Showing 36001 words to 39000 words out of 127646 words

Chapter 13 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

257

tako wace irin siga musamman ma kai, dan ko ita Kareema na hanata fita aikine daga baya bisa wannan dalilin, amma duk sai kuka fahimci cewar saboda Mawaddat ne. Eh saboda itane, dan ita ta ƙirƙiri hakan dan kuɓutar da Kareema daga sharrin Sulaiman batare da koni na fahimci hakan ba sai daga baya. Sai kuma lokaci da baiyi ba kamar yanda na faɗa, dan kasan komai na ALLAH ne sannan yanada lokacinsa.”
       “Hakane Yaya na kuma yarda dakai. ALLAH sarki Maman Mawaddat munata zarginta akan abubuwa da yawa. Ciki harda tunanin ko asiri tai maka a farko, sai daga baya nima na fahimci ba haka bane saboda wasu dalilai. ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata.”
    Cikin lunshe idanu Daddy yace, “Amin Yousuf, ai shiyyasa zargi bashi da amfani. Akoda yaushe da ace munama duk wanda ya shigo rayuwarmu uziri akan al'amuran rayuwa damun zauna lafiya da samun salama a zukatanmu”.
             “Hakane Yaya. Amma duk da haka akwai abinda kayi da har yanzu basu wanke a zuciyata ba. Na farko akan Mawaddat daka nisantata da samun karatun Addini dama sakaci akan tarbiyyarta. Na biyu nuna mata goyon baya akan duk abinda tai dai-dai ne harda nuna ƙyamar talaka a matsayin mijinta. Why Yaya? Bayan nasa wannan ba ɗabi'un da iyayenmu suka horar da kai bane ba”.
       Ɗan jimm Daddy yay cikin tsantsar damuwa. Kafin ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya zubawa Uncle Yousuf. “Tabbas Yousuf wannan shine babban kuskuren da nai da cutar da rayuwar Mawaddat a rayuwata da bazan taɓa yafema kaina ba. Da farko halin Sulaiman ya rufemin ido da abinda naji dangin mahaifiyar Kareema na faɗa mata. Sai nake ganin nisantata da ƙasar kamar yanda mahaifiyarta ta roƙan tun farko kamar shine masalaha agareni da ita. Namanta shi UBANGIJI shine mai tsarewa a duk inda kake. Na tauye rayuwar Mawaddat akan rashin ilimin addini da kaita wata ƙasa da kafirci yafi ƙarfi a gaɓar da komai idan ta gani bazai zama abin ƙi ba a gare ta. Wannan itace jarabawata ni da ita. Maybe hakkin yarinya da Sulaiman yayma fyaɗe na ɓoye ne bayan nasan gaskiya UBANGIJI ya jarabceni da hakan, shaye-shaye kuwa a dalilin haɗa hannu da nai da su Sulaiman da bamu san iya adadin yaran da wannan safarar tamu ta gurɓatawa rayuwa ba duk da ban sani ba inaga shine nan UBANGIJI ya jarabceni akan ta. Sai kuma soyayyar da na dinga dana sani akan ƙin nuna ma mahaifiyarta har sai da ta roƙa gareta bayan ita ɗin jinina ce shima ya taka rawar gani. Sai tausayi da ya zama jagora Da silar zama komai. Ban taɓa ƙin Aliyu a zuciyata ba game da alaƙarsa da Mawaddat. Hasalima a kullum cikin tashin hankali nake kar adalilina su Sulaiman su cuta masa. Saboda har sacesa sun taɓa yi Sulaiman ya bashi aiki akanmu ni da ita. Amma yaron nan ko sau ɗaya bai taɓa gwada cutar damu ba. Yousuf baka san irin kalar ƙaunar da nakema yaron nan bane. Wlhy a duk sanda ya kawo Mawaddat gida nakan laɓe naita kallonsa da sanya masa albarka. Ko kuɗi da gida da mota dana bashi na bashine bada wata manufa ba sai don nima na ƙyautata rayuwarsa kamar yanda UBANGIJI NA ya ƙyautata tawa da silar Baba Garko, sai dai idan na fito da sigar da za'a kalla a masalaha komai zai iya faruwa da shi. Saboda yanda ya tsunduma kansa a al'amarin Mawaddat wanda na tabbatar zai iya cutuwa har sakawa nai ƴan sandan farin kaya na bin sa batare da ya sani ba. Inaga bayan aurenka ban taɓama wani aure kukan farin ciki ba sai na Mawaddat, dan a randa aka ɗaurashi na kwana yima ALLAH godiya, hakama randa ta tare na kwana roƙon ALLAH yasa gidan zamanta ne. Amma sai Kareema take ganin al'amarin nawa a juye. Ko nawa auren na farko dana biyu duk sunzo da dalilai ne, dan haka ban jisu a jinin jikina ba kamar wannan auren, ni kaɗai nasan irin addu'oi da nake maka a zuciyata. A randa na kirashi game da barinta ta fita aiki nayi hakane dan na tunzurashi da kai ku hanata fitar, dan hakan da zanyi ne kawai zai sake tabbatar min da yaron zai iya abinda nake fata akan Mawaddat. Sannan zai iya juyata a yanda kowane namiji ya kamata ya juya gidansa bawai ita a matsayin mace ta juya shi ba. Sosai na dinga dariya akan maganar da ya faɗa min, na yini raina fes, sai dai a fuska kowa ya gagara gane kaina har Kareema. Yousuf ina son Kareema sosai dan matar ƙwarai ce, sannan ita ɗin jinin jikina ce, zuciyata na mata uziri akan abubuwa da dama. Soyayyarku a gareni ta dabance Yousuf, ku nakema kallo tamkar iyayena, dan kuna iya gayamin gaskiya duk ɗacinta. Garama Khareema tana jin shakkata, wasu lokutan takan haƙura ta shanye”
