Showing 30001 words to 33000 words out of 127646 words
𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣
.......Tun a randa suka fara fitowa Lulu ta fahimci zagaye suke da idon yaran Alh. Sulaiman, amma maimakon ta razana sai ma tayi murmushi. Batace da tacema Ummita komai ba akan hakan, sai ma zunguran Ummita data shigayi game da sanin wacece ita? Da yanda akayi ta yarda ta biyosu Canada. Tuni hawaye suka cika idon Ummita. Bata hanasu zuba ba sannan bata sharesu ba, sai da ta jiƙe gaban rigarta sosai kafin cikin shashshekar kuka ta ce, “Sunana na yanka Fatima. Naci sunan kakata ne shiyyasa ake kirana Ummita. Asalinmu ƴan wani garine ɓagwai a ƙauyen bichi. Anan nai karatun primary ɗina, da ga baya aka kaini boarding school a wata makaranta da ake kira GGASS Ɗan/zabuwa. Naje har js 3 aka cireni na koma cikin garin Kano hannun yayata da ke aure acan sakamakon rashin lafiya data kwanta. Jeka ka dawo na koma zuwa ina kula da yayata a gidan mijinta tsahon shekara biyu harta fara samun lafiya. Tun ban wuce shekara ɗaya a gidan ba mijin yayata ke nunamin wasu abubuwan rashin ɗa'a, sai dai bana kulashi sai da naga abin na neman wuce gona da iri na nuna inason komawa gida dan ban son faɗama yayata na tayar mata da hankali. Amma sai iyayenmu sukaƙi yarda yayar tawa ma harda kukanta, acewarta idan na tafi wazai ringa kulawa da ita da ƴaƴanta biyu kamar ni. Tausayinta ya kamani sosai, dan haka na haƙura na zauna, sai dai na ɗauki matakan kare kaina tako ina har takai mijin nata shima ya daina shiga sabgata ya kama kansa. Ashe lumbu-lumbu yay min, dan sai da ya bari na shagala sannan a wani dare ina gab da kammala ss3 ya bankama yayar tawa maganin barci ya keta mun mutuncina. Maganin daya banka mata yay sanadin barinta duniya, na shiga tashin hankali irin wanda baida misali, sai dai na gagara faɗama kowa asalin al'amarin har akai sadakan uku. Ina murna zan koma gida sai babana yace na zauna tare da gwaggonmu mu kula da yaran harna ƙarasa jarabawar neco da waec da zamu fara. Naso tada hankalina amma akaita tausata, ganin akwai gwaggonmu ya sani jin zan daure ɗin. Mun fara jarabawa ina a cikin yanayin rashin jin daɗin jikina. Haka dai naita daurewa yayinda iyayenmu a bayan fage batare da sanina ba suke shirye-shiryen aurar da ni wa mijin yayata matsayin madadi waina riƙe yaranta. Da farko ya yarda sai dai a randa muka gama jarabawar ƙarshe na kaita a wahalce, tun daga makaranta aka wuce dani asibiti, inda a gwajin farko aka sanarma gwaggona da tazo inada shigar cikin wata biyu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, babu bin ba'asi babana ya hau dukana Sakamakon zugar da mijin yayata yay masa akan dama ance ina yawon banza ai, baya son ya faɗa ne ace dan karya auranne yake son zamewa. Iya jijjiga kamalamansa sun jijjigani, yayinda ɓacin rai ya saka baba rantsewa bazan zauna masa a gida ba. Hankalin mahaifiyata ya tashi, amma sanin halin mahaifinmu ya hanata cewa komai, sai shawarar turani Abuja data yanke wajen ƙaninta. Matar ƙanin mamana na samu damar