Showing 81001 words to 84000 words out of 127646 words

Chapter 28 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

275

rayuwar ƙuruciyarta ko firar kishiya bata so, kai ko ƙawa ko cikin ƴan uwa akaima wata kishiya daina zuwa gidan mutum take saboda yanda ta tsani kishiya. Amma a yau sai gata da ita a wannan shekarun nata, harma da ciki na haihuwa.....

       (🤣🤣🤣🤣🤣 Kar kuce dariyar mugunta nakema Dadaras😜)

         ____________★

     Tun Ummah na ɗaukar al'amarin ta ƙarami harta fahimci ya wuce da saninta. Kuka ma da hawaye yanzu ta kasa yinsa. Ƴan gidansu sunzo sai dai me suma ƙarewa sukai da fita da gudu harda masu faɗuwa. Wajen Abba suka koma kowa na maida numfashi, yayanta cikin damuwa ya ce, “Anya ba aljanune suka shigi Yahanasu ba Yaya Mika'il”.
    Cikin ɗan taɓe baki Abba yace, “Idan ma sune wajen biɗar baƙar tambayarta ta kwaso su. Ballema bana jin hakanne. Nafi ƙyautata zaton ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Ni yanzu jibirin ban san yanda zanyi da wannan matar ba. Gaba ɗaya ta firgitamin iyali sun kasa sakewa kowa sai zaman ɗaki”.
      Cikin damuwa Jibirin yace, “Amma yaya bai kamata kace haka ba. Ƙilama cikin matanka wata taimata haka kasan dai mata akan kishi”.
    “Wane matan nawa? A'a ƙarya haramun. Ai duk cikin iyalina babu fanɗararre irin Yaha. Nasan halin kowacce a cikinsu da abinda zata iya. Na jima ina zarginta dama da shigen-shigen nan kawai dai ban taɓa gani da idona bane shiyyasa ban kafa hujja ba. Amma a yanzu na gama fahimtar komai. Ko wannan halin da kaga tana cikin sihirin da taima Aliyu da matarsa ne ya dawo mata...”
           “Aliyu kuma Yaya? Aliyu Aliyu dai namu na nan?”.
       “Shi ɗin fa”.
   “Ikon ALLAH! To shi Aliyu dake matsayin ɗanta kuma zatama asiri. Miye ribarta kenan?”.
             “Oho mata, ita ta sani”.
        Sosai al'amarin ya girmi kan kowa. Cikin ƙarfin hali Zaidu ya bada shawaran to ko za'a samo malamai suyi addu'a ne. Dan wannan yanayin nata abin tashin hankali ne ga kowa tunda gashi hankalin kowa a tashe, shi wlhy yanzu haka baya jin yau ɗin nan zai iya barci lafiya saboda ganin wannan mummunar halitta da Ummah ta koma. Abba dai yace shi babu ko sisinsa a nema mata lafiya. Hasalima ya kirasu ne su wuce da ita dan bazai iya ba. Hankalinsu ya tashi matuƙa, dan sukam bazasu jajibi wannan halittar ba sukai cikin iyalinsu suna zaune ƙalau. Dan haka suka dage bashi haƙuri da roƙo da magiyar ya barta a ɗakinta cikin ƴaƴanta harta samu lafiya sai aji dalilinta na wannan mummunan al'amari, idan ma matakin sai ɗauka sai ya ɗauka. Anfi ƙarfin Abba ne kawai, dan haka yay shiru. Su suka fita suka zo da malamai, da ga tsakar gida suka tsaya aka kwala mata kira ta fito. Su kansu malaman sai da suka zabura da ganin mummunar halittar dake tunkarasu, ganin tana yo kansu gadan-gadan sukaji fa dauriya ba tasu bace. Ai tuni suka dafe kawuna kowa ya ara cikin ta kare yana jan kula'uzai. Bayan su an sake kawo wasu malaman amma fa kowa yazo yana tozali da Umma sai dai a tsincesa waje ya dafe ƙeya. Al'amari kamar wasa sai ƙara faɗi yake. Dan takai ƴan jarida daga gidajen rediyo har sun fara zuwa neman labari. Sai dai suma fa suna shigowa sukai ido huɗu da Umma labarin bai ɗaukuwa garesu sai ƴar reren gudu...
      Tsabar tashin hankali da hawan jini Umma ta koma ko gani batayi da ƙyau. Barci kuwa ya ƙauracema idanunta gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai wata irin muguwar rama mai ban tsoro. Babu abinda ke ɗaga mata hankali sai ganin ƴaƴanta suma gudunta suke da mijinta da ta ɓata tsahon shekarun rayuwarta tana faɗa da faɗi tashi a kansa. tana son jin halin da Hajiya Naqiba take amma babu hali. Rayuwa ta mata duhu, duhu irin wanda ko tafin hannunka baka iya gani, duhu irin wanda zuciya kanta bata iya tuna komai sai ƙunci da ciwo mai raɗaɗi. Hatta salla yinta kawai take amma bata ma sanin mitake yi a cikinta. wanka kam bama'a maganarsa dan tashin hankali. abinci dama yanzu ƙofar ɗaki Abba ke zuwa ya ajiye mata saboda kowa tsoro yake ji, shi kansa dai tausayin rai ne ke sakashi yin ƙarfin halin ajiyewar kawai dan an hanata fitowa.....

