Showing 33001 words to 36000 words out of 127646 words

Chapter 12 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

248

ke mata. Akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su Lulu da Usman, dan shi ke kawo musu duk wasu bayanai akan Alh. Sulaiman, sai dai a rubuce yake basu, a zahiri kam babu wata alamar dake nuna ko kallon arziƙi sunaima junansu. A haka a haka dai har ALLAH ya kai cikin Lulu haihuwa. Inda ta koma zama da ƙyar tashi da ƙyar. Gaba ɗaya ta canja kamanni saboda kumburin da taɗan yi, dan ma Ummita baiwar ALLAH tsaye take a kanta yanda ya kamata, bata gajiya da yima Lulu da abinda ke cikinta addu'a. Ga Usman na iya bakin ƙoƙarin sa akan komai nasu ciki harda fara shirya musu hanyar guduwa daga tsibirin. Lulu bata taɓa kiran lambar kowa ba tun sanda ta gwada Alh. Sulaiman ya ɗaga. Tunda aka kawosu gidan bai zo ba ko sau ɗaya, hakan ya sasu fahimtar kodai duk cikin takune ko kuma baya ƙasar ne.....
  
*_UK (LONDON)_*

      A ɓangaren Smart wasannin link sun cigaba da tafiya cike da nasarori harma da ƙalubale, inda ALLAH ya ɗaga darajar team ɗin su suka ƙare da maki tamanin da shida, Smart ya jefa ƙwallaye ashirin da bakwai. Hakan ya sashi zama best player na wannan kakar wasa ta bana a ƙasar England, inda ya samu ƙyautar takalmin zinare, team ɗin su kuma ya samu damar shiga babbar gasar premier link na england. A randa su Smart sukai wasan ƙarshe ne ya kasance dai-dai da randa Lulu ta wayi gari da naƙuda. Hankali tashe Ummita tai kiran layin Alh. Sulaiman, amma sai ya amsa mata a daƙile cikin halin ko'in kula. Sai da yaga Lulu na neman rasa ranta sannan yay kiran Usman akan yazo ya dubata, a kallo ɗaya Usman da yay mata ya tabbatar da Alh. Sulaiman cewar dole fa akai Lulu asibiti, dan theatre ya kamata ai mata tilas. Da farko Alhaji Sulaiman ya ɗauki abun babu wasa, sai da fuskanci zai iya rasa damarsa sannan ya amince aka a wuce da Lulu asibiti can cikin gari dan shi tunaninsa mutuwar ɗan a ciki ta jawo hakan. Dai-dai ana shiga da Lulu ɗakin theatre Smart da gabansa keta faduwa ya zira ƙwallo a minti ɗayan ƙarshe da ya rage a tashi wasan. A take garin ya ɗauki ihu, yayinda ya kai ƙasa yay sujida hawayen farin ciki na ziraro masa. Gaba ɗaya teammate ɗinsa sukazo kansa aka rungume juna, suna mai ɗunbin farin cikin shiga a jerin manyan team na duniya da zasu buga primier link kenan, abinda ko'a mafarki ba'a taba kawo musu ba. Amma Alhamdullah sai gashi a dalilin ɗan baiwa kamar yanda suka sakama Smart sun shigo cikin jerin masu nasara. Sosai London City take a hargitse yau anata selebration, su Smart na cikin wata irin doguwar mota mai masifar ƙyau da ɗaukar hankali hannunsu rike da kofin da suka ci suna ɗagawa masoya. Wasu a cikin teammate nashi har cire riguna sukai suna jefama fans. Shi kam dai murmushin sa yake mai ƙayatarwa cike da nutsuwa yana mai ɗaga hannayensa duk biyu, yayinda idan idonsa yakai kan yara yakan ma hannun nasa kiss ya hura musu, sai kaga yaran na maido masa da kisa ɗin suma, jin farin cikin yake tamkar ya zarce na cin ƙwallo a zuciyarsa yau, dan fargabar ɗazun nan da faɗuwar gaba duk ta gudu saboda addu'oin da yake ta yi. Haka suka dinga zagaye cikin London City a wannan mota, inda ta ko ina suka gitta imasoyane ƴaƴa da iyaye harma da kakanni da suka fito domin kallonsu. Sunan Smart Mawashi yasha kira a wannan rana tamkar zai ƙare duk da yanda suke kiran Mawashin abin dariya, sai yaji har hawaye na cika masa ido da wannan al'amari da rahama ta UBANGIJI. A rayuwa ai babbar rahamace ma kaga mutum ɗan uwanka na nuna maka irin soyayya balle kowa yasan Bature akan ƙyamar baƙin fata a zahirance.
        Wannan fa nasara ta Smart ta saka hankalin manyan club na ƙasashen turai gaba ɗaya irinsu Italy, Spain, Germany France etc... dawo wa kansa, yayinda aketa kaikawo da cecekuce akan al'amarin yaron a wannan yini, kowacce kafar yaɗa labarai kaje a ƙasar ta England musamman a fanin ƙwallon ƙafa zancen kenan dai Smart Mawashi, Smart Mawashi.. Al'amarin kamar busa usir na alƙalin wasa. Cikin ƙanƙanƙanin lokaci manyan clubs ɗin suka fara ƙwaɗayin nuna zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa........✍️