warwarewa komai da ya faru, ranta ya ɓaci matuƙa ita da ƙanin mamana, dan haka suka ɗaukeni muka juya Kano suka shigar da ƙara kotu tare da neman lawyer daya san aikinsa sai aka haɗamu da ke. A lokacin baki jima da dawowa Nigeria ba kamar yanda naji ance, dan hausanki ma ba wani sosai yake fita ba. Kin taka rawar gani a rayuwata ta hanyar tabbatarma mijin yayana MACE MUTUM ce (Rahma Abdull-majeed. Wanda bai karanta littafin nan ba wlhy anyi bashi🥱). Dan sai da kika turashi gidan yari har yanzu kuma yana can. Uncle ɗina bai saurari iyayena ba da suka shiga nadama sosai ya ɗakkoni muka sake dawowa Abuja. Inda ya nema min makaranta na fara. Ga rainon ciki inayi, cikin danai matuƙar tsana a rayuwata har ALLAH ya kaini ranar haihuwa. Sai dai alhmdllh jariri baizo da rai ba. Hakanne ya sani farin ciki na maida hankali a karatuna. Bana zuwa gida saboda gudun zunɗen mutanen ƙauye harna kammala karatu na na samu result mai ƙyau, ina cikin neman aiki ne sai ga Hajiya Shuwa a gidan mu kasancewar tana huɗɗa da aunty na, tana kawo mata turaren wuta. Jin ina neman aikin taimin tayin wannan aikin, sai dai tace aikin na shekara ɗaya ne kacal shiyyasa kawuna ya amince da sauri, ni dai bance komai ba dan banjin zanje ɗin, sai a randa na ganki matsayin wadda za'aima aikinne ya sani yarda da sauri-sauri domin rama alkairi da kikai min nima....”
Tuni hawaye sun jiƙe fuskar Lulu, jik 10inta har wani tsuma yake kamar wadda ake kaɗama gangi. Lura da hakan ne yasa Ummita kamata suka koma ciki batare da ma lokacin da aka basun ya cika ba.....
_________★
A ɓangaren Dada tun a washe garin da Alh. Sulaiman yasa aka canjama su Lulu wajen zama yay kiranta cikin tashin hankali da makirci yake sanar mata baiga su Lulu ba, yazo gida ya samu sun gudu. Yasa ƴan sanda nemansu da ga baya suka fahimci sun bar ƙasar ne da taimakon wani dan har note aka bar masa. Hankalin Dada yay masifar tashi har takai ta kasa controlling kanta Baba Garko ya fahimta. Tambaya ya shiga jera mata wadda ta kaita da gaya masa cewar Lulu ta gudu da ga Canada, kuma suna zargin wani ne ya sace ta. Cikin matuƙar mamaki Baba Garko ya ce, “Canada kuma Hajarah, miya kai Mawaddat Canada ko ita da mijin nata ne?”. Wannan kalma ta Baba ce ta dawo da Dada a hayyacinta. Duk kuma sai ta daburce ta rasa abin cewa har takai Baba Garko ya daka mata tsawa, tasan halinsa baya ɗaukar raini, idan ya juye mata takan rasa gane kansa, kafin yay hakanne akan jima shiyyasa take samun damar iskancinta. Waya ya ɗauka ganin bazata bashi gamsashiyar amsar da yake buƙata ba yay kiran Daddy. Sai dai wayarsa taƙi shiga, yasan hakan nada nasaba ne da yanayin network. Ganin zancen waya ma bazai bashi yanda yake buƙata ba a ranar ya saka autansa namiji da tunda yazo da iyalinsa bai koma Saudiyya inda yake aiki ba ya yanka musu ticket, dan yace yau bazai sake kwana a ko'ina ba sai a Nigeria, saboda ya fahim al'amarin babba ne. Hankalin Dada ya sake tashi, amma tasan a wannan gaɓar bata isa yi masa wani daɗin baki ya dakata ba, dole ta shirya suka wuce a tare.