        Shiru kawai Uncle Yousuf yay yana kallon Yayan nasa da murmushi a fuskarsa mai ƙayatarwa, a zuciyarsa kam sai ayyana (Namijin duniya) yake. Tare da jin nadamar abubuwan da ya dinga yi game da ɗan uwan nasa musamman zargi. Cikin ƙarfin hali Daddy ya katseshi da tambayar ina Smart yake a yanzu?. Kai tsaye Uncle Yousuf ya sanar masa komai akan Smart daya sani da ga wajen Abdull-Hameed Coach. Sosai Daddy yaji tausayin yaron ya ratsa masa zuciya, tare da ƙaunarsa ta haƙiƙa na sake ratsashi...
      “ALLAH ya bashi nasara akan burinsa ya kuma yimasa albarka” Daddy ya faɗa yana miƙawa Uncle Yousuf wayarsa. Uncle Yousuf dake amsa addu'ar Daddyn ya amshi phone ɗin ya tsirama hoton ƙyaƙyƙyawan jaririn ido, tunani yake ina ma yasan wannan fuskar?. Kasa hasasowa ya sashi faɗin, “So cute Yaya, yaron wanene haka da nake jinsa a raina tamkar jininmu”. Murmushi Daddy yay mai haɗe da ƴar dariya, sai kuma ya dafa ƙafaɗar Uncle Yousuf ɗin da faɗin, “Jininka ne Yousufa. Dan ka zama Grand father yanzu”.
       “Grand father? Ta yaya Yaya? Ni da bayan Mawaddat ɗina ban aurar da kowanne ɗa ba, duk da itama an sanar mana tana da ciki, sai dai rashin sanin ina take yasa bama musan yaushe ne haihuwarta ba”.
     Sake faɗaɗa murmushin Daddy yay da tsare ƙanin nasa da ido dan san ganin irin reaction ɗin da zai nuna. A hankali ya furta, “Ai Mawaddat ɗin taka ce ta haihu jiya ɗin nan...”
          “What!!!!”.
     Uncle Yousuf ya faɗa da ƙarfi cikin wata irin zabura da ta saka jikinsa har yana karkarwa. Cikin rawar murya ya ce, “Yaya Please karka min wasa irin wannan dan ALLAH. Wlhy zan iya maka kuka”.
     Dariya sosai Daddy keyi masa, kafin ya jinjina masa kansa alamar tabbatarwa. “Babu wasa a maganata Yousuf, bakaga ɗan na maka kama da ƙanin naka Aliyu ba.”
             “Ya subahanalillah! Yaya dan ALLAH mafarki nake ko ido biyu? Idan a barci nake jin wannan zancen ka taimakeni karka bari na farka. Idan ko a zahiri ne ka faɗamin dama kasan inda Mawaddat take duk wannan kaiwa da komowar da nake yi”.
        Daddy dake murmushi har yanzu ya kamo hannun Uncle Yousuf ya sake zaunarwa a kusa da shi. “Please relax sweet heart. Ai ina sane da duk wani shigi da ficinka, na Barka ne har zuwa irin wannan ranar ta yau sannan kasan gaskiyar al'amarin. Dan na sanka da rashin haƙuri farin ciki zai iya sakawa ka buɗe min aiki. Ai tun a randa Dada ta tabbatar min Mawaddat na'a wajenta na ƙara tsananta bibiyar Sulaiman. Saboda na tabbatar duk inda Dada zata kaita sai da gudumawarsa. Nace maka na tafi Hong Kong ne kawai dan na ɓatar da kowa a lissafi, da ga can na bibiyi Sulaiman ƙafa ya ƙafa har zuwa ƙasar Canada da ya nufa shi da ɗansa. Ban wani sha wahala na a bibiyar tashi ba na gano inda Mawaddat take. Sai dai ban zauna ba na kamo hanya na dawo, tare da jin ƙarfin gwiwar barinta cikin ƙudirar UBANGIJINA. Sai dai na saka wani yaro Usman ɗan Alhaji Bashir Sa'eed dake Canada cigaba da bibiyar min al'amarin su dama na gidan gaba ɗaya. A bakinsa naji Mawaddat na ɗauke da ciki, har ma da kaita asibiti da sukai domin yunƙurin zubar da shi, da ceto cikin da yay har zuwa yau........” kaf ya kwashe komai da ya sanar masa. A abin mamaki sai ga hawaye share-share Uncle Yousuf na sake zubarwa. Daddy ya cigaba da faɗin, “Ina kan sani na barta can a wajen nasu duk da nasan Sulaiman zai iya cuta mata, sai dai kasancewar Usman na sanar min duk wani motsinsu ya sani sake samun ƙwarin gwiwa. Nasan hakan shine kawai zai sake koyama Mawaddat sabuwar rayuwa ta fahimci mi ake nufi da gundarin rayuwar ma kai tsaye. Ta kuma san wanene Sulaiman ta yanda duk sanda za taji komai game da shi abin bazai zo mata a bazata ba balle harta cutu. Sannan zata sake sanin muhimmancin mijin da darajarsa tare damu family nata gaba ɗaya. dan a yanzu haka Dada ta sanar mata mijinta ya saketa”.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣



.........Ji Uncle Yousuf keyi kamar yay ta kuka, ga wani jin zafi da takaicin Dada da Alh. Sulaiman na cimasa zuciya. Sai sake kallo Jaririn yake a hotuna harda ɗan gajeren vedion. Uncle Yousuf ya rungume Daddy jikinsa na tsuma. Babu wanda ransa ke hango masa kamar Smart a yayinda zaiji wannan labari mai cike da al'ajabi da mamaki. Dan koda Dada ta sanar musu samuwar ciki da kasancewarsa basu faɗa masa ba saboda yana kan gaɓar da kwanciyar hankali yafi buƙata, ga shi su kuma ba sanin inda zasu samo Lulun sukai ba a lokacin balle su ƙarfafa shi.
      “Yaya yanzu yaushe zata dawo gida? Dan tana buƙatar kulawa a yanzu sosai”.
     “Ya sake kwashe musu passport ɗinsu ne shiyyasa, amma ina kan ƙoƙarina na son ganin an dai daita musu komai sun baro ƙasar. Sai dai ba Nigeria nake so ta dawo ba, dan ina son nai amfani da wannan damar ne wajen ɗaure Sulaiman da jijiyoyin kansa sannan na ɓata abinda na gyara akan Mawaddat.”
               “Wannan tunani ne mai ƙyau Yaya, inaga kawai ta wuce wajen mijinta to”.
         “Zan so hakan Yousuf, sai dai zai iya zama matsala. A yanzu yaron yana a wata gaɓa ne da kowa zai iya kai masa hari ya kumayi tasiri a kansa cikin sauƙi. Bai kamata mu bada gudunmawar maida shi baya ba bayan al'amura sun ɗakko hanyar warware wa. Su Sulaiman shu'umai ne ta yanda komai zasu iya aikatawa. Sannan suna huɗɗa da manyan ƴan iskan duniya a fagen cinikayyar kayan shaye-shaye. Wannan babbar dama ce a hannunsu da akowane ƙasa mutum yake, ko wane irin matsayi ya taka zasu iya ƙulla masa. Abinda kawai ya dace muyi yanzu shine mu rufe bakunan mu ruf zuwa wani lokaci, amma mahaifinsa da mahaifiyarsa su san da wannan haihuwar. Shima kuma na aika a sanar masa yanzu hakan. Daga iya mu huɗun nan kar kowa yasan inda Mawaddat take Please”.
        “Na fahimceka ƙwarai da gaske Yaya. Kuma insha ALLAHU a yanzu bakai kaɗaine zakai wannan aikin ba. Ni da kai ne zamuyisa dan na fara ji a jikina Sukailan ne ya koyama Mawaddat shaye-shaye”.
     Sosai Daddy yaji daɗi da farin ciki, duk da yana tsoron kar a cutar masa da ɗan ƙanin nasa ɗaya tilo kuma. Amma ya bar komai a hannun UBANGIJI, sannan idanunsa a buɗe suke a yanzu kam kowane irin ƙalu bale ya shirya masa. Zancen Alh. Sulaiman ne ya koyama Lulu shaye-shaye kuma shima kansa yana wannan tunanin, a yanzu haka kuma yana kan bincike ne sosai har ma da yanda akai Nanny ɗin Lulun ta mutu duk zuciyarsa na masa zargin Sulaiman. sai dai a yanzu bai cema Uncle Yousuf ɗin komai akan hakan ba....

