Showing 15001 words to 18000 words out of 127646 words

Chapter 6 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

244

ta dawo gab da magrib, daga nan bata sake ganinta ba a tunaninta ta kwanta ne a ɗaki, dan yanayin jikinta na masu sikila yasa bata da kwaramniya sam. Sai da kusan sha biyu taje leƙata sai ta samu ɗaki wayam. Da farko bata damuba ta shiga kwala kiran masu aikinta da tambayar Sultana. Sai dai amsar ɗaya ce su basu sani ba, dan tunda ta dawo islamiyya basu sake ganinta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci Dada ta birkita lissafin kowa na gidan, dan gaskiya ALLAH ya jarabcesu da ƙaunar Sultana matuƙa, kodan tazo a ƙarshe ne batare da tunanin zuwan nata ba. Iya bincike babu Sultana a cikin gidan, dan haka nema ya koma har waje bisa zargin ko sanda ake sallar magrib ta silale ta fita duk da kowa yasan hakan ba halin yarinyar bane. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga ta an ganta, sai dai cikin jini kuma babu rai. Hakan bai hana a garzaya da ita asibiti ba, inda a gwaje-gwajen farko doctor ya tabbatar musu fyaɗe akai mata, amma ta farfaɗo daga doguwar sumar data tafi. Hankalinsu ya tashi, sai dai jin tana raye yasa sun ɗan ji sassauci. Alh. Sulaiman ne ya kawo police aka tattare duk ma'aikatan gidan zuwa police station. Harda kukansa kamar wani ƙaramin yaro, bayan lokacin har Auta an haifa masa Tajuddeen. Bin cike iya bincike ba'a gane komai ba, inda Sultana da ake tunani da murnar ta fara samun lafiya a wani dare tabar duniya. Dan haka kawai aka samu tana fisge-fisge da girgiza irin na firgitar wanda ya tsorata, duk da tana yin hakan dama tunda abin ya faru sai na ranar yafi na kullum. Da ƙyar doctor suka iya kwatanta ceto numfashinta, da ga ƙarshe dai tace ga garinku nan. Mutuwar Sultana ta zama kamar wata mutuwar babba a gidan, dan kowa ya koɗe ya jeme saboda kuka, sai dai halin da Mawaddat ta shiga yafi na kowa a gidan. Har asibiti ta kwanta na tsawon kwanaki kafin ta dawo dai-dai. Watanni sun ɗan sake shuɗawa har zukata suka haƙura da shiga dangana game da Sultana, yayinda jami'an tsaro ke cigaba da bincike, sai dai maimakon a cikin gidan sai hankalinsu ya fara karkata waje akan cewar ƴan hamayyane kawai sukai hakan. A ranar da Sultana ke cika wata biyu a cikin ƙasa Mawaddat ta tunkari Daddy da al'amari mai firgitarwa game da abinda ya faru da Sultana, inda ta nuna masa video data ɗauka a lokacin suna a cikin ɗaki tare da Alh. Sulaiman ga Sultana yashe cikin jini. Tare da ɗakko masa zancen da ya san bayan Alh. Sulaiman da shi sai UBANGIJI kawai suka sani, wato ɓatar maƙudan kuɗaɗe a hannunsa wanda yayanta Alh. Sulaiman ɗin ya ranta masa ya biya batare da sanin mahaifinsu ba har yanzu. Iya ƙoƙarin yayi danta fahimci gaskiyar al'amurin amma ta nuna sam bata da wannan lokacin, sai ma barazana data fara masa na in har bai aureta ba to lallai zata fallasa wannan video a gidansu dan kowa yasan yanda akai suka rasa Sultana. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa, sai dai Mawaddat ta masa mugun ƙullin da yay imani da in har bai aikata yanda take so ba tofa lallai bashi da wata mafita. Dole badan yaso ba ya amsa mata, tare da tunkarar mahaifinsu Alhaji Garko da batun yana son aure Mawaddat. Alhaji Garko yayi farin ciki, yayinda Dada tai tsalle ta dire tace sam bata yarda ba. Ankai ruwa rana sosai game da wannan aure, dan an samu rabuwar kai wasu na goyon bayan Dada, wasu Alhaji Garko da Mawaddat. Inda dai daga ƙarshe bayan an cuɗa an cuɗo ALLAH yay wannan aure da babu wanda yasan manufarsa sai ALLAH sai kuma su ma'auratan. Mawaddat ta shiga gidan Daddy da gigiwar izza da gadara, inda daya motsa zai taka mata