_To insha ALLAHU dai mun kusa zuwa gaɓar da komai zai cigaba da tafiya a buɗe, ina zazu ɗin nan ne ɗan can mu samesa yanda muke so🥱 dan nasan kunfi kauri acan😜🚴🚴🚴_



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣



.........*_CANADA_*

   Sosai Lulu ta riga ta sakama ranta tsoron haihuwar ne, duk yanda su Usman suka so ta haihu da kanta hakan na neman gagara. Ga naƙudar tata da gani mai zafi ce, dan tayi wujiga-wujiga a ƙanƙanin lokaci. Tun ma tana hawayen har idanun sun bushe, Ummita dai nata maimaita mata addu'a tana faɗa. Har ALLAH ya isa sai da tama Smart cikin fitar hayyaci😜, akace kuma sai anyi Shari'a da shi yayi jail😂. Abin yaso bama Usman dariya ya dai danne da ƙyar. Dr Lameer yaja Usman gefe cikin damuwa ya ke faɗin, “Ussy inaga fa muyi mata CS ɗin nan kawai, ta riga ta saka tsoro a ranta ga shi kuma jinjirin yayi girma da yawa sosai saboda ciye-ciye data dingayi. Sannan an taɓa taɓa cikin hakan ya raunana mata mahaifa. Amma da ace bata saka tsoro a ranta ba wannan bakomai bane zata iya haihuwa da kanta. Yanzu kam ina tsoron kar wahala tasa mu rasa abinda ke cikinta”.
       “No no Doctor bana fatan a rasa babyn nan wlhy, inaga kawai ayi mata cs ɗin”.
           “Shike nan babu damuwa, wazai saka hannu a cikinku?”.
      “Bara na saka hannun kawai ni”.