        *_CANADA_*

    Sosai Alhaji Sulaiman da ya iso Canada yau ɗin nan ke a cikin tashin hankali. Dan duk iya bincikensa yayi amma babu Usman babu su Lulu. Har asibitin da aka kaima Lulun cs yaje sai suka ce masa su basuyi wata theatre wa mai sunan ba. Neman haukace musu yayi, daga ƙarshe akasa security fiddashi tare da warning ɗinsa mai ƙarfi na in ya sake dawowa yay musu hayaniya zasu saka jami'an tsaro kamashi. Baya haɗa sabga da jami'an tsaro ko'a Nigeria, dan kun san mai kaza a aljihu baya jimirin ass. Balle ya samu labarin mahaifinsa ya saka a bincika a nemo inda yake tun kusan wata uku da suka wuce. Shiyyasa ma yaƙi zama waje guda yaƙi kuma shiga Nigeria kwata-kwata duk da labarin da ya samu har na sakin mahaifiyarsa Dada da Baba Garkon yayi. Yana tsaka da kasancewa a haukacensan saƙo ya iso masa. A birkice ya saka hannu a littafin ɗan saƙon, tun kafin ya koma cikin gida ya buɗe, inda ya fara cin karo da hotunan ƙyaƙyƙyawan jariri har kala uku. Hoton ƙarshe da ke ɗauke da rubutu ya juya cikin tsumar jiki. *_Zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi. Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi ya iso duniya lafiya_*
      “What!!” Ya faɗa cikin bugawar ƙirji da rawar hannu. Sai kawai ya saki wani irin ihu mai ƙaraji tare da yin watsi da hotunan. “Usmaann!!” ya sake ambata da ƙarfi. Sai kuma ya ƙyalƙyale da wata irin dariya mai ƙona zuciya, tare da faɗin, “Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Ka taro babban match ɗin da kaf family naka basu isa zamar maka defenders ba. Sai na tarwatsa rayuwarka ta inda zaka dawwama dana sanin yaudara ta da ka shirya yi. Yarinyar kuma da hannunka zaka maidota gareni”. Da ga haka ya fisgi rigar sanyinsa da ke a hanger ya fice gidan.....