birki tamai barazana da wannan video recording da maganar kuɗaɗe. Hankalinsa a tashe yake, yayinda Mommy da Uncle Yousuf suka kasa fahimtar halin da yake a ciki lokacin duk da yanda yake son fahimtar da Mommy amma sai kishi ya rufe mata ido ta kasa fahimtar ba dukiya ko wani matsayi bane ya sashi aikata yin auren ma kansa balle biyema iskancin Mawaddat a gidan. (Wannan shine kuskuren Mommy. Mata ya kamata mu dinga sanin kowanne yanayi da mazajenmu suka shiga koda akan mace ne. Mu dinga sassauta kishi a wasu gaɓoɓin rayuwa dan wani abun kanzoma bawa ba yanda ake kallonsa ba.) Daddy yata gwada son sace camara ɗin nan daga wajen Mawaddat sai dai a ankare take da duk wani motsinsa. A magana ta gaskiya a zamanshi da Mawaddat bai taɓa jin sonta ba kona yini ɗaya, dan ko'a harkar auratayya ita ke kiɗanta ke rawarta game da shi. Sai dai yana yin dauriyar sauke hakkinta har ALLAH yasa aka samu cikin Lulu, sanadin cikinne ma yasa shi ɗan fara sassauta zuciyarsa. Hatta da son ƙyautatama Mommy idan yay niyyar yi Mawaddat kan masa barazana, ga shi Mommy taƙi fahimtarsa, a kullum kawai tana kallon yana cutar da rayuwarta saboda ya auri ƴar masu kuɗi ƴar ogarsa. Ana baifi sati guda a haifi Lulu ba a wani dare yana tsaka da barci Mawaddat ta tashesa. Hakan ba sabon abu bane da take masa, sai dai kuma bayan tashinsa cikin ɓacin rai ya fahimci tashin yau yasha banban da wanda take masa a baya. Dan a mamakinsa ma sai gata durƙushe gabansa a ƙasa tana hawaye da neman gafararsa akan duk abinda ta aikata masa. Ta ce, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, nasan na aikata abubuwa masu yawa a gareka tare da tilastaka aurena badan kaso hakan ba. Na kuma azabtar da matarka itama ta hanyoyi da dama. Ba komai ya jawo hakan ba sai ɗunbin so da ƙaunar da nake maka har ƙasan zuciyata. Duk da inajin kishin matarka banso shigowa cikinku ta wannan sigar ba. Sai dai komai ya canja a dalilin wannan video na fyaɗe da kukaima Sultana kai da Ɗan uwana Sulaiman da kuma kuɗin daka salwantar a Companyn mahaifina bisa son zuciya kamar yanda ma samu labari. A ranar da kukaima Sultana abun nan nayi kuka kamar zan mutu tare da jin tsanarku irin wanda ban taɓama wani mahaluki a duniya ba, na saƙa abubuwa daban-daban akan ku a ciki harda shafe numfashinku a bayan ƙasa. Sai dai zuciyata ta gargaɗeni da yin hakan tare da bani shawarar na dafaku da ranku cikin ruwan sanyi. Na fara da kai ne ta hanyar maka barazana harka aureni, tare da nisantaka da matarka da nasan kana matuƙar so da ƙauna. Da farko naso na haɗa harda Yousuf, sai dai nutsuwarsa da hankalinsa yasa naji tausayinsa nama tsaya masa akan ya tafi makaranta dan bana son yaga abinda na tanada muku. Burina sai na gama da kai sannan na koma kan rayuwar ɗan uwana Sulaiman shima, daga ƙarshe na fallasaku a idon duniya ku kunyata. Sai dai duk wannan lissafin nawa ƙaddara ta canjashi Isma'il a dalilin wannan cikin da ya shiga jikina a mistake, sau biyu ina yunƙurin zubar da shi amma hakan ya gagara, a karo na biyun ma sai likitoci suka tabbatar min idan na sake zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Wannan yasa na haƙura na barshi badan naso ba. Sai dai kuma kana naka ALLAH na nashi, tashi kuma itace gaskiya. Wlhy Isma'il a ƴan kwanakin nan inajin kamar barin duniya ke gabatoni. Ji nake kamar bazan yi rayuwa mai tsaho ba. Shiyyasa na shirya faɗa maka gaskiya da neman afuwarka. Tare da baka shawarar kaima ya kamata ka fito ka sanarma iyayenmu gaskiyar al'amurin game da abinda kuka aikatama Sultana kai da Sulaiman koda bazaka faɗi maganar kuɗaɗe ba. Ku karɓi kowane irin hukunci hakan zaifi zama masalaha a gareku da zuri'arku gaba ɗaya”.
