Showing 108001 words to 111000 words out of 127646 words

Chapter 37 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

803

kayan ƙamshi da kansa. Idan yaga AA zai takura mata ya ɗaukesa ya kaima Iya Tabawa. Ya bata kulawa sosai harta samu sauƙi. Da ga haka aka shirya kamar basu ba aka koma nunama juna soyayya da tattali. Sai aikinsu da suka saka a gaba. Ita aunty Bilkisu ma sai abin ya koma bata dariya. Shiyyasa dai akace duk wanda ya shiga tsakanin mata da miji ya matse. Dan zasu shirya ne su barsa a ciki. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa mura na damun Lulu akai-akai. Ita abin har mamaki yake bata dan bata cika yawan mura ba a da. Sai dai ta danganta yanayin da sanyi da ake yi sosai harda dusar ƙanƙara.
     Wasan su Smart na tafiya cike da nasarori da kalubale. Yayinda sunansa keta ƙara cigaba da amsa kuwa saboda yanda yake zura ƙwallaye a raga babu ko ɗar. In dai za'a kirayi sunan wani yaro mai tashe a wannan ƙarnin a harkar ball idan sunansa baizo na ɗaya ba dolene yazo ana biyu. Ballema ALLAH ya bashi farin jinin da akan ambacesan a farko. Sam baya wasa da addininsa. Sannan tsaye yake akan Lulu itama dan har yanzu shine mai ɗora mata karatu datai matuƙar maida hankalinta a kai. Wani lokacin kuma aunty Bilkisu ke ɗora matan.. A gefe kuwa sun matuƙar saka rayuwar Alh. Sulaiman a gaba, dan a yanzu haka ana tsaka da dambarwa ne tsakaninsa da amaryarsa akan Flash. Anyi-anyi ta bada taƙi. Yayi haukan yayi hargagin yayi kurarin duk da tana a gidan nasu tayi kememe. Hajiya Turai dai ce ƴaƴanta suka dawo da ita. Acewarsu sai da Mahaifin nasu ya bar mata gidan badai ita ta bar masa ba. Dan babu kunya suka dinga yaɓa masa magana musamman ma Tajuddeen, Alh. Sulaiman ranar harda hawayen baƙin ciki. Bai taɓa tunanin soyayyar da yakema Tajuddeen zai iya kallon tsabar idonsa ya masa rashin kunya haka ba, al'amarin ya girgiza zuciyarsa kam..

(Abinda kayi dole ai maka ai dama🚴🚴🚴😂).

