Showing 87001 words to 90000 words out of 127646 words
janye jikinsa amma taƙi barinsa, sai ma baya yake tana binsa har suka faɗa saman sofar ɗakin. Bata daina ba duk rokon da yake mata sai da ta tabbatar ya jigata sannan ta barshi tare da faɗawa kansa suna dariya su duka.
“ALLAH ke muguwa ce”.
Ya faɗa yana ja mata hanci. Amsa ta bashi da “Ai kai ka koya min dan kaine malamin koya mugunta ma”. itama tana dungure masa kai. Sai suka sake ƙyalkyalewa da dariya.
“Kin fara nauyi ALLAH, ɗaga ni karki fasa min ciki”.
Fuska ta ɓata da duban kanta, sai kuma ta hararesa da faɗin, “Ta ina na ƙara ɗin? Ni ALLAH bana son sharri”. Kallo ya bita da shi irin a ɗan ɗagen nan, sai kuma ya nuna mata yana gimtse dariya. Inda ya nuna ɗin ta kalla. Da sauri tace “ALLAH zai saka min” tana kai masa duka da filo. Ƙoƙarin riƙewa yake tana dariya da faɗin, “Daga faɗar gaskiya. To shikenan na yarda baki ƙaraba. Ƴar ƙanwata na nan yanda take ƴar sawalwala abinta cas-cas”. Sauka tai da ga jikin nasa ciki nuna irin nayi fushinnan, shima sai ya miƙe da sauri ya riƙota tare da ɗagata gaba ɗayanta suka fice a ɗakin. Tana zille-zille da faɗin ya sauketa bai kulata ba ya fita ta baya inda swimming pool ɗinsu yake. Direta yay a bakin ruwan ya cire bathrobe ɗin jikinsa yay hanging a kan ɗan ƙarfen da aka saka domin hakan kawai dama. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallonsa, dan har yanzu ta kasa iya daina jin kunyarsa, duk da bawai haka nan yake ba akwai ƙaramin boxer jikinsa bazata iya jurar kallon nasa ba kai tsaye a haka. Shima komai baice mata ba sai murmushi da ya saki kawai, cike da kwarewa yay tsalle da sufa irin na masu wasa da ruwa cikin ruwan. Yanda ya fantsama ciki sai da ruwan ya tarwatso mata a jiki har a fuska. Fuskar ta kwaɓe tana kallonsa kamar zatai kuka, shi baima san tana yi ba sai da ya kai ƙarshe zai juyo ya kula. Dariyar mugunta ya kwashe da shi, sai kuma yay ƙasa cike da kwarewa ya sake dawowa gabanta ya miƙe tsaye yana dariyar da ɗibar ruwan a hannu ya sake watsa mata a fuskar. Lulu ba haƙuri idan akai saita rama. Hannu takai itama zata ɗibo danta rama ya fisgota ta faɗo ciki. Kokawa suka fara a ruwan yana kunnata da dariya, sai kuma yay mata gwalo yay ƙasa cikin ruwan. Itama da sauri ta nutse ciki ta bisa saikace wasu kifaye...
Sun jima a cikin ruwan suna nishaɗin su kafin suka fito saboda tunawa da AA shi kaɗai a ɗaki. Bathrobe ɗin da yazo da ita ta saka, sannan taje ta ɗakko masa wata shima. Tun shigarta ɗakko masa rigar ta samu AA ya tashi, dan haka bata zauna jiransa ba ta juya ciki. A ɗakin ya sameta tana cirema AA kaya, yana ganin shi ya shiga miƙa masa hannu dan yanzu ya daina masa ƙiwa. Shima cikin farin ciki ya ɗauki abunsa yana mai sumbatarsa da faɗin, “Oh oh Baban Ammah ya tashi kowa ya ɓoye kayansa kafin a cika musu aiki”.
Cikin dariya Lulu tace, “Aikam dai, dan yanzu zai fara haɗa gwaramar tasa”.
“Ai ke ya gado, dan Uncle Yousuf ya cemin kema kina ƙarama hummm”.
A shagwaɓe ta ce, “Shi Uncle You ɗin ya faɗa, ni dai ALLAH babu ruwana salaha da ni, sai dai kai dan dama Ammah tace tasha rashin jin ka”.
