Showing 66001 words to 69000 words out of 127646 words
tace bazata sake ɗagawa ba. Amma da an kira bata iya haƙuri sai ta ɗaga ɗin...
★A gidan su Smart kam nasarori da ƙalibalen suma dai basu tsallake su ba. Sai dai Alhmdllh a ɓangaren Ammah babu abinda zata cema UBANGIJI sai godiya. An tsaida Ranar auren Maryam da Ahmad. Yayinda ɗaukakar da ALLAH ya bama Smart ta sake fiddota a cikin ƴan uwa dama jama'ar gidan har da dangin Abbah. Smart ya dakatar da Abbah fita kasuwa duk watan duniya ya yanka masa albashi shi da Ammah a cikin albashinsa da ake biyasan duk sati-sati. Sannan Ahmad zai kawo kayan abinci bisa Umarnin sa.
Wannan abu na ƙara ɗaga hankalin Umma har ma da Mama. Sai dai banbancinsu ita mama kan balbale nata yaran da faɗa ne akan suma su san ciwon kansu su dinga ma mahaifinsu in ba hakaba smart zai ƙwace dukkan power ɗin su, sannan ita bata bin malamai, kishi ne dai irin na matan bahaushe da jin ƙyashin cigaban kishiya. Itakam Umma tsantsar hassada da baƙin ciki sunbi sun kanainaye mata zuciya da ruhi. Ta kasa zaune ta kasa tsaye. Duk ɗan abinda ta samu suna a yawon malamai da bokaye ita da Hajiya Naqiba aminiyarta. Aikin suke iya ƙarfinsu amma basu sake jin wani sabon abu ba bayan zaman Lulu gida. Ga malamin nata ya tabbatar mata akwai fa matsala idan aikin bai kama Smart ba shi. Dan su duka biyun akai musu ai akan su tsani juna. Wannan dalilin yasa take ta faman bibiyar al'amarin Smart dan taji shi ya wajensa yaya akan matar tasa amma ta kasa samun kowacce irin mafita. Ga lamarin Huwaila na caja mata kai. Dan ta girmi Maryam amma har yanzu babu tsayayye, saka auren Maryam kansa ya hargitsa mata lissafinta. Balle da taji cewar itama mai hannu da maiƙo zata aura. Wayyo ina wuta ta saka Ammah ne. Ta rasa wane irin sirri keda Ammah ɗin da dukkan ƴaƴanta suke auren ƴaƴan masu kuɗi. Yanzu dai abu biyu ta saka a gaba. Wato tarwatsa rayuwar Smart da rusa auren Maryam. Duk ta fige ta lalace a tsaye saboda saka wa kai musiba. Itace kullum faɗa da ƴaƴa akan su bata kuɗi, musamman ma Salim dake nuna mata shi fa ya gaji da wahalarta, mitake da kuɗi wai kamar wata ƴar caca..
Duk abinda take a yanzu idon Ammah ƙyam yake a kanta, dan haka ta dake dagewa da addu'oi da sadaka.. Tare da kiyaye duk wani abinda Umma zata basu koda abincin gidanne yanzu ranar girkin Umma sai suka daina ci, miya Ammah ke musu mai yawa tasa a freight, duk ranar da Umma tai girki sai tayi musu abinci a a ɗaki suci, na Ummar a fitar waje aba mutane cikin hikima.. A tunanin Ammah Abbah bai san mike faruwa bane, sai dai idonsa na akan komai yana dai biye yaga iya gudun ruwan kowannensu musamman ma Ummah..
________★
A garko family kam abubuwane keta ƙara tsamari. Abu na farko shine Baba Garko dai tunda ya tsallake bayan kama Sulaiman bai sake dawowa ba, sai labarin a washe garin da Dada taje gidan su Lulu suke jin cewar an ɗaura masa aure matar ma ta bisa. Ranar sunga abinda ya girmesu a wajen Dada. Dan zaman ƴan bori tayi a gaban surukai ta saki ƙaƙƙarfan ihun da ya nema girgiza ginin gidan. Ba ita ba su kansu yaran hankalinsu ya tashi, a ganinsu mi mahaifin nasu zaiyi da wani aure a shekarunsa haka, kuma abin mamaki wai ma budurwa ya aura sa'ar ƴaƴan cikinsu. Matansu kam dai wannan al'amari yay musu daɗi, sai dai suna ƙoƙarin dannewa a gaban mazan nasu.. sai an koma gefe asha gulma da dariyar Dada..