    Alhamdullah an samu nasarar zaro baby boy a jikin Lulu ƙamshi. Lafiyayyen yaro ƙyaƙyƙyawa da bai baro komai na ubansa ba, ga shi ƙaton gaske masha ALLAH. Dan hatta wani tawadan ALLAH da Smart ke da shi a gefen kunnensa babba shima jinjiri na da shi. Ankai Lulu ɗakin hutu, yayinda Ummita ta rungume yaro tana mai jin ƙaunarsa a ranta kamar jininta. Shi kansa Usman yaron ya shigar masa rai. Bai kira Alh. Sulaiman da ke can yana jiran ace Lulu ta haihuwa ɗa a ruɓe ba, dan yau shine target ɗinsa akan kuɓutar da su Lulun dama. Shi yay duk wani tsare-tsarensa na nemawa Lulu transper da taimakon Dr Lameer zuwa wani ɓoyayyen ƙaramin asibiti a Derby city. A wannan daren aka fita da Lulu cikin ambulance da Ummita, abinka da turai tsaro kaca-kaca hankalinsu kwance suka iso Derby city zuwa gabannin asubahi. Sanin Alh. Sulaiman zai iya bibiyarsu komai ya tafi ne akan tsari da kulawa. Dan wani gida ne a kusa da asibitin aka ajiyesu, acan gefen gari wajen ana noman fruits, sai gidan abinci da ke gaba kaɗan kasancewar babban hanya ce, sannan bature shi babu ruwansa da daji duk inda yay masa alƙarya ce. Komai da Lulu zata iya buƙata na kulawar lafiyarta su Usman ya tanada a gidan, dan bashi da damar barin ƙasar da su a yanzu kasancewar passport nasu na hannun tsule, fita dasu kai tsaye zai zama mai wahala.
       Kusan ƙarfe takwas Lulu ta dawo hayyacinta, inda cikin amincin ALLAH ta farka bakinta ɗauke da addu'a. Da sauri Ummita da ke zaune a gefenta rungume da jariri dake ta barcinsa tai saurin kallonta da faɗin, “Alhamdullah aunty kin farka?”. Idanu kawai Lulun ta zuba mata ita da jaririn, sai kuma ta sauke numfashi a hankali da motsa lips ɗin ta tana mai bin ɗakin da kallo. “Ina ne nan Ummita? Miya faru da ni?”. Cike da farin ciki Ummita ta ce, “Aunty an miki C'S ne ga baby boy mun samu, nan kuma sabon wajene da Usman ya kuɓuto damu da ga hannun kawunki.” Lulu batace komai ba sai idanu data zubama jaririn hannun Ummitan, da sauri Ummita ta miƙe zuwa gabanta da jaririn, Lulu ta zuba masa ido zuciyarta na wani irin harbawa na masifa. Dan duk da yaron da sauran ɗanyantakarsa ta kasancewa jinjiri kamaninsa da mahaifinsa a bayyane suke. A hankali ta lumshe idanunta tana sakin wasu irin ajiyar zuciya a jajjere, sai kawai ta samu kanta da sakin kuka. Hankalin Ummita ya tashi, ta shiga jera mata tambayoyi akan ko wani waje na mata ciwo ne? Bata iya bata amsa ba har su Usman suka shigo, Dr Lameer ya dubata yayinda Usman ke faman lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta, insha ALLAH sun kuɓuta kenan, zai kumayi duk yanda zai yi na ganin sun koma gida Nigeria. Ummita ita ta bada shawaran ya kamata ama jaririn huɗuba fa, dan haka suka tambayeta wane suna take so a saka masa. Ita kanta batama san lokacin da ta furta, *_“ALIYU”_* ba. Usman da ya saki wani ɗan murmushi ya ɗauki jinjirin yaymasa huɗuba da suna ALIYU HYDAR ZAKIN FAMA. tare da masa addu'a dan duk lalacewar Usman yanada iliminsa na addini. Kawai zama a waje ne ya sashi zama mara jin magana.
        Lulu da idonta ke a lumshe a zuciyarta ta furta (ALLAH ya albarkaci rayuwarka *_Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi_*) sai kuma ta ɗan yamitse fuska kamar wadda take jin hakan banbarakwai a zuciyarta...

      _(To muma dai munce ALLAH ya raya Aliyu Aliyu Mika'il Mawashi. Dangin Smart kar ace bamuyi Barka ba🥱🚴)_
           