Shima fuskar ya ɓata da faɗin, “Sharri ba haushi zanji ba ai” daga haka ya nufi bedroom da AA a kafaɗa domin yimasa wanka. Dan yanzu in har yana gida kusan komai shikema yaron, acewarsa yana koyane koda ta haifo ƴan uku basai sunje neman Nanny ba. Takan hararesa kawai idan yace hakan.....
★ Zaune suke a wajen cin abinci yana cin abincin da tai masan idanunsa a lumshe alamar dai yana jin daɗin sa, itako sai murmushin farin ciki takeyi. Dan a yanzu babu abinda ke sakata a farin ciki sama data gansa cikin farin ciki. Batai zaton zaici abincin haka da yawa ba, sai gashi ko yaci sosai har yana faɗin jikinsa yay masa nauyi. Bayan ya kammala ta gyara wajen suka koma falo. Zama yay yana wasa da AA ita kuma ta kwashe kayan da ya shigo da su zuwa ciki, na kitchen kuma takai kitchen. Sosai taji farin cikin ganin kayan sakawa ne ya siya mata, sai turarruka na mata masu daɗin ƙamshi duk da tazo da su khumra da turarrukanta abinta. Sai kayan kwalliya da batazo da su ba, shima AA an saya masa nasa. Tana cikin kwashe kayan taci karo da camara. Tsai tai tana kallo da jujjuyata a hannu, sai kuma ta ajiye cikin taɓe baki ta cigaba da gyara kayan. Sai da ta kammala tsaff ta ɗauka camara ɗin ta koma falo da ita. Kwance yake a ƙasan carpet yana waya da Ahmad, AA na gefensa yana wasa da kayan wasansa, yanda ya nutsu sosai ya tabbatar mata da magana suke mai muhimmanci, dan haka ta kai zaune Camara ɗin a hannunta tana kallonsa shi da AA ɗin cike da jin farin cikin su ɗin duk nata ne fa. Abinda ya ɗan fara jan hankalinta ga wayar tasa shine kalmar daya ambata cikin yanayin ɗan ƙaraji har yana tashi zaune. Sosai ta zuba masa idanu, yayinda shi kuma ya cigaba da faɗin, “Kaga Ahmad relax please. Karka ruɗar da kanka, ni dama nasan dolene wannan binciken ya tono mutane da yawa a ciki, aiba abin mamaki bane ba hakan karma ka tada hankalinka a banza. Yanzu abinda zamuyi shine dole mu tafi mataki na biyu, wato plan B.”
Cikin matsanancin ruɗani da ga can Ahmad ya ce, “Dole ne hankalina ya tashi Aliyu. Mahaifin aunty Khadijah fa! Kasan kuwa yanda nake ganin mutunci da kimar mutumin nan, amma ace har da shi a cikin mutanen nan. Kasan kuwa irin muggan miyagun kwayoyin da yaron nan ya sanar min ana saidawa a pharmacy ɗin nan! Ban taɓa sanin haka ƙasar nan tamu ta lalace da rashin doka da bin ƙa'ida ba sai yau. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”.
“Humm Ahmad kenan kana wasa da mutanenmu. Abinda yasa kake ganin irin waɗan nan abubuwan abin mamaki saboda rayuwar daka tashi ne. Amma mu da aka haifa a getto eria muka rayu a ciki munsan irin waɗan nan abubuwan fiye da yanda kake zato, kawai dai mutum dan baida ƙarfin ɗaukar matakine shiyyasa. Ni dai abinda nake so da kai yanzu dolene fa ka sake ƙara ɓoye kanka, dan ko Yaya Hameed da Uncle Yousuf ban san susan da hannunka a ciki, shiyyasa ma kaga nace Uncle Yousuf ɗin yabar komai a hannuna shima saboda suma suna huɗɗa da mafi yawan manyan ƙasar, zamu iya zuwa gaɓar da al'amarin wani zai girgizasu su buɗe mana aiki”.