           *_NIGERIA_*

   Watanni kusan huɗu kenan abubuwa na'a rincaɓe musamman a ɓangaren Alh. Sulaiman Garko. Dan anata musu tsinci ɗai-ɗai na masifa ta yanda gaba ɗaya kasuwar tasu ma ta tsaya cak. Ga manyan kayansu da ke gaf da zuwa Najeriya ɗin. Duk yay wani iri da shi duk da har yanzu ma shi bako a fara taɓashi ba. Dan ko'a cikin yaransa kaf babu wanda aka taɓa. Sai aminansa da Hon. Nakowa kawai ya rage sauran duk suna hannun hukuma anyi ram da su. Kullum cikin kiran Daddy yake yana masa barazana. Shiko Daddy na maida shi mahaukaci da naɗe komai a waya tare da kunnashi. A gefe ɗaya ga al'amarin amaryarsa da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Burinsa kawai ya amshi Flash ɗin hannunta koda zai kasheta ne shi babu ruwansa. Tayi-tayi ya saketa kuma yaƙi. A randa yaje har gida ya cima mahaifinta mutunci ta tabbatar masa anzo gaɓar da take jira, dan haka a ranar ta aike ma su Baba Garko da video. Da kanta ta shirya taje har gidan ta danƙama Baba Flash. Har wulaƙanci Dada taimata saboda taje ta gaida amarya da duba yaranta. Ita dai bata tanka mata ba har Dadan tayi ta gama san ranta. Bayan wucewarta ne Dada ta nufi wajen Baba Garko. Ta sameshi da ƴan biyunsa da sukai kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa. Takaici kamar zai tsayar mata da numfashi amma ta danne da ƙyar. Dama bata taɓa ɗaukar yaran ba tunda aka haifesa, dan haka yanzun ma kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta. Ko'a ƙwallar rigar Baba Garko, dan ya jima da fahimtar bakin ciki take da yaran. Sama-sama ya amsa mata gaisuwa ya cigaba dama yaransa wasa kamar ma ya manta da ita. Hakan ya sake Zafafa mata zuciya taji ta tsani yaran fiye da ko yaushe. A cikin tunzura ta ce, “Amma dai Alhaji bai kamata ka fifita rayuwar ƴar wasu akan naka ba. Yanzu yarinyar nan ta gama fetse mana yaro da iskance-iskanceta ta dawo tana mana barikanci. Ni na rasa mi Sulaiman yayi maka haka da zafi ne. Kabi ka tsangwamesa babu laifin tsaye babu na zaune. Idan ma maganar Mawaddat da Tajuddeen ce ya kamata ace ta wuce tunda dai tana gidan mijin da kuke son ganin nata da shi yanzu ai ko”.
        Idan ɗakin ya tanka Baba Garko ya motsa, hakan ya sake harzuƙa Dada. Miƙewa tayi a fusace zuwa gabansa ta ɗauke Flash ɗin dake ajiye kusa da shi. Nan ɗin ma bai tanka mata ba harta fice, bai kuma nuna damuwa da ya bita akan flash ɗin ba ya cigaba da yima yaransa wasa. Hajiya Dada kam da masifa ta nufi sashenta. Harta ɗauki waya da nufin kiran Alh. Sulaiman akan yazo ya amsa sai kuma ta ajiye tana faɗin, “Bara dai naga wai ubanmi akema wannan tashin hankalin ne a ciki.” Ta ƙwalama mai aikinta kira. Jiki na rawa ta iso, a gabanta ta zube cike da girmamawa. Umarnin ɗauka mata tab.. a ɗaki ta bata. Babu jimawa ta dawo ɗauke da tab.. ɗin. Ita ta saka mata flash ɗin. Cike da gadara da ƙasaitar mulkin masu akwai Dada ta amsa ana wani gyara zama da busa iska tace mai aikin ta kawo mata lemo. Ita dai mai aiki umarni take bi.
        Fuskar data fara bayyana ta saka ƙirjin Dada bugawa, jikinta ya fara tsumar kewa. Mawaddat ɗinta ce, yarinya mai hankali, mai sonta da ƙaunarta, sai dai ita kullum tana a cikin hantararta ne saboda tana ce mata kaza ba daidai bane kaza ne daidai. Kalaman Mawaddat suka cigaba da jan hankalinta kafin kace mi ta jiƙe sharkaf da zufa. Maimakon hasken ɗakin ta koma ganin duhu. Tun tana iya jin sauti da motsi har komai ya tsaya mata cak sai razanannen ihunta daya karaɗe kunnuwan duk wanda ke a kusa da sashen nata. Rige-rigen shiga masu aikin nata suka shiga yi inda take, sun sameta wanwar a ƙasa kofin lemon da aka ajiye mata ya kife da alama ma a kansa ta faɗa. Duk da hankalinsu ya tashi da ganin a yanda take sai da suka ɗauki tab.. ɗin suka kalla abinda ya razanatan. Yayinda mai tausayin cikinsu ta fita a guje kiran Baba Garko. Ai suma sai suka ƙare da ƙwalla ƙara a dai-dai shigowar Baba Garko da amaryarsa, dan tana tare dashi sanda mai aiki taje kiransa....

