Showing 75001 words to 78000 words out of 127646 words
a waje guda tsire da allurai suka zube a ƙasa. Ƙara ta daddage ta fasa na tsananin fita hayyaci da tashin hankali batare data farga da ɓaranɓaramar da take neman yi ba. Su Huwaila dake falo suna kallone farkon shiga a ɗakin nata a gigice. Ganinta kwance wanwar a ƙasa babu numfashi ga wata ƴar tukunya-tukunyar tsafi zube a ƙasa harda allurai a jikin tsokar nama ya sasu suma fasa ƙararar data ankarar da su Ammah. Kusan a tare suka afko ɗakin tare da gayyar yaran gidan. Babu wanda idonsa bai gane masa wannan tarkacen tukunya ba idan ya shigo, har Abba da ya shigo a ƙarshe dalilin kiran da Salis yaje yay masa akan tarkacen ya fara sauke ido kafin Ummah dake kwance wanwar ana sheƙa mata ruwa amma babu alamar numfashi tattare da ita.
Wani irin harbawa ƙirjinsa yayi tare da jin kansa ya sara. Yana sake maida idonsa akan Ummah ya ga ta koma masa wata irin mummunar hallita. Da sauri ya kauda kansa yana mai ambaton sunan ALLAH. Yanda yay baya zai faɗi sai da Ammah ta tarosa tana faɗin, “Ya Salam Abbansu yi ahankali”.
Hannun Ammahn ya riƙe yana jujjuya mata kai, muryarsa na rawa ya ce, “Hafsat fiddani a ɗakin nan kaina zai fashe”.
Furucin Abba yasa gaba ɗaya hankalin sauran yaran da su Aunty Amarya dawowa kansa. Sai kuma hankalin kowa ya sake tashi ganin halin da Abba ke a ciki. Amma mi abin mamaki yana fitowa ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya da sakin kan. Kallonsa Ammah tai da faɗin, “Yaya dai Abbansu?”.
Kamar bashi ya gama cewa kansa kamar zai fashe ba ya ce, “Wlhy Hafsat kinji kuma ya saki kamar ba'ayi komai ba.” Sosai abin ya ɗaure kanta. Bata gama fita a mamaki ba kuma sai ga yaran na fitowa da ɗaɗɗaya hannayensu dafe da kansu. Wasu ma a guje suke faɗin, “Dodo! Dodo!!”. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya gama rikicewa. Kowa ya fito a ɗakin Ummah, da kuma sun fito sai su jisu sakawai kamar an zare musu komai. Umma da hayaniyarsu ta sakata farfaɗowa cikin tashin hankali tabisu da kallo ganin yanda suke fita a guje. Ganin babu kowa sai taga damace ta sameta ta tattare kayan nan. Da sauri ta tattarasu jikinta na mazari ta ɗaure a ɗan kwali ta tura ƙarƙashin gadonta. Sannan ta fito cikin ƙarfin hali. Tana sakko ƙafarta waje yaran suka shiga yanka ihu suna kwasa da gudu zuwa ɗakunan iyayensu da faɗin, “Wayyo Umma ta zama dodo! Ummah ta zama dodo!”. Ba yaran kawai ba sai ga su Aunty Amarya suma duk sun rufta ɗakunansu. Abba ma har tuntuɓe yake na barin wajen sai Ammah ce ke kallonta da ambaton addu'oi a bakinta. Dan itama kam yanzu a wata irin mummunar siffa mara ƙyan gani tane kallon Ummahn. A nutse ta nufi nata ɗakin itama aka bar Umma ita ɗaya a tsakar gida cikin tashin hankali da mamaki. Sai kallon jikinta take taga minene sukema gudu amma bataga komai ba. A take jikin nata ya kama rawa. Ɗakinta ta koma ta jajibi waya tai kiran Hajiya Naqiba....