“Hakane Smart na fahimceka yanzu, kuma in sha ALLAHU zamu basu mamaki, tabbas mune matasa ya dace muyi hanƙoran gyara ƙasar nan tamu akan wannan mummunar safarar dake cigaba da yaɗuwar gurɓatamu tamkar wutar jeji a kasarmu, in ba haka ba sai anzo lokacin da babu wani matashi da zai iya amfanar kansa balle wani ko ƙasar, zasu cigaba da mana illa ta hanyar dafe madafin iko su barmu da raɗaɗin shan miyagun ƙwayoyin da suke mana safara mu kuma muna sha da tunanin rage raɗaɗi, wlhy Smart naji na tsanesu, natsanesu, su azzalumai ne.....” Kukan da ya tahoma Ahmad ya hanashi ƙarasawa, shiru kawai Smart yay yana saurarensa shima zuciyarsa na ƙuna. Tuni idanunsa sun gashe zuwa jajur. Yana jin raɗaɗi fiye da wanda Ahmad yake ji, tun yana yaronsa ya tsani shaye-shaye, baya son yaga anayi, yana jin ciwo matuƙa idan yaga matashi ya lalata rayuwarsa da shaye-shaye, shiyyasa cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin Lulu yay tasiri a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya furta, “It's okay Ahmad. Kuka bashi ne magani ba, aiki tuƙuru domin ganin mun karya su. Sannan inaga dolene zamuyi amfani da ƙungiyar Mawaddat a wannan gaɓar domin tattarro hankalin matasa dan wannan aikin yana son taron dangi ne. In ba hakaba zaƙulosu da muka ɗauka ɗammarar yi bazai magance mana matsalar ba tunda zasu iya sayen hukumomi da kuɗi kasancewar wasu a cikinsu suma ruɓaɓɓune”.
“Tabbas haka ne nima nayi wannan tunani, kuma na yarda da shawarar nan naka. Sai dai yanzu ban san yaya zamuyi ba tunda kaga ita tana nan”.
Cikin ɗan ɓata fuska da kallon Lulu ta gefen ido ya ce,,......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣
.......“Ni kuma gashi gaskiya bazan iya baku Matana ba yanzu dan kaima dai kasan ango nake”.
Dariya Ahmad ya kwashe da shi da faɗin, “Ɗan iska shegen sama. Banza ta faɗi ko anata kwasar romon dimakuraɗiyya. Sai kaita riƙo ai ko tana nan zata mana aiki”.
“Shegen sa idon ka dai a kanka zai ƙare. Sai dai fa daga nan ɗin dan mai kawo min mata Nigeria yanzu ban gansa ba”. Ya ƙare maganar yana kashema Lulu dake kallonsa ido. Kanta ta ɗauke tana ɗan murmushi da harararsa. Dan ita ta ƙagara ya kammala wayar ya mata bayani. Sun sake tattaunawa sosai da Ahmad ɗin kafin suyi sallama. Yana yanke wa kiran Uncle Yousuf na shigowa. Tashi yay yabar falon ma gaba ɗaya, Lulu ta bishi da kallo cikin jin tsarguwa. Bai jima ba sai gashi ya dawo. Ganin yanda ta turɓune fuska ya sashi zuba mata ido.
“Lafiya kuwa Madam?”.
Baki ya taɓe da ɗauke kanta gefe. A hankali ya kai zaune kusa da ita yana mai kamo fuskar tata. “Please miya faru kar kiyi fushi mana.” harara ta sakar masa da buge masa hannu tana son tashi, yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. Rungumeta yay da ƙyau ta yanda bazata iya tashin ba. Cikin tallafo kanta da ɗaura goshinsa a saman nata ya ce, “Please Baby luv, kin san fa da fushinki gara kawai a tada yaƙin duniya na uku. Faɗamin minene?”.
“Ba kai bane kake ta wani ɓoɓɓoye abu dan kar naji”.
“Haba ni na isa. Kikama san Aliyu ciki da bai ɗinsa balle abinda ke a zuciyarsa. Dama fa zan yi maganar dake”.
“Babu wani ban yarda ba. Bayan tun randa mukazo kaketa wani magana da Ahmad a cuccure, hakama idan Uncle Yousuf ya kiraka sai ka koma gefe ko Daddy”.