Sosai jikin Daddy ke rawa a wannan lokacin, ya kama kafaɗun Mawaddat ya tadata daga durƙushen da take ya rungumeta a jikinsa. Sai kawai ya samu kansa da sakin kuka. Itama saita shiga tayashi. Sosai sukai kukansu kafin su zauna dan bata jurar tsaiwa yanzu. Suna zaune a tsakkiyar gadon suna fuskantar juna hannunsa cikin nata ya ce,........✍️


_🚴🚴🚴🚴Dan ALLAH wazai tayani typing._



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣



.........“Wlhy wlhy wlhy Mawaddat ban aikata komai ba wa Sultana, sannan ban san yanda akai muka rasa kuɗin nan ba a cikin Company, iya bincike kuma nayi amma ban gane komai ba har zuwa yau. Yanda kike kallon al'amarin ba haka yake ba. Kinƙi bani damar na warware miki ne tun farko shiyyasa amma yau zan sanar miki komai. Sai dai dan ALLAH ina son ki fahimceni, sannan kiyi bincike dan ki tabbatar da gaskiya ta. Ina zaune a gida tare da iyalina Sulaiman yay kirana hankali tashe yana kuka. Cikin sauri na shirya na nufi Garko house da yace min yana can a zatona ma wani abu ne ya faru da Baba wlhy, kasancewata ba baƙo ba a gidan yasa kai tsaye aka buɗen gate na shiga, hakan ya ƙara sakani sake shiga ruɗani, bayan nai parking nayi kiran Sulaiman ya sanar min na zagayo ta baya sashen masu aikin gidan yana acan. Na ɗan ji mamaki, amma sai bance komai ba nace masa ina zuwa. Wannan ne karo na farko danai ta wajen, da kwantace na shiga sashen dan alokacin duk masu aikin na can cikin gida suna aikinsu. Na samu Sulaiman zaune yana kuka ga yarinya gefensa kwance ya rufa mata bargo. A lokacin bansan matsayin Sultana a gidan ba, zamma iya cewa ranar ne nai mata ganin farko dan har sannan ba wani shiga gidan nake ba Sosai ai. Cikin tashin hankali da ruɗewar da nake a ciki nima na shiga jera masa tambayoyi. Da ƙyar ya iya sanar min fyaɗe yayma yarinyar. Kuma wlhy shi bada manufar hakan ba a zuciyarsa. Yazo ne wajen yarinyar mai aikinku dan sun saba kasancewa a tare kawai sai ya samu Sultana a ɗakin, kasancewar baya cikin hayyacinsa saboda abinda wai wani abokinsa ya yaudaresa ya basa da kayan maye a ciki kawai ya afka mata dan tana masa gizo ne like yarinyar da yake zuwa wajen nata sai daga baya ya fahimci abinda ya tafka ɗin. Kuka yake riris da roƙon na taimakesa, wlhy idan wani yasan wannan al'amarin to gaba ɗaya farin cikin family ɗin ku zai ruguje. Kai iyayenku ma zasu iya rasa ransu musamman ma Baba. Dan ya ɗauki son duniya ya aza akan Sultana kamar kowa na gidan gashi bata da isashiyar lafiya. Bani na aikata al'amarin ba amma wlhy na shiga matuƙar gigitaccen ruɗani a lokacin jin yarinyar ƙanwarku ce, dan wlhy bamma san sanda hawaye nima suka fara zubomin ba. Shine ya kawo shawaran yana son na taimaka masa mu kaita can waje ta yanda in mu ajiyeta kamar wani ne yay mata za'a fi saurin fahimta a kaita asibiti, muma kuma hakan zai fi bamu damar kaita asibiti da wuri karta rasa ranta. A ɗan gajeren tunanina a lokacin sai na fahimci hakan shine dai-dai saboda a ruɗe nake ni kaina bana iya gane komai dan tashin hankali, inba hakaba kafin a farga anan tabbas za'a iya