*_★UK★_*
Cikin mamaki Smart ke kallon Lulu da ta buɗe gasashen kifin ta maida ta rufe da sauri fuskarta a ɗan yamutse. Dan shi dai a sanin da yay mata tana son kifi sosai. Shi kam baya so, dan ko a yanzu haka dauriyar shaƙar ƙamshinsa kawai yake yi. Da farko yayi tunanin halin nata ne ya motsa, sai ya so ɗauke kansa. Amma ganin yanda ta tura baki da faɗin, “Nifa bana cin kifi yanzu” ya sakashi zuba mata idanunsan nan.
Cike da shagwaɓa ta ce, “Ni ka daina kallona da wannan idanun”. Ƙaramin murmushi yayi da janye idanun nasa, da kulawa ya furta, “Yaushe kika daina cin kifi kuma Madam?”.
Harararsa tai saboda Madam ɗin da ya kirata da shi, sai ya riƙe kunnuwansa alamar sorry. Mikewa tai tana ƙara tura bakin. Hannunta ya riƙo da sauri dan yasan kaɗan daga aikinta tace zata koma bedroom ɗin da da ƙyar ya samu ta fito. Saman cinyarsa ya zaunar da ita, cikin lallashi kamar wata ƴar yarinya ya ce, “Faɗa min yaushe kika daina cin kifi?”.
A ɗan tunzure ta ce, “Da cikin ɗanka”.
“Woow really?!”.
Kanta kawai ta jinjina masa da yunƙurin tashi ya hanata damar hakan yana dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Oh oh like father like son. Babie luv anya akwai wanda ya kaini sa'ar nasara a ƴakin ƙasa da ƙasa kuwa?”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa tana kallonsa a karo na farko. Gira ya ɗage mata tare da kwantar da kasa a kirjinta ya ce, “Aliyu ɗan Aliyu a suna. Aliyu ɗan Aliyu a kamanni. Aliyu ɗan Aliyu a hallaya. Ya kamata ki bani Award na gwarzon shekara ALLAH kuwa.”
Ƙoƙarin ture masa kai take ya riƙe hannun, cikin mamaki ta ce, “Wai dan ALLAH yaushe ka lalace haka Aliyu? Ko abinda zama cikin turawan ya koya maka kenan kai?”.
Idanunta da suka canja launi ya ɗago yana mata wani irin narkakken kallon da ya sanya jininta da tsigar jikinta yamutsawa a lokaci guda. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Kece kika lalatani fa Mawaddatan'warahmah.”
Da sauri ta waro manyan idanunta a cikin narkakkun nashi. “Ta yaya?”.
Bakinsa ya kai dai-dai kunnenta ya raɗa mata maganar data sakata jin inama kasa ta tsage ta shige kawai. Dan a take ta wani daburce ta shiga kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen ya shiga ƙoƙarin riƙewa yana dariya. Har sai da ta kai shi da kaiwa kwance a kujerar, bata barshi ba ta bisa tana a saman jikinsa ta cigaba da mintsininsa shi kuma yana tarewa da faɗin, “Wayyo fatana da zafi fa ban san mugunta baby luv”. Yanda taga yana ɓata fuska alamar zafin dai yake ji da gaske duk da bada wani ƙarfi take masa ba ya sata fara dariyar itama. Abu mai wahala ga Lulu kenan, kaga tana dariya haka tab ɗin, ai ko murmushi sai a inda taso ga kuma wanda taso. Gaba ɗaya ma sai ya shagala ma shi yana kallonta tamkar ya samu television.
Dariyar ta daina yi ganin yanda ya zuba mata mayatattun idanun nasa da gaba ɗaya suka canja launi da ƙanƙancewa, sai dai murmushi bai bar fuskarta ba, ta ɗan lakace masa hanci da ɗage gira ta ce, “Kallon fa?!”