        An ɗauki Dada babu alamar rai a tattare da ita ga jini na zuwa ta inda gilashin kofi ya jimata ciwo. Shi kansa Baba Garko a kiɗime yake dan bata taɓa kasancewa a irin hakan ba duk wannan rikicin da akeyi. Iyaka dai ta suma da'an zuba mata ruwa ta farfaɗo. Amma yau babu abinda basu gwada mata ba ko motsi. Da tab.. ɗin ya fita a hannunsa, dan yasan koma mi ya sakata a wannan halin bazai kasance ƙaramin ba.
      Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya isa kunnen ƴaƴanta da jikoki. Kafin wani lokaci asibitin da aka kaita ya cika da Garko family, zuri'ar Uncle Khamil dake Abuja ne kawai babu suma suna tafe sai na auta dake a Saudiyya. Har zuwa washe gari ba'a samu kan Dada ba, dan haka hankalin kowa ke'a tashe. Hatta shi uban gayyar a wannan karon hankalin nasa a tashe yake. Dan koba komai fa yana son matarsa, sannan itace uwar ƴaƴansa. Tun shekarun ƙuruciya suke tare har zuwa tsufa da daɗi babu daɗi tana zaune da shi. Washe gari zuwa sha ɗaya na safe auta ya iso tare da nasa iyalinsa, tamkar shi Dada ke jira ya iso ta farfaɗo, sai dai fa numfashin farko da taja ta fesar da jini ta fesoshi. Wani sabon tashin hankalin kenan, dan likitocin ma sun kasa musu bayani, sai kai-kawo da shigi da fici sukeyi. Duk wanda suka tunkara sai dai ya zame da faɗin yana zuwa. Duk wannan abun da akeyi babu Alh. Sulaiman sai ƴaƴansa da uwar gidan sa. Karan farko da Tajuddeen yaji baƙin cikin halin mahaifin nasa. Shin wai minene na wannan gabar, a ganinsa mahaifiya ai tafi gaban wasa. Dada na a irin wannan yanayin har yace yanada wata hujjar cigaba dayin gaba. Duk wanda yaga Dada a jiya zuwa yau dolene ya tausaya mata. Shi kansa Baba Garko ya ajiye makaman yaƙinsa harda hawaye yake da sambatun ta tashi dan ALLAH kada ta tafi ta barsa. Cikin ɓacin rai Tajuddeen ya dannama ubansa kira. A lokacin yana ɓoyayyen Companyn sa suna tattaunawa da yaransa malami da wasu abokan cinikayyarsa mazauna Legos akan kayansu da suka iso Nigeria a daren jiya. Sai dai sun rasa yanda zasu fidda kayan daga bakin ruwa saboda kamar fa an saka musu ido... Yana ɗaga wayar Tajuddeen ya fashe masa da kuka cikin masifa yake faɗa masa “Yanzu nan Dad har kanada lokacin nishaɗi haka mahaifiyarka kwance ranta a hannun ALLAH tana aman jini likitoci tun daren jiya tsaye a kanta. Anya kuwa kana fatan gamawa da duniya lafiya Dad. Ace iyayenka ne abokan gabarka. In dai dan ni kakeyi toka ajiye dan nikam dai na haƙura da Mawaddat koda ace sonta zai zamar min ajalina. Duk ƴan uwanka gasu nan har wanda basa ƙasar kai kaɗai ne ka fita zakka a cikinsu saboda son zuciya. Idan ta mutu sai kazo zaman gaisuwa ai” ya faɗa yana yanke kiran wani irin kuka mai cin rai na kufce masa...

*_★UK★_*

    .....A dalilin wayar Tajuddeen da mahaifinsa su Lulu suka san halin da ake ciki. Domin suna tsaka da ganin zaman meeting ɗin Alh. Sulaiman da abokansa ta direct camara ɗin su. Hankalin Lulu ya tashi matuƙa, dan koma minene ya faru Dada ba abar yardawarta bace ba. Kuka ta fara cikin tashin hankali ta shiga neman layin ƴan uwa. Da kyar ta samu Uncle Amin ya ɗaga. Cikin kuka take faɗin yanzu nan Dada na'a irin wannan halin amma babu wanda ya faɗa mata. Lallashinta Uncle Amin ɗin ya farayi akan ta kwantar da hankalinta tai mata addu'a daga inda take. Amma ina Lulu taƙi saurarensa. Shima Smart ɗin ta matuƙar tayar masa da hankali, dole ya saya mata ticket dan bazai juri ganinta a haka ba. Sai dai ita kaɗai zata taho banda AA. Ta barsa wajen Iya Tabawa da aunty Bilkisu da har yanzu bata kammala ganin likita ba duk da tana a gida lokaci-lokaci dai take zuwa ana dubata asibitin........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣7️⃣