“To yi haƙuri bazan sake ba. Bani ɗan lokaci yanzu zan miki bayanin komai dan kema kina daga cikin tawagar ai. Dama ba'azo gaɓar da naki aikin zai fara bane kawai shiyyasa. Haɗamin coffee yanzu ina zuwa”.
Babu musu ta miƙe zuwa kitchen, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya tashi yana sauke ajiyar zuciya. Bedroom ya shiga, babu jimawa ya fito ɗauke da laptop a hannu da Flash drive kusan huɗu. Centre table ɗin falon ya jawo gabansa sosai yana kaiwa zaune da zube kayan hannunsa, sai lokacin idonsa ya sauka akan camara ɗin data ɗakko. Ɗauka yay ya ajiyeta a gefe yana girgiza kansa, sai gata ta fito ɗauke da ƙaramin tray da coffee 2cups sunata turiri.. gefensa ta zauna tana ajiye masa nasa gabansa itama ta ajiye.
“ALLAH yay miki albarka”.
Ya faɗa yana ƙoƙarin saka flash a jikin Laptop ɗin. Cikin jin daɗi da farin ciki ta amsa masa. Dan a duk lokacin da yace ALLAH yay mata albarka tana matuƙar jin kanta on top ne. Sai da ya gama saita komai ya kalleta. “Ina son ki nutsu sosai dan maganar da zamuyi mai matuƙar muhimmanci ce”.
Kanta ya jin jina masa da sake maida hankali garesa sosai. Cikin nutsuwa shima ya fara mata bayani ta yanda zata fahimta tun daga randa Daddy ya fara aiki a maikatar da Alhaji Sufi Garko ke shugabanta, wanda a dalilin haka ne ya ja Daddy a jikinsa, a maimakon aikin gwamnati ya maidashi akan harkokin kasuwancinsa. Yanda abubuwa suka dinga tafiya har zuwa sanda kuɗi suka ɓata da shiga jikinsa da Sulaiman ya farayi ta hanyar nuna masa zai taimakesa da kasuwancin da suka fara tare har zuwa sanda ya fahimci abinda ke cikin business ɗin da haduwar Daddy da mahaifiyarta, da abinda ya faru a dalilin aurensu, fyaɗen da Alh. Sulaiman yay ma Sultana da yanda Daddy ya tayashi ɓoye sirrin zamansa da mahaifiyarta, rasuwarta, mutuwarta, ɗauketa a Nigeria har zuwa girmanta, shigowa rayuwarta da yayi dama kamun da Alh. Sulaiman yay masa har zuwa aurensu da buɗe musu ciki da Daddy yayi akan komai da dalilinsa na ɓoyewa. Yanayi yana nuna mata abubuwa a laptop ɗin nashi, yawanci duk wayoyin barazana ne, da wasu harƙalloli tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman ne, dama hotunan abokan da sukai huɗɗar kasuwanci da Daddyn ya adana matsayin hujjar da ya dinga tsorata su Alh. Sulaiman da tawagar su Nakowa da ita. Tunda ya fara Lulu ke kuka na tashin hankali, har takai AA ma ya fara kuka sai da Smart ya ɗaukesa ya ɗaura a cinya. Jikinta tsuma yake matuƙar tsuma, idanunta sun masifar kumbura saboda kukan da taci. Cikin damuwa ta ce, “Na cikin camara ɗin ma dan ALLAH ka nuna na gani”.
“Ba yanzu ba”.
Ya faɗa yana jawota jikinsa ya rungume cikin lallashi. Sai ta sake tsage masa da kuka. Muryarsa a raunane shima kamar zai saki kukan ya ce, “Please mana ya isa kukan haka kinji, mugodema ALLAH tunda babu abinda ya faru da shi. Duk da ina ji a jikina da saka hannun Sulaiman a zuwan Felix gareki, hakama su Alace da Luna da suka koya miki shaye-shaye ina zargin sakasu akayi mawaddat duk da dai bani da tabbaci.”
