Showing 54001 words to 57000 words out of 127646 words
ƙasar ɗinne. Lulu dai tayi mamakin a ina suka kwasosu? Da yanda suke girmama Smart ɗin da wani tattalinsa duk ya ɗaure kanta dan kowa dai yasan waye bature. Sai dai batace komai ba dai ta bar abinta a zuciya tana taɓe baki. Gaba ɗaya taron nasu dai basu fi su ashirin ba. An kuma yisa cike da birgewa da ƙayatarwa, gashi babu wata hayaniya sai ɗan cool music da aka saka na waƙoƙin masoya, duk da dai Ahmad ya saka waƙar data shiga har cikin jini da ɓargon Lulu da Smart ta hausa. Wato (Labarina baya zama nawa ta Salim Smart da KEWA ta Auta Waziri). Amma da farko basu saka ba saboda su Abbah. Sai da sukai addu'oi wa jariri da mai jego dama uban jego sannan. Can cikin lambun Abbah da Daddy da mahaifin Usman suka koma abinsu suka baje suna hirarsu ta dattijai da tarin abinci da aka shirya musu. Yayinda Ahmad da Usman da hali yazo ɗaya a rawar kai suka warware sautin sai dai bamai hayaniya ba. Ansha hotuna kala da iri, sai dai a duk sanda za'ai Smart na naniƙe da Lulu, idan da namiji za'ai tana gefensa ta inda babu kowa bai yarda wani ya raɓar masa mata ba. Tunma su Usman basu farga ba har suka fahimci mutumin nasu fa akwai kishi. Sai suka kama kansu suma yanda bazasu takaloshi ba. Ahmad ne dai kam ya addabesa tako ina da ina, sai dai tunda ya iso AA na hannunsa ya kasa bama kowa. Har cikin rai ƙaunar yaron yake ji tamkar shiya haifa. Yace dai surukinsa ne dan shi da Maryam ɗinsa zasu haifa masa mata. Anyi dariyar zancen nashi, yayin da Smart ya ce, “ALLAH ya shiryeka kai dai. Kadai fara tara ƴaƴa sai ka fara canjawa”.
“To dama ance maka ban canja bane. Kana ganin har na fara furfura zuwan My Son duniya kuma surukina.” cewar Ahmad yana hararar Smart. Murmushi kawai yay masa da girgiza kai. Taro kam Alhmdllh, sai dai Lulu ana kammala hotuna ta koma ciki wajen Ammah da Mamy da suka basu waje suma saboda yanayin jikinta. Shima dai AA ba'a saki jiki da shi a wajen ba saboda sanyi. Sun ɗan samu gift dai-dai misali, zuwa dare taro ya tashi kowa ya kama gabansa. Gajiya ɗan kai da kawon da suka sha a yinin jiya yasa su Smart wucewa da wuri domin kwanciya.
Washe gari suka tashi Lulu nata rakin ciwon kai. Sai da Ammah tai mata addu'oi a ruwa tasha aka kama mata kan sannan. Lokacin da su Smart suka iso ya lafa mata. Tana cikin rubutu a littafinta Smart ya shigo da sallama su Ahmad biye da shi. Sai da ta saka mayafi yace su shigo. Sun gaisa da tambayar juna gajiyar taro Ahmad ya ɗan tsatstsokaneta sannan suka fito suka barsu. Smart da tun shigowarsa hankalinsa ke akan book ɗin da takema rubutu sanda ya shigo ta ɓoye. Suna fita ya kai hannu bayanta zai ɗauki littafin tai saurin buge masa hannu tana ɓata fuska. Idanun nan nasa ya kafeta da su babu walwala sam tare da shi. Duk sai taji ta daburce saboda mugun kwarijin ya mata da cika waje. Shima babu wasa a tattare da shi murya a dake ya furta, “Kinada wani abun ɓoyewa ne da kike ganin saninsa a gareni illa ne?”.
