Showing 39001 words to 42000 words out of 50448 words

Chapter 14 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

237

yanzu Kuwa tun da sun nuna Wan su ba zasu iya tan?warashi ba, to y'ar su bazata zauna ciwon zuciya ya kamata ba, ta ji ma da wanda yake damina, da wannan lamari dai mara daWin ji Hafsah ta koma gaban iyayenta, duk da sun lura ita kamar abun bai wani dameta ba , amma suma suna da ha??in kare mata mutuncinta, da ?yar Ammey ta yadda suka tafi, bayan tabada ha?uri sosai a faWawa Annah kafin tazo da kanta.


Masu iya magana suka ce, rana bata ?arya sai dai uwar Wiya tabi kunya, to wannan haka yake, domin dai Khadijah da Jabeer a safiyar asabar aka Waura aurensu akan sadaki ddubu Wari, bayan tashi da suka sha kafin zuwan wannan rana Ubangiji yau ya amsa musu, babu wani Sata lokaci yace a tawo masa da amaryarsa, domin ba kuma zai ?ara kwana ko Waya a Abuja ba, haka suka yi a ranar y'an uwan babanta da wa inda suka kamata suka Wauko hanyar tawowa kaeota gidan mijinta.

Ko cikin mota abinda Mommy tace take ta nanatawa cikin zuciyarta, saboda kar asami akasi, ''kar ki kuskura yau ki bari ya kusanceki, idan kuma kin bari, ya yi to duk wani aiki da muka samu ya ci shi, ki tabbata a ranar zai warware , batun kuma kishiyarki, an gama da ita domin Wan tsito ya sanar dani bazata ?ara yin magana ba sai dai idan aikin ya warware, sannan ki kula!'' da wannan tunanin take ta nanata shi cikin zuciyar ta har suka kawo garin Kano , ko abu Waya ta kasa sakawa abakinta, ga halin da zata tsinci kanta acikin na rashin son da uwar mijinta bata yimata, duk da wani sashin na zuciyarta na raya mata, ai sun gama da kowa babu wanda zai tada maganar sai dai idan ita tayi wasa aikin ya War gaje.

Shi kaWai Haidar yake tunanin mafita ta yadda 'yar uwarsa zata samu lafiya, ko iya maganar ta ta suna so ta dawo, har wajen wani malami, abokinsa Usman ya kai shi, amma kuma an ce dole akwai abinda suke Soyewa ita da mijinnata, kuma shi gaskiya tun da yaji an ce zai ?ara aure ya ji gaba Waya ya fitar masa daga ranshi, har ?wara Khalid tun da yana yawan zuwa gidan wajen Ummey, wata ?il ya faWa masa sai asan abinyi, don in dai ba haka ba, to wallahi bazai iya tun kararsa da zancen ba.


Gida na musamman ya Jabeer ya gina wa amarya, gidan da ko Hafsah nata bai kai tsaruwar sa ba , amma qaddara ta sa shi yin abubuwa bisa rashin sani, ko Hafsah rabon da ya tunata har ya manta, yau ma abinda yasa ya shiga cikin gidan, yana so Ammey ta saka masa albarka, da ?yar da suWin goshi da zai tafi, ahankali tace '' ubangiji ya bayyana gaskiya! Ya kuma tsare min kai a kowanne yanayi'' ya ji daWin addu'a da ta yima sa haka ya tashi jiki babu wari ya fito, ko Sangaren Daddy' bai kallaba , burin sa yaje yaga amaryar sa kaWai, shine cikin rayuwar sa.

Matsalaa da aka samu, tun bayan da aka Waura aure, yake jin matsananciyar sha'awa, kuma ya yi wa kan sa , Wure Wuren maganin maza, yana shiga cikin gidan, ya tarar da ita saman gado, tana zaune , cak ya Wagata suka tafi parlo, babu batun yin Sallah ta godiya ga Allah, ko abincin da ake tsayawa aci bai wani tsaya yaci na kirki ba sai gani tayi ya rungumeta............



Ya haka ango=??=??=??=??




