Showing 42001 words to 45000 words out of 50448 words

Chapter 15 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

239

da babanta ba sai ta mike domin ta sanar dashi abinda ke faruwa.


Bayan komai ya lafa , Jabeer ya shirya tsaf cikin shiga ta alfarma ya tafi gidan su Hafsah, tarba mai kyau ya samu a wajen Annah Kamar babu abinda ya faru, har zuwa wajen mai maganin da zasuyi ranar Alhamis, sosai Annah ta tausaya mai tare da yi musu addu'a ta fatan alkhairi tare da kariya da neman tsari, aduk in da suke, ganin yana ta kalle kalle sai ta kwalawa Ameerah kira, tace ta yi masa iso wajen Hafsah Wakinta.

Suna shiga cikin Wakin Ameerah ta juyo tare da cewa '' ka jira tana toilet yanzu zata fito'' hakan ma nine da godiya' duk cikin zuciyarsa yake faWa, yana nan a zaune yaji ta fito da Wan ?aramin showel iya ?ugunta, da sauri ya mi?e tare da nufar wajen da take tawowa, baiyi wata wata ba yakai min wata kyakyawar runguma, tare da sakin wata wahalalliyar ajiyar zuciya, ?o?arin turesa nake amma ya?i bani dama har sai da ya dan gantani da gefen gado, zame zanin ya yi tare da cewa '' nayi missing Winki sosai beautina, idanuna gaba Waya ashe makancewa suka yi har na ke ?o?arin jefa kaina cikin masifa, badan Allah na sona ba, da har yanzu ina nan cikin wahala, duk da nasan kina ji na, magana ce kawai baza ki iya yimin ba, amma dan Allah ki yafemin, ki dubeni da idon rahama ki tausayamin ki yi ha?uri'' ya faWa tare da Wago haSata, duk abinda ya faWa ina jinsa, kuma ina ?o?arin buWe bakina nayi masa magana amma na kasa, take naji wasu hawaye masu zafi sun biyomin ta gefen idona, ganin ina hawaye da sauri ya ?ara ru?o ni yadda babu ta yadda zan iya kwacewa yace '' haba zumata har yanzu baki ha?ura ba ko?ni nasan mai laifine awajen ki, amma ki tuna da kalar soyayyar da mukayi abaya ki yafe min, ko sai na tuna miki da baya neeeee'' ya faWa tare da k'yalk'yalewa da dariya, ban san lokacin da murmushi ya suSucemin ba tare da rufe fuskata, haka ya ci-gaba da yimin hira, wata nayi dariya wata kuma nayi murmushi, sai da yaga gaba Waya ya goge duk wani Sacin rai dake tare dani sannan ya rabu dani, shi ya shiryani cikin kayana masu kyau, har dare ya yi Abba ya dawo suka gaisa, sannan da ?yar ya yi sallama ya tafi gida tare da al?awarin zuwa ranar talata Win idan zamu tafi gidan me maganin.



Babu wanda ya ?ara jin Wuriyar Khadijah har tsawon kwanaki uku basu ji Wuriyarta ba, sai a kwana na huWu sannan Mommy murja tana zaune tana saurar labaran yamma duk ta yi Saki ta rame, ban da tunani babu abinda take yi kullum cikin neman y'arta take amma babu labari, sunyi neman har sun gaji, can aka hasko fuskar wata yarinya, an lulluSeta da wani farin yadi,, a'a sai ta sake muskutawa ta ?ara ?ura idanunta, da kyau tana ganin kamar gizo idanunta suke mata, ai wa zata gani.................







Kuyi ha?uri da typing Wan kaWan abubuwan ne sai a hankali





Comments and share*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan muosse* (Oum Inayah)



*Mikiya writers association*

https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

Page Win nan gaba Wayansa naki ne kiyi yadda kike so dashi maman Ayshat.




Page 48&49



Khadija ce gaba Waya kamannin fuskanta ya sauya, idan baka yi da gaske ba bazaka taSa cewa itace ba, saboda yadda ta yi jina jina abun babu kyan gani.

