Showing 105001 words to 108000 words out of 127646 words

Chapter 36 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

274

ko arziƙin ta saka ɗin ma bata da. Jiki a saɓule ta saka tana mai karanto sunayen ALLAH a ranta, zuciyarta fal tunanin mi yaje yayo a wajen doctor ɗin. Rashin amsa ya sata jan bakinta tai shiru. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, ya ɗauki ɗansa yay shigewarsa. Sai itace ta taimakama aunty Bilkisu da Iya Tabawa data fito dan ita suka bari a gidan. Baya falo sai AA kawai da ya fara karakainar ɓarnar da yafi ƙwarewa a kai. Da'alama anan ya ajiyesa ya shige. Dole ta cigaba da daurewa suka zube a falon suma. Suna nan zaune ya fito cikin shirin fita, tayi mamaki dan tasan a irin wannan lokacin yana a gida baya fita ko ina. Tana son masa magana tana tsoron ya yaɓa mata mai zafi. Duk da dai bai taɓa kwatanta hakan a gaban wani ba. Aunty Bilkisu ya cema tasha magani ta kwanta, da ga haka ya ɗauki AA suka fice.  
       “Wai shi wannan mike damunsa? Naga tunda ya gama wayar nan ya wani canja gaba ɗaya kamar wanda ke'a cikin ɓacin rai?”. Aunty Bilkisu ce mai maganar tana kallon Lulu. Murmushin ƙarfin hali ta saki da faɗin, “Ƙila wani abu mara daɗi aka faɗa masa a wayar aunty, kin sanshi da zurfin ciki. Idan bashi yaso a sani ba ba faɗa zaiyi ba”.
      “Aike naga ma da sauƙi Mawaddat. Amma a sanin da naima Hydar akan shiru-shiru banyi zaton zai iya sakewa da mace haka ba. Dan da idan yana abu saika ɗauka yana jin ƙyanƙyamin mutane ne ma. Ka faɗa masa magana ashirin ya baka amsar ɗaya sauran in zata kasheka ne ma ta kasheka babu ruwansa”.
    Dariya zancen aunty Bilkisu ya bama Iya Tabawa. Lulu ma sai tai murmushin ƙarfin hali kawai....