.......Uncle Yousuf da kansa yaje ɗaukar Lulu airport. Da ga airport ɗin kuma asibiti suka wuce kai tsaye. Ba ƙaramin girgiza zuciyarta tayi da ganin kowa da kowa na asibitin ba. Ashe ƴan Saudiyya ma har sun ƙaraso. Kasa haƙuri tai sai da ta leƙa Dada ta window. Dan an hana kowa shiga wajenta Baba Garko ne kawai ya shiga bayan likitoci sun sami kanta da ga aman jinin da take yi. Kuka sosai Lulu keyi da ya sake ɗaga hankalin duk wanda ke a wajen. Uncle Taheer Auta ne ya kama hannunta suka bar wajen, da ga gefe ya zaunar da ita yana lallashinta akan ta daina kuka addu'a Dada ke buƙata a yanzu. A hakama an samu kanta ba kamar da safe ba. Wannan ɗan lalashin da autan Dadan ya mata ne ya ɗan saka mata nutsuwa kaɗan ta rage kukan da take yi. Lokacin da zasu wuce gida tace ita a barta anan zata kwana. Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ce tai ƙarfin halin cemata, “A'a Mawaddat kema kulawar kike buƙata ai a wannan halin da kike ciki. Ga tafiya mai nisa kinyo”. Da yawan ahalin wannan family sun san ALLAH ya bama Hajiya Turai baiwar gane ciki koda ƙarami ne, dan haka kowa ya fahimci abinda take nufi akan Lulu ballema duk mai lura yaga Lulu yasan tana da ciki saboda illahirin halittun jikinta sun nuna hakan duk da kuwa akwai jin daɗi da samun kwanciyar hankali. Abinda bata sani ba hatta Iya Tabawa ta jima da fahimtar tana da ciki, tayi gum da bakinta ne kawai har ya bayyana kansa. Ita kanta aunty Bilkisu cikin kokwanto take magana ce kawai batayi ba. Amma har so tai ta tseguntama Ammah da ga baya kuma dai tai shiru dai. Lulu dai ba fahimtar Hajiya Turai tayi ba, sai dai babu yanda zatai ta yarda ta bisu. Kasancewar motar Hajiya Turai ɗin ta shiga sai kawai ta wuce da ita can gidansu (Gidan Alh Sulaiman kenan).

