusan iri d'aya ne , maashaa Allah kawai yake cewa ganin irin kyau da Allah yayi wa Humairan shi, shi ko kallon Hafsah bai tsaya yayi ba ta abar k'aunar shi kawai yake yi, fita yayi suma suka take mai baya cikin nutsuwa da d'aukar hankali, gaban mota ya bud'ewa Humaira ita kuma Hafsah ta shiga baya sannan suka kama hanya bayan tayi wa su Babangida kashe din kar wanda ya fita yaje ko bakin get.
Tafiyar mintuna k'alilan ta kawo su katafaren gidan Alhaji Ibrahim, suna shiga cikin harabar gidan ita kuma ummey ta rako y'an makarantar su bakin get taga fitowar su Hafsah, murmushi akan fuskar ta bayan ta sallami k'awayen ta sannan ta k'araso tun kafin su yi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login