Fuska ta tsuke cikin cuna baki batare data amsa masa ba. Shima sai ya sake dakewa da koma mata Smart ɗin nan mai ɗaukar kai da manna mata hauka sanda yana drivern ta. A kausashe ya furta, “In ma baki son na sani kin makaro. Domin ɗayan littafin ai yana gareni. Banyi niyyar karantawa bane kawai dan nafi son jin komai daga bakinki ba'a rubuce ba.” Da sauri ta ɗago tana kallonsa, ya ɗauke kansa gefe kamar bai ganta ba. Sai kawai taji hawaye sun cika mata ido. Cikin rawar murya ta ce, “Da gaske kakeyi?”.
“Na miki kama da ɗan wasan kwaikwayo ne da zan miki ƙarya?. Mawaddat ɓoye-ɓoyen nan bazai kaiki ko'ina ba face cigaba da dasa miki damuwar da zata iya maidaki ga abinda kika baro. Mi kike ɓoyewa? Miye baki son a sani? A zatona ko zaki iya cigaba da binnewa kowa abinda kike kallo a sirrinki ni zan kasance ba'a cikinsu ba saboda kasancewata mafi ƙololuwar SIRINKI a yanzu. Amma bazan cigaba da takura miki son sani ba ki cigaba da riƙon abunki in dai nine bazan sake tambayarki ba”. Ya ƙare maganar kamar cikin ƴar fusata zai juya yabar ɗakin. Hannunsa ta riƙo da sauri, hakanne ya sashi tsayawa cak sai dai bai juyo ba, ya dai lumshe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Itama batare data tashi ba cikin shashshekar kukan da ke sukar masa zuciya a hankali ta furta, “Aliyu ban san miyasa kake son ji ba? Babu wani abin sha'awa ko birgewa a son jin abinda ya shuɗe da ga tarihin rayuwata. Babu wani abin alfahari ko ƙayatarwa face baƙin ciki da takaici a cikin jiyana. Taya zan faɗa maka na taɓa kashe mutum da hannayen nan nawa ne?, kuma wlhy ban taɓa jin nadamar aikatawar ba har yau har gobe da ma ƙarshen numfashi na. Aliyu ban san taya kake son na faɗa maka na rasa Nanny na data raineni tamkar uwa ba a dalilin kisan da nayi ba, ta amshi laifin daba nata ba, ta rasa ranta a dalili na, Aliyu alhakinta bazai barni na rayu cikin salama ba...” ta sake sakin kuka mai tsuma zuciya.
Sosai shima yake haɗiyar zuciya, maƙogwaronsa sai faman kai kawo yake a cikin wuyansa. Idanun maza sun masifar kaɗawa. Da ƙyar ya iya controlling temper ɗinsa tare da firzar da numfashi mai nauyi ya juyo a hankali gareta. Har lokacin hannunta a cikin nasa ya zauna a kusa da ita. Jikinsa ya jawota ya rungume, hakan sai ya bata damar sake sakin kuka tana ƙanƙamesa kamar mai gudun a rabasu. Bai hanata ba, sai tambaya da ya jeho mata kai tsaye. “Taya akai kika aikata kisan kai? Dan nasan kinada dalili mai ƙarfi Mawaddat, bakiyi kalar masu aikata irin wannan laifin bisa son zuciya ba. Please faɗamin miya faru a shekarun baya a tsakaninki da Nanny ɗinki?”.