?arar da tayi ita tafito da daddyn su Khadijah daga cikin bedroom Win sa, adai dai kuma lokacin aka daWa hasko fuskar matar sosai yaga fuskar 'yarsa ce, da hotel Win da duk bayanan, duk da namijine amma sai da ya zubar da ?wallah ganin yadda aka yi wa Khadijah kaca kaca babu kyan gani, ganin babu lokaci sai kawai ya kira drever aka saka murja wadda gaba Waya kamar babu numfashi a tare da ita cikin motar suka yi asibiti .

Sai da yaga komai ya yi numfashin nata ya dawo sannan ya tafi Wauko gawar Khadijah domin ayi mata sutura.

Mitina kaWan ya kai sa hotel Win, bai sha wahala ba wajen amsa duk wasu tambayoyi da jami'an tsaro suka yi masa, tare da tabbatar da cewa shine mahaifinta.


A hanyar su ta zuwa gida suka ga tana motsa y'an yatsun ?afarta, duk da kallo Waya zaka yi mata ka gano kalar ta'asar da aka yi mata, amma haka ya daure da yake shi namijine, ganin tana motsi alamu sun nuna da sauran kwananta a gaba, sai kawai suka canja hanya zuwa hospital.


Yau tun safe muke shirin zuwa gidan mai magani, gashi har muka yi sallar azahar bai zo ba, amma haka na daure ina yin duk wani abu da ya kamata nayi, duk da ina jin jikina wani iri, sannan ga rashin ganin mijina duk su suka daWa min na rin?a jin kamar bani da lafiya, haka na daure naje na sake yin wani wankan, jin su Amerah na faWawa Annah Jabeer ya zo, ban tsaya su zo faWamin ba kawai sai tashi nayi na shige toilet domin yin wanka.



