Showing 15001 words to 18000 words out of 50448 words

Chapter 6 - Izinaa Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

242

?i ci, ta?i sha, kullum in banda ramewa babu abinda takeyi, To wallahi da sake ki tashi mu koma wajen wannan annamimin daya bamu abubuwa marasa kyau'' ta faWa tana me ?ara jin kamar ta rufe Laraba da duka, ita dai Laraba tsayawa tayi ta hangame baki kamar shantu tana kallon ikon Allah, cikin zuciyar ta cewa take '' tunda ke banza ce ki ta kawo kuWi abanza muna rabawa da nakan tudu, ai dama nayi al?awarin duk dukiyar ki sai naga bayanta sai ya zaman to ko zanin Waurawa ya gagare ki'' Amma a fili cewa tayi haba ?awar arzik'i ai komai a hankali ake binshi ba da faWa ba, yanzu ki barikki ?ara tara wasu kuWin Sai mukoma wajen nakan tudu ya ?ara yin wani aikin' kin san farin cikin ki shine nawa'' ta faWa tana yimata gwalo ta yadda ba zata taSa ganewa ba, ita kuwa sakarar sai washe jajayen ha?oran ta take tana dariya wai har ta fara imagen 'yar ta tayi aure a birni itama mijin yace azo a Wauki babar matar tashi' ta Wauka a zuciya ta ke wannan haukan ashe duk Laraba taji ta, itama harara ta banka mata ta gefen ido sannan tace'' sai dai in a lahira Amma a duniya dai bazaki taSa ganin wannan abu ba , 'yar ki sai dai Wan ?auye Wan ?auye ma idan ban yi niyya ba ita da aure sai dai taga anayi badai yazo akanta ba'' duk cikin zuciyar ta take wannan zance, Allah karabamu da mugayen ?awayae ameen.
Mintina kaWan ta ?ara sannan ta tashi tayi gida da alwashin samo kuWi ko ta wacce hanya.






*********


Da kuka ta shiga Wakin ammey mahaifiyar Jabeer, abinda batayi ko shiga Wakin sai ta ga dama Amma yau da ke tatace ta kaita taje , ummi kaWai ta tarar a Wakin' Da har zata juya sai kuma komi ta tuna ta dawo baya''ke'' khadijah ta faWa tana wani kumbura hanci kamar anzuba yiss, ko kallo bata ishi ummi ba ta ci gaba da gyaran gadon da takeyi, har sai da ta ga ji tace '' wai ummi ba magana nake miki ba?''sai a sannan ummi ta juyo cikin maganar ta me sanyi tace'' Aunty Khadija banji me kikace ba ina aiki ne'' ganin ita take nema sai tace wa ummi ''ina ammey?" A yadda take aikin ta bata jiyo ba tace mata '' tana Wakin Daddy'' to idan tazo ina Wakin Khadijah kizo ki kirani'' ta faWa tana me banko ?ofar kamar ita ce tayi laifin'' oho inshallah Yaya Jabeer bazai taSa auren ki ba saidai ki mutu'' ummi tace''tana me murguWa Wan ?aramin bakin ta.









***





Gaba Waya muna cikin farlor, mune 'yan rakiya dani da Humaira da Amira, da ?yar Humaira ta yadda zata je ganin hadda mala'ikan nata a 'yan rakiya Annah dai fatan alkhairi take tayi masa, ganin cewa duk hankalin su yana wajen yaya Khalid na mi?e naje kusa da Humaira nace'' idan mun dawo ba gida zamuyo ba xansa driver ya kai mu wajen sha?atawa'' na faWa ina dariyar jin daWi ganin tun yanzu xan fara wata yawa kafin Wayan shima yazo ya ?ara gaba, ''to dariya me kuke yi kuke ta faman gwara kawuna'' cewar yaya Haidar bayan ya kira sunana har sau biyu yaji shiru ban amsaba, ''babu komai kawai ce mata nayi ta tashi ta shirya yanzu za'a tafi'' dasauri yace" dawa za'a je?" Ya faWa yana kallon b'angaren da Humaira take , jin wula?anci da zai yi da sauri Annah tace ''to sannu ishashe kaine zaka bada list Win sunayen da zasuyi tsakiyar? Ku tashi kuje Allah ya tsare babana ya bada Abinda aka je nema,, ''ameen Annah '' ya faWa yana me mi?ewa tsaye,.