         *_NIGERIA_*

    Sosai Daddy ke fama da ciwo a tsaitsaye, sai dai yanata dauriyar ganin bai bari ko Mommy ta fahimta ba. Sai dai ya gagara ɓoye damuwarsa akan halin da suke ciki tsakaninsa da ɗan uwansa Yousuf. Yousuf nada matuƙar muhimmanci a garesa ta yanda baki bazai iya furtawa ba. Su fa kaɗaine ƴan uwansa shi da Mommy sai zuri'ar da suka tare a yanzu. Tunda yake da ɗan uwansa bayan rikicin Kasancewar Mawaddat (Maman Lulu) a rayuwarsu baya jin akwai wani saɓani daya taɓa shiga a tsakaninsu kamar haka da Yousuf ɗin ya ɗauki zafi da shi. Ba wai baya son fitowa ya faɗa masa gaskiyar al'amari bane, bai son tada masa da hankaline kawai ko sakashi a matsala. Shiyyasa ya zaɓi shanyewa shi kaɗai a tsahon rayuwa. Amma yana gani a wannan gaɓar in har yana son ɗan uwan nasa ya fahimcesa dolene ya buɗe masa sirrin nan dai da yake ta faman biznewa a tsahon shekaru badan tsoro ba sai don dalilai guda biyu. Na farko baya son tarwatsa farin cikin family ɗin mutum mai mutunci da daraja a rayuwarsa irin Alhaji Sufi Ado Garko. Ya taka rawar gani a rayuwarsa da har a yanzu ake iya kallonsa a nuna a matsayin wane. Duk da yasan wannan rubutaccene daga UBANGIJI ko babu shi ɗin komai zai iya tabbata. Amma UBANGIJI ya sakashi zama matsayin sila. Idan ya kasance mai tarwatsa farin cikin wannan ahali yana jin kamar ya rama sharri ne da alkairi. Na biyu shine kare rayuwar yarinyarsa duk da yasan shi bai isa hana komai ba daga ƙaddarar ALLAH. Tunda gashi nan a sanadin hakan har Lulun ta faɗa shaye-shaye batare da ya iya bata kariya akan hakan ba. Hasalima bai taɓa sanin tanayi ba sai a shekarar nan. Tun daga ranar jikinsa yay sanyi matuƙa da sake tabbatar da wayo ko dabara bata kare maka abu sai UBANGIJIN talikai masanin sirrin fili da ɓoye. A hankali ya kai hannu ya ɗauke ƙananun hawayen da suka ciko masa idanu. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da ɗaukar wayarsa ya rubuta gajeren text message wa Uncle Yousuf ya tura masa, duk da yasan a gajiye yake dan jiya ya dawo daga UK kamar yanda yake ji a bakin Mommy dan shi dai Uncle Yousuf ɗin bai sanar masa ba sam.

       Uncle Yousuf na tsakiyar iyalinsa suna kallo, yayinda Deen da Ra'is ke home work text ɗin Daddy ya shigo masa. Kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka ya duba ganin kallon da aunty Saliha tai masa. Shiru yay yana kallon text ɗin da bai wuce layi biyu da rabi ba. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya dan shima harga ALLAH yana azabtuwa da rashin ɗan uwan nasa a kwanakin nan. Dauriya kawai yake yi. Tunda ya san kansa bai taɓa wayar gari da yini harda kwana baiyi waya da yayan nasa da yakema kallon kamar mahaifi ba. Dan ko baya ƙasar sukan yi waya sama da sau uku a rana. Dan ƙa'idarsa ce duk safiya ko suna a ƙasa ɗaya ko basa nan zai gaishesa, sannan da dare kafin ya kwanta zai kirasa yay masa sai da safe. Idan ma bai kira ba bisa wani uziri na yau da gobe shi daddyn zai kirashi da kansa. Bayan wannan wayoyin biyu na ƙa'ida wasu wayoyin kan shiga a tsakaninsu game da Business ko wani muhimmin abu da ya shafesu. Jin zuciyarsa ta kasa nutsuwa waje guda ya miƙe yana kallon aunty Saliha. “Sweetheart ɗan bani key Please”. Da mamaki ta ce, “Key kuma?. Ina zakaje kaiko a daren nan kamar wanda ke a tarkon mace?”. Karan farko yay murmushin da bai niyya ba. Dan tun a kallon da tai masa sanda text ɗin ya shigo yasan akwai magana a bakinta. Komai baice ba sai wayar da ya miƙa mata. Dan tsakanin shi matarsa akwai yarda mai ƙarfi da fahimtar juna. Duk inda ƙofar zargi ta nema buɗe musu sukan yi saurin tosheta kafin a samu ɓaraka. Cikin sanyin jiki ta miƙa masa wayar da faɗin, “I'm sorry dan ALLAH, ALLAH ya bashi lafiya”. Murmushin kwantar da hankali ya mata da nuna mata hanya alamar taje ta ɗakko masa. Babu jimawa kuwa sai gata ta dawo. Ta miƙa masa tare da ɗan rungumesa. Bayanta ya ɗan bubbuga yana faɗin, “Thanks” daga haka ya saketa ya fice yanama su Deen bye bye.