        *_★UK★_*

    Sosai tasha barci, dan ko da lokacin salla yayi da ƙyar ya iya tashinta tayi ta sake komawa. Bata tashi ba sai gab da la'asar. Yana falo suna kicimilli da ɗansa ta fito. Tsaye kawai tai tana kallonsu har bata san tana murmushi ba. Mayataccen ƙamshinta ya fargar da Smart kasancewarta a wajen. Zaune ya tashi da ga kwancen da yake yana ɗaga AA dake sukuwa a saman cikinsa. Cikin lumshe ido da sakar mata murmushi ya ce, “Kin tashi?”. Cikin falon ta ƙarasa takowa tana marairaice fuska. Hannunsa ya miƙa mata alamar tazo garesa. Babu musu ta ƙaraso, ya riƙo hannunta ya zaunar gefensa yana mai rungumota ta gefen jikinsa kanta a saman kafaɗarsa. AA dake neman haye mata jiki ta dungurema kai batare da tayi magana ba. Smart dake kallonsu da murmushi ya shafo fuskarta da faɗin, “Yaya jikin naki?”.
       “Ba sauƙi”.
    Ta bashi amsa cikin tura baki.
Sosai ya waro idanunsa waje. “Ba sauƙi fa Nooru Nisa”.
      Fuska a gimtse ta ce, “Eh mana dan ni dai jikina ciwo yake mun har yanzu”.
     “Kai Madam bansan ragwantaka fa. Ni da nake shirin yanzu a sake tafiya yaƙin ƙasa da ƙasar again.”
           “Dawa?!”.
      Yanda tace dawa ɗin cikin waro idanu da ƙwaɓe fuska kamar zatayi kuka ya sashi kwashewa da dariya. Mintsini mai zafi ta sakar masa tana miƙewa. Ya riƙe wajen da sauri yana yamutse fuska da faɗin, “Wai ALLAH na! wannan zalincin fa? Kefa kin iya mugunta”.
    Gwalo ta masa tana dariya, ta ce, “Mugayen ai da yawa kai ne malamina”. Tai wucewarta kitchen Dan yunwa takeji.
        “Haka kika ce ko? Ba komai zan rama ne”.
    Dariya ta shige tanayi, babu jimawa ta fito ɗauke da apples data yayyanka a ƙaramin bowl. Ƙasa ta zauna dan taji daɗin miƙe ƙafa. Smart dake binta da kallo ya ce, “Badai wannan ne abincin ba?”.
        Muryarta a marairaice da shagwaɓa ta ce, “ALLAH bakina babu daɗi, ina son naci kozai washe. Sannan wannan ɗin ma ni kam ya isheni”.
     Idanu kawai ya tsira mata yana kallonta. Ta ɗan hararesa da faɗin, “Kallon fa?”. Murmushi yayi da janye idanun nasa cikin yin luuu da su. Sai kuma ya sake zuba mata su cikin yanayin kasala. “Yarinyar nan anya kuwa?”.
             “Anya kuwa mi?”.