Tafiyar awa Waya ta kawo mu gidan, a gaskiya babu wanda zai ga gidan yace gidan wani malami ne' saboda haWuwa da tsarin gidan, tun a cikin mota yake ta shishshige min yake yi kamar wani maye, bayan an buWe mana sittiroom na gidan muka zazzauna, tun daga lokacin da muka haWa ido dani da malam gaba Waya naji kaina ya sara, daga lokacin ban kuma sanin in da kaina yake ba, kallon Annah ya yi sannan bayan sun gaisa cikin mutumci da girmamawa ya ce '' Hajiya alamu sun nuna yarinyar ki tana cikin matsala tun kafin ku faWa min na gano wani mugun aljani ne a jikinta, saboda haka zamuyi iya bakin ?o?arin mu wajen ganin ya rabu da ita lafiya, amma kuma aikin yana da hatsari sosai, yanzu bari na yi magana dashi domin yana kusa tun da kuka shigo Wakin nan shima ya iso saboda yasan idan na haWu dashi karanmu baya yin kyau, daga dukkan alamu kuma ya daWe atare da ita yana cutar da ita, sannan kuma dole mijinta ne zai yi wannan aikin'' ya faWa tare da kallon Sangaren da Jabeer yake wanda ya yi tsuru tun bayan da Hafsah ta faWi yake cikin jin zafi cikin zuciyarsa, '' to malam ni yanzu gaba Waya ban fahimci in da zancen ka ya nufa ba , saboda ni gaba Waya ban san tana fama da wannan matsala ba sai yanzu da kake faWamin, abu Waya na sani tun bata fi 15 year da muka je wani ?auye acan ta haWu da wannan lalurar, kuma an yi magani tun wancan lokacin ta rabu da shi, anamu ganin ashe bai rabu da ita ba'' Annah ta faWa tare da share wasu zafafan hawaye , kallon ta malam yake cike da tausayawa abu Waya ya gano shine, sun daWe suna Soye mata abubuwan da suke faruwa, dan kawai matsala nan da ta zo na rashin magana amma da bazata sani ba, a yadda ya lura shima mijin nata yana da zurfin ciki sukaWai suke ri?on zancen a cikin ransu,. Ajiyar zuciya malam ya sauke tare da cewa '' yanzu dai duk ku kwantar da hankulan ku, in dai wannan matsala ce da yardar Allah ta zo ?arshe, dai a ki ya yi gaba'' ya faWa tare da Wauko wani ruwa a cikin babban mazubi na glass, sannan ya ce '' kai mijinta tashi ka mi?ar da ita daga kwance'' tun da Jabeer ya ji an ambaci sunansa ya mi?e da sauri , sannan ya aiwatar da abinda malam yace masa, sau biyu yana watsa mata ruwan addu'a sannan ya ji wata ?atotuwar murya ta yi magana '' me yasa kake so ka rabani da matata?'' shima cikin wata kalar murya malam yace '' kai kuma kafurin Allah mai ya sa kake cutar da baiwar Allah bata ji ba bata gani ba, sannan a ina ka taSa ji an yi aure tsakanin mutum da aljan?" ko tsayawa ya sauraresa bai yi ba ya ci gaba da cewa '' ina so ka fita ta arzi?i ka rabu da yarinya ko kuma na yi maka abinda zaka rabu da duniyar gaba Waya''' wani irin juyi ta yi tare da mimmi?ewa kamar ita keyin maganar, sannan ya ?ara cewa '' aurena ni da suhana mutu ka raba ne, babu wanda ya isa ya rabamu, tun da yanzu haka y'ay'anmu bakwai kuma duk muna bu?atar ta a kusa da mi, ta ya ya kake tunanin rabamu, sannan ina zaka da ha??in yaran da zaka rabasu da uwarsu, su tashi cikin maraici da rashin kulawa'' wani kuka Annah ta saka tare da tsinewa wannan mugun aljanin da babu imani a tare da shi, can suka ji Muryar malam ita ma ta sauya sannan ya sake cewa '' yanzu dai ka sakar mata ma?oshi da ka ri?e tun kafin yanzu na ?ona ka a wajen nan '' ya faWa tare da Wauko wani abu acikin Wan kwano ya yi wata addu'a take wajen ya fara kamawa da wuta, ihu yake yana kururuwa jin yadda jikinsa yana ci da wuta, sai da ya ji azaba sannan ya ce '' ka kyaleni zan saketa zata yi magana, karabu dani ka ta kuramin can suka ji ta yi wata aitashawa tare mi?ewa a jikin Jabeer ta koma bacci, ''munafikin ba tafiya ya yi ba, yana nan ajikin ta kawai dai ya gudu da yaji zan babbakasa, kuma ba tsira kayi ba da akwai shirin da nake yi maka'' ya faWa tare da mi?ewa tsaye ya yi wani Wakin daban, kallon kallo a ka shiga yi tsakanin Jabeer Annah Haidar da kuma Usman abokin Jabeer, kowa zuciyarsa cike da tausayawa Hafsah wannan wahala da take sha, suna haka sai ga malam ya dawo tare da wata zungureriyar wu?a sai kyalli take, daganin irin wannan sai abu ya tsananta ake nemota, samun waje ya yi ya zauna tare da mi?awa Jabeer ita a hannunsa, hannu na rawa ya mi?a ya karSa tare da jiran ?arin bayani, ilai kuwa malam ya yi gyaran murya sannan ya ce masa '' wannan wu?a da na baka abu biyu zuwa uku zaka yi da ita, idan har kana son matarka ta samu lafiya, sannan masu haWarin gaske har sai ka cire tausayi da soyayya sannan duk wani imani da kake dashi sai ya tafi, domin bama bu?atar sa awannan lokacin, shiyasa ka ga ina ta nanata maka ka cire soyayya ka kawo ?iyayya idan har ba haka kayi ba, ina mai tabbatar maka da wannan mugun bazai taSa barinta tayi zaman aure ba'' gaba Waya Jabeer an Wauresa da igiyoyi babu yadda zai yi haka ya daure ya cewa malam '' in Sha Allah komai kace baza'a samu akasi ba'' ''to masha Allah haka na ke son ji daga bakinka, kaga wannan wu?ar tafi shekara talatin ana irin wannan aiki da ita, sannan kaima daga lokacin da ka aiwatar da komai, zaka dawo min da ita '' kallon su Haidar ya yi tare da cewa su basu waje kaWan, babu damuwar komai suka mi?e tsaye har Annah tare da ficewa harabar wajen, sai da ya ga sun tafi babu kowa daga shi sai Jabeer sannan ya ce '' a duk lokacin da ka ga yazo yana tare da ita, zaka samu wannan wu?ar ko nace addah, sai ka dai daici saitin farjin nata sannan zaka Sara ka kuma sarawa har sau uku, to wallahi daga lokacin ka kashe shi sannan matarka zata samu lafiya, kar kayi tunanin ita ka sarawa a'a ko Waya ita abun baze shafeta ba illah ciwon jiki da zata yi na wasu lokutan, daganan kuma sai ta warke, abu Waya zan ?ara nanata maka shine kar kasake baka karanta wannan addu'a ba kafin ka Wauki wu?ar, saboda nasan halin wannan mugun shu'umi ne zai iya guduwa ka sami baiwar Allah, sannan daga nan kar ku wuce ko'ina sai gidan ku daga yau aikin zai fara'' ya faWa tare da mik'o mai wani abu a leda yana nanata ya ri?e komai da muhimmanci kar ya yi wasa ko kaWan da su.............














