Showing 99001 words to 102000 words out of 127646 words
tashi hankali, itama ta fashe da kuka. Da ƙyar ta iya cewa Ummita sukai Nadia asibiti, amma ta kira Uncle Yousuf a waya. Koda Ummita tai kiran Uncle Yousuf ta sanar masa babu ɓata lokaci ya iso wajen shi da ƴan sanda da ambulance. An ɗauki Nadiya zuwa SHIRA'S HOSPITAL. Babu ɓata lokaci likitoci suka rufu a kanta, kamar jira cikin nata keyi dama sai naƙuda ta tashi. Doctors sun tabbatar bazata iya haihuwa da kanta ba, dole akai mata cs. Ana shiga da ita ɗakin theatre Uncle Yousuf ya nema gidan iyayenta. Sai dai koda yaje babu wanda ya sauraresa duk da ya sanar musu tana can a asibiti an shiga da ita theatre basu saurarensa ba. Haka ya baro gidan ransa a ɓace, sai bayan tahowarsa ƙanwarta ta biyosa asibitin a sace bisa umarnin mahaifiyarsu......
(ALLAH sarki Uwa kenan😭🙏).
*_★UK★_*
Fuskarsa ɗauke da murmushin zancen Iya Tabawa ya tura ƙofar bedroom ɗin a hankali ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, zuciyarsa cike da ɗokin san ganin sahibar ruhin nasa.. Cak kalaman bakinsa suka tsaya sakamakon tozali da ita zaune fuska share-share da hawaye ta zubama waya idanu...
“Mawaddatan-warahmah!”.
Ya kirayi sunanta cikin wani irin salon taushin murya mai amo da ratsa zuciyar mai saurare. A bazata ta ji saukar muryar tasa duk da a tsumayen isowar tasa suke. Dan hatta kwalliyar da taci yau a cikin skert da riga na atamfa da sukai mata ƙyau tayine da shi. Harda kwalliyar da hawayen tausayin Nadiya suka gama batawa. A hankali ta ɗago idanunta da suka kaɗa harda ɗan kumburowa. Sai ya samu kansa da lumshe nasa da sake buɗe su a kanta ya ware mata hannayensa alamar tazo garesa. Babu musu ta taso da ɗan gudu-gudu ta shige jikin nasa ya maida hannayensa ya naɗe a nata jikin. Wani kukan da ya sakashi runtse idanu da ƙarfi ta sake saki tare da ƙara ƙanƙamesa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata tayi kukan ba har tsawon mintina biyu. Sai da ya tabbatar tayi ya wadaceta sannan ya ɗagata cak zuwa saman gado. Kwantar da ita yayi tare da kishingiɗa a gefenta ya tokare hannunsa da tallafo kansa ta yanda zai iya mata runfa. Ɗayan hannun kuma ya tallafo fuskarta ya zuba mata ido. Itama kallonsa take tana jan ajiyar zuciya. Karo na farko ya sakar mata murmushi mai sanyi da saka babban yatsansa ya ɗauke mata hawayen.
“Waya taɓa Final Choice ɗin Aliyu Mawashi? Maman Aliyu Mawashi? Kin san kuwa yanda nake jin ƙunar zuciya a duk sanda naga hawaye na sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskar nan taki. A gaɓa ɗaya kawai nake son naga waɗan nan hawayen da rakinki, amma ba'a banza haka ba okay”.
Hawayen ne suka sake ciko mata idanu, a hankali ya shiga girgiza mata kansa alamar kar tayi. Haɗiyesu ta shiga ƙoƙarin yi, sai kuma ta juya ta sake rungumeshi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a goshinta da hancinta ya sakko saman lips ɗinta. “In sha?”. Ya faɗa cikin raɗa yana nuna mata lips ɗinta da yatsa. Murmushi ta sakar masa a karo na farko da hawaye. Shima sai ya murmusa da kai nasa lips ɗin saman nata. A hankali suka lumshe idanu a tare kowanne na sauke ajiyar zuciya, daga haka tsarin ya canja zuwa wani fage daban...