Idanun ya lumshe a hankali da sake buɗesu a kanta, “Dariya na miki matukar ƙyau my heartbeat”. Ya faɗa cikin wata irin murya mai laushi da sanyi. Samun kanta tai da lumshe nata idanun itama tana ɗan kauda fuskarta gefe da ƙoƙarin sauka a jikin nasa. Hannunta ya riƙo ya dawo da ita ta kwanto jikinsa fiye da farko, fuskarsu gab-gab da juna suna musayar numfashi. A hankali ya sake faɗin, “Kada ki sake barina dan ALLAH. Ina azabtuwa matuƙa Mawaddatan'warahmah. Wlhy kece farin cikin Aliyu, kece bugun zuciyarsa, kece sanyin idaniyarsa, bayan mahaifiyata bana jin na taɓa jin wata mace a cikin jinin jikina da komai na sama da ke. Ki bani dama koda ƴar karama ce domin tabbatar miki da hakan Pleassseee!”.
Wani irin luuuu tayi da idanunta ta lumshesu, sai kuma ta sake buɗesu a kansa. Cike da basarwa ta kai yatsanta saman lips ɗinsa ta fara zagayawa. “Dama kai ɗan ƙwallo ne?”. Ta faɗa cikin basar da zantukansa. Idanunsa da ke rufe ya buɗe a kanta. Jan ajinta na sake rikita masa lissafin rayuwa, ya ce, “Humm!”.
Gira ta ɗaga masa kaɗan tana wani cije lips da jan hancinsa. “Miye wani Hummm amsa nake so da baki?”.
Kauda fuskar tashi ya ɗan yi gefe yana murmushi, kafin ya sake maido idanunsa a kanta da ɗan juyasu alamar tunani. Sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe baki kaɗan ya furta, “Tun ina yaro ma”.
“Uhhyim! Shine ka zama kuma driver?”.
“Ƙaddarata ce wannan”.
“Bani labari to”.
Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Ba yau ba amma?”.
“Miyasa?.”
“Saboda ina da abinda yafi labarin muhimmanci. Ango fa nake ki tausayawa min? Niba ɗan jarida ba na ƙare da bada labari haba ai ace min ma shakatafi”.
Kalmar shakatafin ta bata dariya, dan haka ta murmusa har haƙoranta na bayyana. Ta ce, “Miye shakatafin? Ni Bama gane manya-manyan hausar nan naka suna yin girma da yawa”.
“Oh kefa na manta rabi da rabi ce baki cika bahaus”.
“Kai ka rabani ɗin ko?”.
“Inba ni ɗin ba waya isa kaiwa ga wannan aikin”. Ya faɗa cikin fassara maganar tata da wata siga daban.
“Kai kana da matsala ba'a hirar arziƙi da kai. Sakeni naci abinci na fara jin yunwa”.
“Sorry na daina ayi hirar arziƙin. Abinci kam nan kawai ya isheki ƙoshi yau ai”. Ya ƙare maganar da nuna lips ɗinsa.
“Lips ɗinne kuma ya zama abinci?”.
“Sosai kuwa, kona gwada miki”.
“A'a na yafe girmana bai kai can ba”. Ta faɗa tana ƙoƙarin sauka a jikinsa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣
.......Ƙaramar dariya yayi da ɗage gira sama ya ce, “Nima naga alama ƴar ƙanwata babu abinda ta sani sai cin abinci da barci”. Ya ƙare maganar da lakace mata hanci.
Hannunsa ta buge da sake yunƙurin tashi tana faɗin, “ALLAH dai ya shiryaka kai kam”.
Sakin nata yay yana dariya da tashi zaune shima cike da shaƙiyanci.
“Miye na dariyar to”.
“A'a babu komai ƴar ƙararrama, ai ko cikin AA ma a ruwan madara kika sha ni shaida ne.”
“Kaji da shi dai. Fitinanne”.
“Kema zaki zama fitinanniyar”.
“ALLAH ya tasreni wlhy”.
“Sai dai na gaba wannan dai ya faru tunda ga AA a duniya”.
Da sauri ta miƙe cikin ɗage kai tana faɗin, “Oh kama tunamin, yaron nan zai iya tashi ya ce zai sakko wlhy”.