Comments and share*IZINAA*


Story and writing
By.
*Abeedatou Alhassan muosse* ( Oum Inayah).


https://chat.whatsapp.com/BvvQMkjyJjyAYY8e9O6WG1

*Mikiya writers association*




Page 50&51



___________A hanyar su ta dawowa babu wanda ya yi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????magana, zuciyoyin su babu daWi ko kaWan, har gwara Usman shi yana Wan taSa hira da Haidar tunda motar su Waya, a haka har suka kawo gidan su Annah domin a sauke su, duk da malam yace su tafi gidan su daret amma yanzu saboda gidan na bu?atar gyara shiyasa Annah tace sai gobe sa koma, har wannan lokacin Hafsah bacci take yi bata farka ba.


Haidar na shiga gida ya tarar da Madam na malelekuwa saman cafet, shiyasa baya nisa da gida tunda ya duba yaga watan haihuwarta ya tsaya, ai da sauri ya yi wulli da abun hannun sa ya yi kanta, bai sha wahala ba wajen gano na?uda ce ba, tun da shi doctor ne, daret hospital ya yi da ita, suna zuwa a ka shiga da ita labour room, domin tazo gaf haihuwar, hum mata fa sun ji maza tuni Humaira ta canja kala, ga mijin shima ya ?i barin Wakin a ta?aice dai wannan haihuwa su biyu suka yi ta, kiran sallah farko na la'asar ta santalo zankaWeWiyar yarinyarta mai kama da ubanta kamar ya yi ka ki ya ajiye, ''shikenan Hafsah ta zo'' cewar Humaira bayan an gama yiwa bebyn wanka gwanin sha'awa, gashi daman Hafsah da Haidar suna kama, kunga yarinya kyau har sai ya yi mata yawa, sai dai muce Allah ya raya mana ita bisa tafarkin addinin Muslunci. Ko kafin 'yan mintuna tuni asibitin ya cika da yan uwa da abokan arziki Kowa burinsa ya Wauki beby, sannan ?arin wani abin farin cikin a ranar bakin Hafsah ya buWe.

Bayan an duba beby da maman kowa lafiya sai aka rubuta musu sallama domin tafiya gida, da kyar Haidar ya yadda za'a tafi da Humaira gidan Annah a cewar sa shi zai iya kula da beby da maman beby, haka dai babu yadda zai yi aka kama hanya aka tafi gaba Waya.


Daga lokacin da muka dawo gida nima nasan na samu lafiya, domin wasu abubuwa dayawa na samu sau?in su, sannan wani ikon Allah, tun ranar da Humaira ta haihu a ranar na fara buWe bakina wajen yin magana, murna sai ta zamo kashi biyu, ta kowanne bangare farin ciki ake, sosai Abba ya dage wajen sauyamin kayan Waki da komai na gida, acewarsa yanzu nake amarya tunda na samu lafiya.