Yana zaune a bakin gado yana goge jikinsa da ƙaramin towel ta fito itama sanye cikin bathrobe. Idanu ya zuba mata cike da jin ƙarin ƙaunarta da tausayi, suna haɗa ido ta ɗauke nata cikin jin nauyi. Wucesa tai niyyar yi ya riƙo mata hannu. Batare data juyo ba ta furta, “Zan shirya ne fa na haɗa maka abinci”. Murmushi yayi da jawota baya ya zaunar a saman jikinsa. Cikin kunneta ya raɗa mata maganar da ta sakata jin rikicewa dan kunya, shiko ya shiga darawa abinsa. Tashi tai zumbur a jikinsa ta gudu zuwa gaban mirror tana murmushi da faɗin, “Ni dai babu ruwana wlhy”.
“Daga baya kenan yarinya”. Ya bata amsa yana tasowa zuwa gaban mirror ɗin shima. Da jikin mirror ɗin ya jingina, hakan ya basu damar facing juna. “Miya sakaki kuka?” ya jeho mata tambaya dai-dai tana ƙoƙarin warware gashinta data naɗe a cikin ƙaramin towel. Numfashi ta ɗan firzar a hankali idanun nata na sake cikowa da hawaye, murya a raunane ta ce, “Nadiya ce”.
“Nadiya kuma? Who is she?”.
“Ƙawata ce, sai dai bama tare yanzun”.
“Ya akai banji sunanta a labarinki ba?”.
“A Nigeria na santa ai, kaima kuma ka santa ma. Dan ka taɓa kai ni shagonta saloon”.
Cikin ɗan yin jimm na alamar tunani ya ce, “Okay na gane, ba itace kikace zata taimakemu ba?”.
“Yes ita”.
“Uhmum miya faru da ita?”.
Wayarta ta ɗauka ta miƙa masa. Amsa yay ya duba. Recording ne na video call da sukayi ita da Nadiya. Shi kansa da farko bai ganeta ba. Al'amarin ya girgiza shi da bashi tsoro. Jiki a sanyaye ya miƙa mata wayar batare da ya iya furta komai ba. A bazata Lulu data sake fashewa da kuka ta ce, “Aliyu nagode da ƙoƙarin ka a kaina, bani da abinda zan iya biyanka da shi a duniyar nan face na dawwama ina maka addu'a har ƙarshen numfashi na kai da Uncle Yousuf. Yanzu nima da ALLAH bai taimakeni, kun tallafi rayuwata kun cireni da ga wannan mummunar ƙazamar rayuwar ba da hakance zata kasance da ni. Abinda nake sha ko rabinsa Nadiya bata iya sha fa. Amma kaga yanda rayuwarta ta koma, bata da maraba da mahaukatan kan layi masu wucewa yara na musu atire. Iyayenta sun korota a makaranta data lalace take kwana tsakkiyar kazaman ƴan shaye-shaye. Na shiga uku Hydar wace irin rayuwa ce muke jefa kammu ne haka?....”
Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yanda take kuka na fitar hayyaci. Ɗagota yay ya rungumeta a jikinsa, tare da fara jera mata kalaman lallashi da nasiha. Sun jima a wajen tsaye ya karasa busar mata da kan nata ya ɗaure mata shi. Cikin son kauda mata yanayin ɓacin ran nata ya ce, “Ina auntyn taki wai, naga da Iya Tabawa kawai muka gaisa tana goye da AA”.
Murmushi ta ɗan saki kaɗan, sai kuma ta kallesa tana ɗan lullumshe ido cike da salon dake narkar da mutumin nata tace, “Tana asibiti ai, tun randa suka zo”.
Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce, “Asibiti kuma Madam”.
Sai da ta ɗan hararesa saboda kiranta Madam sannan ta bashi amsa. “Eh ai abinda ya kamata ayi kenan, mizai sa na riƙeta a gida har sai ka dawo kuma. Yanzu kam kaga har sun bamu ranar da zasu mata aikin ma. Sai ka ƙarasa shiryawa muje ka ganta dama Doctor ɗin ta buƙaci ganin mijinta, sai dai nace mata baya kusa sai ƙaninta dai.”