Cikin haɗiyar zuciya da shashshekar kuka ta furta, “Johanna itace Nanny na dana buɗa ido na gani a tare da ni tamkar uwa mahaifiya. Duk da dai kafin a kaini gareta na ɗan rayu a Nigeria hannun mahaifina da matarsa, sai dai babu abinda zan iya tunawa a wannan rayuwar saboda ƙarancin shekaru na. Nanny na da nake kira da Mah-mah Ta raineni ne tamkar zinariya, tana bani dukkan gata da uwa ke bama ƴaƴa duk da kasancewarta kafira. Bata taɓa cewa nabi addininta ba balle akai gata tilasta ni. Duk da na kasance mai tsiwa da rashin ji komai nai a gareta abin farin ciki ne, sai taga zan kauce da yawa ne take saurin gyara min duk da bata kasance muslma ba. Daddy na yawan zuwa gareni, dan haka nake ɗauka shi da ita duk iyayena ne, sai da na fara ɗan wayo na fara damuwa akan ƙin kwana da Daddyna keyi a gidanmu idan yazo Germany, ya yarda ya yini da ni a gida koma ya ɗaukeni mu fita yawo amma dare nayi zai wuce masaukinsa. Nakan masa ƙorafin hakan amma sai yay murmushi kawai. Itama idan na tambayeta miyasa Daddyna baya kwana tare da mu kamar sauran abokaina da iyayensu takance min aiki ne ke hanashi hakan.........✍️
NEXT PAGE PLEASE 🚴🚴🚴🚴
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣
........Ban fara shan jinin jikina ba sai dana ga wani yana yawan zuwa wajen Mah-mah. Atake naji na tsanesa, ko yazo gidan bana kulashi duk iya maganar da zai min, ko abu ya kawo min bana amsa. Idan kuma ya ba Mah-mah ta bani indai nasan shine ya kawo bana ci. Yana shiga damuwa da yanda nake masan har ya kasa daurewa ya sanar da Daddy. A wani zuwa da Daddy yay ne yake sanar min ai Felix yaronsa ne na amana, duk wani kai-kawo akan business ɗinsa na Germany shine ke masa. Yana zuwa wajen Mah-mah Kuma saboda harkar business ɗinne, dan itama akwai abinda take riƙe masa. Wannan zance na Daddy ya sani ɗan sakin jikina da shi, a dalilin haka na gane ashe basu da wata alaƙa da Mah-mah ɗina, A duk sanda yazo suna tattauna harkar business ɗin ne kam da gaske. Hakan sai ya sani sake sakin jiki da shi har ina kiransa Uncle, yakan ɗauke ni randa ba makaranta ya fita dani yawo yayo min shopping kamar hauka. A wani zuwa da Uncle You yayi ne yaga wannan al'amari, cikin tashin hankali naji yanama Daddy faɗan mizai sa ya bar Felix ya shiga jikina har irin hakan a matsayinsa na namiji da Business ne kawai ya haɗa su, miyasa ma ya nuna masa wannan gidan. Shi ya yarda da Mah-mah na shiyyasa damuwarsa a kasancewarta mai kula dani ilimin addini da ake neman tauyeni ne kawai. Amma sam baiji ya yarda da Felix ba sam. Naji haushin Uncle You a lokacin, dan akwai shaƙuwa tsakanina da Felix, Kun san yaro dai. Har Uncle You ya gama min hutu a wannan karon ban saki jiki da shi ba, bai damuba bai kuma daina kulani ba. Tun daga wannan lokacin naga Felix ya daina zuwa gidan. Ba irin tambayar da bamma Mah-mah ba sai tace min yayi tafiya ne mai nisa. Akwana a tashi na fara mantawa da Felix a zuciyata, sai wataran katsam gashi, a lokacin inada shekaru goma sha kusan uku, dan kaɗanne ya rage na ƙarasa tunda har secondary na shiga, duk da dai su kasan karatun nasu bawai kamar namu ne na Nigeria ba, shiyyasa ma na kammala karatuna da wuri gaba ɗaya a ƙarancin shekaru. Zuwa lokacin na manta da shi, shiyyasa ban wani sake masa ba, ga shi kuma na fara hankali. Yaso jana jikinsa amma sam naƙi sake masa, idan ma yazo gidan ko fitowa falo bana yi sam. Ni ban san ashe wannan abun naci masa rai ba har yanama Mah-mah korafi, takanyi dariya tace masa na girma ne yanzu na zama ƴammata na fara kuma mantawa da shi..