rasata. Sannan su masu aikin zai zame musu tashin hankali. Ace a sashensu abun ya faru da ƴar masu gida dolene ace su nemo wanda ya aikata. Na biyu tashin hankalin daya tabbatar min Baba da Dada zasu iya shiga koma su rasa ransu. Wannan shine ya ƙarfafani muka ɗakko Sultana cikin duhun magriba muka saka a motata muka kawota ƙarƙashin bishiyar da aka ɗakkota. Bakuma mubar anguwar ba har sai da aka ɗauketa zuwa asibiti. Ban fahimci nayi kuskure babba a bama Sulaiman gudunmawa ba sai da na dawo gida nake bama Kareema labari kamar akan wani abun ya faru. Kalamanta ne sukai matuƙar rikitamin lissafi da zama nayi nazari nima. Matuƙar damuwa na shiga, har na yanke shawarar tunkarar Sulaiman da batun akan magana ta gaskiya mu fito kawai mu sanar da iyayensa gaskiya, musamman ganin yanda aka kama maigadinsu da wasu masu aikin gidan aka rufe kuma da taimakonsa ne koma nace shine ya saka akai hakan. Sai dai mi koda nai masa zancen sai ya shiga roƙona da kalaman da suka sake rikitamin lissafi, ina tsaka da neman mafita ke kuma kikazo da naki kalar salon..”
       Kuka suka sake haɗe kai sunayi, sai da sukai mai isarsu sannan ta ɗakko masa camara ɗin ta bashi, hankalinsa ya tashi da ganin komai, dan tabbas duk wanda zai gani inba yasan gaskiya ba zai ce harda shi aka aikata, sai dai idan kai nazari a yanayin shi akwai sutura jikinsa saɓanin Sulaiman zaka iya fahimtar gaskiya. Laifinsa dai biyewa da yay aka fitar da Sultana a gidan. Roƙo sosai Mawaddat tai masa akan karya bar Sulaiman yasha ruwa a rayuwarsa akan wannan kuskuren har sai ya fito ya tonama kansa asiri, sannan maganar kuɗin Company ya binciki yayan nata sun salwanta ne da haɗin kansa, kuma kuɗin na hannunsa, dan taji suna tattaunawa da yaronsa Malami akan batun, sai dai ba komai taji ba da ƙyau gaba ɗaya. Wannan shine abinda take so ya mata koda bayan ranta. Ya tabbatar mata zaiyi amfani da shawaranta, dan yana son ya samu salama shima a ransa, hakan kuma bazata faru ba har sai ya fidda wannan ɓoyayyen sirrin da neman gafarar su Baba garko. Maganar kuɗi kuwa da tace ya bincika itama tai matuƙar girgiza masa zuciya, har ya fara shiga waswasi akan al'amura da dama game da abotarsa da Alh. Sulaiman ta rana tsaka. Kwana biyu da yin haka naƙuda ta tasarma Mawaddat, a lokacin daya samu Mommy na bata abu harga ALLAH a ruɗe yake, sannan ko Mawaddat ɗin ce tai mata haka a irin yanayin itama zai iya kawo hakan a ransa dan ya fahimci Mommy nada zafin kishi na masifa, shi da yake fuskantar ƙalubalen daga gareta shi yasan wannan saboda a zahiri da wahala ka gane tanada kishi a ƙanƙanin zama da ita. Dan ga wanda bai santa ba bazaice akwai ba, duk da yasan sun cuta mata, sannan tabbas tanada ƙyawawan halaye kishinne mai zafi kawai matsalarta, amma shi laifinta da yake gani shine kasa fahimtarsa da tayi tun farko. Lokacin daya ɗauki hanyar asibiti da Mawaddat cikin kuka dana azaba ta kamo hanunsa ɗaya ta ɗora a kan cikinta da faɗin, “Isma'il dan ALLAH ka yafe min, ka sake roƙamin matarka ta yafemin, ga amanar abinda ke cikina nan na baku, soyayya ta gaskiya