       
  *_NIGERIA_*
   
    Tun randa taji Smart baya Nigeria ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko kaɗan zuciyarta da gangar jikinta sun gagara hutawa. Ba ita kaɗai ba, hatta ƴaƴanta ta cusa musu hassada da ƙyashin da ya ingizasu fara bibiyar al'amuran Smart har suka gano irin cigaban da yake samu a yanzu haka, duk da dai a farko dariya suka fara da ganin Smart ɗin ai a ƙaramin team yake ma. Sai dai kuma a hakan ma dai UBANGIJI sake bayyana shi yake ga duniya a bisa kowane matakin nasara koda akwai ƙalubale a cikinsa. Abu na biyu yanda Abba ya fara jiƙewa a ƙanƙanin lokaci, dan bai iya ɓoye alkairin da Smart ɗin ke turo masa. Duk da ba wasu maƙudan kuɗi bane na tashin hankali, sai dai suna riƙesa ta yanda a yanzu haka baima fita kasuwa sai yaran. Duk da aikin da Malam Na-zuru ya sake mata a kan Smart ɗin hankalinta ya kasa kwanciyar jiran nashin kaɗai. Tuni sun bazama ga wasu malaman harma da bokayan babu inda Hajiya Naqiba bata zuwar mata. Wani lokacin kuma suje tare ma.
        Ammah ce ta fara fuskantar al'amarin na Umma a randa ta kamata tana bizne abu a bayan windown ta ga sunan Smart tana kira. Hankalin Ammah ya tashi matuƙa a wannan ranar, amma bata yarda Umma ta ganta ba harta kammala. Bayan barinta wajen tai kiran ƙanwarta Gwaggo Sa'adah ta sanar mata komai cikin tashin hankali. Gwaggo Sa'adah ta kwantar mata da hankali akan tana zuwa, sai dai karsu taɓa abinda Umman ta bizne tunda akwai jinin Smart a jikinsu. Gwaggo Sa'adah ce tazo da wani almajirinta, inda cikin hikima ya tone abinda Umman ta bizne ɗin. Layune da wasu sirkulle a kwalba an ɗaure. Koda aka kunce layun abinda ke rubuce a ciki su dukansu ya daga hankalinsu. Amma sai almajirin nan ya ce su kwanatat da hankalinsu addu'a tafi gaban komai ai. In sha ALLAH tunda an farga da wuri babu abinda zai faru, zai je da su ya lalata. Gwaggo Sa'adah taso a ajiye a nunama Abban. Amma sai Ammah tace a'a a ƙyaleta a rufa mata asiri idan halintane zata ƙara ai har Abban ya gani da kansa wataran. Har Gwaggo Sa'adah taji haushi sai kuma da ga baya ta fahimci hikimar Ammah.

      Tunda ga faruwar wannan al'amari Ammah ta sake dagewa da addu'a akan ƴaƴanta gaba ɗaya. Tare da sadaka akoda yaushe. Duk inda taga maraya tana ƙoƙarin taimaka masa. Suma yaran kullum cikin ƙara ƙarafafasu take da ibada har Smart. A duk sanda sukai waya sai ta sake nusar da shi. Alhmdllh yana fahimtar ta sosai, kuma dama baya sakaci akan ibadarsa duk da wataran gajiya kan hanashi iya tashi sallar daren daya sabama kansa yanzu. Amma a koda yaushe bakinsa bai rabo da ambaton ALLAH.

     Yau ma kamar kullum gidan yana ruɗe da hayaniyar yara da jikoki kasancewar juma'a ce ta ƙarshen wata. Dan an sakko massalacin kenan sai ga Abdull ya shigo yana sanarma Ammah Abbah yace a bada ruwa anyi baƙi. Kasancewar itace da girki babu wanda ya damu. Ta haɗa ruwa harda zoɓon da Maryam tayi domin zuwan Ahmad ɗinta kasancewar duk juma'a yake zuwa hira bayan sallar la'asar (Kun san fa Ahmad da Maryam an jone🥱). Har Abdull zai wuce Ammah ta sake dakatar da shi, dan tunda taga Abbah ya aiko a amshi ruwa da alama baƙin masu muhimmanci ne. Masar da tayi matsayin abincin rana ta zuba ta ce Asma'u ta ɗauka ta bisa da shi.
         Sosai Uncle Yousuf ya tsirama Asma'u da ta kai har ƙasa tana gaishesu idanu, dan sosai tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login