A wata ranar asabar Mah-mah ta wuce wajen ibadarsu sai ni kawai a gida da mai aikinmu. Ina ɗakina na baza books na makaranta ina dubawa, jikina daga ni sai ɗan bomshot da best, kaina ko ɗan kwali babu sai jin mutum nai kawai ya faɗo min. Raina ya ɓaci ganin Felix. Dan ko sanda inada ƙuruciya baya shigamin ɗaki ai, balle yanzu da a iyayin tashi cikin jar fata yake sakani jin na zama ƴammata ni da ƙawayena. Cikin masifa nace mizaisa ya shigo min ɗaki, ya fita bana son shirme. Maimakon ya fitan sai ya tsaya kawai yana kallona, dan gaskiya inada tsiwa sosai tun da ƙarancin shekaru na. Dariya ya shigayi irin ta shaƙiyanci, batare da ya damu da masifar da nake masan ba ya murzama ƙofa key ya nufoni. Da farko na ɗauki al'amarin nasa wasa, sai da naga yana yunƙurin rungumoni jikinsa ne raina ya ɓaci, duka na shiga kai masa ina janye jikina, ganin bazan bashi haɗin kai a yanda yake so ba ya kamani ya ɗaure, hankalina ya tabbatar min da yana son wulaƙantamin rayuwa ne. Ina kuka da roƙonsa da magiya amma bai sauraren ba ya ciremin kaya kaf shima ya cire nashi. Aliyu wlhy ban taɓa sanin minene tashin hankali ba sai a wannan ranar, tsabar tsoratar da nai da ganinsa babu sutura ban san na suma ba, sai da ya ɗiba ruwan sanyi a Despenser ɗin ɗakina ya sheƙamin na farfaɗo. Zaginsa na shigayi cikin matsanancin tashin hankali bayan dawowa a hayyacina ina tofa masa yawu a fuska, shiko ya shiga marina yana dariya, da yaga na ƙi daina zagin nasa marin ma bazai masa ba ya cire belt dinsa ya dinga dukana da ita, tamkar ya samu wata babbar mace yay min duka na hauka, har yanzu da sauran tabbunan dukan a jikina wasu basu ƙarasa ɓacewa ba. Ga jini a sayin inda ya bugeni, ga kumburin fuska data sha mari da fashewar baki, ga haɓo da dukan da yay min a gefen ido duk bai duba wannan ba ya nema haike min. Na riga na suma saboda firgita dan ya na gab da cimma burinsa na suman, shiyyasa ban san yanda akai Mah-mah ta samu nasarar shigowa ɗakin ba, ita ce ta kuɓutar dani batare da ya samu nasara a kaina ba. Kiciniyar kwanceni da dukan da yake mata ya sani farfaɗowa, sai dai kafin ta ƙarasa kwanceni ya kaita ƙasa da duka itama. Ina kuka da zaginsa a saman lips dan ko magana bana iyayi dan wahala ya kekketa mata suturar jikinta ya ɗaureta kamar yanda ya mun, a gaban idona ya keta mata mutuncinta ta hanyar mummunan fyaɗe, ya kuma juyata ta baya nan ma ya wulaƙantata. Suma ta biyu ko a lokacin dan tashin hankali. Ban taɓa sanin ana suma a dawo a suma a dawo ba sai a wannan ranar. Kaina ya dawo yana wata ƴar iskar dariya da tabbatar min sai ya wulaƙanta min rayuwa fiye da yanda yay ma Mah-mah dake kwance cikin jini face-face bata ko numfashi sosai. Ban san yanda akai wani irin ƙarfi yazo min ba na halbesa da ƙafata a gabansa, azaba ta sakashi duƙewa, pen ɗina da nake aiki da shi kafin shigowarsa na ɗauka na buga masa a wuya, banyi tunanin zai iya mutuwa ba, a haukana hakan da zan masa ai zai tashi idan aka kaisa asibiti kamar yanda naga a film yana faruwa. A take ya saki razananniyar ƙara da zubewa a ƙasa hannunsa ɗaya riƙe da gabansa ɗaya ya riƙe wuyansa. Dai-dai nan mai aikinmu ta shigo, ashe matsiyacin aikenta yay kasuwa dan ya samu damar min illa ALLAH ya kawo Mah-mah ta dawo gidan. Ihunsa ya sata shigowa, koda ta shigo taga a yanda muke mu duka ukun sai itama ta fasa ihu da komawa da gudu, itace tai kiran ƴan sanda, abinka da inda akasan kimar ɗan adam, cikin ƙanƙanin lokaci sai gasu sun iso, a gaggauce aka tattaramu duka zuwa asibiti muduka ukun. Ban dawo a yahhacina ba sai bayan kwana biyu, a hakan ma ko yaya namiji yazo kusa dani na dinga firgita kenan harda ihu ina roƙon karya cutar dani, duk wanda ya ganni sai ya tausaya min sosai. Ashe nawa wasane, dan Mah-mah ita gaba ɗaya ma brain ɗinta ta birkice, ga wata irin jijjiga da jikinta keyi, a taƙaice dai kamar ta haukace ma kawai..... Felix Kuwa ashe abinda nai masa ya mutu. Ƴan uwansa sunce bazasu yarda ba tunda kashesa akayi, wannan dalilin ne ya saka aka maida hankali akan bama Mah-mah kulawa harta ɗan dawo hayyacinta, an tattara case zuwa kotu. Daddy bai zo ba, Uncle Yousuf bai zo ba har sai da muka samu kusan sati uku a asibitin, zuwa lokacin an miƙa case kotu har an ajiye ranar zaman shari'a. Ana gobe fara shari'ar Daddy ya iso Germany, ya shiga matsanancin tashin hankali da ɓacin rai akan abinda Felix ya aikata, a ranar bai zauna ba sai da ya samo ƙwararren lawyer, washe gari aka shiga kotu. Mah-mah, bata wani bari shari'ar ta ɗauki lokaci ba ta ce itace ta kashe Felix saboda yayi mata fyaɗe ta ƙarfi. Duk yanda naso faɗar gaskiyar abinda ya faru bani da dama saboda tun a daren jiya ta roƙeni akan kar nace komai, na rufa mata asiri kar Daddy yasan ni Felix ya fara hara, dan hakan zaisa ya kalli rainon da tai min a matsayin sakaci, koma ya ɗauka dama a haka take sakaci da al'amarina tun can baya. Kawai idan anje kotu zatace a wajen cetonta ne Felix yay min wanna dukan. Yanda ta tsara ɗin haka ta faɗa a kotu, bayan gama saurarenta da lawyer da dangin Felix suka kawo alƙali ya yanke hukunci, wannan yanke hukunci ne ya sake birkita ƙwaƙwalwar Mah-mah take a wajen ta shiga wani yanayi irin na masu taɓin hankali sosai, a gaggauce aka maida ta asibiti kamar yanda alƙali ya bada umarni, hakan bai wa dangin Felix daɗi ba, dan ba haka suka so ba, sai dai babu yanda zasuyi. Sashin masu taɓin ƙwaƙwalwa aka kaita, ana kula da ita yanda ya kamata bisa tsayawar Daddy. Hankalin Daddy ya tashi matuƙa game da halin da ya ga Mah-mah ta shiga ciki, sai dai rashin sanin yanda abin ya faru yasa shi bai yi tunanin da yanzu fa akaina abin zai faru ba, tunda Felix ni yaso ketama mutunci ba, ya ɗauka kawai wajen son ceton Mah-mah ɗin nawa ne kamar yanda ta faɗa na samu wannan mahaukacin dukan, wai dan ma na samu sauƙi sosai a lokacin. Kwanan Daddy uku da zuwa Germany Mah-mah ɗina ta mutu, ta bar duniya tana kuka da sunana bakinta....”
Kuka ne yaci ƙarfin Lulu, ta sake ƙanƙame Smart da tun ɗazun idanunsa sun kaɗa sunyi jazur alamar yana kukan zuci ne. Sake ƙanƙameta yay shima jikinsa na wata irin tsuma, ji yake kamar zuciyarsa zata fashe, kukanta na sukar masa zuciya da ruhi. Tayi kuka sosai kafin ta cigaba da faɗin, “Wannan al'amari shine sanadin barowata Germany, na fahimci Daddy kamar yana tsoron maidani Nigeria ne a wannan halin saboda su Uncle You, ya maidani U.S, in da aka sake sama min sabuwar Nanny sai dai baƙar fata ce, asibiti aka sake kwantar da ni a can farko dan nima