        “A'a ni bance komai ba. Kawai dai dama sai nake ga kamar fa wannan karon ma kin amshe ne, kin san fa ni bana saɓa saiti a zahirin fili wasa da na ɓoye”.
     Da farko bata fahimci mi yake nufi ba. Sai da tai ɗan shiru sai kuma ta dago ta hararesa. Dariya ya ƙyalƙyale da shi, zai sake magana ta tura masa Apple ɗin data tsiro a bakin tana sake harararsa. “Kai dai ALLAH ya shiryeka wlhy”.
         Murmushinsa ya cigaba da yi shi dai, koda ya shanye apple ɗin data saka masan sai ya sake matsowa da buɗe baki wai ta ƙara masa. Kafaɗa ta maƙe alamar anƙi ɗin. Ya bata fuska cikin yanayin shagwaɓa. “Kina sha, kina bama AA ni kuma sai a wareni. ALLAH sarki nima da Ammah na kusa da banga haka ba. Bari na kirata na faɗa mata”.
      Da sauri ta fisge wayar ta tura ƙasan ƙafafunta. Sannan ta tsiro apple ɗin ta tura masa abaki tana harararsa. “Mai kwaɗayi, kai yanzu in an barka saika faɗa?”.
         “Sosai kuwa. Harma da Daddy da Abba duk zan kira, ince tunda kika zo baƙya kula da ni.”
     “Sharri Master kenan. Daka kasheni dan ina jin kunyar Abba sosai ALLAH.”
     “Ni kuma baƙya jin kunyata ko?”.
Murmushi tayi tana sakama AA da ke tsaye jikinta yana wasa da gashinta apple ɗin a baki. Cikin basar da zancensa ta ce, “Da kai Daddy ya haɗa baki kuka kawoni nan ko?”.
            Kwance ya kai yana ɗora kansa a saman cinyarta, sai da yay ƴar dariya da tsokano AA ya ce, “Nikam babu ruwana. Daddy ne yay miki wayonsu na manya saboda yana jin tausayina. Shekaranjiya dai muna magana da shi yake cemin akwai saƙo da zai aiko min da shi, idan kuma ya samu shigowa London to, dan zaije Manchester city ne”.
     “Lallai ma Daddy nice saƙon yake nufi ko mi! Sai kace wata kayan wanki”.
   Dariya sosai Smart ke ƙyalƙyalawa har AA na faɗawa jikinsa shima yana tayashi. Sai kawai Lulu ta zuba musu ido tana kallo. Sai da sukai mai isarsu ya jiyo yana kallonta. Ganin yanda ta zuba musu ido ya ɗan ɗage gira da faɗin, “Kallon fa Madam”.
            “To ba dole na kalleku ba naga kun zare. Wai nikam dama kana dariya har haka? Amma da kaita tsuke fuska kamar wanda akaima saƙon mutuwa!”.
     Kansa kawai ya shafa yana murmushi baice mata komai ba. Itama sai ta share ta cigaba da shan Apple ɗin ta. Lokacin-lokaci tana saka masa a baki shi da AA da ke saman jikinsa yana wasa da ƙasumbarsa.......✍️