Miƙewar yay shima da cewa, “Yi zamanki ina zuwa, bari na duba shi.” bata Musa masa ba ta koma ta zauna. Sai dai har ya gama haye ɗan steps ɗin hanyar bedroom ɗin nasa tana binsa da kallo, sai da ya shige ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu tana sakin wani ɗan murmushi mai sanyi. Babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da AA kuwa a hannu, sai zillewa yaron yake da ɓata fuska irin na ƙiwa, shi adole bai sanshi ba. Yana ganin Lulu ya wani zabura wajenta yana ɓare baki. Dole ta amshesa dan ya cika mata kunne, yana ganinsa a hannuta sai yay shiru yana kallon Smart da sauke ajiyar zuciya. Zaune Smart ya kai kusa da Lulu cikin damuwa da ɗan murmushi, ya zubama yaron idanu da faɗin, “Kayi fushi da Papa ko Sweet heart? Kayi haƙuri Papa yayi laifi da baizo ya ganka ba tsahon lokaci. Please ka daina min ƙiwa kaji my sweet friend ɗina”. Ya ƙare maganar yana ɗan lakacema yaron hanci. Da sauri AA ya sake lafewa jikin Mamansa ya zata ɗaukar yasa zai sake yi.
Murmushi ya sake saki da girgiza kansa kaɗan. Sai kuma ya dubi Lulu dake saurarensu da kallo kawai. “Yana cin abinci ne?”.
Cikin ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki tana kallon yaron ta ce, “Da ga Kunu sai tea kawai yake sha, sai biscuits haka da ɗan sweets suma wani lokacin ko an bashi bai sha”.
“In dai ya biyo Babansa kam bazai sha ba, dan bana shan zaƙi nikam. Bari na haɗa masa tea ɗin maybe yunwa ce ta tashesa”. Kai kawai ta iya gyaɗa masa. Har ga ALLAH wannan halayyar tashi na saka mata ganin girmansa da kimarsa. A haka idan ka dubesa sai ka ɗaukesa a wani mutum mai jin kai da girman kai, amma sai ka zauna da shi kaga baida damuwa akwai sauƙin kai. Babu jimawa ya dawo da cup ɗin tea, zama yay a gabansu yana fuskantarsu, ya ɗan ɗebi tea ɗin a spoon ya kai bakin AA. A mamakinsu sai sukaga yaron ya ɗan kallesa kamar zai yi kuka sai kuma ya amsa. Dariya suka sanya su duka. Smart ɗin ya ɗan dungure masa kai da faɗin, “Ana son kayana amma ana guduna”. Ita dai Lulu dariya take musu. Tun yana amsa daga cinyarta harya zamo ya rarrafo jikinsa.
“Oh ashe ƙiwar bamai nisa bace Sweetheart”. Smart ɗin ya faɗa yana ɗaukarsa zuwa jikinsa. A haka ya cigaba da bashi tea ɗin suna hira da Lulu duk dai akan yaron ne da yanda yake samun soyayyar ƴan uwanta da nashi. Sosai Smart kejin ɗari a ransa, dan kuwa maganar nan ce dai ta malam bahaushe da kan ce mai ɗa wawa shima ke ɗawainiya da shi....
*_NIGERIA_*
A karo na farko tun bayan sakinsa da dawowarsa ƙasar yau sukai zaman meeting na farko da abokan cin mushen nasa. Wato Alh. Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau. Sai yaronsa Malami da aka dakatar daga waje kafin lokacin tasa shigowar yayi, dan akwai abinda ya ke son su fara tattaunawa da ba dole bane sai malamin yaji duk da kuwa a cikin sirrikansa babu abinda bai sani ba. Wani abu ma daya sani su su Alh. Baitan basu sani ba. Sun ƙara jajanta masa abinda ya faru cikin nuna ɓacin rai da tattara laifin gaba ɗaya akan Daddy da ɗan ka-ce-na-ce akan yanda akai suka san inda Lulu take. Shi dai shiru yay kawai yana saurarensu har suka gama bai ce uffan ba. Sai ma ya ɗakko musu batun kayan da yayo order da lokacin da yake ganin zasu iya shigowa Nigeria. Sun ɗan tattauna sosai akan hakan sannan suka dai sake komawa batun Daddy. Duk wani tsare-tsare a kansa sun yisa ne a wannan ranar harda ita Lulu da Smart suna a cikin plans nasu. Hatta da Abba wannan karon shima ya shigo lissafinsu.....
*_UK_*
.....Tunda suka dawo bedroom ɗin domin kwanciya sai tsoro ya shigi Lulu saboda ganin take-taken Smart ɗin a kanta. Sai dai tana ta ƙoƙarin basarwar cike da ƙarfin jali. Alwala tayo zatayi shafa'i da wutri yace ta jirashi. Jitai kamar zatai kuka, ta ɗan kai dubanta kan AA da ya haɗa da tarkacen kwalaben turarensa. Babu jimawa ya fito shima da alamar alwalar yayo. Kayan jikinsa ya canja zuwa jallabiya, cikin umarni ya jasu jam'in salla raka bibbiyu har sau uku, da ga ƙarshe suka rufe da shafa'i da wutrin. Juyowa yay gareta ya ɗaura hannunsa na dama saman kanta ya karanto addu'a. Zuwa yanzu tana da ɗan iliminta na addini gwargwadon iko, dan haka ta fahimci sallar da sukayi, duk da kuwa ita bawai ankawota bane matsayin amarya, sai dai a wancan lokacin ma ai sunyi irin sallar a randa komai ya shiga tsakaninsu. Sai ko ga shi shi da kansa yana faɗa mata cikin tsokana da murmushi ya ke cewa, “Kin san ke yau a amarya kike, dole ai miki tarba irinta amarya”.
Bata iya cewa da shi komai ba, sai dai tuni taji zuciyarta ta fara gudu a cikin ƙirjinta tuno da wahalar da tasha a waccan ranar da sakamakon abinda ya biyo baya na samuwar cikin AA. Sai ma taji ta gagara tashi a wajen. Ganin ya tashi shi ya koma saman gado waje ɗansa hankalinsa a kwance jiki a sanyaye ta jawo handbag ɗinta ta fiddo Alkur'ani itama ta fara karatu. Ta wutsiyar ido Smart ke kallonta yana jin wani irin farin ciki mara misali har tsigar jikinsa na tashi, sai dai baice komai ba dan a ganinsa lokacin cewar baiyi ba. Ya cigaba da yima AA wasa har yaron ya sake ɓingirewa barci. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da kwashe kayan ya gyara masa kwanciya, dan tunda suka shigo Mamansa tai masa wanka da canja masa kayan barci, sai ƙamshi yake mai daɗi. Kwanciyar yay shirin yi shima abinsa bayan ya shiga bayi ya gama uzirinsa ya fito ya canja kayansa zuwa na barci da feshe jikinsa da turarruka ya haye gadon harda yin addu'ar barci. Hakan ya saka Lulu ɗan jin nutsuwa, ganin har ya ja bargo ya rufama kansa ta saki ajiyar zuciya. Mintuna kusan goma sha huɗu baya ta rufe Alkur'anin ta miƙe itama. A tunaninta Smart yayi barci. Toilet ta shiga ta ƙara gyara jikinta kamar yanda aka koyar da ita salo-salo a wannan fanin duk da ita batayi da manufa ba, dan bata ma fatan a kai ga hakan saboda tsoro yake ji sosai. Ta jima tana kallon kanta a mirror kafin tai ƙundunbalar fitowa. Ta ƙasan ido Smart da yay likimo yake kallonta, gaba ɗaya tsigar jikinsa ta shiga tashi dan rigar barcin da ke jikinta ba wata ta kirki bace, sai dai a gareta ita bawai tasa da wata manufa bane dan dama can tana sakawar a ita kaɗanta. Gadon ta nufa zuciyarta dai na kai-kawo, dan haka data ɗan kai zaune a bakin gadon ta tsurama Smart ɗin ido. Ganin bai ko motsa ba ta sake yarda yayi barci, sai kuma ta dubi a inda ya kwantar da AA, da ga gefensa sai dai ya kakkaresa da filos ta yanda ko juyi yay bazai faɗi ba, shi kuma ya kasance kamar a tsakkiyar gadon ya bar mata ɗayan gefen