Comment and share=?O?=?O?>?p?>?p?*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan mousse* ( Oum inayah)

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

*Mikiya writers association*


Maashaa Allah, mun samu ?aruwar baby girl daga Aunty Binta, ubangiji ya raya mana surayya.




Page 44&45

_________________________
Duk wani yunkurin hanawa ya yi sex da ita, Khadijah ta yi ?o?ari kar ya yi, amma kuma ?arfin magunguna, da daWewa yana ha?uri, shi ya yi tasirin da yasa ko jin ta ba ya yi, saboda lalurar matarsa, yau kuma ya samu, kura taga nama, ihu take kamar gaske, tana tureshi, kar ya shigeta, amma ina Jabeer ya yi nisa ta yadda ko sauraranta baya yi, sai da ya gama jagwal gwalata, sannan ya fara ?o?arin buWata, numfashi ta Wauke gaba Waya, tana jira taji ya fara dukanta, duk abinda yake yi har yanzu bai shige ba, sai yanzu ya dawo hankalinsa sakamakon wani azababben rami da yaji ya shiga, kuma adai dai nan yaji kansa ya sara, tare da ?walla wata gigitacciyar ?ara mai ?arfi da ya yi.

Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, yau shi Khadijah ta shiga, Sangare Waya ga jikinta wani ciwo da yake yi mata, bayan tumurmusata da Jabeer ya yi , a hankali da jan jiki ta mi?e tsaye, sannan ta raSa , ta gefensa ta sauko k'asa daga saman gadon, ruwa ta Webo a kofi, ta zo saitin fuskarsa ta Wan yayyafa masa, bayan ta tabbatar da ruwan ya ratsasa, sannan tasan ko wani lokaci yana iya farkawa cikin hayyacinsa, kuma komai na iya faruwa idan ya farka, ai kuwa da azama ta fice daga Wakin, kai tsaye toilet ta shiga, ta wanke jikinta, sannan ganin lokaci na tafiya, gashi har an fara kiraye kirayen sallah, da sauri ta shiga haWa y'an kayanta, a madaidaiciya akwati, burinta ta samu tabar gidan kafin ya farka ya yi mata dukan tsiya, cikin zuciyarta addu'a kawai take '' ubangiji ya sa kar ya farka yanzu'' sai da ya yi awanni bayan bacci da yasha sannan ya farka, tare da kiran sunan Allah.


Gudu gudu sauri sauri ta kama hanyar get, zuciyarta cunkushe da ba?in ciki na yadda kwana Waya da zuwanta gidan mijinta, ace yanzu har tabar gidan, wata kwalla mai zafi ta goge, sannan ta ci gaba da tafiya, lokacin gari har ya fara haske.


A hankali yake buWe ido, saboda nauyin da suka yi masa, take ya fara tunanin duk abinda yake faruwa, da sauri ya mi?e tare da neman in da ya ajiye wayarsa, number wayar Ammey ya laluba, sai dai har ya yi ringing bata Wauka ba, take ya fara tariyo duk abinda yake faruwa, tashin farko Hafsah ya tuna tare da rashin lafiya ta, a wani dalili ma ya yadda ya auri Khadijah, har ya kusa yin tarayya da ita, kuka mai tsanani ya fashe dashi tare da tsinewa Khadijah, dan shi a ganinsa ya ci amanar Hafsah, duk da bai wani yi abu da ita sosai amma ya gano ko budurci babu a jikinta, ko a yadda ya sameta yasan ta daWe da sanin Wa namiji ba wannan ne karon farko ba, ganin tunani bazai yi masa ba, sai ya yanke shawarar tafiya gidan abokinsa Usman, shaf shaf ya yi wanka tare da alwala, bayan ya yi sallah, biro da takarda ya nemi a drower, yana tunanin kalar hukunci da zai yiwa Khadijah, kyawawan saki ya yi mata har guda biyu , sanin cewa ko a shari'ar muslunci babu kyau yin saki uku lokaci Waya, daga nan mukullin mota ya Wauka, da sauri ya fito tare da rufe gidan, kai tsaye gidan Usman ya nufa, zuciyarsa na tunanin ko ya zai fahimcesa ya gane ba a hayyacinsa ya auri Khadijah ba, idan ya kasance shi ya fahimcesa to kowa zai fahimta.