daban samu daga gareka ba ina roƙonka dan ALLAH abinda zan haifa in har ya rayu shi ya samu. Kada ka bama kowa daga cikin ahalina abinda zan haifa ka riƙesa a wajenka ciki harda Dada. Idan da hali ma ka nisanta shi da su dan duk sanda Sulaiman yasan gaskiyar lamari kowane irin mataki zai iya ɗauka, kaima ka nisanta kanka daga al'amarin sa, inba hakaba wataran sai kayi dana sani, dan ƙarya yakeyi babu wani abokinsa daya bashi kayan maye da kansa yasha har cocaine yana sha dama, sannan ya jima yana lalata rayuwar masu aikin gidanmu, na taɓa tarar Dada da zancen amma bata yarda ba, sai ma balbaleni datai da faɗa akan idan taji batun a bakin wani saita ɓata min raina. Wannan dalilin yasa kaga na shige masa kamar munfi kowa shiri, amma ba haka bane ba, ina binciken abubuwa ne a kansa dan na jima ina zargin yana safarar miyagun kwayoyi a ƙasashe daban-daban musamman ƙasar Mexico, sannan yanabin hanyoyi daban-daban wajen ɗibar kuɗin baba. Na yi shirin idan na kammala bincikena na bama Baba bayanan ta hanyar gani da ido da zai tabbatar. Dan haka akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a cikin camara ɗin nan da suka shafesa sai kayi takatsantsan dan dama saboda shi na mallaketa...”
       Wannan magana ta Mawaddat ta saka rayuwar Daddy sosai a wani hali bayan rasuwarta, shine dalilinsa na hana ahalinta jaririya daya maidama suna Mawaddat, tare da nuna mata soyayyar data roƙa garesa kuma yay mata alƙawari, wadda harga ALLAH bayan rasuwar tata kuma sai yake jin soyayya mai nauyi a kanta. Sai tausayin yarinyar da ya ringa ɗibarsa kuma shima. Dalilinsa na hana Mommy Mawaddat shawarar da yaji dangin mahaifiyarta na bata ne, hankalinsa ya tashi da jin abinda suka faɗa mata akan marainiyar ALLAH da batama san minene duniyar ba, sai dai ita Mommy bata san yaji ba. Yaso yay mata uziri amma jin itama ta karɓama ƴan uwan nata da cewar ai duk abinda Mawaddat tai mata saita ramashi akan Lulu ya saka zuciyarsa a razani lokacin. Dan baiyi tunanin kishin Mommy zaisa idonta rufewaba ta karɓi shawarar ƴan uwan nata. Wannan dalilan yasa ya sake tsayawa akan al'amarin Lulu ya hana kowa jingina da ita. Sai kuma ga abinda yafi na Mommy ya ɓullo masa, bai san yanda akayi Alh. Sulaiman yasan da camara ɗin hannunsa da Mawaddat ta bashi ba, kawai a wata rana ya samesa da batun a rikice, yace ya bashi camara ɗin Please. Amma sai shi Daddy kansa tsaye yace bazai bada ba har sai Alh. Sulaiman ya sanar masa gaskiyar al'amari game da harkar shigo da kayan shaye-shaye daya tsunduma shi, sannan ya faɗa masa gaskiya akan ya akai kuɗaɗen nan suka salwanta da kuma haikema Sultana a sashen masu aiki bayan kowa ya shaida bata zuwa can ɗin sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Wani banzan kallo Alh. Sulaiman yay masa tare da masa nuni da baida hankali. A kausashe ya ce, “Isma'il kai wanene da zaka titsiyeni? Yaushe ma ka kai inda kake tunanin ka kai ɗin? Kana almajirin gidanmu dan na jawoka kaci arziƙi har kake ganin idonka yay tsaurin sanin abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login