Soyayya mara algus ita ke gudana tsakanin Ummey da Khalid yanzu haka bikin ya kusa, saura bai fi two weeks ba, amma Ammey ta hana har sai Hafsah ta samu lafiya za'a yi, yau ma tunda suka tafi kai Hafsah gidan me magani shi kuma ya kama hanya ya yi tafiyarsa wajen ta hira, har sai yanzu da yaji anyi musu haihuwa, amma an Soye masa samun lafiyar ?anwarta sa, babu yadda ya iya haka ya yi mata sallama tare da al?awarin sake dawowa washegari ya kaita tayi barka a gidansu, tana shiga cikin gidan take sanar wa Ammey Humaira ta haihu, addu'a ta yi wa babyn tare da fatan alkhairi, suna cikin hirar sai ga kiran Annah yya shigo cikin wayar Ammey, da sauri ta Waga tare da cewa '' Assalamu alaikum'' ta Waya b'angaren itama Annah ta amsa da '' waalaikumussalam, dafatan kowa yana lafiya'' nan ta zayyane mata duk abinda ke faruwa tare da cewa '' dawowarmu kenan ita ma Humaira ta haihu, yanzu haka sun dawo gida an sallame su'' to ubangiji ya raya in sha Allah zuwa gobe zamu shigo, itama Hafsah ayi mata sannu da barka da arzi?i, Allah ya ?ara kiyayewa'' '' ameen ya Allah, sai kin shigo'' '' okay sai anjima'' Ammey ta faWa tare da mi?e zuwa kitchen domin Wora sanwar dare.


Tunda likitoci suka fara duba Khadijah suka gano cewa fyade akayi mata mai muni, a ?iyashi kamar ba mutum Waya ya yi amfani da ita ba, sannan har ta Saya suka yi mata aika aikar ta in da ko an yi aiki kafin ta dawo dai dai za'a ci ba?ar wahala, shiyasa babu dogon jan lokaci suka kira Daddy office sannan suka sanar dashi ga halin da ake ciki, a take anan bayan sun sanar dashi komai ya Wauki waya domin faWawa Jabeer halin da ake ciki tunda bai san abinda ya faru ba ko kaWan,, ringing Waya ana biyu ya Wauka bayan ya yi sallama ya ?ara da cewa '' ya har yanzu ba'a samu labarin Khadijah ba'' a take Daddy ya zayyane masa komai tare da cewa '' yanzu haka aiki za'a yi mata shine nace yakamata, amatsayin ka na mijinta kasani'' '' ba matata bace Alhaji, yanzu haka takardarta na ajiye ko wani lokaci kuna iya karSa,, na gaji da ri?on ta a hannuna'' ya faWa tare da yin amfani da wannan damar wajen isar da sa?on da yake son isarwa, da sauri shima yace '' what, mai kake nufi da cewa ba matar ka bace, oh kana nufin kace ka saketa ko ya ya'' ya faWa tare da mi?ewa tsaye duk ya wani firgice, ashe tuni Jabeer ya kashe wayarsa ba, sai da ya yi magana yaji shiru sannan ya yi wurgi da wayar tare da bawa likitan umarnin a shirya komai na aikin yanzu shi zai saka hannu a matsayinsa na mahaifinta.


Yau ake suna gida ya cika da yan uwa da abokan arzi?i ko'ina ka duba hada hadar abinci ake, me jego ta samu abin arziki sosai ta kowanne fanni, Abba akwati biyu ya yi mata ita da bebyn, sannan ga Ammey ta kawo akwati cike da kaya, mutane ?auye suma ba'a barsu a baya ba, shi Baffa gona sukutum ya Wauka ya bawa jaririya ga innah kulu har da ita tazo suna da abin arzikinta da ta kawo wa mai jego, yanzu tana sana'a tun bayan mutuwar Lanto tayiwa kanta faWa tare da watsar da Laraba Aminiyarta, abindai sai wanda ya gani, ko ni da ba nice na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login