Dukkan mu muka Wunguma bakin get Anan muka samu ado drever yana jira, Ni da su Amira muka shiga ciki, shi kuma yaya Khalid ya shiga motar yaya Haidar,.

Tafiyar awa Waya ta kawo su filin jirgin sama na malam Aminu Kano'
Duk muka fito ashe ma Lokaci ya kusa ?urewa,muna zuwa ana kiran sunan su, Amira kawai muka ji ta fashe da kuka wai sai ta bi yaya anan tasa kowa ya zubar da ?walla, to Nima ganin anata hawaye sai kawai na fasa wani ihu ina cewa''wayyyo Allah na yaaya na ya tafi ya barni na faWi ?asa ina birgima, wata razananniyar tsawa Haidar ya daka min da hankalin jama'a da dama ya dawo kan mu, dai dai Jabeer da yake sallama da abokinsa ya Wago kanshi sakamakon tsawar da yaji anyi.............









Comments Win ?u shine zai bani ?warin gwiwa na cigaba da typing kullum>?p?>?p?>?p?





07049484066


Comments and share fisabillahi=?O?=?O?=?O?=?O?**IZINAA**


By.

Abeedah Alhassan muosae (oum inayah)


**Mikiya writers association**



Page 20&21



_________Ina can Ina shirme na har jirgin su yaya Khalid ya Waga sai fatan sauka lafiya, sai ji nayi Humaira na cemin ''To idan kin gama kukan ?aryan! Ki ta so mu tafi drever na jira'' ta faWa tana me Wago min hannu na, dariya Nima nayi sannan nace mata ''yarinya naki wasa ne, ke kina tunanin yaya Haidar zai barmu mu sha?ata to wallahi daban nuna nima na damu da tafiyar ba kinsan zai iya samana ido a cikin gida Amma yanzu da nayi haka kinga jikinsa shima yayi sanyi kamar gaske''. Na faWa ina me she?ewa da dariya kamar ba nice na gama zun duma ihu ba kamar Allah ya aiko Ni, haka muka shige mota na cewa drever shopping zamu je ba gida zai kai muba, Duk wannan abin da ake Jabeer kallo Waya yayi mata ya Wauke kansa ya na ji cikin ransa kamar ya taSa jin Muryar Amma haka ya juya ya shiga cikin mota drever yaja suka bar wajen.

***

Khadijah yau tun safe ta saka momy murja a Gaba sakamakon wula?anci da Jabeer yayi mata da taje Wakin sa jiya da daddare kuka harda hawaye, sai da tayi mai isar ta sannan momy murja ta ce mata ''wai ke duk akan namiji kike wannan Sata lokacin kika zauna kika sani agaba kamar 'yar yaye kina wannan kukan alhalin kinsan Jabeer bashi da mata in bake ba, ya gama wula?anci nasa, duk tsiya gida bai ?oshi ba, ba za'a kai dawa ba''.

Suna cikin wannan yanayi umme ta shigo da sallama abakin ta sannan tace ''momy kizo inji Daddy'' tana gama faWa ta juya ta fita, wani wawan tsaki Hajiya murja ta yi sannan tace wa Khadijah''kinga yanzu dama na samu dazan faWawa yaya Abinda ake ciki yasan kalar wula?anci da Wan sa yake miki domin ya Wauki mataki, ko yayi min magana tafiya zance masa ke anan zaki zauna Ni kad'ai zan tafi'' Da sauri Khadijah ta juyo tana dariya fuska shaSe shab'e da hawaye Amma tsabar jin dad'in maganar da momyn Nata ta fad'a sai taji duk wata damuwa da take da ita kamar an d'auke mata ita cikin zuciyar ta ''Na gode momy shiyasa nake alfahari da samunki a matsayin mahaifiya ta ,da yanzu Ban san yadda zanyi ba, wallahi idan yaya Jabeer bai Aure Ni ba mutuwa zanyi momy'' Dad'i kamar yayiwa Khadijah me, kamar ance an d'aura aure haka take ji, sallah da bata tashi tayi ba sai taji k'warin gwiwa yanzu haka ta tashi tashiga torlet domin ta samu tayi alwala tayi sallah kafin momy ta dawo daga wajen Daddy''.