A haka har aka Waura auren ko su Annah basusan da cewa an Waura auren Jabeer ba, bareni da ba'a ta tawa, ko hira suke sai dai na bisu da ido, idan abin dariya ne, to zan dara, kuma zuwan Ammey uku dubani, duk da ba wani hira suke yi da Annah ba, amma ya kamata ta sanar da ranar, da aka yi mata maganar sai cewa tayi alhakin sanin zancen baya wajen ta, tunda ba da yawunta ya yi auren ba.

Neman magani dai kullum cikin yi ake amma babu wani cigaba, yanzu ko ni na gano silar kurmancewa ta, wani lokacin idona biyu zan ga yara sun zagayeni da fararen kaya, ko mafarkin yanzu ban fiya yinsa ba, a haka ido biyu zai zomin babu yadda na iya bare na faWawa Annah ko yayyena, sai dai nayi hawaye don ni kaWai nasan halin da nake ciki .


Bata sha wahala wajen ganin mai adai daita ba, kasancewar yanzu garin Kano ya yawaita, addu'a take Allah yasa Jabeer kar ya farka har tabar Kano kar ya biyo bayan ta, Allah ya bata Sa'a motar farko ta samu, lokacin da ta isa tasha har ta kusa cika, babu Sata lokaci kawai ta biya kuWin mota suka kama hanyar Abuja, tana shiga wani kuka ya ?wace mata mai tsanani gaske.



Lokacin da ya isa gidan Usman ko tashi bai yi daga bacci ba, sai waya ya yi masa yace gashi a bakin get, Jamila dake bacci jin mijinta na waya, da safiya da sauri ta mi?e tare da cewa '' ya ya dai Abban teema?'' ta yi maganar da san sanin meke faruwa, '' wallahi wai angon da muka raka jiya ne, yanzu haka yana bakin get wai yazo, shine abin yake ta bani mamakin mai ya kawo shi gidan nan da sanyin safiyar nan'' ya faWa yana mai tashi ya sauka daga kan gadon, ita ma jin abokin mijinnata ne yazo sai ta shiga tunanin mai zai kawo shi gidan yanzu, abu Waya ya share ?o?anton da take sanin yadda abubuwa suke wakana tsakanin Jabeer da Khadijah, duk wani abu da aka yi tana da labari har faWan da suka yi da mijinta, duk akan faWar gaskiya da ya yi, saboda alokacin duk wani dazai kawo mai cikas a auren baya raSarsa, da wannan tunanin bata san lokacin da ya bar Wakin ba, itama kawai ta juya ta koma bacci.


Bayan dogon jawabi da ya tsaya yiwa Usman tare da bashi labarin duk abinda ya faru dashi a daren jiya duk a dalilin Khadijah, sannan ya ?ara da cewa, ''kaga Allah ne ya yi yanzu duk wani shiri da suka yimin ya warware, alamu sun nuna na dawo hayyacina, yanzu ni abu Waya yake damuna ta yarda zan shawo kan Ammey, duk da kace zaka je har gida kayi mata bayani, amma ina tunanin sai an haWa da yaya Hameed dan kaf y'ay'an gidanmu ya fi kowa hankali da sanin ya kamata, ga kuma masoyiyata a gefe ban san a wani hali take ciki ba'' ya faWa tare da share gumin da ya cika masa fuskarsa, duk da sanyin safiya ne amma haka yake zabga uban gumi, Usman sai ?unshe dariya yake saboda duk wanda yaga abokin nasa a wannan halin dole yayi dariya, gefe guda kuma ya tausaya masa, hamdala ya yi cikin zuciyar shi sannan yace '' Alhamdulillah daman addu'a ta a kullum zuwan wannan rana, da zaka gane gaskiya da kanka, ka duba kaga halin da matarka take ciki babu tausayi bare imani haka ka murzawa idonka toka kace aure zaka yi, a lokacin da take bu?atar kulawarka, kai kuma a lokacin ka guje mata, haba Jabeer ta ya ya Allah bazai tambayeka ba, da ha??in baiwar Allah nan, sannan ga na mahaifiyarka, ina tunanin bakasan matarka ta koma gidan iyayen ta ba ko??'' kamar wani soko haka ya Wagawa Usman kai tare da cewa ''eh'' jinjina kai Usman ya yi sannan yace '' tsaya na samo maka ko ruwan tee ka fara gasa cikinka kafin azo abin yi, a kwai wani mutum da yake yin irin wannan maganin, babu nisa gidansa, sai mu fara zuwa mu biyu ayi masa bayanin matar taka, kaga daga baya sai a tafi tare da ita idan yace sai tazo'' ya faWa tare da mi?ewa ya shige cikin gida, ya bar Jabeer da tunanin halin da matarsa take ciki