Kanta ta sake turawa a jikinsa tana kuka mai cin zuciya. Duk sai hankalin Smart ya sake tashi. Dole ya rufe laptop ɗin ya maida hankali a lallashinta da bata baki. Duk yanda taso suga abinda ke a cikin camara ɗin a yau yaƙi yarda. Da yaga ta damu sai yace mata dole sai an kwashe abinda ke cikinne zuwa flash shiyyasa. Badan ta yarda da shi ba ta haƙura, sai dai ta ɗauka waya tai kiran Daddy. Yanda yaji tana kuka shima sai hankalinsa ya tashi, cikin ruɗewa ya shiga lallashinta da tabbatar mata tayi haƙuri zuwa gobe zai shigo birnin London shi da Uncle Yousuf. Hakan ya ɗan sakata jin sassauci, dan babu abinda tafi buƙata a yanzu sama da taga Daddyn a kusa da ita. So take ta sake tabbatar da babu abinda ya samar mata shi. Uncle Yousuf ma ya amshi wayar ya lallasheta, hakan ya ɗan ƙara saka mata jin sauƙi, bayan ta yanke wayar ta shige jikin Smart tana hawaye. Murmushi yay yana mai ɗagota, cikin zuba mata idanu ya kai lips ɗinsa kan nata a hankali. A nutse ya canja yanayin nasu zuwa wani abu daban, babu kunya a falon akai yaƙin ƙasa-da-ƙasa, sai dai ƙura ta lafa kuma ta koma jin nauyi. Shi kuma yana mata dariya da tsokana wai dama abinda take so kenan ashe. Itama dai yanzu ta zama babbar mayaƙiya. Tashi tai ta bar masa falon bayan ta gama mimmitsinesa da bubbuga masa filo. Da kallo ya bita yana mai jin ƙarin ƙaunarta mai faɗi da girma na sake mamaye sa tako ina. Da ga ƙarshe ya miƙe da ƙyar ya bita bedroom ɗin. Bathroom ya nufa inda yake jinta sukayo wankan tare. Shine ya koma falon ya ɗakko AA da ke barci. Suma dai kwanciyar sukai domin hutawa ransu.....
*_NIGERIA_*
Sau biyu ana ɗorata amma ƙashin ya gagara zama saboda tanada ƙiba, gashi a cinya ta karye. Su kansu malaman asibitin lamarin neman fin ƙarfinsu yake. Ƙaninta dake tsaye kan lamarin nata ne ya yanke shawarar su nemo masu ɗorin gargajiya. Dan mijinta tunda yazo zuwan farko asibitin yaji irin sambatun da takeyi da tona ma kanta asiri ita da aminiyar tata da ayanzu kowa ke kira da Dodo ransa yay masifar ɓaci. Ashe itace ta rabashi da matarsa mai sonshi dan ALLAH tun bashi da komai, sannan ta rabashi da manyan ƴaƴansa da sam yanzu ko kallon arziki bai musu da ma danginsa. Hatta da karatunsu bai saka hannu ba gashi yanzu duk ALLAH ya tallafesu sun samu ayyukansu. Ranar yayi kuka da hawayensa da yin dana sani. Yana zaune da matarsa lafiya ƙyale-kyalen Naqiba da suka haɗu a wajen aiki ya kwashesa har yana kushe matarsa akan bata iya komai ba sai gidadanci saboda kawai batai zurfi a ilimin boko ba. Shagalin biki akai na alfarma lokacin ya zubda kuɗi tare da sakata a danƙareren gidansa da ya gama gini. Itace ta gaban mota idan zai fita, itace ta zuwa jahohi idan aiki ya kaisa, acewarsa itace mai ilimi. Duk da bawai wani mahaukacin kuɗi ne da shi ba yanada rufin asirinsa dan har Saudiyya yaje kusan sau uku, kuma duk tare da matar son nasa Naqiba. Yakan je Dubai kuma saro kaya a yanzu haka, dan yanada manyan shaguna a cikin kasuwar kwari. Yakan yima Naqiba abu sau sama da goma kafin yayma matarsa da ƴaƴansa, a haka har suka haihu ɗaya da ita, dan Maheer kawai ta haifa sai mace ita kuma ta rasu tun tana 3years....
An sake ma Hajiya Naqiba ɗorin gargajiya da taci