Sai da Baba Garko ya kwashe watanni kusan shida da amaryarsa suna yawan hutawa a ƙasashe sannan suka dawo Nigeria da cikinta da ya fito kowa na gani. Ƙyaƙyƙyawar mace ƴar gaye mai tarin ilimin addini dana boko. Sannan gata yarinya ƙarama, dan bazata wuce sa'ar Lulu ba ma. Da gani dai kasan kuɗi ta gani ta shige, duk da dai Baba Garko ba baya ba wajen ƙyau amma tsufa ai ya ƙwace komai sai godiyar ALLAH kawai. Wannan ciki ya saka ƴaƴansa jin matuƙar kunya, sai dai babu damar yin magana ya maka wankin babban bargo, dan shi ko'a jikinsa. Kuma yace dole su girmama masa mata. Suna son sake bashi haƙuri akan mahaifiyarsu suna jin tsoro, dole sukai gum da bakunansu.
Washe gari Daddy da Uncle Yousuf sukaje gaishesa suma da masa murnar aure anan ne su dai suka fidda kunya da tsoron suka roƙesa akan yay haƙuri itama Dada ta dawo. Ai an mata gargaɗi. Shima Alh. Sulaiman ai masa afuwa dan ALLAH ya dawo cikin iyalinsa. Bai tanka musu ba dai, sai sakawa da yay Uncle Yousuf ya kira masa Smart a waya. Yako kira masa shi suka gaisa. Yana jin ƙaunar yaron matuƙa yanda yake bashi girma. Yay masa faɗa akan rashin kiransa su gaisa, tare da tayasa murnar cigaban rayuwa da ya samu. Yace shi ai bai sani ba sai kwanan da ya gansa ana hira da shi ya shiga mamakin kamannin har yay kiran Daddy shine fa yake tabbatar masa da shi ɗinne. Haƙuri Smart ya bashi cikin girmamawa da tabbatar masa zai gyara insha ALLAH. Cikin gamsuwa Baba Garko ya sake saka masa albarka. Sai kuma ya tambayesa yaushe ne zai zo ya ɗauki iyalinsa. Ɗan jimm Smart yay na wani ɗan lokaci, kafin ya firzar da numfashi yana jan ajiyar zuciya. Cikin tausasa harshe ya ce, “Baba yanzu ni lokacin nawa ne sai a hankali, dan gashi ana tsaka da fara buga wasan premier link ne. Sannan kuma itama bana son a takura mata har sai idan itace da kanta ta yarda zata nemeni nake ganin hakan zai fi zama masalaha, itama bazataga an takura mata ba kamar farko”. Murmushi irin na manya Baba yayi. Tare da cewa, “Shike nan shawaranka yayi sosai”. Daga haka suka ajiye wannan maganar Smart ya koma bashi hakuri shima akan maida Dada da sakin Alh. Sulaiman. Acewarsa shi ya yafe komai ya wuce a tari gaba........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣
........Wannan roƙo nasu Smart da Daddy da Uncle Yousuf harma da Abba da shima yazo masa murnar ƙara aure akasha hira da barkwanci na tsoffin abokai bayan sati biyu Dada ta dawo. Dawowar data zame mata matsanancin jin zafi. Gashi ba abun tace bazata dawo ɗin ba ta rasa sauran damarta. Ga muzantatan da surukanta keyi na sake ɗaga mata hankali. Ta samu gida fa komai ya sauya. Hatta masu aiki kowa dai Aunty Amarya dai aunty amarya dai. Dan yarinya ta kwantar da kai tana cin garar arziƙi abinta. Ta kuma kame kowa na gidan da ƙyautatawa bayan uban gayyar Baba Garko da taima ram da zuciya yake jinsa kamar wani ɗan shekara talatin, dan more tsufansa yake hankali kwance ya manta da batun wata aba Dada... Ganin cikin amarya da Dada kejin wai-wai a bakin mutane ya sake ɗaga mata hankali ta ɓarke da kuka. Wai itace yau tsofai-tsofai da kishiya, kishiyar ma sa'ar jikokinta kai jama'a wane irin cin zarafine wannan Alhaji Sufi yay mata ne ita kam a duniya, duk wahalar da tai a ƙuruciya na hana wata shigowa gidanta sai a wannan gaɓar za'ace wai ga ɗan uba a cikin zuri'arta. Ga shi Baba Garko yaƙi ko saurarenta tunda ta dawo, duk ranar girkinta fa zai yi kamar suna tare amaryarsa bata zuwa inda yake, amma kuma bai barin itama Dadar tazo. Ko kuma ma ya ƙirƙiri tafiya. Bayan wata ɗaya da dawowar Dada yasa aka saki Alh. Sulaiman shima.....