Rasama mizaice mata yayi shi kam, sai kawai ya zuba mata idanu yana kallonta, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya huta ma kawai. “Kallon fa?”. Ta faɗa tana wani tura masa baki da kashe masa ido ɗaya. Hannu ya kai zai cafkota ta zille tana dariya. Shima sai ya murmusa yana dimtse gefen lip ɗinsa da haƙori. Kayanta ta maida dan bata son Iya Tabawa ta zargi komai tunda ta ganta da su. Ta dawo gaban mirror ɗin ta maida ɗaurin ɗan kwalinta kamar yanda yake ɗazun da yin ƴar kwalliya.
Shima sai ya nufi closed ɗinsa ya saka kaya. Tsaff suka fito suna zuba ƙamshi da annuri, ita sai yanzu ma ta san ashe tare yake da Ahmad. Amma yake komansa hankali kwance a ciki kamar bai bar kowa na jiransa ba, shiyyasa da zata fito ya sakata sanya abaya ashe. Sun gaisa da Ahmad yana faman tsokanarta kamar yanda ya saba. Ita dai nata murmushi ne musamman daya kasance boss ɗin nata ya watso mata kallon gargaɗi. Abincin da suka sha wahalar yi ita da Iya Tabawa ta gabatar musu. Sosai Smart yaji daɗin ganin tuwo, dan zai iya cewa tunda ya baro Nigeria bai sake ci ba. Kasa haƙuri yayi ya tambayi inda suka samo garin tuwo haka. Lulu ta bashi amsa da cewar su Aunty Bilkisu ne sukazo musu da shi. Bayan sunci sun ƙoshi kaɗan suka huta Lulu ta takura musu dole suka fice zuwa asibiti duba aunty Bilkisu, zuwa lokacin AA ya tashi yana hannun Babansa da yay kewa.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣
......Sosai Smart ya tsinta kansa cikin farin cikin ganin ƴar uwarsa, duk da tana kwance a gadon asibiti hakan bai hanasu yin hira ba. Anan ne take basu labarin halin da Ummah ke ciki a yanzu. Babu ɗigon tausayinta a zukatansu sai Smart kawai, duk da yana jin ɗacin rabashi da matarsa da tayi hakan bai hanashi jin tausayinta ba. Dan ko babu komai tunda ya taso kallon uwa yake mata, sannan jininsa ce ita tunda ƴar uwar Abba ce. Sun jima a asibitin, dan Smart ya gana da doctor sun tattauna, daya buƙaci yanda biyan kuɗi zai kasance sai ya samu Lulu ta biya komai har kuɗin aiki dana gaba ɗaya zaman da zatayi ma a asibitin. Kasa cewa komai yayi har suka dawo gida. Sai dai sun sauke Ahmad a masauki. A falo suka sake zubewa aka ɗaura hira, Iya Tabawa na basu labari suna kwasar dariya. Sun jima a wajen kiran wayar Smart da akayi ne ya sashi miƙewa ya shige bedroom, hakan ya bama Lulu damar bin bayansa bayan wani lokaci. Ta samesa har lokacin yana waya da Usman da ke bashi labarin irin halin ruɗanin da Alh. Sulaiman da abokan cin mushensa suke a ciki. Sai saƙon daya bada aka aika masa ɗin nan. Sosai Smart ke kwasar dariya har yana jin inama yana Nigeria yaga wannan ruɗani a fuskar Alh. Sulaiman. Sai dai babu komai yasan zai gani ta cikin direct camara ɗin da suka sanyama Alh. Sulaiman batare daya sani ba. Bayan sun gama wayar ne yake bama Lulu labari, itama dai dariyar tasha da jin inama tana 9ja ake wannan irin cakwakiya haka.
AA ya tambayeta ta ce ai ya koma kwana wajen Iya Tabawa. Da mamaki yace, “Abincinsa fa?”.
“Wane abinci kuma bayan wanda yake ci ya ƙoshi. Ai ni na yayesa”.
“Yaye a wata goma sha ɗaya? Wane irin rashin tausayine haka Baby luv”.
“Haba kai kam miye abin rashin tausayi anan. Nifa wlhy dama so nake ya taka kawai, yaron da dama ba wani ya damu da shan nonon bane ba.”
“Kin dai so yayesa saboda kina buƙatar wani babyn”.
