Showing 18001 words to 21000 words out of 127646 words

Chapter 7 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

247

ni kaɗai ya shafa. To daga yau ka kama kanka. Camara kuma idan baka bayar ta arziƙi ba zaka bada ta tsiya. Sannan ita wannan yarinyar ka shirya dan dolene na hukunta rayuwarta da laifin mahaifiyarta, dan ni bana yafiya bana kuma barin bashin gaba. Sannan sabo da kaza a wajena baya hanani yankata. Ba ita data zama ɗiyar ƙanwata ba, ko ita ƙanwar tawa da tana raye saina ɗan ɗana mata azabar sanin ainahin Sulaiman, amma duk da haka wannan ƴar tata zata fansheta ne”.
      A lokacin tsawa Daddy ya daka masa, sai dai kafin yace komai Alh. Sulaiman ya bar wajen.
      Wannan ne sanadin komai da zama mafarin ɗauke Lulu daga Nigeria Daddy ya maidata Garmany ya nema mata Nanny da tunanin ya kuɓutar da ita daga sharrin Alh. Sulaiman, shine kuma mafarin duk wani rikicin dake a tsakaninsu, dan har yanzu dai camara na a hannun Daddy duk barazanar da Alh. Sulaiman ke masa yaƙi bashi ita. Ya kuma kasa gayama kowa ciki harda Uncle Yousuf da Mommy dama Baba Garko....

     Wannan kenan.
        

        *_★CANADA★_*

    Zuwa yanzu wata irin nutsuwa ce ke saukarma Lulu maiban mamaki, yayinda girman da cikinta keyi ya fara ɗaukar hankalinta. Da farko ta ɗauka tunbi ta fara tarawa, hankalinta ya tashi ta fara tunanin ko kunun gyaɗar da take shane ya kawo mata haka. Ta yanke hukuncin fara fita motsa jiki kawai da alƙawarin daina shan kumun gyaɗa duk da tasan hakan bamai yiwuwa bane. Sai dai bata san yaya zatai hakan ba dan yanzu hatta security ɗin gidan na ƙofa Alh. Sulaiman ya canja shi, idan zata fita dole saita kira Dada ita kuma ta kirashi sai yasa a buɗe. Gefe guda ga cid ko bodyguard zata kirasu ma ita bata sani ba yasa suna bibiyar al'amarin ta. Ta fahimci hakanne a randa sukai fita yin wani shopping ita da Ummita. Hankalinta ya ƙara tashi, dan zuciyarta zuwa yanzu ta fara ayyana mata abubuwa da dama. Cikin harda tunanin anya kakar tata da kawunta basu da wata manufa a kanta. Wannan shine mafarin data fara natsar da zuciyarta waje guda da hankalinta domin fahimtar abubuwa a matsayinta na lawyer. Abu na biyu shine randa ta amshi wayar Ummita da nufin kiran Daddy a karo na farko. Dan ita nata wayoyin ma ta mantosu a Nigeria tun sanda ta taho, tanata ma Dada naci akan a kawo mata sai taita cewa ta manta. Koda Lulu ta saka number Daddy ta kira sai taji Alh. Sulaiman ya ɗaga. Hakan ya ɗaure mata kai akan miya kawo wayar Daddy hannun Uncle ɗin nata, amma sai ta tsinkayi Alh. Sulaiman ɗin na ƴar dariya da faɗin,........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟

__________________

*3 DAYS CLASS*

Ko kunsan cewa duk shekara ana samun rararar kudade a turai wanda ake cewa *unclaimed scholarship funds?* Kunsan irin ayyuka Jobs da zaku nema ku samu daga Nigeria zuwa kowace kasa? Ana samun rararar kudinne sakamakon rashin neman scholarship da bama yi, mun bude 3 days class don koya muku yadda zaku samu scholarship a kasashen waje, da yadda zaku nemi karatu da yadda zaku nemi Aiki Skills or unskills Job daga gida Nigeria zuwa kowace kasa da takardun secondary diploma ko degree da yadda zaka canza kasa Relocating daga Nigeria zuwa kowace kasa, Canada, Us, etc a tuntubeni