Yau tunda garin Allah ya waye nake jina cikin farin ciki da annashuwa, ni kaWai nake murmushi, har Ameerah take cewa '' yau kuma Aunty Hafsah ko dai an tuno da yaya Jabeer ne'' ganin kamar zan ri?o hannunta da gudu ta haye sama, kasancewar tunda nazo a Wakin Annah nake kwana, acewarta babu ta yadda zan kwana ni kaWai a cikin Waki babu kowa, ina zaune sai ga ta da gudu da rubutu a hannunta , tana zuwa ta mi?omin tare da cewa '' gashi Annah ta ce ki shanye, Abba ne ya kawo yanzu yace abaki ki sha,'' karSa nayi, kamar gaske ta ruga da gudu tayi waje, ganin ta fita , ni kuma na mi?e tsaye tare da nufar hanyar toilet naje na watsar, sannan na dawo na zauna, domin duk wani abu da za'a bani nasha a yanzu bana sha gaskiya, fakar ido nake na zubar ko na bari sai kowa ya bar in da nake sai nayi kamar xan yi wani abu a toilet sai na watsar dashi.

Kuka kawai take tunda suka Wauki hanya, ko ruwa bata samu ta sha ba, sai tunani da ya ci ?arfinta, a haka wani ya lura da ita cikin motar, ai kuwa babu Sata lokaci, bayan sun zo Abuja ya samu ya yaudareta da kalamai, maimakon ta kama hanyar gida sai kawai tabi mutumin nan in da yace mata yazo.


Sai da Jabeer ya ci abinci a gidan Usman sosai ya ?oshi, sannan suka ?arasa hirar tasu.
Bayan sunyi sallama, anan suka yi al?awarin a gobe zasu tafi gidan malamin, da wannan shawara suka rabu, zuciyoyin su fal da tunanin samun nasara, kai tsaye gida ya nufa, bai tsaya a ko'ina ba sai harabar gidan, sai da ya shiga Sangaren Daddy' suka gaisa, duk da ya yi mamakin ganinsa yanzu ko ?arfe 7 bata yiba, haka ya bar abin cikin ransa, tare da yi masa fatan alkhairi. Yana fitowa ya shiga sauran b'angaren y'an gidan kowa ya gaidasa ana ta tsokanar shi wai ango ango, shi dai ya?e kawai yake musu, saboda baya so tun yanzu su san mai ke faruwa, da haka ya ?arasa Sangaren Ammey, yana shiga farlon farko babu kowa kasancewar safiya ce, har sai da ya shiga ciki sannan yaji Surintu a kitchen.

Ummey ya gani ta fito maimakon Ammey duk a tunaninsa itace a ciki, cikin ladabi Ummey ta dur?usa tare da cewa '' yaya ina kwana'' amsawa ya yi tare da neman waje ya zauna cikin kujerun farlon, daga gani yana cikin damuwa, sannan yace '' ina Ammey?"......................








Comment and shareIZINAA



Story and writing
By.
Abeedatou Alhassan mousse (Oum Inayah)

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1


Mikiya writers association


07049484066

Labarin *IZINAA* akwai tausayi, cin amana, tare da faWakarwa.



Page 46&47



____________________
Kallonsa tayi tare da cewa, '' tana cikin Waki yaya'' sannan ta juya tayi gaba abinta, har ta kusa shiga cikin kitchen taji yace,'' kije ki ce mata nazo'' ba ta musa masa ba, kamar yadda ya ba ta umarni haka ta juya tare da nufar Wakin Ammey.