         Tsahon lokaci basu dawo gidan ba. Lulu ta kasa samun nutsuwa sau uku tana kiran wayarsa bai ɗaga ba. Sai da ta gama galabaita da rashin dawowar tasu sannan sai gasu. Iya Tabawa ce ta amshi AA da yay barci, shi kuma ya shige ciki abinsa bayan ya ajiye musu abinda ya shigo da shi ya shige da sauran ciki. Taja mintuna kafin ta tashi tabi bayansa, dan ita dai kam da wannan fisge-fisgen gara ayita ta ƙare kawai yamayi komi zai yi yafi mata sauƙi. Ta samu har ya shiga wanka, dan haka ta zauna bakin gado zaman jiran fitowar tasa. Zuwa can kuwa sai gashi ya fito da bathrobe a jiki yana faman goge kansa zuwa wuyansa da ƙaramin towel. Kallo ɗaya yay mata ya kauda kansa. Gaban mirror ya ƙarasa ya fara shafa mai, dan haka ta taso jiki a saɓule cikin dauriya tana faɗin, “Wai mike damunka ne? Gaba ɗaya ka canja ko wani abu ya faru? Idan abinda kaji doctor ta faɗa ne dan ALLAH ka saurare ni na maka bayanin da zaka fahimta”.
         “Anyi wani abu ne?”.
    Ya faɗa kamar a gatsine”.
Rasama mi zatace masa tayi. Sai kawai tai tsaye ta zuba masa ido. Suna samun saɓani, amma bata taɓa ganin ɓacin rai a tattare da shi irin yau ba. Dan saɓanin da suke samu ƙaramine a take su shirya kuma. Amma wannan duk ya ɗaureta da jijiyar wuyanta. Harya kammala shafa man ya miƙe zuwa wajen kayansu bata sake iya cewa komai ba. Babu jimawa ya fito sanye da pyjamas masu laushi, turare ya fesama jikinsa ya haye gado abinsa tamkar ma ya manta da ita a ɗakin.
        Da ƙyar ta iya furta, “Coffee fa?”. Dan yana shansa sosai. Batare da ya kalleta ba yana jan duvet jikinsa ya ce, “Naƙoshi.”
     Zuciyarta tuƙuƙi take mata, dan haka cikin rawar murya ta sake faɗin, “Dan ALLAH ka tashi muyi magana, dan nasan wlhy abinda likitar nan ta faɗa ne ya ɓata maka rai, tunda kafin hakan ai cikin farin ciki muka fita, kuma ko'a can ma babu wani canji a gareka sai da akai maganar. Ni gask.....”
               A wani irin fusace ya ɗago yana kallonta. Tuni idanunsa sun kaɗa jazur. Cikin kaushin murya da ɓacin rai ya ce, “Mawaddat bana son damuwa. Kinji nace miki wani abu ne? Kin tambayeni na faɗa miki babu komai, to mikike son nace miki. Please bana son hayaniya ki barni nai barci na. Idan kuma ɗakin kike so na bar miki ki cigaba da damuna”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa da sake jan bargo ya rufa. Jikin Lulu rawa ya farayi dan ɓacin rai. So take itama ta masa masifar amma ta kasa, ta rasa miyyasa take jin shakkarsa a yanzu har bata iya maida masa murtanin magana balle yin wani yunƙuri. Gaba ɗaya cika mata ido yake da wani irin kwarjini, girmansa take gani mai girman gaske da bayan mahaifinta da Uncle Yousuf bata ganin wani ɗa namiji da shi a duniya. Bata son ganin ɓacin ransa a yanzu balle ace itace ta ɓata masa. Ko yaya taga yayi fushi hankalinta tashi yake yi har sai taga sun shirya....

_____★

        Sam babu daɗi a tsakaninta da mijin nata ɗan tsakanin nan, zai zauna yay wasa da yaronsa suyi hira da Iya Tabawa da Aunty Bilkisu amma ita banda ita. Ya ƙaurace mata a shimfiɗa, abinci ma idon su Aunty Bilkisu ke sakashi ya ci. Amma idan daga ita sai shine sai yace ya ƙoshi. Suna a wannan halin ya wuce Coventry wasa. Tafiyar tasa ta bata damar zuwa asibiti ta nunama doctor ɓacin ranta akan abinda ya faru da tambayarta su dama basu da sirri ne tsakaninsu da patient nasu, haƙuri ita dai doctor ta bata dan batai zaton al'amarin zai zama a haka da girma ba. Sannan ta faɗa mata bata san mijinta bai sani ba ai.
      Kwanansa uku ya dawo. A ranar ne ta gama shirya sai dai suyi duk wacce zasuyi. Dan ta haɗa kayanta tsaff akan zata koma Nigeria. Kamar yasan shirin nata bai shigo gidan ba wannan karon sai dare. A yanayin gajiyen da yake yasa bai zauna ba suka gaisa da su aunty Bilkisu sama-sama ya shige ciki........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣




......... Da kayan data haɗa na tafiya ya fara cin karo. Yay ma kayan kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Har ya gama wanka ya kimtsa bata shigo ba, duk da yaji hakan babu daɗi sai ya daure. Ganin bata da niyyar shigowa shi kuma yana bukatar shayi ya sashi mikewa ya fita da kansa. A falo ya sameta zaune ta zubama tv ido. Ɗan tsai yay yana kallonta na wasu sakkani, sai kuma ya ɗauke kansa ya wuce kitchen. Babu daɗewa ya dawo ɗauke da cup ɗin shayi, wucewarsa yay nan ma ya barta da ƙamshin turarensa. Takaicinsa ne ya turnuƙe mata zuciya, taji kamar ta fasa ihu. Sai kawai ta ɓige da sakin kuka mai cin rai. Wayarta ta ɗauka, tai tsai tana kallo da tunanin wanda zata kira ta sanarma damuwarta, sai kuma zuciyarta ke kwaɓarta da yin hakan. Wani gefe na bata shawarar gara taje suyi duk wacce zasuyi ita da shi amma karta yarda sirrinsu ya zama abin kasawa a fai-fai. Sannan ba lallai ne ba ta samu goyon bayan wani, musamman idan tai la'akari da yanda mutanenmu suka ɗauki haihuwa abu mai matuƙar muhimmanci. Wayar ta yarfar a kujera wasu hawayen masu zafi na silalo mata. Ita da wannan shariyar da yake mata gwara ya balbaleta da masifa kawai, idan yaso ma ya haɗa harda duka yafi sauƙi. Batun yanzu ba ta tsani ta samu saɓani da mutum ya mata shiru, gara a sanar mata ayi hayaniyar da za'ayi komai ya wuce, saboda ita bata iya riƙo ba sam. Shiyyasa tafi yarda da da'an mata ta rama kawai a wuce wajen sai wata kuma ta taso.
        Aunty Bilkisu da ke karance da yanayinsu a kwanakin nan leƙowarta biyu tana ganin Lulu zaune a falon. Ana ukun ne ta sameta tana kuka. Shiru tai tana kallonta cikin nazari, kafin ta ƙaraso cikin dakin ta kai zaune a kusa da ita ta zari tissue ta miƙa mata. Lulu bata musa ba ta amsa ta share hawayenta. Sai dai duk da haka basu daina zubowa ba. Lokaci sosai ta bata ta rage nauyin zuciyarta da kukan kafin ta fuskanceta. Cikin tausasa harshe ta ce, “Wannan shine auren! Shine kuma haƙurin da iyayenmu ke yawan jaddada mana akan muyi idan za'a kaimu gidan aure da bayan an kaimu. Su maza haka suke zuma ne ga zaƙi ga harbi. Zaka iya kuma cin karo da kowanne a garesu a kowanne irin lokaci koda babu wani ƙwaƙwƙwaran laifin da kai musu. Mawaddat kada ki kalleni a matsayin yayar miji, kalleni a matsayin yar uwarki mace da tasan zafinki da sanin ma'anar kalar raɗaɗin da kike ciki. Minene ke faruwa tsakaninki da shi?. Karki damu ki faɗa min, zan koya miki dabarun da zaki cimmasa, dan nasan Hydar nada zuciya, kafiya, da taurin kai akan abinda yake ra'ayinsa.”
         “Aunty ni ban san mina masa ba. Na tambayesa amma yaƙi faɗa. Har roƙonsa nayi bai saurareni ba. Ni gaskiya ina son na wuce gida bazan iya ba....”
      A bazata batare da sun san yana a bayansu ba suka ji saukar muryarsa a kansu, “Ai dama bazaki san mi kikamin ɗin ba, gida kuma ga hanya nan a buɗe tunda dama shine burinki tun ba yanzu ba!!”.
         A zafafe itama Lulun ta ɗago zatai magana aunty Bilkisu ta jinjina mata kai tare da jimƙe hannunta cikin nata alamar kar tace komai. Shirun tayi sai dai ta fashe da kuka. Tsaki yayi da juyawa zai koma dan dama kofin da ya sha shayi ya fito maidawa kitchen, da sauri aunty Bilkisu ta dakatar da shi da faɗin, “Hydar dawo ka zauna”.
          “Aunty ni mizan zauna na mata, kina jin fa abinda take cewa. Dan taga na ƙyaleta bance komai ba har tanada bakin faɗama mutane zata wuce gida. To zuciya take tunanin ta fini ko mi?...”
     “Hydar Please cool dawn mana. Nace ka zauna. Idan kuma Ammah kuke son na kira muku nikam sai na kirata. Maybe ita kufi jin maganarta”.
   Ransa a ɓace ya dawo ya zauna. Sai faman sauke huci yake. Yayinda ita kuma Lulu take kuka. Sai da aunty Bilkisu ta basu mintina kamar uku zuciyoyinsu suka ɗan risina kafin tai gyaran murya kaɗan tana fuskantar Smart. “Aliyu mike faruwa? Kasan dai Mawaddat amana ce a hannunka, sannan ni shaida ce tanada haƙuri da ƙoƙarin ganin ta ƙyautata maka a matsayinka na mijinta da kiyaye duk wani ɓacin ranka. Shin miya kawo wannan fitinar a tsakaninku haka babu daɗi? Kuna ganin kunmin adalci abu ya faru kuna irin wannan tashin hankalin ina a tsakkiyarku. Wane laifi ta maka? Miya faru kake fushi da ita? Tunda ita ta tabbatar min bata san abinda tai maka ba...”