_🚴Ya kamata mu taya Ummah da Addu'a 🥱🥱🥱_



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣


.......Haka suka cigaba da kasancewa cikin farin ciki da nishaɗi a wannan yini. Sai zuwa wani lokaci yayi kiran Ammah kasancewar su a Nigeria ba daren bane. Sun gaisa sai yake jinta kamar cikin damuwa. Cikin kulawa ya shiga jera mata tambaya. Sai cewa tai babu komai ya haɗata da Mawaddat. Kafin ya bama Lulun ne take tambayarsa babu dai wata damuwa kowa?. Ya ce Alhmdllh yanzu haka ma gasu nan AA ya ishesa da ɓarna. Murmushi Ammah tayi har yana iya jiyo sautinsa. Ta ce, “Ai wannan baban nawa yana ji da ƙarfi da lafiya ne, nima ɗakina ya huta da ɓarnarsa ai yanzu, ga shi nan duk yamun fashe-fashe kala da iri. Dan Babana ne kawai yasa bance a biyani ba”.
      Cikin dariya Smart ya ce, “Ai ba'a shiga tsakaninku da Baban naki kam Ammah. Sai dai nayi mamakin yanda yay girma haka, ashe hoto na rage min girman nasa.”
         “Ai duk kai ya kwaso Hydar. Babu wani abu naka da yaron nan ya bari. Yanzu dai Alhmdllh komai ya zama labari, sai ku sake dagewa da addu'oi dan ita matsalar rayuwa da jarabawa basa ƙarewa. Idan wannan ta wuce watace kuma zata iya kutso kai a kowane irin lokaci. Abinda dai kawai ake buƙata shine bawa ya tsarkake zuciyarsa kada ya nufi kowa da sharri, domin shi ɗan aike ne duk inda ka aikashi sai ya je ya dawo ya tabbatar maka yaje. A zauna da mutane lafiya dan ALLAH, kar a zalunci wani koda da ganganci ne, idan kaima mutum kuskure ka bashi haƙuri ka kuma nema afuwa, sannan ka gyara wannan kuskuren. Ga matarka nan dai ta dawo gareka, sai aji tsoron ALLAH ka sauke hakkokinta da ALLAH ya ɗaura maka, karka zalunceta saboda kana amsa suna Namiji shugaba ita tana mace kai rauni, karka ce akoda yaushe dole kaine a sama da ita, shi aure ƙauna da haƙuri da kawaici ke jagorantarsa yay ƙarko. Sannan shi babba shi aka sani da shanye komai daga na kasa da shi, idan laifi tai maka kayi nazari da bincike kafin yanke hukunci, karka yarda ka yanke hukunci cikin fushi, karka yarda kace zaka zagi iyayyenta a bisa kuskurenta, kada ka aibantata ko hantararta dan kawai ta maka abinda bashi kake so ba. Nasiha da jawowa a jiki shike saka zuciyar waninka maka biyayya komai taurinta, a duk lokacin da ka kasance mai adalci da tattalin rayuwar mace da ƙyautata ma da yin haƙuri da ita ba sai kace ta kiyayeka ba, ita da kanta zata dinga jin shakkar maka laifi ma, bakuma zata taba samun nutsuwa ba idan ta ganka cikin damuwa. A duk kuma sanda tai kuskure ka tsawata mata zata fahimceka fiye da yanda kake buƙata. Ka yabama matarka a duk sanda tai abu mai ƙyau, ko kwalliya ta maka kwarzantata ka nuna mata duk duniya babu ƙyaƙyƙyawa a wajenka sama da ita, idan girki ta maka nuna mata tafi kowa iyawa, babu kuma wani abinci dake maka da ɗi sama da nata. Idan tana magana da kai ka bata hankalinka da ɗaukar kowane furucinta da muhimmanci koda kai a wajenka bamai muhimmanci bane. Ina mai tabbatar maka Aliyu matarka saita maidaka tamkar sarki, zaka zama ɗan lelenta, zaka zama amininta, zaka zama mata ɗan uwa, zaka zamar mata jarumi, zataji babu wanda take so ta birge a duniya sama da kai. Komai iyawar waninka za taga taka itace a sama da kowa. ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka. ALLAH ya kiyaye gaba”
     “Amin ya rabbi Ammah, in sha ALLAHU zaki sameni mai biyayya akan shawaranki da umarninki. Nagode sosai, ALLAH ya ƙara muku lafiya da tsohon rai mai albarka. Ga Mawaddat ɗin dan naga ta ƙagara kamar ta kwace wayar”.  Dariya Ammah tayi, yayinda shi kuma yake mannama Lulu wayar a kunne yana dungure mata kai. Alamar zan rama tai masa tana faɗin, “Ammah na” cikin zumuɗi. Cike da farin ciki itama Ammah da ga can ta amsa mata da “Na'am Mawaddat ɗina. Kun sauka lafiya ko?”.