Duk da dariyar dake tasoma Daddy ganin yanda Uncle Yousuf ɗin yazo a ƙanƙanin lokaci yay ƙoƙarin danneta. Sai ma sake langaɓewa da yay. Cikin sassarfa da ruɗani Uncle Yousuf ya ƙarasa garesa. Sai faman jera masa tambayoyi yake a jajjere. “Yaya mike damunka? Dama baka da lafiya? Tun yaushe kake a kwance? Kasha magani? Miyasa baka kirani munje asibiti ba?”. Cikin murmushi Daddy ya kamo hanunsa dai-dai yana kaiwa zaune kusa da shi a bakin gadon nasa. “Irin wannan tambayoyi haka a jere auta wanne zan amsa a ciki?”. Kai Uncle Yousuf ya langaɓe gefe kamar mai shirin fasa kuka, dan da gaske yaga yayan nasa ya rame masa a idanunsa sosai. Daddy ya sake sakin murmushi tare da lumshe idanunsa. Sai kuma ya yunƙura da niyyar tashi. Da sauri Uncle Yousuf ɗin ya taimaka masa ya zauna da ƙyau. Shima sai ya zauna gab da shi sosai hannayensu cikin na juna. Cikin tausasa murya Daddy yace, “Kana fushi dani saboda ɗiyarka ko? Kayi haƙuri Yousuf kaji. Yayanka ba son zuciya bace ta lulluɓe masa ido. Idan ma a kwaita to ajizancine kawai irin na ɗan adam. In sha ALLAH yau zan fiddaka a cikin duhu tun daga lokacin da kuka fara tuhumata kai da Kareema har zuwa yau ɗin nan. Amma dan ALLAH ina son kai min ƙyaƙyƙyawar fahimta kaji.”
       “Insha ALLAH Yaya”. Uncle Yousuf ya faɗa a sanyaye.......✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣9️⃣



........Murmushi Daddy yay masa tare da sake damƙe hannayensu cikin na juna sannan ya fara da faɗin, “Tun ranar dana wayi gari da salwantar maƙudan kuɗaɗe a cikin Company hankalinna yay masifar tashi, nabi diddigi tako wane fanni amma ban fahimci komai ba akai. Na shiga ruɗani matuƙa da tunanin ta ina zan iya samun waɗan nan kuɗi haka, dan ko za'a saida duka ƙaddarar dana mallaka a wancan lokacin bazasu biya ko kaso biyu bisa goma na abinda ya salwanta ba. Ina cikin wannan ruɗani da ɗimuwar Alh. Sulaiman ya shigo rayuwata.........” kaf ya kwashe labari ya sanarma Uncle Yousuf da jikinsa ke wata irin tsuma, ga hawaye shaɓe-shaɓe kaca-kaca da fuskarsa kamar wani ƙaramin yaro. Shima dai Daddy ɗin hawaye yake, ya jawo Uncle Yousuf jikinsa ya rungume yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Sai da yaji ya bar kukan sannan ya ɗagoshi. Zama Uncle Yousuf ya gyara cikin dasashiyyar muryarsa ya ce, “Yaya miyasa ka iya barin wannan babban al'amarin masu nauyi irin haka a ranka. Miyasa baka taɓa sanar damu ba dan ALLAH? Haba yaya har wanene Sulaiman da makircinsa da zai maka irin wannan ƙullin haka ka zauna kallonsa?”.
        “Yousuf ka fahimceni hakan dolene a gareni saboda dalili masu yawa. Sannan ma lokacinne bai yiba shiyyasa, maybe UBANGIJI yay masa talalane da kuma hukuntani akan kuskurena nima. Na farko na yarda da shi da kallonsa da siffa irin ta mahaifinsa na mutumin kirki kasancewar a haka yazo min. Sannan bazan so maida sharri da alkairi ba a yanayin riƙon da mahaifin nasa yay min. Sannan dolene nayi komai domin kare ku a matsayinku na ahalina, dan shekarunka a lokacin sunyi ƙanƙantar da bazaka iya fahimtata ba yanda ya kamata. In da ban shanye komai ba za'a iya cutarmin da ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login