______★
A ɓangaren uban gayya kam al'amura sai dai Alhmdllh. Dan komai yana tafiya fiye da yanda akai fatansa. Ya zama cikakken ɗan wasan Arsenal da yanzu duniya ke kallo ta faɗa da kiransa *_GWARZON ZAKI_* Sunan Smart Mawashi sake dilmiya yake a duniyar ƙwallon ƙafa. Dan a yanzu haka ya fara taka sabuwar rawa a sabon team ɗin nashi na Arsenal. Duk da kuwa wasanni uku kenan suka buga kacal. Sai dai aduka wasan babu wanda bai saka musu ƙwallo ba. Wannan ya sake jawo hankalin al'umma kansa tako ina a duniya. Ya zama ɗaya daga cikin matasan yara masu tashe a duniyar ƙwallon da ake faɗa ake ma kan faɗa a kowane yini. Al'amarin matarsa bawai baya damunsa bane, ya miƙama UBANGIJI al'amarinsa ne kawai da fatan cinye waɗan nan jarabawoyi kashi-kashi. Shi kaɗai yasan abubuwan da yake jurewa a irin wannan tsukun. Amma yana matuƙar begen matarsa a kusa da shi har ma da gudan jininsa takwaransa.....
____________★
Yau ma a gajiye ta dawo gidan kamar kullum Ummita biye da ita da tarkacenta. Tunda aka kammala bikin buɗe ƙungiyar nan tata bata huta ba. Ga aikin kungiya gana office ga karatun islamiyya ga shago. Dan rainon AA dai bazatace komai ba kusan Mommy da su Afrah ne keyi da Iya Tabawa. Tsakaninta da shi kawai ta shayar da shi. Kasancewar ma yana shan tea da koko hankali kwance bai cika damuwa ba. Shiyyasa ma bata fita da shi ko'ina. Ba kuma ya kuka dan shi ɗin mai iyayene da yawa. Itada kanta ma wani lokacin har tausayi yake bata da rashin samunta yanda ya kamata. Amma yaya zatayi.
Tunda sukai sallama AA da ke a bayan Suhaib na masa doki ya fara zillo. Saukesa yay suna masa dariya. Ya rarrafo da saurinsa zuwa gareta. Kamar yanda suke dariyar itama dariyar takeyi. Daukarsa tai ta jefa sama ta cafe tare da rungumesa tai masa kiss. Shima yay mata a kumatunta biyu. Lakace masa hanci tayi cike da farin ciki da jinjina wayonsa. A kullum kamar ana ƙara masa wayo ne. Baya magana dai sannan tafiya bata nuna ba, amma idan ka gansa bazakace watansa tara ba. AA akwai zafin nama da ɗankaren wayon tsiya. Shiyyasa ɓarna babu kama hannun yaro. Idan aka kaisa hira wajen Daddy har korosa yake saboda ɓuruntu. Hakama Mommy sunta faɗa kenan.
Cikin zubewa a kujera Lulu ke faɗin, “Wayyo ALLAH ku bani ruwa kafin na shiɗe Please”. Amrah na dariya ta miƙo mata ruwa da kofi, kofin ta ture ta ɓalle murfi goran ta kafa kai kawai. Neman ƙwacewa AA yake tana buge masa hannu, bata kulashi ba sai da ta kusan shanyewa ta bar masa ɗan kaɗan sannan ta bashi.