Sunma Nigeria ƙasar haihuwarsu saukar dare, hakan sai ya sirranta dawowar tasu suka samu damar isa gida cikin kwanciyar hankali. Kowa ka gani a gidan Baba Garko ma'aikata cikin farin ciki yake da samun lafiyar tsohon abin son kowa. Mai tausayi da son ƙyautata rayuwar na ƙasa da shi, mai jan ɗan aiki jikinsa tamkar ɗan uwa ba bawa ba. Bayan albashinsu da ba'a taɓa tauyewa ba a koda yaushe cikin musu alkairin yake. Ko Zakka ya fitar sukan samu kaso mafi tsoka duk da Dada bata son hakan. Sannan duk abinda ya samu iyalansu ko lafiyar jikinsu yakance su sanar masa dan shine da hakkin wannan. Wannan yasa su jin ƙaunarshi da shiga a tashin hankali a duk lokacin da suka ga yana a cikin damuwa ko farin ciki. Sam hankalin Dada baya a jikinta, suna isowa sashenta ta wuce, layinta na Nigeria ta ɗora a waya sai dai kafin ya gama dai-daita duk ta ƙosa, hakan ya sata amsar wayar mai aikinta domin kiran Daddy. Amma abin mamaki sai ta samu number busy, bata kawo a ranta da mijinta Daddy ɗin ke kiran ba, dan haka ta cigaba da jera masa kira. Shiko Daddy dake waya da Baba Garko ganin baƙuwar lamba ce yasa koda ya kammala bai ɗaga ba, ganin ma za'a damesa ya sashi saka wayar a airplane mode kawai. Haukane kawai Dada batayi ba a wannan dare jin daga baya ma ta daina samun Daddy ɗin. Karo na farko da taji takaicin rashin riƙe number kowa na jikinsa da ga shi sai Lulu. Dan ko Yousuf ita bata da lambarsa. Matarsa kuwa (Mommy) dama ba huɗɗa take da su ba. Barcin kirki dai Dada bata sameshi a wannan daren ba sam. Tana sallame sallar asuba sai kuma ta fara jerama Daddy kira, sai dai har lokacin wayar bata shiga. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kuma kasa zuwa inda Baba Garko yake. Dan gani take kamar yana riga ya gama jin komai da komai. Tayi kiran Sulaiman kuma shima wayarsa bata shiga ba sam...
A ɓangaren Baba Garko ya gama fahimtar akwai matsala, sannan koma minene akwai saka hannun matar tasa a ciki. Yay kiran Daddy kuma dan yaji gaskiyar zance game da zuwan Lulu Canada sai ya samu numbersa busy. Akan Uncle Yousuf ya maida akalar kiran nashi, inda yaji komai da komai, yana gama wayar da Uncle Yousuf ɗin ne kuma kiran Daddy ya shigo masa. Maimakon ya tambayesa kamar yanda ya tambayi Uncle Yousuf sai ya canja kawai suka gaisa ya sanar masa yazo Nigeria, yana son da safe ya samesa a gida da wuri. Daddy yayi farin cikin jin Baba ya samu lafiya, sai dai ya shiga mamakin jin kiran gaggawa da yake masa. Wanda yasan koda bai kirashi ba tunda yaji ya dawo ƙasar da safen dole zaije gidan duba shi.
Zuwa ƙarfe bakwai da rabi duk wanda Baba Garko ya buƙaci gani a gidan nasa ya iso. Dan harda ƴaƴansu ƙannen Alh. Sulaiman ɗin. Uncle Khamil da auta da suke kira Uncle Sadiq ne kawai babu dan shi sun barosa acan, sai kuma Alh. Sulaiman da shima dai fushin da Baba keyi da shi yasa bai saka shi a cikin meeting ɗin gaggawar ba. Sosai kowa ke cikin farin ciki da ganin yanda mahaifin nasu ya samu lafiya kamar bashi ba. Zamansu babu jimawa ƴan sandan dake bincike akan case ɗin sa suka iso gidan. Ya ce suyi haƙuri suje zuwa anjima zai nemesu yanzu yanada muhimmin uziri ne da iyalansa.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣
______________
*3 DAYS CLASS*
Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni
Class ze fara ranar jumaa insha Allah
WhatsApp group 👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA
WhatsApp 08144147273
_________________
........Bayan anyi gaishe-gaishe da taya juna murnar samun lafiyar Baban kai tsaye ya jehoma Uncle Yousuf tambaya kamar jiya. Uncle Yousuf da tunda suka shigo bai kalli inda Daddy yake ba, ko gaisuwa sama-sama yay masa kansa tsaye ya fayyace komai kamar yanda ya faɗama Baba Garkon a dare jiya. Jikin Dada tuni ya jiƙe da zufa, amma tsabar makirci sai ta fashe da kuka wai Uncle Yousuf ɗin ya haɗa mata harda sheri dan ya baƙantata kawai. Ita koda ta ɗakko Lulu dan bata da lafiya ne ta ɗakkota.....” tsawa Baba Garko ya daka mata da cewar, “Yima mutane shiru mutuniyar banza da kullum bata sanin ta girma a rayuwarta. Bance miki ki fita cikin al'amarin auren yaran nan ba tun farko? Rashin lafiya shi mijin nata ne yay dake bazai iya kula da ita ba? Ko kin fishi sanin abinda ya dace yayi akan iyalinsa?!.”.