Class ze fara gobe jumaa insha Allah

WhatsApp group 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/Ir0qcUHVd8VI3tTlCHPeIA

WhatsApp 08144147273

_______________

........“Karki cigaba da wahal da kanki wajen kiran kowa da wayar nan Mawaddat, koda kuwa Dada ce. Dan duk wanda zaki kira ni ne zakiji na ɗaga, dan lokacin da zasu san ina kiken baiyi ba”. Da ga haka ya yanke wayar ya barta da baki a sake. Na uku har gida ake kawo mata kayan shaye-shaye sai dai yanzu bata iya sha, kallon magani kawai ma tayar mata da zuciya yake yi, jima take ta tsani koda ganinsu. Na ƙarshe shine rashin dawowar Dada Canada tun tafiyarta kusan wata uku kenan. Idan sunyi waya kuma sai tace mata zatazo uziri ne ya riƙeta. Tajuddeen na zuwa gidan kusan duk bayan kwana biyu. Amma ko kallo bai isheta ba. Dan in yazo idan zai yini mata magana ko a bata furta masa har ya gaji ya tafi. Daga baya ma sai ta koma duk randa yazo kulle kanta take a ɗaki har yabar gidan baya ganinta. Duk da yanda waɗan nan abubuwan ke mata kai kawo a rai sai yanayin canjawar jikinta yafi komai ɗaga mata hankali. Da gaske fa komai nata ya canja, tayi ƙiba hallitun jikinta sun sake cikowa, ga wani mugun fresh da tayi kamar ka taɓata jini ya fito. Sai period ɗinta, duk da dama tun kan tai aure yana mata haka tai wata uku bata gani ba, idan kuma zai zo tasha wahalar ciwon mara. Tasha ganin doctors akan matsalar amma amsa ɗaya take samu shine yanayin halittar tane kawai haka lafiyarta lau. To amma a wannan karon idan fa zatai lissafi kusan watanta biyar kenan batayi ba, sai jinin data zubar na lokacin da su Dada suka zubar mata da ciki. Ganin al'amarin na neman sakata a wani hali ya sata saka Ummita ta kira mata Dada. Dada da har yanzu basu koma Nigeria ba sai dai suna shirye-shiryen hakan cikin mamaki take sauraren Lulu dake mata bayani akan rashin ganin period ɗintan. Amma ganin yanda Lulun ta tada hankalinta sai ta shiga kwantar mata akan ta bari zata turo mata Dr Olivia ko kuma ta shirya suje asibitin su sameta. Ɗan son fita da take ne yasata cewa gwara su sametan to. Sai Dadan tace to bari ta samu Alh. Sulaiman da maganar. Kasa shiru Lulu tai ta jehoma Dada tambaya akan miyasa yanzu komai nata sai Dada tace sai Uncle Sulaiman ya sani. Ita kanta Dada sai hakan ya tsikari zuciyarta, rashin sanin ƙwaƙwƙwarar amsa ya sata faɗin Lulun ta bari har sai tazo zasuyi wannan maganar. Badan Lulu taso ba tayi shiru.
       Sunje asibiti sun sami Dr Olivia, inda akaima Lulu gwaje-gwaje da duk suka dace, babu wani wahala aka gano ciki ɗan watanni biyar a mararta sai dai kwanakin sa sun ɗan koma baya kaɗan, hakan kuma nada nasaba da yunƙurin zubar da shi da akayi kenan. Ba Lulu ba hatta Dr Olivia ta shiga ruɗani, dan al'amarine da bata taɓa cin karo da shi ba. Saboda tabbas ita shaidace sun zubar da cikin Lulu, sun kuma tabbatar da hakan, amma a yanzu ace musu kuma a kwai shi gashi yana rayuwa cikin ƙoshin lafiya. Dada ma da taji al'amarin hankalinta ya tashi, ta kira Alh. Sulaiman a rikice ta sanar masa. Tamkar wani sumamme haka ya daskare a waje ɗaya, har Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen da suke tare a lokacin na tambayarsa ko lafiya? Bai iya cemata komai ba face furzar da wata irin iska mai zafi daga bakinsa ya miƙe ya fita. Kaɗan ta taɓe bakinta tare da binsa da kallo, gaba ɗaya kwanakin nan ta gagara gane kan mijin nata, iya tambaya da lallaɓa tayi shi kuma ya dage mata akan babu komai.....