“Wai lallai aunty Lu.. kinji ƙishi fa”.
Cewar Mubeen dake ƙoƙarin ɗaukar AA da ke miƙa masa hannu. Dan shigowarsa kenan shima da ga makaranta. Tace, “Ka bari kawai broth wlhy yau munsha wahala ne. Ai bazan iya driving-driving ɗin nan ba a nema min driver please. Sai dai mai hankali dan ALLAH ban son mai surutu da ƙazanta”.
Dariya Amrah da Afrah da Mubeen suka sanya. Mubeen ke cewa baki son irin su Dallatu yake ko wa ma mai shegen ƙaryar nan ga yalalen haƙora”.
Itama dariyar tayi, dan ta tuna da wanda suke maganar, shine ta kora aka kawo Smart. Akwai shegen surutu da son fafa amma ba tsafta. Aiko yasha marukanta babu adadi. Haka kawai sai Smart ya zo mata a rai. Taɗan lumshe idanu da jan ajiyar zuciya, gaba ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Tsam ta miƙe tabar falon suna cigaba da hirarsu bama su farga ba. Dan Ummita suka shiga bama labarin direbobin Lulun da akasha kala-kala a gidan. Tana shiga ɗakin nata da ke tsaf-tsaf yana ƙamshi mai daɗin gaske dan yana nan a yanda kowa ya sanshi da tsafta, iya Tabawa bata wasa da gyaransa saboda Lulu sam bata son ƙazanta. Abayar jikinta ta saɓule, wando da rigar data saka a ciki suka bayyana. Suma zaresu tai ta shiga wanka. Tana fitowa ta gabatar da sallar magrib da aketa yi. Alkur'ani ta ɗauka tai karatu gwargwadon abinda ya sawwaƙa kamar yanda ta saba a yanzu, kafin ta ɗora da azkar na yamma da bata samun damar nutsuwar yi sai irin iyanzu ɗin. Koda Ummita ta shigo mata da takardun ta da Laptop bata katse abinda take ba, sai ga Iya Tabawa ma da tea da Lulun kesha duk dare AA goye a bayanta. Tea ɗin ta fara ajiyewa a inda Lulun ke zama yin ayyukanta sannan ta matsa gaban gado ta sauke AA ta kwantar a hankali. An masa wankansa an masa shirin barci sai ƙamshi yake yi kamar ba dare ba. Fita sukai gaba ɗayansu suka ja mata ƙofar, dan babu kuma mai sake shigo mata kenan, itama da wahala ta sake fita in ba Daddy ne bai shigo gidan da wuri ba taje su gaisa. Kamar dai yau da suka samu baya a gida bai dawo ba.
Bayan kammala addu'ointa tsam ta miƙe ta maida komai a inda yake tare da zare abayar sallarta ta maidata a inda take ajiyewa. Doguwar riga mara nauyi da bata kai mata har ƙasa ba ta saka mara hannu. Ta ɗan rage gudun acn ɗakin saboda AA mai saurin ɗaukar mura sannan ta nufi gadon nata. Zama tai a hankali gefen da yaron yake da ga can ɗan tsakkiya tana sauke ajiyar zuciya da ɗaukar wayoyinta. Ɗan dudduba massages tayi da miss calls da akai mata ɗazun bata samu amsawa ba. Ta kira wanda zata iya ta share sauran. Sakwanin ma amsa wanda suke da muhimmanci tayi sauran ta barsu. Tana ƙoƙarin ajiye wayar kira ya shigo. Number nan ce dai da ko ta ɗaga ba'a magana tayi masifar har ta gaji, har blocking tayi amma tarasa yanda ake cigaba da kiran nata. Har ta tsinke bata daga ba, aka kuma sake kira. Tasan idan bata ɗaga ɗin ba dai ba dainawa za'ai ba koda za'a jera mata kira hamsin ne, dan haka ma take ɗagawar ta samawa kanta lafiya tunda bata san wane aljani ne ba kuma. Kamar kullum shiru anƙi ace komai, sai dai tana iya jiyo saukar numfashi da fitarsa a hankali. Itama yau sai taƙi yin magana. Haka sukai shiru kusan na mintuna uku kamar ba kuɗi ake ci ba.