****

Dai dai bakin k'atan wajen ciye 'ciye motar mu tayi parking, Ameerah sarakan Shan zak'i da gudu tafito daga cikin mota ina kiranta ta tsaya mu jera Amma ina' har ta k'ule ciki, cikin tsokana na cewa Humaira''kin tuno zuwan farko da kika yi wajen nan mrs Haidar'' dariya tayi harda rufe fuska wai ita ga mai kunya, bata kula Ni ba domin tasan tsokana tace sai kawai ta bud'e murfin motar itama tayo waje mayafinta a hannu, Ni dake shahararriya ce ko mayafin ban d'auka ba haka na fito ban damu da maxan da suke kallo na ba na bi bayan su Humaira ciki.


*******

K'auyen DUGUL, lamari yayi tsamari yanzu abin ya kai Lanto ko abinci bata iya ci, kullum da tunanin masoyin ta Khalid take kwana, sau biyu tana yunk'urin guduwa Amma tana fasawa saboda in dai akasan Abinda ta aika to zaman k'auyen sai ya gagareta da ita da iyayen ta domin abin kunya ne ace tana Fulani ace tabi saurayi garin su to gaba d'aya itama sai ta tsani kanta shiyasa ta fasa guduwa Amma har yanzu zuciyar ta Bata Dena sak'a mata ta gudu ba, innah kulu ta gaji da shawo kanta kullum cikin yimata addu'a ta ke Allah ya raba ta da san maso wani abu sai gaba yake kamar ana k'ara ruruta mata sanshi cikin zuciyar ta.
Yau innah tayi shiri zata koma gidan Laraba saboda ta tara kud'in da tace ta tara, dasu za'a koma gidan boka.

Bayan taje suka D'unguma sai gidan boka na kan tudu, basu sha wahala ba yau saboda babu layi sosse mutane duk sun tafi shiyasa suna zuwa ana cewa su shiga, yau din ma irin kayan daya bata wancan lokacin da suka zo sai dai tayi mita wai maganin sa baya aiki ita idan yasan kud'in ta zai ci ya fad'a mata sai ta canza wani, da ido Laraba tayi masa magana sai kawai ya sassauta murya irin ta shed'anun farko Sannan ya fara magana babu dad'in ji ''ki kwantar da hankali ki indai kin bi k'aidojin da na fad'a miki to duk in da yake zai ji hankalin shi ya dawo kanta ki dai kiyaye kawai'' ya fad'a yana wani huci kamar alade fuska kamar ta Yahudawa, .
Bayan sun fito kai tsaye hanyar gida kowa yayi zuciyoyin su kowa da kalar tunanin da yakeyi Amma kuma a fuska bazaka tab'a gane wani yanayi suke ciki ba, har suka zo hanyar da kowa zai kama gaban sa sai alokacin Laraba tayi magana tace ''to k'wata Allah yasa a dace ki kula fa kar azo asami matsala'' ta fad'a tana me juyawa tayi saitin layin su bata jira abinda kuluwa zata ceba.
****

Dai dai lokacin da muka zo wajen shima Jabeer yazo saboda abokinsa ne mai wajen, ya kira shi a waya yana san ganin shi.
Ban kula da shi ba kawai sai jinayi munyi karo da mutum abin tsautsayi kuma nayi baya zan fad'i akan idon Ameerah da ta cika manyan ledoji da kayan zak'i, da gudu ta tawo tana cewa ''Auntyyyy kar ki fad'i, ko kafin ta gama magana Da sauri ya taro ta' ta fad'a saman k'irjinsa............,...







Comments and share fisabillahi=?O?=?O?=?O?**IZINAA**


By.

