Showing 3001 words to 6000 words out of 127646 words

Chapter 2 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

238

ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al'amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta....)

Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England.

Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci....

Wannan kenan.

____________________★

*_CANADA_*

Amai take sosai cikin galabaita da fitar hayyaci, a kallo ɗaya zaka fahimci yanda duk jikinta ya saki sai huttai take da ƙyar. Cikin tausayawa mai aikin da suka taho tare tun daga Nigeria ta ke jera mata sannu. Bayan ta gama aman ruwa ta sakarma kanta daga inda take zaune tana hawaye. Haka take tun can da ma bata da juriyar ciwo, a yanzu kuma da take jin ciwon tamkar ya bambanta da duk wanda ta sabayi ne ke sake galabaitar da ita da raunana mata zuciya, har tana jin anya bazata bijirema kakar tata ba ta bayyana kanta kota koma gida Nigeria. Tsahon watanni uku kenan da barowarta gida Nigeria bisa taimakon kakarta Dada. _(Dan a waccan ranar bayan fitar Smart da ga gidan ta fito toilet da taje yin fitsari, duk da tai masa kurarin barin gidan ba'a ranar tai niyyar hakan ba, sannan batai niyyar sanarma wani nata abinda yay matan ba kamar yanda aunty Khadijah ta bata shawara. Saman gado ta koma ta ɗauki book nata da take adana muhimman sirrikanta ta fara rubutu tana hawaye, bata kai ƙarshe ba ya cika dan haka ta buɗe sabo ta cigaba. Tana tsaka da rubutun ne taji sallamar Dada a bazata, kafin ma ta farga har ta shigo bedroom ɗin nata kai tsaye. Hawayen da Dada ta gani a fuskarta ya sata nuna tashin hankali da fara jera mata tambaya, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya ta sakarma Dadan kuka kawai. Komai Dada bata tsaya tambayarta ba ta hau haɗa mata kaya, bayan ta kammala drivern da ya kawota ya shigo har ciki ya dinga kwasar kayan, yana kammalawa ita kuma ta ce Lulu ta tashi suje, da farko Lulu taso tirjewa akan ta bari Aliyu ya dawo, amma Dada ta balbale ta da masifa. Dole badan taso ba tabi umarninta ta sako. Sai dai tanayin taku biyu uku Dada ta rabga uban salati da antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba'in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al'amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu).........✍️

Wannan kenan.

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣



.......Dole da taimakon Ummita mai aikin nata ta gyara jikinta ta kamota ta fito da ita bedroom. Cikin wando dogo da sweater ta shirya tare da Safa mai kauri sosai, ta haye gadon cikin rawar ɗari taja bargo har saman kanta. Tare da bama Ummita umarnin ƙara mata gudun room hitter ɗin ɗakin. Dan wani irin rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa waje guda. Ga hawaye sun gagara tsayawa (yau fa an taɓo manyan mata🤣🙏).

Yanayin da Lulu ke ciki ya tada hankalin Ummita, number da suke waya da Dada jefi-jefi ta lalubo ta kira, kamar baza'a ɗagaba ma sai kuma aka ɗaga, cikin ladabi Ummita tai sallama da gaida Dada, daga can ta amsa a gadarance da tambayar ina Lulu. Cike da damuwa Ummita ta sanar mata gata kwance babu lafiya, dama kusan kwanakin nan haka take ganinta sama-sama, sai dai rashin tabbatarwa yasa bata faɗa mata ba sai yau. Rai a ɓace Dada ta shiga zagin Ummita ɗin, duk ta rikice dan tana bala'in son Lulu, zamu iya cewa soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta. Ita dai Ummita haƙuri kawai take bama Dada kawai. Dan ta tabbatar masifar tsohuwar original ce.

Ba'a rufa mintina goma da katse wayar Dada ba alerm ɗin gidan ya kaɗa, miƙewa Ummita da ke falo tai ta nufi ƙofar, bata buɗe ba kai tsaye ba, ta danna numbers dake jikin ƴar computer ɗin kusa da ƙofar dake manne a bango dan ganin wanene. Baturiyar mace ce tsaye, cikin nuna alamar tana ganin Ummitan da ga wajen itama ta ce, “Hy” cikin ɗaga hannu. Amsa mata Ummita tai itama da “Hy” ɗin. Cikin murmushi matar ta cigaba da magana cikin harshen nasara. “Sunana Doctor Olivia, Nazo nan ne bisa umarnin Mrs Garko”. Yanda ta kira kalmar Garko ɗin taso bama Ummita dariya, amma ta dake da ƙyar sai murmushi da tai mata tare da ɓuɗe ƙofar. Sun sake gaisawa da Dr Olivia, Sannan tai mata rakkiya ɗakin da Lulu ke kwance.

Ganin yanda jikin Lulu yay zafi sosai yasa Dr Olivia cewa dole suje asibiti, a take tai kiran ambulance cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu. Lulu na rawar sanyi da faɗin su barta ita bazataje ko ina ba su Dr Olivia suka ɗauketa a ambulance ɗin tare da Ummita suka wuce. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka shiga da Lulu ciki tare da rufuwa bata gudunmawar gaggawa.

*_UK_*

Hankalin Dada da ke jiyyar mijinta ya tashi sosai, amma tanata ƙoƙarin dakewa dan kar Alhaji Garko da ya fara samun sauƙin jikinsa Alhmdllh ya fahimta tare da sauran yaransu da sukan zo dubashi. Idan wannan tawaga ta wuce sai wata kuma tazo, abinka da masu hannu da shuni, kallon fita ƙasar ake kamar barin Kano a shiga Katsina ne. Alhaji Garko da bai san halin da ake ciki ba har yanzu dan babu wanda ya sanar masa saboda halin da yake ciki ya zubama matar tasa ido cikin tausayawa, dan shi ya fassara yanayin nata ne da gajiyawa musamman da yake akwai tsufa. Cike da kulawa ya ce, “Hajarah kina buƙatar hutu, ya kamata kije gida haka nan tunda jikina da sauƙi nima, har ma muna sa ran sallama nan da ƙarshen watannan”.

“Haba dai Alhaji ya hankalina zai kwanta kana nan ina can, duk da dai jikinka Alhmdllh amma har yanzu kana buƙatar kulawa. Danni ko sallamarka sukayi bana son ka koma gida Nigeria yanzu har sai ka sake hutawa anan magana ta gaskiya.”

Murmushi yay irin nasu na manya da faɗin, “Hajarah rigima kenan. Yanzu ni da abubuwa ke jirana tari-tari tunda ALLAH yasa da sauran kwanana a gaba mizai sa na kuma sake sabon zama anan ai gara na koma gida ko?”.

“Humm Alhaji wlhy wannan gaskiya ce ba rigima ba. Gara dai ka sake hutawa dan muna komawa can hayaniya ma ta isheka musamman ta ƴan siyasar nan da ba gajiya suke ba. Dan haka dan ALLAH ka yarda kawai sai ka sake hutawa, nima yanzu inaga maimakon tafiya Nigeria bari na ɗan je Canada na huta na kwana biyu kafin a sallamekan ko.”

Ɗan jimm yay na alamar tunani, sai kuma cikin nuna fahimta ya ce, “Shike nan idan hakan kike so uwar garke na. Yanzu yaushe zaki wuce Canadan?”.

“Eh to ko zuwa yamma haka tunda ga su Khamil da iyalansa nan sun iso ko, auta ma yace min zai baro Saudiyya shi da matarsa gobe in sha ALLAH. Kaga dai ai ka sake samun masu kulawa”.

Murmushi yay mata cikin nuna gamsuwa. Dan Dada kam a wajen bama miji kulawa jaruma ce, tsaye take kan abinta ta kankane ko ina tunda ƙuruciya har girma babu wata mace data taɓa raɓar mata miji da sunan kishi. Wannan tsananin kishin nata yasa hatta matan ƴaƴanta take jin kishinsu akan ƴaƴan nata da suma take matuƙar so da ƙauna tamkar ubansu. Babu ɓata lokaci ta hau shirin wucewa Canada, dan ji take kamar ta rufe ido ta isa taga hanlin da ƴar jikarta take a ciki, saboda a nata bahagon tunani babu abinda zuciyarta ke raya mata sai kodai Smart, ko Uncle Yousuf wani ya sakema Mawaddat asiri ne.

Dai-dai lokacin da Lulu ke cika awanni goma sha ɗaya a asibitin su Dr Olivia Dada ke isowa ƙasar ta Canada. Tunda ƙuruciya an riga da an san lungu da saƙo na ko'ina, dan a duk ƙasar da suke yawan zama suna da gidansu na kansu musamman manyan ƙasashen nan masu ji da kansu irinsu England, America, France Chaina, Saudiyya, Dubai, dan da gasken gaske wannan family sunada dukiya, bayan wadda mahaifinsu ya gada a wajen nasa mahaifin ya kuma tara nasa na kansa, su kansu yaran kowanne ba ƙyalan bane wajen kuɗin, dan babu wanda ke zaune kaf ɗinsu a neman na kansu suke. Ko marigayiya Mawaddat mahaifiyar Lulu data kasance mace ɗaya tilo a cikinsu sanda tana raye tsaye take akan neman na kanta saboda haka aka gina musu rayuwa, duk da yana da dukiya kuma ya gada ne shima a wajen mahaifinsa bai yarda yaransa su zama cima zaune ba, suna ayyuka a cikin gwamnatin ƙasarsu da na wasu ƙasashe, suna kuma Business ƴaƴa da iyaye har ma da jikoki. Cab ta ɗauka tun daga airport zuwa asibiti kai tsaye, dan a ƙage take da son ganin halin da jikar tata ke ciki. Wadda har yanzu ana kan tafka rigima akan ɓoyetan da tai dan bayan ita sai Alh. Sulaiman kawai suka san ina Lulun take. Hatta da Tajuddeen sunƙi sanar masa. Ita Dada zuciyarta ɗaya ce game da ɓoye Mawaddat dan kawai ta rabata da Smart ne matsayinsa na talaka jikanta Tajuddeen ya samu. Yayinda shi Alh. Sulaiman ba haka kawai bane a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara aiwatar da plan ɗinsa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa ɗaya suke samu a bincikensu shine ya ɓoye kansa dan kar ya saki Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya ɓoyesa amma a ɗan tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf ɗin ma ya sake baro Nigeria ɗin zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Daddy tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al'amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu haɗin kan Lulu Dada bazata taɓa iya ɗauketa a gidan aurenta ba harta ɓoyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa.

*_NIGERIA_*

Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.

Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”.

“Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.

“Ka shirya ganinta yanzu kenan?”.

Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login