      “Lafiya lau Ammah ina yini?”.
   Da kulawa Ammah ta amsa mata da tambayarta AA. Tai murmushi kawai batace komai ba dan sosai take jin nauyin Ammah akan al'amarin AA ɗin. Ta rasa miyasa hakan. Saboda ita kaɗai take iyama wannan karan. Garama Mommy itama akan ɗan ɗaga mata ƙafa wasu lokutan. Hira sukayi da Ammah sosai, itama tai mata nasiha tamkar yanda taima Smart, dan tana jinta babu bambanci da ƴaƴanta ne, sosai Lulu taji daɗin shawarwarin Ammah, harda ƴar ƙwallarta. Sun cigaba da hira har takai kunnen Lulu ya jiyo ihu da hayaniya. A tsorace take cema Ammah suwa ke ihu haka?. Rasama mi Ammah zatace mata tayi, shima Smart jin an ambaci ihu ya amshi wayar yasa a hansfree. Cikin ƙarfin hali Ammah ta ce, “Babu komai yara ne ke wasa”.
     Haka kawai Smart yaji bai gamsu ba. Amma sai baice komai ba har sukai sallama. A yanayin damuwa Lulu ta ce, “ALLAH kamar Ammah na cikin damuwa”.
        Kai Smart ya jin jina mata. “Tabbas akwai abinda take ɓoyewa. Kuma tunda kikaga taƙi faɗa mana bamai daɗi bane. Ina zuwa bari na kira Aunty Bilkisu”.
     Wayar ta miƙa masa, yana kira kuwa aka ɗaga. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaya jikin ta. Ta amsa masa cewar da sauƙi. Sai dai jiya mai gidanta yayi maganar cewar wai zai kaita Egypt, “Amma ina zargin dan Abba yay masa maganar cewar kace zanzo wajenka naga likita ne. Dan tunda matarsa ta dawo na kasa gane kansa a gidan nan Aliyu. Ni wlhy zaman nan yama isheni. Hatta yaran nan baya shiga harkarsu, jiya dan Sadiq yay faɗa da yarinyar wajenta bakaga dukan da babban yaronta yay masa ba, wai nayi magana shine yake faɗin banda haƙuri akan yara da kawaici.”
      Sosai ran Smart ya ɓaci, amma sai ya shanye cikin danne zuciyarsa ya shiga bata haƙuri da lallashinta akan karta damu. A yanzu haka ma yana nan yana mata shirin tahowar cikin satin nan Ahmad zai zo ya kaita tayi visa, shi kuma mijin nata ta share batunsa kawai. Yaran kuma ta kaisu wajen Ammah daga can a dinga kaisu makaranta. Taji daɗin shawararsa sosai. Da ga haka take tambayarsa ina Mawaddat. Shekaranjiya abinda ke faruwa a gidan nasu yasata ɗan taƙarƙarawa taje shine Ammah kece mata ai sun komo wajensa. Har take tsogumin basuje musu sallama ba shine Ammah tace ai tafiyar ta shamattace akai babu wanda ya sani..
       “Wani abu ya faru a gidan ne?”.
   “Ammah bata faɗa maka bane? Ai mugun abin waccan azzalumar matar data muku ne ya koma kanta. Dan yanzu bakaga yanda ta koma wata irin mummunar halitta ba wlhy Hydar. Kowa fa bai iya zuwa inda take yanzu gidan nan cika yake da ƴan kallo harda ƴan jarida. Ai Umma taga ƙarshenta”.
          “Ni duk kin sake dilmiyar dani wlhy Aunty. Please kimin dalla-dalla miya faru da Ummahn?”.
      Tsaff aunty Bilkisu ta zayyane masa labarin abinda ya faru tun jiya da Lulu ta taho. Sosai suka girgiza da jin wai Ummah ce ta musu asirin nan, kuma yanzu haka ma kowa ita yake zargi akan abinda ya dinga faruwa da shi lokacin da yake faɗuwa idan ya shiga filin ball. Komai bai iya cewa ba sai ALLAH ya ƙyauta ganin yanda Lulu duk ta ruɗe harda su kuka. Dole yay sallama da aunty Bilkisu ya rungume matarsa a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya. Gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jazur. Ganin yanda Lulun ta tsorata ya sashi ɗan sakin jikinsa shi. Fuskarta dake cikin tafukan hannunsa ya ɗago suna kallon juna. Ya ɗan ɗaga mata gira cike da tsokana. Sai kawai ta sake fashe masa da kuka. Dariya yayi a karo na farko. “Wai anya kuwa keda AA kunada maraba kuwa?. Shagwaɓanki yayi yawa. Yanzu minene abin kuka anan?. Ko kina jin haushin an rabaki da mijinki ne harna wata kusan goma bakiji ɗuminsa ba. To yanzu ba gaki tare da ni ba barci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login