Abeedah Alhassan mousse (oum inayah)
**Mikiya writers association**

Page na kune
Ammyn laila
Real lemmah
Oum Nihal
A'isha s maibankeey



Masuyimin comment Ina godiya



07049484066


Page 22&23



_______Ganin hankalin jama'a ya dawo kaina yasa, na zame jiki na daga nashi, cikin basarwa yace ''ki ringa lura idan kina tafiya saboda baki san wanda yake bayan ki ba, yanzu da wani ne haka zaki fad'a kanshi?'' ya fad'a yana me tsare Ni da idanunsa masu haske da sanya mutum kasala, ''borin kunya kawai yake yi sai kace wani mijina zai ce da wanine ai duk d'aya kuke'' na fad'a ina me kallo gefe d'aya, duk cikin zuciya ta nake maganar kai na, na mayar k'asa ban san lokacin da ya bar wajan ba, sannan nayi kamar banji Abinda yake cewa ba, na kalli b'angaren da Ameerah take nace mata ''idan kun gama muje abiya kud'in kayan mu wuce gida yamma ta nayi'' sai jinayi Humaira tace''Aunty Hafsah Naje zan bada akace wai an biya mana kuma na tambayi wanda ya biya sunce yace kar afad'i sunan shi'' ''ikon Allah'' na fad'a ina me tunanin waye ya biya kud'i masu yawa irin haka duk tunanin da nayi ban kawo wannan mutumin da ya taimake Ni d'azu gaba d'aya tunani na bai kawo shine zai biya kud'in ba, ganin zan damu kai na yasa nace musu ''ku wuce mu tafi gida na fasa shiga Ni, tunda ku kun d'auko Abinda kuke so'' Duk mu ka ranka ya mukayi wajen mota.


Ganin sun shiga cikin mota, shima a hankali ya shiga tashi motar ya tayar sannan yabi bayan su, yana fatan yau kar ta b'ace masa, har sai ya ga gidan su.

Sun zo dai'dai Danja ta kabuga kad'an ya rage basu b'ace masa ba, hamdala yayi cikin zuciyar shi sannan ya k'ara wa motar shi mai yabi bayan su.

Hon mai k'arfi direban ya danna sannan mai gadi ya tawo da gudu ya bud'e musu get d'in.

''Thanks ya Allah'' abinda ya furta kenan ganin yaga gidan da suka shiga sannan ya juya yayi baya, a hankali yake tuk'in zuciyar shi yau tana cikin nishad'i yau yasan dad'in da yake ji bazai fasaltu ba, shi har ya hango ta aminta dashi domin kallo d'aya da yayiwa yarinyar yaji ta kwanta masa cikin ranshi, kuma ya ga irin matar da yake so ta zamto uwar 'ya'yan shi. Tunanin da yake tayi kenan cikin zuciyar shi har ya zo dai dai kwanar layin su, Anan yaga wata almajira tana Bara da 'yar sandar ta, parking yayi dai-dai saitin da take ya zaro rafer 'yan d'ari biyar ya bata, sannan ya k'ara wa motar shi mai
Kiran da yaji Daddy na masa yasan bana lafiya bane, yana ji tana ta zabga godiya Amma bai saurare ta ba yayi gaba, yana addu'a Allah yasa lafiya Daddy' ke masa wannan kiran.


Muna shiga muka tarar Annah na Safa da marwa a tsakanin parlor da kitchen tana aiki sannan ga tunanin yaran ta da akace tun d'azu suka tawo gida Amma har yanzu la'asar ta kawo kai basu dawo ba, shiyasa gaba d'aya hankalin ta a tashe yake, ko abincin rana bata samu tasa a cikin ta ba, tana wannan jimamin taji sallamar autar ta, ta cika cikin parlon, ko dana yi sallama Annah hankalin ta yana wajen autar ta, tana bata labarin wajen da muka je , ganin haka sai kawai na haye sama Domin naje na watsa ruwa a jikina yau garin zafi akeyi sosse ga kuma hadari da yake ta had'owa kamar ruwa za'a yi.