“Kamar ya?”.
“Kamar yanda kika ji mana”.
Ganin kamar cikin ɗan zafi yay mata maganar ya sata jan bakinta tai shiru. Ita matsalarta da shi kenan saurin fushi. Abu kaɗan bazai fahimcesa ba sai ya hau kamar fulawar burodi, sai idan shi yaso shanyewa ya nuna kamar bai gani ba. Bata yarda ta sake magana ba. Shima sabgar gabansa ya cigaba da yi batare da ya kulata ba. Ganin abin nasa babbane ta fita ta bar masa ɗakin dan bata buƙatar wani ɓacin rai kuma a yanzu....
Bayan kwana biyu da dawowarsa akaima Aunty Bilkisu aiki. Duk halin da ake ciki jama'ar gida sun san komai. Dan haka kowa nata faman addu'ar nasara. Alhamdullah anci nasarar kuwa, dan anyi aiki har an kaita ɗakin hutu, basu sami ganinta a wannan ranar ba sai washe gari da safe. Sunji farin cikin samunta a cikin hayyacinta. A take kowa farin cikin sa ya gagara ɓoyuwa. Fatansu kuma yanzu ALLAH ya bata lafiya. Smart bai sake ma Lulu magana akan yaye AA ba, itama bata sake tayar masa da zancen ba har ya sake barin London ɗin a weekend daya zagayo. Sunje yin wasa, yayinda ita kuma take cigaba da zama tsaye akan al'amarin aunty Bilkisu daketa samun lafiya. Kullum sai sunyi waya dasu Ammah da kuma ƴan gidansu ta video call, musamman ma Ummita da ke tsaye akan al'amarin Nadiya dake a asibiti ita da Uncle Yousuf. Kwanan Smart uku ya dawo, yayinda Ahmad ke shirin komawa Nigeria. Taka tsantsan ta dingayi a ƴan kwanakin nan na ganin saɓani bai shiga tsakaninta da mijinta ba. Alhamdullah kuwa anci nasara, dan banda murzar juna babu abinda sukeyi sai zuwa asibiti wajen aunty Bilkisu da ɗan fita hutawa domin bama kansu farin ciki. Sosai kuma suna samu, dan yanda suka murje tsaff da su, ga tattalin juna da nuna kulawa kowa yasan hankalinsu ya kwanta. Sun kuma samu nutsuwa irin wadda duk wani mai aure ke buƙata a rayuwa. Sai ɗan saɓanin da ba za'a rasa ba na tsakanin harshe da haƙori dake zuwa yau da gobe. Duk yanda Lulu zatayi kuma takanyi na ganin abin baiyi nisa ba ta shawo kan abinta ya huce, shima kuma da yake bason ganinta a damuwa yake ki ɓacin rai ba baya barin abin yay nisa sam.....
*_NIGERIA_*
Alhamdullah an samu nasarar dawowar Ummah dai-dai, nakan dutse ya gama kunce ƙullin daya ƙulla su Salim suka miƙashi hannun ƴan sanda batare da sun saurari bayanin da yake musu akan bafa wai Ummah ta kuɓuta bane ba ɗari bisa ɗari, dolene sauran bala'oin data saka akai mata aiki akan Smart ɗaya bayan ɗaya zasu cigaba da dawo kanta. Sai ta shirya. Babu wanda ya sauraresa, sai yan jarida da suka kafa suka tsare har sai da suka samu cikakken bayani a bakinsa. A take fa al'amarin Umma ya shiga media da duniyar yanar gizo dana kafafen ƴaɗa labarai musamman irin na rediyo. Kafin kace mi mutane da yawa sunji kuma sun sani anata ALLAH wadai da al'amarin nata tare da mata irinta.
Ana wucewa da nakan dutse dole itama Ummahn aka kwasheta zuwa asibiti dan hawan jini ya mata biji-biji. A asibitin ma dai ƴan jarida basu barsu sun huta ba da jama'ar gari ƴan so da jin ƙwaƙwaƙwaf. Musamman ma da ya zam hotunan Ummah sun gama zagaye gari a suffar Dodo, saboda lokacin da nakan dutse ke ƙoƙarin warware asirin mutanen da suka samu shigowa musam yaran maƙwafta ɗauka suka dinga yi a wayoyi suna sakawa a shafukan su na sada zumunta. Dan danan fa sunan Ummah da Hajiya Naqiba yay amsa kuwwa a duniyar labarai da yanar gizo. Dan hatta Hajiya Naqiba basu bari ba sai da suka bibiyi al'amarinta.