“Ka gaya min. Kuma ni naga shi ba wani kuɗin da zai iya kulane da ita ga resa ba”.
“Mtsoww zancen banza kenan. To raini ne da son tozarta ni da nunama duniya ban isa ba ya saki zuwa ki ɗakko yarinya a ɗakin mijinta har ki kaita wata ƙasa?”.
“Bafa haka bane sam Alhaji ka fahimceni, yarinyarfa da bakinta ta fayyace min gaskiyar manufar auren .......” nanta ta kwashe komai da komai da Lulu ta sanar mata ta faɗa musu. Karo na farko Uncle Yousuf yay murmushi, yayinda Uncle Muneer ɗanta dake bima Alh. Sulaiman cikin son danne ɓacin ransa da taushin murya kamar yanda ya saba girmamata matsayin mahaifiya ya ce, “Amma Dada duk da a ta gaya miki haka a matsayinmu na wanda muka fita hankali nazata zamu taimaka mata ne ta hanyar kwantar mata da hankali ta haƙura ta zauna a ɗakin mijinta dan yaron nan mutumin kirki ne da duk wasu iyaye na ƙwarai zasu so haɗa zuri'a da shi”.
Harara Dada ta ɓalla masa, yayinda Baba garko ya amshe da “A'a ina zatayi haka ga matar ƙaruna ƴar ƙaruna kuma da hankali bai gama game mata jini ba, ai Mawaddat ɗin ma ta fiki hankali. Wai Hajarah mi kika ɗauki rayuwa ne? Mi kika ɗauki dukiya ne? A zatonki dan ALLAH ya yomu a haka mun zama mafifitane a cikin mutane har a wajensa? Kamar yanda talauci yake jarabawa itama dukiyar da kike gani jarabawace. A wani fanin ma babbar fitina ce ga bawa. Shekara nawa ya rage miki a wannan duniyar da har kike jin wai dukiya har zata cigaba da zame miki abin tinƙaho. Ba tonon silili ba naga ai kema ɗiyar talakawance amma na aure ki, ƙarewa ma mahaifinki masinja yake ga mahaifina mutuncinsa da sanin Yakamata yasa mahaifina cewa na auri ƴarsa. Ban yi musu ba kuma na aureki nake zaune da ke har tsawon shekarun nan matsayin ke kaɗai matata Ashe albasa batai halin ruwa ba....”
Sosai Dada ta daburce dajin kalaman mijin nata irin wanda koda kwatance bai taɓa yinsu gareta ba tun aurensu. Su kansu yaran sai da sukaji shock su dukansu. Dan basu taɓa sanin wannan tarihin ba kasancewar a sanin da sukaima mahaifin mahaifiyar tasu hannunsa a jiƙe yake, sosai Baba kema Dada cin mutunci da ya sakata kuka rurus, agaban ƴaƴan nata ya kuma turketa saita gaya masa inda suka kai Lulu koya bata mamaki da hukuncin da bata taɓa zato ba. Ganinfa ruwa ya ƙarema ɗan kada dole Dada ta fayyace komai game da kai Lulu Canada ita da Alh. Sulaiman harma da yunƙurin zubar mata da ciki da sukayi amma bai fitaba sai da ga bayan nan kuma suka gane hakan, sai kuma kiran da Sulaiman yay mata a jiya cewar ya nema su Lulu ya rasa wai wani ya sacesu, amma yasa ƴan sanda na bincike. A yau da safe kuma yake turo mata text message akan yana zargin Yousuf ne da Smart. Da matuƙar mamaki Uncle Yousuf ke kallonta cikin nuna kansa ya ce, “Ni Yousuf ɗin ko wa?”.