         “Ai bazata sani ba tunda ta ɗaukeni wawa da bai san ciwon kansa ba....”
       Cikin kuka Lulu da ke kallonsa ta ce, “Toni ya kake so nayi maka ne Aliyu. Na tambayeka kace ban maka komai ba. Amma kana fushi da ni. Ko magana baka son kayi dani, idan ka gaji da zamanmu ne ka sallaman na wuce tunda ai ba dole bane. Ni dama bance inayi ba balle kaji su bini da tsatstsaga....”
            “Oh nine kazar kenan? Ai ba sai kin faɗa ba dama nasan ba ƙaunata kike ba. Dan baki da yanda zakiyi da ni ne kawai kike zaune. Sai dai ban san ƙiyayyar da kike min ɗin takai girman haka ba, har ki guji haihuwa da ni. Na farkon dama ALLAH ne yayi maganinki ya samar da shi a lokacin da bakiyi zato ko tsammani ba, shine yanzu kika bi hanyar takaita ni. To sai ki sake ɗaura ɗammara dan wannan batai dai-dai da ke b.....”
      “Ya ALLAH Aliyu...”
Aunty Bilkisu ta katseshi cikin tashin hankali. Dole yay shiru shima yana hucin. Yayinda Lulu ke kukanta ita dai. Shiru falon yayi kusan mintuna biyu sai ajiyar zuciyoyinsu sannan aunty Bilkisu ta sake dubansa. A nutse ta ce, “Kai waya gaya maka bata son haihuwa da kai Hydar? Banji daɗi wannan furucin naka ba sam gaskiya”.
           “Gaskiyar kenan ai aunty, inda tana son haihuwa dani bazataje tai planing babu sanina ba. Da haka zamuyita tafiya ni ina tunanin akwai matsala ita kuma tana cutar dani. Da yake bani da hakkinta sai gashi ALLAH ya sanar dani ta hanyar likitar da taje ta dubata. Ni na taɓa cemata bana son yarane? Gidanmu mu kusan talatin aka haifa, yanda na tashi na gammu nima haka nake fatan tara zuri'a. Amma shine zata zaluntan....”
      “Niba azzaluma bace, kuma nima bance bana son haihuwar ba ai...”
    “Ƙarya kike yi wlhy, idan ba zalunci ba mi kikayi? Da lafiyata da ƙuruciyata ki cutar dani ta hanyar katangeni da ganin jini na. Ke wlhy kika sake maidamin magana zan fasa bakinki ne har sai haƙoranki sun zuba. Bana son raini ki shiga hankalinki kar kiga ina ƙyaleki ki ɗaukeni wani banza can!!....”
            A hargitse Lulu take dubansa. Zatayi magana Aunty Bilkisu ta hanata. Shiko sai huci yake yi dan ya gama kaiwa wuya. Abinda Lulu bata sani ba Smart ya tsani yana magana ana maida masa. Musamman idan shi akaima laifin yana sake harzuƙa ne. Duk yaran gidansu sun san wannan halin nasa, shiyyasa suke kiyaye wa. In ko kai kuskuren dagewa akan dole sai ka masa bayanin da zaka fidda kanka zai iya maka dukan hauka ne ya bar uwarka da jiyya. Wannan itace babbar matsalarsa, idan yay ƙololuwar fushi baya iya controlling temper ɗinsa sam. Shiyyasa yake da ƙoƙarin kauda kansa akan abubuwa. Ganin yanda ya fusata ya saka aunty Bilkisu cewa suje su kwanta da safe sa ƙarasa. Shi ya fara tashi fuuu ya wuce, dan haka ta hana Lulu tashi. Nasiha ta fara mata da sanar mata halinsa na son rashin maida murtani ko bama kai kariya. Dan shi idan akai masa laifi ko bayani wani lokacin baya buƙatar ai masa. Gara ka masa banza idan ya gama hawa da saukar zai huce da kansa ya dawo ya binciki gaskiya in ma hukuncinne ya maka. Ta nuna mata kuskurenta tare da bata shawarar taje ta cire abinda ta saka ɗin. Haihuwa ai komai na ALLAH ne. Ayi fatan kawai ALLAH ya bada masu albarka. Lulu taji daɗin nasiha da shawarar aunty Bilkisun, dan haka ta ɗan ji zuciyarta ta rage mata nauyi.
        Koda ta shigo ɗakin kwance ta samesa. Batai magana ba ta shiga toilet tayi wanka ta gyara jikinta. Kamar yanda sukeyi a tsakanin nan kwanciyar kai da ƙafa haka ta kwanta yau ma. Ta lulluɓa da bargon data ɗakko. Duk abinda take yana jinta, amma ko motsawa baiyi ba. Sai can cikin dare sosai ya tashi yayo alwala ya zo ya kama salloli. Sai da ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa da karatun Alkur'ani sannan ya tsagaita. Ganin asubahi ta gabato ya haƙura bai kwanta ba har sai da yay sallar asubahi. Alerm ne ya tada Lulu, dama haka yake mata tunda suka samu saɓanin. Kafin ta fito bayi ya haye gadon yay kwanciyarsa...