***

Cikin jin dad'i innah kulu ta fara gabatar wa da Lanto bayanin da boka yayi mata, sai dai cikin rashin Sa'a a lokacin da take wannan surkullan, shi kuma Khalid yana zaune saman sallaya hannun shi rik'e da Alkur'ani mai girma yana tilawa, sau biyu aljanin da boka ya tura yana dosar d'akin wani hayak'i ke hankad'o shi Amma saboda naci haka ya kuma komawa, wannan karon tsabar sautin Muryar da Khalid ya bud'e yana karatu cikin salo da k'warewa na mahaddacin Alkur'ani mai girma ,har sai da gefen fuskar shi ya fara k'onewa, sannan ya rabu dashi ya koma wajen wanda ya turoshi.
***
Taron gaggawa Daddy' yau ya had'a a babban farlon shi, sai da kowa ya hallara sannan 'ya'yan d'akin Ammey dana d'akin Ummah ga kuma momy murja itama da 'yar ta kowa wanda yake cikin gidan sai da yace yana san ganinshi amma banda wanda yayi aure, yanzu a cikin samarin gidan Jabeer ne kad'ai bashi da aure, mata kuma Khadijah da umme sune y'an mata, sai da kowa ya zauna sannan ya bud'e taro da addu'a, zuciyar umme ita dai sai bugawa take saboda tasan ita ko d'an kaza be tab'a cewa yana san ta ba, to ina ma Ta fita kullum mutum yana cikin d'aki a kulle daga makaranta sai gida babu inda suke zuwa, har gwara ma Aunty Khadija ita tana k'arya ta fita kuma tana da samari, ita dai sai dai auren had'i za'a mata'' duk cikin zuciyar ta take wannan zancen.
Bayan Kowa ya shafa ya fara jawabi kamar haka ''Abinda yasa a tara ku Anan shine murja tayi min wani bayani wanda nima yayi dai'dai da ra'ayi na , nason had'a Aure tsakanin Jabeer da Khadijah y'ar wajen ta, sannan ya nuna umme da Khadijah, kuma ya kamata ku fitar da wanda zaku Aure atsakanin waenda suke sanku, gaba Wayan ku nake so ayi bikin ku, idan muna da rai da lafiya'' ya fad'a yana me d'auko ruwa ya kurb'a kad'an sannan ya ajiye ya ci gaba da bayanin da ya kusa tarwatsa zuciyar Jabeer ido kawai yake bin mahaifin nashi dashi har ya kammala sannan yace yaran su tashi abar iyayen yana san yayi Magana dasu har ita murjar.

Tafiya yake bai san inda yake saka k'afar shi ba, duniyar gaba d'aya juya mai take yi, yau yayi danasani so babu adadi na rashin sanar wa da Daddy' yana da wacce yake so, har yayi wannan hukunci da ya kusa tarwatsa zuciyar shi, shi ko rasa mata yayi bazai tab'a auren jinin Mommy murja ba, matar da ta tsani Ammyn shi tun suna yara suka san irin wula?anci da take yi idan tazo Kano, Amma shine yanzu zata ce shi take so uhm lalle Daddy' zai san yanzu ba kamar da, bane ba, da komi yace yayi mashi babu musu yake yi Amma wannan karon babu wata biyayya da zai yi ya cuci kansa shi.
Da wannan tunanin ya k'arasa part d'in su, ko ya samu yayi Bacci ya huta.

Bayan sun fita ya jiyo da kallon shi b'angaren da Ammey take sannan yace''kinji Abinda na fad'a ko ko kina da Abinda zaki fad'a'' ''a'a Alhaji duk Abinda ka yanke ina mara ba dashi Amma ina da magana akan umme, Alhaji katemaka ka janye banda ita a wannan lokaci Saboda tun da muke babu wanda yace yana santa, gashi tayi k'ank'anta da yawa duka duka yanzu tayi 16 year aduniya ka daure kabarta ta k'ara girma tukun'' ta fad'a tana me sunkuyar da kanta k'asa domin wannan maganar ma da tayi daurewa kawai tayi saboda bata so ace an samu b'araka ta b'angaren ta , ''Naji duk bayanin ki zan duba yanzu zan gana da bak'o

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login