     Wani irin rikicewa da daburcewa Dr Olivia tai lokacin data juyo sukai ido huɗu da Lulu da bata san tana bayanta ba. A yanda taga Lulun kuma ya tabbatar mata taji wayar da tai da Dada. Cikin harshen turanci take ma Lulu magana harshenta na sarƙewa. Hannu Lulu ta ɗaga mata kawai alamar bata son jin komai, daga haka ta bar wajen cikin tangaɗin hajijiyar da take ji na kwasarta. Amma koda ta fito sai ta sauya yanayinta saboda bodyguard ɗin da Alh. Sulaiman yasa suke biye da su. Magana taima Ummita akan tazo ta rakata restroom. Ganin ɗaya daga cikin b.g ɗin na ƙoƙarin biyosu ta kallesa sheƙeƙe da faɗin “Can ɗin ma sai ka bimu. Ko an faɗa maka ma na gama abinda nake a asibitin!”. Tsayawa yay kansa a ƙasa dan ya fahimci masifar Lulu tafi tashi.
         Tsaki taja da sake ɓalla masa harara sannan taja hannun Ummita. Ba restroom ɗin suka shiga ba, da ga can gefensa suka tsaya, karo na farko a rayuwar Lulu da taji ya cancanta ta sanarma wani damuwarta, dan zurfin ciki babbar ɗabi'arta ce shiyyasa abubuwa da yawa sukai mata nauyi a zuciya.
     “Ummita so nake na gudu”.
“Sosai Ummita ta waro idanu waje, sai kuma ta kalla inda Bodyguard ɗin nan da Lulu bata lura ya dai biyosun ba a laɓe, ƙasa Ummita takai kamar mai son gyarama Lulu takalmi, dan Ummita wayayyar mace ce da taga jiya taga yau, hasalima tashin ƙauye ce ita, daga baya ta dawo wajen yayarta a cikin Kano, sai dai matsalar data fuskanta ya sata komawa Abuja a yanzu.. “Aunty karki ruɗar da kanki dan munafukin nan ya biyo mu. Muyi tamkar takalmin nake gyara miki”. Lulu ta fahimceta dan haka hankalinta ya sake tashi. Amma sai Ummita ta ce, “Karki tada hankalinki zamu samu mafita. Aunty tsakanina da ALLAH nake jin ƙaunarki a cikin raina, saboda kin min abinda bazan taɓa yarda a cutar dake ba. Nima halin da kike a cikin gidan nan na tada min hankali. Na kasa tunkararki da batunne saboda ina jin tsoron karki kasa fahimta ta. Sannan ke kanki kin kasa gane tamkar anyi kidnapping ɗinki ne anzo an ajiye anan. Dan gaskiya akwai manufa a al'amarin kawun nan naki a yanda nake lure da shi, na fahimci hakanne tun sanda aka zubar miki da ciki da ɗauke passport ɗin mu da yayi”.
     Lulu dake jin hawaye da wata matsananciyar tsanar Alh. Sulaiman ta cika mata zuciya ta ce, “Nima na fara jin haka a raina Ummita, sai dai gani nake mizaisa Dada a matsayinta na grandma ɗina ta aikata hakan, shiyyasa kawai nake hora zuciyata da ƙin yarda. Amma a yau zuciyata ta kasa karɓar al'amarin, cikin da suka zubar ashe bai fita ba”.
      Da sauri Ummita ta ɗago tana kallonta. Lulu ta gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, “Yana nan Ummita, kuma wlhy naji ina matuƙar son sa. Idan har kakata nada manufa a kaina itada Uncles ɗina dama family ɗina duka ashe bani da babban abinda ya kamata na runguma sama da wannan cikin, yafi kowa kusanci dani a yanzu, banda uwa, banda ƙani, banda yaya. Daddy na da Uncle Yousuf sun fifita soyayyar wani a sama da tawa. Wlhy a yanzu-yanzu Ummita naji ƙauna da soyayyar abinda ke cikina harda zumuɗi da fatan zuwansa duniya lafiya, a wannan karon bazan