      Ranar yini yay barci, dan sai azhar ya tashi. Babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai. Yay wanka ya shirya cikin ƙananan kaya marasa nauyi. Suna falo zaune Iya Tabawa na basu labarin sanda suna ƴammata Lulu na kwasar dariya kamar ba ita tasha kuka jiya ba ya fito, sam ita bata da riƙe abu, shiyyasa idan aka riƙeta take jin zafi. Da gudu AA dake wasa ya nufosa. Cak ya ɗaga yaron sama yana mai sumbatarsa cike da jin ƙaunarsa. A haka ya kai zaune cikin kujera suna dariya shi da AA ɗin da yakema cakulkule. Iya Tabawa ya fara gaisarwa sai aunty Bilkisu. Ya tambayeta yaya jikin tace Alhmdllh sai fatan komawa gida lafiya. Murmushi yay da faɗin, “Ai keda Nigeria sai nan da shekara ɗaya”.
      Idanu ta waro sosai da faɗin, “Shi kuma mijin nawa kuyi yaya da shi?”.
    Cikin kauda kai da taɓe baki ya ce, “Uhm su miji”.
Kafin aunty Bilkisu ta sake cewa wani abu a fisge Lulu tace masa “Good Afternoon”. Kallonta yayi shima a karo na biyu cikin ɗauke kai yace, “Afternoon” a taƙaice. Daga haka babu wanda ya sake kula ɗan uwansa. Abinci ma sai da aunty Bilkisu ta zungureta ta tashi ta kawo masa. Batai zaton zaici ba, amma sai taga yaci sosai yana bama AA. Bata san yayi matuƙar kewar girkin nata ba ne. Basarwar da yake ɗin ma ta dole ce. Haka ya ƙarasa yinin nan a gida yau ko waje bai leƙa ba har washe gari. Washe garin ma sai zuwa yamma ya fita training center ɗinsu........✍️


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣



.......Kwana uku ya ɗan fara hucewa a dalilin murar zazzaɓi da Lulu ke fama da shi. Duk da dai tana nuna ita ƙalau take. Sai da murar tai mata tsanani ne ta haƙura takai zaune. Mata da miji sai ALLAH sai gashi yana tattalinta da matsa mata tasha magani. Harda haɗa mata shayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login