Tana shiga ta tarar da ita saman sallaya hannun ta ri?e da carbi, sai da ta bari ta kai ?arshe sannan tace ''Ammey! wai yaya ne yazo yana falo, yace kizo'' kallon rashin fahimta tayi mata tare da cewa, '' wani yayan??'' dariya ita ma Ummey tayi jin wai Ammey ta manta da Wan nata, cikin yanayin sha?iyanci irin na yaran zamani tace, ''kema Ammey da wani zance, kike har yaya nawane anan Wakin?, yaya Jabeer man'' mamaki abun ya bata, jin wai Jabeer ne yazo da sanyin safiyar nan, bayan wula?anci da yagama yi musu shekaranjiya duk akan ta hanashi auran Khadijah,, duk da haka sai da ta ce '' yo me yazo yi wajena, tun da ya zama Wan kansa ai shikenan yaje can ya ?arata, da wadda ya zaSawa kansa rayuwa'' ta faWa tare da mi?ewa tsaye tana naWe abin sallar.

Duk wannan faWan da Ammey take yi Jabeer yana ji, kuma yana saurara, take yaji wani tsoro mai tsanani ya kamasa, ganin tun bata ganshi ba ta fara yin faWa ina ga tayi ido biyu dashi, gefe Waya kuma yana jindaWi idan ya tuna in tasamu labarin ya rabu da Khadijah zata yi farin ciki mai tsanani, lalubar takarda daya rubutawa Khadijah saki yaji tana nan babu abinda yasameta, yana cikin wannan zancen zucin yaji muryar Ammey tana cewa '' a'a kaga ango mijin amarya!mai kuma ya kawo ka gidan da ba'a sonka?, T tun wuri ka tashi ka koma in da ka fito kafin dare ya yi maka'' ta faWa tare da nuna mai hanyar ?ofa, saukowa ya yi ?asan kujerar tare da ru?o ?afafuwanta, sannan ya fara bata ha?uri '' Ammey kiyi ha?uri dan Allah ki yafemin ni nasan mai laifi ne, amma yanzu na tuba, idan kina fushi dani aduniyar nan ai nayi asara'' nan ya bata labarin komai da yafaru dashi bayan bijire mata da ya yi na?in bin umarninta, amma ya Soye mata wasu abubuwan da suka danganci Khadijah tunda wani abin sirrine baya faWuwa,.

Shiru ta yi tare da mi?ewa tsaye sannan tace '' yanzu kana nufin Khadijah tana Abuja?'' '' eh Ammey, tunda ina farkawa banganta a gidan ba, kuma kinsan bata da wajen zuwa idan ba nan ba, gashi nan ma bata zo ba, kin ga kenan can Abuja ta tafi'' daga nan take ta yi wajen Daddy' duk abinda Jabeer yazo ya sanar da ita, har da zancen sakin sai da ta faWawa Daddy' bata rage komai ba, salat1 da sallallami Daddy' ya fara bayan ya gama jin zancen, a take ya dannawa number murjah kira, bugu biyu ana uku ta Wauka tare da cewa ''Assalamu alaikum, ina kwana yaya'' bai wani tsaya amsawa ba yace mata '' ina Khadijah tazo nan gida ne?'' wani abu mai kama da saukar aradu taji yana yi mata yawo saman kanta, fatan ta dai Allah yasa kar ace asirin sune ya tonu tun ba'a je ko'ina ba, jin tayi shiru babu amsa ya ?ara tambayarta tare da cewa ''ina sauraranki fa murja'' ajiyar haert ta sauke tare da cewa '' wallahi yaya bata zo ba sai dai ko zuwa anjima'' ta faWa tare tashi daga kwancen da take, take ta fara safa da marwa a cikin Wakin, abun duniya ya taru ya yi mata yawa, duk wani tunani ya riga ya ?wace mata, a hankali ta lalubi wayarta tare da nemo number khadijah ta fara kira, sai dai kuma har ta yi ringing ta gama ba'a Wauka ba, ganin cewa bata sanar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login