“Inba kaiba waye Yousuf anan, munafuki algungumi. Ai dama kana biye damu tunda muka ɗauke ta kai da shegen yaron nan mara kunya dan bakinku ɗaya ne dama. Dan haka saiku fito da ita tunda ankai ga yanda kake so”.
Tuni fa falo ya hargitse, dan sai kawuna kuma suka nema rabuwa. Yayinda Daddy da tunda ya shigo falon baice komai ba ya zuba musu ido kawai. Hakama Baba Garko. Cikin ɓacin ran yin shirun Daddy Uncle Yousuf ya tashi ya fice a falon dan zuciyar ƴan maza ta motsa da gaske a yau. Ganin bazasuyi shiru ba Baba Garko ya katse hayaniyar tasu da faɗin, “Hajarah kije na sakeki saki biyu, kuma ki barmin gidana a yau har sai kun maido Mawaddat idan da yiwuwar ki dawo sai ki dawo”.
Waɗan nan kalmomi masu dukan zukata na Baba Garko ne suka saka falon yin tsitt, yayinda ya miƙe abinda ya shige cikin bedroom ko waiwayen su bai yi ba. Dada kam da taji kanta na juya mata sai ganinta kawai sukai a ƙasa babu numfashi. Cikin tashin hankali sukai kanta. Duk hayaniyar da ake Baba na jinsu amma har suka kwasheta zuwa asibiti bai ki leƙo ba.
Wannan shine sanadin kwanciya Dada a asibiti na tsawon sati biyu tana jiyya, dan hawan jininta ne yay masifar motsawa. Koda ta samu sauƙi kuma Baba yace duk wanda ya kawo masa ita gida a cikin ƴaƴan nasa wlhy sai ya kwashe masa albarka. Duk kuma wanda yazo yay masa maganarta a gidan nan ma sai ya kwashe masa albarka. Wannan ya saka yaran tsorata matuƙa dan sun san wanene mahaifin nasu akan zuciya, balle yanzu ya sake birkice musu irin yanda basu taɓa gani ba. Gashi sunata kiran Alh. Sulaiman dake matsayin babba garesu kuma silar wannan tashin hankali amma sam sun gagara samunsa. Dole dai aka wuce da Dada gidan Uncle Muneer aka gyara mata sashen baƙi....
*_CANADA_*
Labarin Ummita da Lulu taji ya ƙara musu shaƙuwa matuƙa, yayinda Lulu ta fara tunanin buɗe ƙungiya domin taimakon yara marasa zuwa makaranta dan al'amarin yaron nan data taɓa amsar Number a wajensa bisa titi har yanzu yana ranta bata manta ba, tana jin babu daɗi kuma da bata sami ziyartarsa ba. Ƙungiyar zata riƙe abubuwa uku ne. Karatun yara da rashin galihu ya hanasu yi, sai harkar fyaɗe da kuma shaye-shaye. Ɗari bisa ɗari Ummita ta bama Lulu goyen baya game da wannan ƙyaƙyƙyawan ƙudiri nata. Dan haka suka hau tsare-tsaren su kamar waɗanda akacema gobe zasu bar wannan wajen. Lulu ta cigaba da rainon ciki yayinda Usman ke zuwa dubata da bata magungunan ƙarin lafiya ita da abinda ke cikinta. Alh. Sulaiman kuwa na tunanin allurar gubar da zata ruɓar da tayin cikin Usman