bari su taɓamin shi ba, ina son na rayu da shi, bana son na rasashi ko shi ya rasani kamar yanda na rasa mahaifiyata”. Sosai Ummita taji itama hawaye na cika mata ido. Miƙewa tai tana murmushin yaƙe dan har yanzu munafukin na laɓe, sai dai bazai iya jin abinda suke faɗa ba. Hanya ta nunama Lulu alamar su koma tana ɗan murmushin yaƙe. “Muje restroom ɗin karsu fahimci wani abu, ina son ki kwantar da hankalinki ko'a fuska kada ki nuna musu kina son cikin balle yunƙurin guduwa. Na miki alƙawarin kozan rasa raina zan taimakeki. Dan nima kin min abinda bazan taɓa mantawaba, wanda shine dalilin amsar wannan aikin da nayi a lokacin da na ganki cewar kece wadda zan zauna da ita anan”. Sosai Lulu kema Ummita kallon mamaki, amma sai Ummitan tai mata murmushi kawai. Restroom ɗin suka shiga, Lulu ma sai tai fitsari sannan suka fito. Ganin sun nufo hanyar dawowa bodyguard ɗin nan yay saurin yin baya yana sanarma Alh. Sulaiman cewar gasu nan zasu dawo da gaske restroom ɗin suka shiga. Sarai Ummita taga waya a kunnesa, hakan ya sata sake gaskata zarginta. Sun koma wajen Dr Olivia wadda suka sameta tana waya da Dada. Dan haka Lulu ta laɓe tana saurarenta. Dr Olivia da bata lura da Lulun ba ita cikin harshen turanci ta cigaba da faɗin, “Idan akace sai an fidda cikin nan a wannan gaɓar akwai babbar matsala, dan za'a iya taɓa lafiyar ta ɓangarori da dama, koma a rasata baki ɗaya. Kawai Mrs Garko kuyi haƙuri ta haifi abinta. Amma dai har na mutu bazan daina mamaki da al'ajab ɗin wannan al'amarin ba, harma na sakashi a cikin manyan record namu na ban mamaki da suka faru a asibitin nan. Sannan zanyi bincike mai ƙarfi akai dan tabbatar da daga ina aka samu matsalar”.
          Shiru alamar tana sauraren Dada itama, sai kuma ta nisa da cewa, “Shike nan sai kin shigo ɗin”. Daga haka ta yanke wayar. Haɗiyar zuciya Lulu ta dingayi cikin wani yanayi, kafin ta saita kanta da ƙyar ta nufi cikin office ɗin. Murmushin da Dr Olivia ta gani a fuskar Lulu ya ɗan sata jin relief, ta rubuta mata magunguna da abubuwan da ya kamata taci dan inganta lafiyarta data abinda ke cikinta. Lulu tai mata godiya ta fito akan zata cigaba da zuwa awo. Koda suka fito a asibitin sai da suka tsaya sukai ɗan shopping sannan suka wuce gida. Sun samu Tajuddeen yazo, amma kamar yanda Lulun ta saba kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta tare da wucewarta ɗaki tana amsa masa gaisuwar da yake mata a taƙaice. Tajuddeen da yake jin kamar ya fasa kuka ya sauke numfashi mai nauyi tare da dafe saitin zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri, da gasken gaske yake ƙaunar Lulu, soyayya yake mata mai zafi wadda shi kansa wani lokaci yana jin abun na neman fin ƙarfinsa. Bai taɓa jin koda ɗigon sonta ya ragu masa a rai ba duk da cin kashin da take masa. Hasali ma duk abinda tayi sai ya zama shi birgeshi take yi tare da ƙara jin sonta a ransa. Burinsa ya mallaketa matsayin matar aure, ta zama uwar ƴaƴansa, randa yaji ta ɗauki cikin wani ba nasa ba har hawaye yayi, dan ƙarshe ma sai da ya ga likitansa.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣



.......Kasancewar Tajuddeen a gidan ranar ya hana Ummita da Lulu sakewa, dan itama dai Ummitan irin mutanen nan ne masu tsantseni akan addini da rayuwa, balle kuma itama ɗin dai tanada tabo irin na Lulu, koma muce ya zarce na lulun tunda ita an riga an keta mata nata mutuncin a sanadin fyaɗen ma harta haifi ɗa sai dai a yanzu babu shi a raye, abin takaicin kuma mijin yayarta data riƙeta ne wanda ta taso tanama kallon tamkar uba ta aikata mata hakan. Sannan tanada matuƙar wayo da lura akan al'amura na rayuwa. Lulu data rufe kanta a ɗaki saboda kasancewar Tajuddeen ɗin tana shiga saman gado ta kwanta tai shiru cikin nazarin abubuwan da suka faru a yayin fitar tasu yanzu. Sai kuma kamar wadda aka tada ta tashi zaune zuwa gaban mirror ta nufa, kanta ta ƙurama ido na tsawon lokaci, kafin takai hanunta ta ɗage rigarta gaba ɗaya ta ƙurama cikinta da ya ɗan turo kaɗan idanu, sai kuma ta kai hannunta saman shi a hankali ta lumshe idanunta hawaye na ciko mata su, ɓul-ɓul taji ya harba tamkar abin shiri, da sauri ta buɗe idonta da hawaye suka cika taf tana kallon saitin daya motsa ɗin, sai kawai ta saki dariya mai haɗe da kuka. Dan abu uku ne ke mata kai-kawon. Wai ita Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi ce ɗauke da ciki na haihuwa, abinda bata taɓa kawowa a jerin tunaninta ba na rayuwa. Duk da kuwa tanada masifar son yara a rayuwarta, amma bata taɓa kwatantasu gareta anan kusa ba ace matsayin ga nata ba a dalilin tsanar maza da tayi a rayuwarta. Sai kuma wata hikima ta UBANGIJI da ikonsa gashi a yau itace aka tabbatarma zata haihu ɗan mutum matsayin mallakinta. (Mallakinku dai ke da ubansa) wata zuciya ta ayyana mata. Idanunta dake a rufe tai saurin sake buɗewa, dan abinda zuciyar tata ta tsikaro mata yay matuƙar dakar ƙirjinta. (Aliyu) ta sake ayyanawa a zuciyarta tare da kaiwa zaune a kujerar mirror ɗin tamkar cikin gajiyawa. Sai kuma a fili kamar wadda aka tunzuro ta furta, “Ai har abada bama zai san da cikin ba balle zuwansa duniya ko rayuwarsa Mtsowww!!” ta miƙe a ɗan hasale. Kokawa ta shiga yi da zuciyarta akan abinda take ta ƙoƙarin sake tsikaro mata game da Smart ɗin. Cikin tsawa-tsawa kamar zararra tace, “Please and Please bana son damuwa a beg”. Ta ƙara jan tsaki ta shige toilet. (Ni sai ma taban dariya sai kace wadda keyi da wani a gabanta😂🤳).
          A haka Lulu ta ƙarasa wannan yini cikin wani irin yanayi mai wahal fassara a gareta ita kanta. Sai dai jaɗan-kaɗan hannunta na saman cikinta, yayinda zuciyarta ke cigaba da kawo mata al'amari mai nauyi dangane da kakarta da kawunta da sukaso rabata da shi batare da ko sau ɗaya sun taɓa tunkararta da batun tana da ciki ba ko tunanin zata so abinta. A ganinta wannan babban taka hakkin ɗan Adam ne ai, sannan bataga minene dalilinsu na zubar mata ɗin ba. Dole tana son tasan dalilinsu musamman ma Uncle Sulaiman data rasa dalilinsa na shishshigema rayuwarta a yanzu. Tunda a baya ita dai takan ma haɗa watanni bata ganshi ba. Ganin damuwa na neman cinkushe mata rayuwa ga kayan shaye-shaye sun gagareta sha a yanzu balle tasha ta manta damuwarta ya sata tattare tunanin ta ajiye gefe. Sai ma wani ɗan murmushin takaici ko damuwa za'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login