(Su Umma an zama celeb.... sai ku tayata murna🤣😂).
A washe garin da aka wuce da Umma asibiti Smart ya buƙaci su koma gidan daya kama musu domin fara gyara wanda suke a ciki. Kusan dama a shirye suke da hakan, dan haka babu ɓata lokaci suka tattara zuwa can ɗin nan kuma aka bajeshi aka fara aiki bisa tsayawar Coach da manyan yaran gidan duk da Salim ya nuna hassadarsa a fili. (Nonon Ummah ba wasa ba ai🤣🙏).
Suko su Mubarak farin ciki suke abinsu ganin za'a gyara musu gida. Sai addu'a da fatan alkairi suke jerama Smart. Mazansu da matansu haka suka dinga kiransa suna godiya. Duk da wasu sun gagara hakan musamman a mazan saboda baƙin ciki. Dan Mama ita kanta a wannan gaɓar Hassadarta ta gagara ɓuya. Sai da taga Abba na neman birkice mata ne fa ta kama kanta. Sai ƴaƴanta mata da suka nuna mata karfa ta tafka kuskure makamancin na Ummah. Dole ta kama kanta ta koma yaƙe da addu'a a fatar baki. Ƙasan zuciyarta kam kamar zata ƙone, a ganinsu dai ƴaƴansu ne sukafi cancanta da wannan arziƙin.
Ni dai nace, “Hummm🥱🚴🚴”.
__________★
A ɓangaren su Alh. Sulaiman suna tsaka da kukan targaɗe sai ga karaya ta samu. Dan kuwa dai al'amarin Nadiya ma ya bayyana wa duniya. Inda ta tabbatar da cikin jikinta na su Hon. Nakowa ne dan su duka babu da wanda bata mu'amula. Ta kuma tabbatar da cewar su ɗin manyan diloli ne na miyagun kwayoyi, dan ko ita sune suka koya mata shaye-shaye. Ta kuma tabbatar da in har sunce ƙarya ne su fito duniya su musa zancenta ita kuma zata bada manyan hujjoji a kansu. Tace bayan itama akwai yara da yawa da suka lalatama rayuwa ta hanyoyin shaye-shaye da zinace-zinace. Wasu sun jima da rasa ransu, wasu iyayensu sun koresu a gida sun shiga duniya. Wasu kuwa a gidan iyayen nasu ake lalata musu rayuwa batare da iyayen ma sun sani ba. Acewarta Bama su kawai ba, akwai manyan ƙasar da dayawa sukai suna da nisa a irin waɗan nan al'amuran, su suyi ƴaƴansu suyi. Ba kunya Uba da ɗa za'a haɗu a club ko da ƴa anama juna kallon kallo. Akwai wanda ake kaima yara ƙanana gida suyi musu fyaɗe, wasu ma harda maza sukemawa. Ta tabbatar da idan zata tona asirin mutane da yawa akan wannan al'amarin tofa manyan nan da yawansu bazasu sha ba a bisa madafun ikon da suke kai. Dan haka a rufe rufau kawai. Wannan video ya girgiza al'umma da yawa. Yayinda ya bama wasu da ke fuskantar irin raɗaɗin da Nadiya ke a ciki fitowa suma suyi magana. Fiye da yanda ba'a zato al'amari ya sake rincaɓewa. Dan kuwa a ranar kame na hauka jami'an tsaro sukayi, kuma duk yaran su Alh. Sulaiman ɗinne da Nadiya ta dinga lissafowa a faifai. Inda kuma duk akayi dacen kamasu dumu-dumu da abinda ta lissafa ɗin kasancewar dama sai da aka shirya musu talala aka saki video ɗin.
Zuwa yanzu kam su Alh. Sulaiman sun tabbatar da akwai mai musu zagon ƙasar nan. Duk da shi