        Alh. Sulaiman da tun wayarsa da Tajuddeen ransa ke'a ɓace yana zaune labarin zuwan Lulu Nigeria ya sameshi. Baida niyyar zuwa asibitin duk da baƙaƙen maganganun da ɗan cikin nasa ya faɗa masa sun kartar masa zuciya amma jin abar farautarsa a kusa da shi ya sashi niyyar zuwa. Sai dai bai baro Companyn nashi ba sai dare sosai saboda bada ƙafa. Sun riga sun gama shirya yanda zasu sace Lulu shida yaransa. Dan haka kai tsaye asibitin ya nufo. Sai dai ya samu kowa ya tafi sai ƙanwar Baba Garko kaɗai da ke tare da Dada. Inna Sadiya nada labarin komai na tsakanin Sulaiman da iyayen nasa, dan haka ta kallesa sheƙeƙe ta watsar, gaisuwar tasa ma sama-sama ta amsa masa. Duk yanda yaso jin wani abu daga gareta bata kulashi ba. Dole ya kama gabansa yana jan tagwayen ƙwafa da jin kamar ya make banza ya wuce. Yana fitowa yay kiran yaronsa Malami. Ya sanar masa su rabu zuwa gidan Daddy da Uncle Yousuf dan Lulu bata asibitin. Sun amsa masa da girmamawa, duk da sun san tsaron dake zagaye da gidajen daya faɗa ɗin, daga haka ya wuce gidansa shima. Koda ya iso bai nema matarsa ba kamar yanda itama ba shiga sabgarsa takeba a yanzun, dan tace zaman ƴaƴanta kawai takeyi ita kam dan ya gama fita mata a rai kasancewar amaryarsa ta sanar mata komai. Dan bayan dawowarta ƴaƴanta mata yayun Tajuddeen da ita sunje gidan su amaryar tasa domin lallashinta itama ta dawo ta nuna musu ai itakam tabar gidan nan har abada. Da suka matsa ne taja Hajiya Turai gefe ta sanar mata komai tare da nuna mata video ɗin nan. Hankalinta ya tashi matuƙa, dan itace ma ta bata shawarar ta kaima su Baba Garko videon inba haka ba mijin nasu zaibi duk wata hanya ya kwacesa a hanunta. Ba ƙaramin ruɗani Hajiya Turai ta shiga ba a week ɗin da ya gabata, da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ko yaranta bata sanarmawa ba har yanzu.
        Zuwa cikin dare jikin Lulu ya ɗume da zazzaɓi, kasancewar kwana biyun nan haka take fama sai bata damu ba. Ta dai sha magani ta kwanta duk da tana jin kewar mijinta ta taushi zuciyarta, sai gabannin asuba zazzaɓin ya saketa. Tana idar da salla kasa haƙuri tayi ta ɗora layinta na Nigeria akan waya. Smart ta fara kira. Bugu ɗaya ya ɗaga mata. A tare suka sauke nannauyan numfashi. Kafin a hankali ya fara furta, “Kin san ko yanda kika bar zuciyata cikin barazana da tashin hankali Baby luv. Tunda kika sauka nake jiran kiranki amma shiru har na fara jin nauyin yawan kiran da nakema Daddy da Uncle Yousuf.”
        “Kayi haƙuri”.
  Ta furta a hankali. Ajiyar zuciya ya sake saukewa da faɗin, “Ya zanyi, na haƙura. Ina dai fatan babu wata matsala ko? Dan wlhy gaba ɗaya na kasa nutsuwa duk da nasan wawan baiyi zaton kina gidansa ba”.
    Murmushi Lulu tayi har yana iya jiyo sautinsa. Cikin ƙara tausasa harshe ta ce, “Bayan ka bashi ƙafa taya zai iya gano ka. Dolene na bama wanda ya saka maka suna Smart ƙyauta gaskiya. Mutum yana nemana ruwa a jallo amma ka turoni gidansa na kwana kuma. Sannan kada ka manta kawuna ne kake cema wawa”.
         Ƙaramar dariya yayi shima. Ya ce, “ALLAH sarki masu kawu yi sorry. Sannan banda wata mafita sai hakan ai. Dan nasan bazai taɓa kawoma ransa zaki zo gidansa ki kwana ba. Yanzu dai sai kiyi taka tsan-tsan kuma.”
     “In sha ALLAHU mijina. Jiya gaba ɗaya kewarka ta hanani isashen barci”.
               “Uhm kamar da gaske. Ni ban san daɗin baki. Ina Aliyu yaga wannan matsayin. Ke dai kawai kice tsoro ya hanaki barci kina a gidan dodoki”.
          “Oh hakama zakace ko? Shikenan ai zan rama. Bazan ma dawo ba sai bayan wata tara kama kanka”.
     Dariya sosai yakeyi da faɗin, “Haba Baby luv ki tausayamin mana. Ni kaina kin ganni nan yanzu haka nama kasa kwanciyar sai lissafi nake da kallon hotunanki kawai. Na gayyato Baban Ammah ya tayani kwana ya addabeni da ɓuruntu.”
          Cikin dariya ta ce, “Kai miya kaika wannan gangancin siyen gida a sama.”
      “To yana iya kewar Mamansa ta isheni ne. Ni da ƙyar ma idan zan iya haƙuri ban taho Nigeria ɗin nan ba”.
   Idanu ta waro sosai kamar tana gabansa. Ta ce, “Are you serious zaka iya barin wannan kwallon ka taho Nigeria?”.
        “Humm yarinyar nan kina wasa da Aliyu ko? Zan baki mamaki”.
    “A'a A'a nagode basai ka bani ba. Ai nasan zaka aika wlhy yi zamanka na yafe. Nima ba jimawa zanyiba ai. Yanzu dai ina son naje naga Ammah yaya za'ayi?”.
    “Kefa rigimarki yawa gareta Mrs Mawashi. Keda ake ɓoyonki ina kuma zaki je yawo?”.
            “Zuwa wajen uwata ne yawo. To nidai kasan yanda zakai dani gaskiya”. Ta faɗa cikin shagwaɓa har yana iya jiyo sautin yanda take buga ƙafa ƙasa.
       “Kirufamin asiri Baby luv nayi barcina lafiya, kinga dai na sakama raina haƙuri tunda kika taho ko kuka banyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login