“Hummm koma waye dai ALLAH ya shiryesa”. Ta faɗa cikin jin haushi da yanke kiran tana jan ƙaramin tsaki. Wayar ta jefar gefe tare da kai hannu ta gyara ma AA kwanciya, sai ta samun kanta da zubama yaron ido kamar yau ne ta saba ganinsa. Ta ja tsahon mintuna biyar tana ma yaron kallon ƙurillah tare da cakuɗa abubuwa da yawa da ke cimata zuciya. Ganin zata zurfafa tunaninta yay yawa ta sumbaci goshin yaron da sauke ajiyar zuciya mai nauyi ta masa addu'a ta gyarashi. Miƙewa tai zuwa inda take zaman aikinta ta zauna, sai da ta haɗa shayi sannan ta kunna laptop tare da rage hasken ɗakin, bakajin komai sai motsin keyboard da na ac. Ta kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ta tashi tana faman miƙar gajiya, toilet ta shiga tai uzirirrikanta ta fito tai shirin barci ta haye gado kusa da gudan jininta ta kwanta.....
Washe gari kamar yanda ta saba da wuri tai shirin fita. Dan ma tana ta fama da AA da ya maƙale mata yau shagwaɓa yake ji, sai da Ummita ta shigo ne ta ansar mata shi ta samu ta ƙarasa gyarawa tana faɗin, “Yaro zaka gane kuranka yayeka zanyi ai a cikin watannan”.
Cikin waro idanu waje Ummita ta ce, “Kai aunty wasa kike amma dan ALLAH?”.
“Oh wasa ko zakuga wasa”.
“Kai aunty wata tara fa, baima cika cif-cif ba. Banda ma yanada kirinki da zafin nama ai bai kai a fita a barsa ba”.
“Uhm Ummita kanku fa akeji, wlhy jira kawai nake ya taka na yayesa. Tunda yana cin abincinsa ba wani ya damu da nonon bane sosai ai gara na hutar da kaina ko.”
“Mudai aunty kiyi haƙuri to ko shekara ɗaya mu cika dan ALLAH mun tuba”.
“Ummita kenan, wai baki tausayina ne ma dai ko. Da wanne zan ji?”.
“Aunty damu mana, ai mune farko kafin komai. Dan kulawar mu da ta Abbienmu itace farko”.
Shiru Lulu tai bata sake cewa komai ba. Dan a duk sanda Ummita zata ambaci Abbien AA ɗin takanji zuciyarta na mata nauyi, shiyyasa bata sakewa hirar tai nisa a kansa take basarwa. Ficewa tai a ɗakin tana faɗin, “Bari na duba Daddy zanyi breakfast a wajensa ki yi maza ki shirya kin san munada aiki yau”.
Cikin girmawa Ummitan ta amsa mata da to tare da Binta da kallo tausayi. Sosai ma'aurata ke matuƙar bata tausayi, bata taɓa ji ko labarin irin aurensun nan ba. Auren kusan shekara ɗaya da fin rabi kaɗan babu a biyu amma zaman wata ɗaya cikakken ba'a samu ba, dan ma UBANGIJI mai hikima da ya saƙa zare mai girma na azurtasu da ɗa. Tana ma kanta addu'a, amma gaskiya Lulu na ɗaya daga cikin manyan addu'ointa a kowacce rana. Fatanta ALLAH ya kawo iyakar komai ta koma wajen mijinta da ayanzu duniya ke faɗa da saurara a fanin ƙwallon ƙafa. Ita tasan duk da Lulun bata nunawa tanada damuwa sosai. Dan tasha kamata tana kallon AA kallo mai harshen damo kasancewar sa tamkar photo copy na mahaifinsa. Sannan shi kansa yaron soyayyar da take nuna masa mai kallo yasan ba tashi bace shi kaɗai harda ta Abbien nasa........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar