Showing 93001 words to 96000 words out of 127646 words
waɗanda ta zano ɗin, har ma da Uncle Yousuf. Shi dai Smart ba kowa ya sani ba sai ɗaidaiku irin su Hon Nakowa suma dan sun kasance sanannun ƴan siyasa ne. Sai dai ganin sunan MM Atik Kumo ya sashi kallonta. Ta fahimci mi yake nufi, dan haka ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Shima Dila ne ai, ko'a ranar daka ɗakkoni a gidan nan tare da tsoffin nan gidansa ne, sannan shine ya sayar mana da kayan”.
“Shi wannan ɗin da nake gani simi-simi?”.
Lulu ta ce, “Humm bakaga komaiba ma, wasu ma dan ban san yanda zan misaltasu bane ku gane saboda sunan banza na sansu da shi, wasu kuma haɗuwar club ne kawai”.
Babu wanda ya sake iya magana dan sun san a zancen Lulun kam babu tantama...
A ranar su Daddy suka koma Manchester, dan washe gari suke son tafiya Nigeria su duka biyun, a Abuja kuma zasu sauka domin wucewa da su Twins, dan har Daddy ya nema musu transper zuwa Kano, duk da dai sun so bijirewa ya nuna musu basu isa ba. Har Mommy sai da ta kirashi akan hakan ya nuna mata babu ruwanta, ƴaƴansa ne, yanda yaso haka zai tafi da rayuwarsu. Dama dai da amincewarsa suke aiki a Abujar yanzu kuma yace su dawo gida suyi a gabansa. Jin ya buɗe mata wuta dole ta kama kanta, dan Daddy nada haƙuri, idan aka ƙuresa kuma akwai hayaƙi.
Tunda su Daddy suka wuce Lulu ta maida Camara ɗin nan abar kallo, sai da Smart ya ga kukan nata yayi yawa ya kwace ya ɓoye, duk roƙon datai masa akan ya bata ƙi yayi. Da ga ƙarshe ma ya ɗauketa suka fita. Wannan ɗan yawon da sukayi ne ya rage mata raɗaɗi da damuwar da take a ciki sosai. Dan basu dawo gidan ba sai da dare ya tsala kasancewar su daren da rana duk babu ruwansu bai hanasu hidimar gabansu. Washe gari ya kwasheta suka sake fita, sune har wajen gyaran jiki da wajen wasan yara aka kai AA duk da shi ba fahimtar komai yake ba. Wannan ɗan busy ɗin ya saka mata nutsuwa ta cire komai a ranta, sai sake duƙufa yima mahaifiyarki addu'a kuma.
Ahmad yay kiran Smart akan pharmacy da jami'an tsaro dana hukumar NDLEA sukaima dirar mikiya. Inda babu wani shan wahala aka gano na mahaifin aunty Khadijah ne dai, ta kai ma har an kamashi shi da yaran pharmacy ɗin gaba ɗaya. Duk da wasu sun rantse su basu san ana wannan baƙin kasuwancin ba. Sai dai ba'a sauraresu ba an ce sai abinda bincike ya tabbatar... Sosai Smart da Lulu suka tausayama Aunty Khadijah, dan Ahmad yace ana faɗa mata yanke jiki tai ta faɗi a asibiti, yanzu hakama tana can, bama ita kawai ba, zuri'ar gidansu gaba ɗaya suna cikin tashin hankalin al'amarin, dan abunne da babu wanda ya taɓa kawowa a ransa.....
*_NIGERIA_*
Tako ina komai a hargitse yake. Musamman ma a fanin iyalan Alhaji Sadi Dikkon da aka wayi gari da labaran kamashi, tare da yima babban pharmacy ɗin da sai yau mutane da yawa suka san nashi ne tsirara. Inda aka dinga nuna miyagun kwayoyin dake danƙare a cikin pharmacy ɗin da yanda ake kasuwancinsu a tsawon lokaci batare da hukumomi sun fargaba balle jama'ar gari da basu taɓa kawoma ransu ba. Gaba ɗaya Kano a rikice take da kace nace, saboda Alhaji Sadi babban mutum ne da ke a cikin jerin ƴan kasuwar da ake ji da su a Kanon dama ƙasar ta wani fannin. Sannan sam a fuska bazaka taɓa kawoma kanka zai iya aikata irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.
Alh. Sulaiman na kwance a gidansa hankali kwance, yana ma tsaka da jin daɗin duniyarsa shi da amaryarsa kira ya shigo masa a waya kusan ƙarfe biyun dare. Rai a ɓace ya ɗaga duk da yaga Hon Nakowa ne a kan layi. Sai dai yana ɗagawar furucin Hon. Nakowa ya sashi zabura yana ture matar tasa gefe da lailayo wata gawurtacciyar ashariya mai kawuna goma sha biyu ya dire. Har neman taune halshensa yake wajen faɗin, “Tayaya hakan ya faru? Shi wane sakaci ne ya kaishi ga haka?”.
“Babu fa wanda yasan yanda akayi, Garko kaima kasan Alhaji Dikko na cikin mutane masu taka tsantsan matuƙa. Kawai dai akwai abinda ya kamata musani, sannan muna buƙatar zaman meeting na gaggawa dan nasan zuwa safiya zasu iya cewa zasu kamashi”.
“Wane zaman jira zai tsayayi ayi meeting da shi, a daren nan ya sayi ticket ya bar ƙasar nan kawai, idan kuma ya bari suka kamashi to tabbas zai mutu, dan mutuwarsa tafi rayuwarsa muhimmanci a garemu yanzu. Sauran aikin zamu ƙarasa a rufe zance. Dan haka kai kiran su Baita yanzun nan mu haɗu, dan muna buƙatar ganin shugaban NDLEA da IG ma kansa”.
Cikin gamsuwa Hon. Nakowa yace “Hakan yayi”.
Alh. Sulaiman na yanke waya idonsa ya sauka akan amaryarsa data zuba masa ido. Wani irin dafe kai yayi da faɗin, “Oh shiitt” dan harga ALLAH ruɗewa tasa ya manta bashi kaɗai bane a ɗakin ya zauna yana sakin zance har haka. A wani irin fusace ya nufeta, babu zato taji ya mata wata irin tsawa da nunata da yatsa. Har sai da ta zabura.
“Me kika ji?!!”.
Ya faɗa a gigice. Kanta ta shiga girgiza masa jikinta na rawa. “Banji komai ba wlhy Alhaji. Kwata-kwata banji komai ba”.
“Idan ma kin jin ki ɗauka baki ji ba, idan kuma kikace zaki nuna kinji kiyi kuka da kanki”. Da ga haka ya wuce fuuu zuwa toilet domin tsarkake jikinsa. Tashin hankali na haƙiƙa ta shiga, dan jikinta har rawa yake yi, zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Gaba ɗaya kalaman mijin nata sun ɗimautata, so take tabar ɗakin ko zata samu iska, sai dai babu dama, dan fitar tata zai iya sawa ya zargi wani zataje ta faɗawa. Bata taɓa sanin atsabibancin mijin nasu ya kai haka ba, karo na farko a rayuwarta da taji ashe garama da ALLAH bai bata haihuwa a gidan nan ba..
Tana a kwancen ya fito, jikinsa duk laima bai damu ba ya saka jallabiya tare da zarar wayarsa da key ɗin mota ya fice. Da kallo kawai ta bishi kamar matacciya, dan ko dogon numfashi bata iyayi saboda tsabar tashin hankalin da take ciki..
★A lokacin da su Alh. Sulaiman ke nufar inda zasu haɗu meeting a lokacin jami'an tsaro sukai dirar mikiya gidan Alhaji Dikko dake ƙoƙarin sulalewa ya bar gidan batare da sanin ko iyalinsa ba. Aiko a take sukai ram da shi. Jiniyar motocin jami'an tsaron ne ya fargar da iyalinsa dama ƴan anguwa. Hankalin kowa a tashe, yaran sai kuka suke suna kiran yayunsu a wayoyi, ta hakane Aunty Khadijah da batasan mike faruwa ba tun safe da aka fara tone-tone a pharmacy ɗin mahaifin nata da ita kanta bata taɓa sanin nasa ɗin bane labari ya risketa daga bakin ƙaninta. A wajen ta yanke jiki ta faɗi tana tsaka da duba mara lafiya. Tun a daren Coach da Ahmad suka nufi asibitin cikin tashin hankali. Shine ma ya samu damar kiran Smart suka tattauna bayan aunty Khadijah ta farfaɗo an mata allurar barci mai ƙarfi. Zuwa safiya labari ya ƙara karaɗe ko'ina da ina, yayinda shugaban NDLEA na Kano dama na ƙasa gaba ɗaya suka ƙi ɗaga kiran su Alh. Sulaiman. Hakama IG da CP basu ɗaga musu kira ba. Abinda basu sani ba shine akwai wata ƙullaliya tsakanin gwamna da Alhaji Dikko, yana samun labarin abinda ke faruwa yay kiran CP da shugaban NDLEA na jiha yay musu gargaɗi. Tare da tabbatar musu in suka bari Alhaji Dikko ya ƙuɓuce musu a bakin aikinsu. Sannan Baba Garko ogan Gwamna ne na amana, dan haka yay kiranshi shima akan su IG da shugaban NDLEA na ƙasa. Shi baba Garko dama abune daya tsana a rayuwarsa, yake kuma yaƙi da masu alaƙa da shi, amma sam bai san akwai alaƙa tsakanin ɗansa Sulaiman da Alhaji Sadi Dikko ba sam...
Matuƙar tashin hankali sun shiga jin an cafke Alhaji Dikko, a take meeting ɗin su ya canja akala zuwa shirya yanda zasu kashe Alhaji Dikkon kawai. Dan sunci alwashin bazasu taɓa barinsa ya tona musu asiri ba. Sai dai dolene suyi komai ta ƙarƙashin ƙasa saboda gujema idon mutane a kansu. Sun nema amintattunsu dake cikin jami'an tsaron, kai tsaye suka basu umarnin kashe Alhaji Dikko ta hanyar guba. Kasancewar suma abokan cin mushen nasu ne sukai na'am da hakan. Dan in dai aiki ya buɗe suma nasu ya buɗe ai........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣9️⃣
.......Kowa da abinda ya damesa. Duk da abinda ke faruwa a jihar ta Kano ya girgiza Abba hankalinsa a rabe yake gida biyu a dalilin halin da Ummah ke ciki. Duk da ma dai malaman da aka kawo a wannan karon su sunyi jarumtar tsayawa, sai dai daga kallo ɗaya da sukai mata sukace ta koma cikin ɗaki kawai. Sun tattauna da Abba akan dolene asan mushurikin da yay mata wannan aiki. Cikin nuna rashin amincewa Abba yace shi babu ruwansa. Babu inda zaije neman wani akan aikin da bai aiketa yi ba. Babu irin lallashin da ba'ai masa ba yace babu gudu babu ja da baya. Da ga ƙarshe dole ƴaƴanta ne suka nufi wajen Hajiya Naqiba da ke gida, dan asibiti sun sallamesu kamar yanda suka buƙata akaje akai mata ɗorin gida. Sun sami Hajiya Naqiba a yanayin daya tada musu hankali, dan ƙafarta tai wani irin mahaukacin kumburin da har tafi gangar jikinta girma. Kuka take sosai da ihu na azabar zogi da raɗaɗin da ƙafar kemata. An kira mai ɗori ya tabbatar musu ta sake gocewa, ma'ana dai ɗori baiyi ba. Ya kuma tabbatar musu da shi gaskiya bai san yaya zai yi ba, sai dai su nema wani kuma ya gwada sa'arsa. Daga haka yay tafiyarsa ma shikam. To shine fa ƴaƴan Umma suka samu ana shawarar neman wani mai ɗorin dan an tabbatar musu na gargajiyar dai yafi kar su maidata asibiti. Ga mijinta ya nuna kamar ma abin bai damesa ba duk da irin kiran sunansa da take famanyi shi da ɗanta Maheer. Shi Maheer ɗin da farko ya zauna, da ga baya yay ficewarsa acewarsa shi gaskiya ihun da take ya ishesa, yana fita suka haɗe da abokansa sukai tafiyarsu wajen ƙwalewarsu da kayan shaye-shaye. Dole yaran Umma suka dawo gida jiki a sanyaye. Sun sake iske tashin hankali Umma dake wani irin nishi a ɗaki amma kowa ya kasa shiga ya dubata, Ammah ce ma ta nuna zatai ƙarfin hali Abba ya tabbatar mata idan ta shiga sai ya ɓata mata rai, dole ta kama kanta cikin damuwa. Suma ɗin dai babu wanda yay yinƙurin shigar saboda tsoro....
Har yamma babu wanda yasan halin da Ummah ke ciki, sai yayanta Jibirin ne ma yay ƙarfin halin bada shawarar a sake kiran malaman nan koda taimakon da zasu musu. Kowa ya bada goyon bayan hakan. Dan haka akai kiransu. Babu jimawa suka iso kasancewar akwai sanayayya tsakaninsu da Jibirin ɗin. Addu'oi sukayi da ƙarfin halin cusa kai a ɗakin, sai gasu suna rige-rigen dawowa a guje. Har yaran gidan dake tsakar gida na tayasu da afkawa ɗakunan iyayensu. Sun tabbatar da gaskiya bazasu iya ba, wannan mummunar halitta ganinta ai tashin hankaline ma. Sun tabbatar da shawararsu kawai ya kamata a bi aje a nemo mutumin da yay musu wannan aiki zaifi sauƙi fa. Wannan al'amari ya sake tayarma da kowa hankali. Dole ƴan uwanta suka tattaru neman mafita su da ƴaƴanta. Dan Abba dai da gaske ya juya musu baya.....
________★
Al'amari kamar wasa Dada sai da ta kwanta asibiti na kwana biyu, randa aka sallamonta ta samu surukanta cike da gida sunata harkokin arziƙi akan zaman bakwai. Wannan abu ya sake dugunzuma mata zuciya. Baba Garko ya shigo dubata da daddare ta sanya masa kuka. Kallonta kawai ya tsaya yanayi, bawai baya jin tausayinta bane, ba kuma baya sonta bane. Ya riga ya ɗaura ɗammarar horatane kawai. Dan ko auren nan nashi yayisa ne da gayya danya ƙona mata rai tunda yasan babu abinda ta tsana a duniya irin kishiya. Kuma ya samu nasara. A yanzun ma cikin ɓacin rai yaja tsaki da faɗin, “Ni al'amarinki kam ya fara bani tsoro Hajara. Shin wai baƙin ciki kike da ƙaruwar dana samu ko yayane? An faɗa miki haihuwa kin yanke jiki kin faɗi sumammiya, yanzu kin sakani a gaba kina kuka. Kin ganni nan ni bana son damuwa ina cikin farin ciki a ɓata min shi. Idan kinga zaki sakama ranki dangana ki saka, idan kuma kinga wannan halin da kike neman jefa kanki ne abin burgewa sai ki cigaba. Dan bakin alƙalami dai ya rigada ya bushe. Takardu sun jima da rubutuwa babu wata cleaner ɗin gogesu. In sha ALLAHU nan da wata shekarar ma wasu biyun zata sake zubomin a gidan nan, sai ki shirya sake suma. Na barki lafiya”. Da ga haka yay ficewarsa. Sama da ƙasa numfashin Dada ya ringayi, jininta yay masifar hawan da har idanunta na koma mata dishi-dishi, ALLAH ne ya taimaketa Uncle Muneer ya shigo ya sameta a lokacin, da tabbas zuciyarta zata iya bugawa komai ma ya faru....
(To Baba Garko ALLAH ya raya ƴan biyu. Koda yake kace nanda baɗi ma wasu kake so. Kaga tsoho da rigima🥱😂😂🤣🚴🚴)
*_★UK★_*
Alhmdllh a ɓangaren ango da amarya komai na tafiya dai-dai. Basu da wata damuwa sai cilin ɗinsu sukeyi. Duk abinda kuma ke faruwa a 9ja a cikin kunnensu yake. Dan suna samun information sosai ta hanyar Ahmad da su Daddy da suka koma gida. A yanzu haka tarko na biyu suke shirin ɗanawa. Dan sun gama shirya komai tsaff lokaci kawai suke jira.
Soyayya suke zubama juna mai tsayawa a rai da zuciya harma da gaɓɓan jiki. Duk da Lulu na dojewa da ɓoye nata sirrin har yanzu ta gagara furtawa a baki sai dai Smart ya gani a aikace. Dan zuwa yanzu kam karatun malamin nata tsaff ta haddacesa tama koma ruɗa masa tunani da salo-salonsa. A ranakun da yake da wasa koda ba'a cikin London bane bata iya zama, binsa take su tafi ga ɗan yaronsu da kowa ya gani sai ya tanka. Dan haka Smart ya dage da tofe abinsa da addu'a itama yana cemata tai masa saboda baki.
Lulu aja rigima bayan ta kira Baba Garko sun masa barka ita da Smart, ta kuma kira maijego da zuwa yanzu sun ƙulle sun zama ƙawaye dan kawai ta turama Dada haushi. Waya ta ɗaga tai kiran Dada. Bayan su. Gaisa Dada na zaton Lulun ta sakko ne daga fushin da take da ita zatai mata yaya jiki sai taji ta fara mata barkar haihuwar gidan. Dada ma bata san ta lailayo ashariya ta makawa Lulu ba. Aiko ta kwashe da dariyar ƙularwa tana mai yanke wayarta. Murmushi kawai Smart da ke zaune yana saurarenta yayi. Dan shi rashin jinta zuwa yanzu tsoro ma yake bashi wlhy. Baice mata komai ba sai da zasu kwanta ya mata faɗa. Tadai nuna masa taji, amma yasan batajin ba. Dan a ɓoye ta haɗa kayan jarirai na gani na faɗa ta bada aka wuce da su Nigeria wai a kaima maijego da jinjiraye....
Ana kwana na biyar da kama Alhaji Sadi Dikko Aunty Bilkisu da Iya tabawa suka iso Unitet Kingdom tare da Ahmad. A ranar Smart baya gida sunje buga wasa. Sai Lulu ce taje tarbarsu duk da Ahmad yasan gidan. Sosai aunty Bilkisu da duk take a tsorace ta samu nutsuwa da ganin Lulu, cikin farin ciki suka rungume juna. Hakama Iya Tabawa yau Lulu harda rungumeta, yayinda Ahmad ya caɓe yaronsa a hannu shima. Cab suka shiga har gida, dan Lulu bata driving anan kasancewar bata da lasisi. Sai Smart kawai. Daga Aunty Bilkisu har Iya Tabawa gidan ya birgesu sosai. Sunata santi da jera addu'a ga Smart. Abincin da Lulu ta shirya musu sukaci, bayan sunyi nak Ahmad yace zai wuce can ya samu Smart. Zuwa gobe sa dawo tare ɗan ba'a ranar Smart ɗin zai dawo ba. Tafiyar Ahamd ta sake basu damar ɓararrejewa, dan ma Aunty Bilkisu ba daɗin jikinta take ji ba sai ƙarfin hali kawai. Sun ɗan taɓa hira kafin Lulu ta kwashesu zuwa asibiti dan a yau take son aunty Bilkisu ma ta fara ganin likita. Kuma ko Smart baisan da hakan ba, dan shi nashi shirin kawai sai ya dawo ya kaita da kansa.
Kasancewar Usman da Dr Lameer ne suka haɗasu da likitan basu wani sha wahala ba na ganinta. A take aka bama aunty Bilkisu gado. Abinka da inda aka san darajar ɗan adam babu ɓata lokaci suka fara mata gwaje-gwaje da duk abinda ya dace. Koda Smart yay kiran Lulu bayan sun tashi a wasan bata sanar masa suna asibiti ba. Sun dai gaisa tai masa congratulations dan ganin sunci wasan suka ɗanyi hirarsu ta soyayya sukai sallama. Da yace ta haɗashi da su yay musu barka da zuwa Iya Tabawa kawai taba tace aunty Bilkisu na barci. Bai kawo komai a ransa ba ya yarda. Sallama sukai fan yana tare da Ahamd daya sameshi a can. Da ga haka itama ta cigaba da kai kawonta tare da Dr Lameer dake taimaka mata. Kasancewar mai jiyya ba zama yake a asibitin bayan ayi mata abubuwan da duk suka dace na wannan lokacin suka dawo gida,