Showing 72001 words to 75000 words out of 127646 words

Chapter 25 - Furar Danko Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

19 Dec 2024

249

ɗan bi falon da kallo ganin fitila a kunne ga wani baƙon ƙamshi, sai dai bai kawo komai a ransa ba ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe bakinsa tunda yasan dai bayan Uncle Yousuf da yasan security ɗin gidan babu wanda zai iya shigo masa, sai ko Ahmad, maybe ya manta ne da zai fita bai kashe fitilan ba. Kayan shopping ɗin nasa ya kai duk inda ya dace sannan ya nufi bedroom ɗinsa hannunsa riƙe da jacket ɗinsa da ya zare ya ɗan sagalota a kafaɗa. Tafiya yake a hankali kamar cikin kasala da gajiya yana latsa waya da alama akwai abinda yake sonyi ko kira. Cikin rashin maida hankali ya tura ƙofar ɗakin da ƙafa ya shiga tare da sake turata da ƙafa ya rufe. Dai-dai nan take fitowa daga Bathroom sanye cikin rigar wanka pink da tazo da abinta. Sosai gabanta ya faɗi da ganin mutum ya shigo mata kai tsaye a inda batai tunanin ganin wani ba, duk da tun shigarta bathroom ɗin ta shiga halin tsarguwa amma ta dake. A bedroom komai need yake babu tarkace babu abinda aka bari a waje da zaisa ka zargin akwai mai amfani da ɗakin sai a toilet ɗin ne, sai dai wani tunani da yazo mata ya sata gamsuwa tai wankanta hankali a kwance.
        “Who are you Man?!”.
     Ta faɗa cikin faɗa da son dake razanar da tayi. Shi kansa gabansa ne ya faɗi, ya ɗago da sauri dan yasan bai bar kowa a gidansa ba shi dai, amma sai ga muryar mace a tsakkiyar kansa a cikin ɗakin barcinsa bama falo ba. A karo na biyu ƙirjinsa yay wata irin jijjiga ganin wadda bai zato ko tsammani ba, wayarsa da ke neman suɓuce masa a hannu yay saurin damƙewa, sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan gannin tayo kansa da masifa hannunta ɗauke da wani deco.. da ke ajiye a bedside drawer ɗinsa. Duk da yana a cikin yanayin ruɗani sai da ta so bashi dariya amma ya dake, yo abinda ta ɗakko ɗin ko buga masa tayi mizai ji duk da glass ne. Tana gab da zuwa ina yake ya ce, “Please Relax Ladyy”.
     Cak taja ta tsaya zuciyarta na harbawa da masifar ƙarfi dan ko'a magagin barci wannan deep voice ɗin bazata layance mata ba. Cikin rawar lips da ta murya ta furta, “Aliyu!”.
         Idanu kawai ya zuba mata ta cikin glasses ɗinsa na kusan sakanni talatin, kafin a hankali ya kai hannu yay ƙasa da mask ɗin fuskarsa tare da zare glasses ɗin. Idanun ya lumshe a hankali tare da sake buɗewa yana mai kamo gefen lips ɗinsa da haƙori. Kallon nasa da yanda gaba ɗaya ya canja fiye da ganin datai masa a lokacin haihuwar AA a Canada ya sata jin kamar jiri na neman kwasarta zuwa ƙasa ne ma. Shima yana jin fiye da abinda take ji ɗin, sai dai ƴan mazan a tsaye suke banda a ƙwayar idanunsa bata iya hango komai da zata iya bama fassara. Son tabbatar da ba aljana bace ko mafarkin da ya saba harta fara masa gizo ya sashi kauda idanunsa a kanta ya fara waige-waige. A saman gadonsa ya hango abinda yake neman a kwance yana barcinsa da alama ya gaji dan yayi wani baje-baje da ƴan kafafu da hannuwa yana zuƙar iskar sabuwar ƙasar Babansa da fesarwa cikin kwanciyar hankali. Karo na farko ya saki murmushi ganin wanda ya bari a jinjiri ya fara zama mutum, dan girman jikin AA yafi watanninsa yawa kasancewar ya ɗakko har tsawo irin na gida. Duk wanda ya kallesa yasan su ɗin jini ɗaya ne dan kamaninsa sun sake bayyana kansu matuƙa a tattare da yaron. Lulu da ke jin wani yamm-yamm kamar zata zube ƙasa a hankali ta furzar da iska mai nauyi tare da jan jikinta baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna cikin dafe kai. Wato ta fahimci Daddy da Uncle Yousuf wayo sukai mata kenan kawai. Shiyyasa taita fama da shi su fara zuwa U.S amma ya dage su fara zuwa UK yana da abinda zaiyi mai muhimmanci. Takun sawayensa ya sata kallonsa ta gefen ido, ganin kamar inda take yayo ya sata ɗagowa sosai tana masa kallo mai kama da harara. Sai kawai ya basar ya wuceta zuwa inda yaronsa yake.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣



........Tattaɓa shi ya shigayi idanunsa na cika da kwalla, sai kuma ya rankwafa da ƙyau daga zaunen da ya kai ya manna masa kiss a goshinsa da kumatu duk biyu. Kamar AA yasan mi ake ya wani juya abinsa ya kwanto a hannunsa. Murmushi yay mai kama da ƴar dariya, sai shima kawai ya kai kishin giɗe ya rungumesa a jikinsa sosai yana sakin ajiyar zuciya masu nauyi da shafa lallausar sumar kan yaron da Lulu ta hana a aske, sai gyaran fuska ake masa. Yaja kusan mintuna biyu a haka kafin ya ɗago idanunsa ya dubi Lulu da ke satar kallonsu. Kanta tai saurin maidawa gefe cikin taɓe fuska. A karo na farko yay magana cikin ɗan sakin murmushi. “Irin wannan bazata haka Madam?”.
       Mikewa tai tamkar bata jisa ba zuwa inda akwatin kayansu yake, dan ɗaya ta ɗakko jal ita da AA, kayansa ma sunfi yawa dan nata basu wuci kala uku ba sai kayan barci. Sai da ta zuge zip ɗin tana ƙoƙarin ɗaukar kaya sannan ta bashi amsa da “Sai yanzu kasan da ni?”. Bata jira amsarsa ba ta wuce closed ɗinsa hannunta riƙe da kayan data ɗauka taja labulen da aka sa a wajen wai dan karya kalleta.
Da ƙyar ya iya danne dariyarsa yana mai lumshe idanu, ya dai fahimci kishi ake da AA ɗinsa kenan. Mintuna kaɗan ta fito sanye da wando da riga marasa nauyi, sai dai yanda suka bi jikinta da fidda mata surarta fes ya saka zuciyar ƴan maza motsawa. Ga Lulu hakan normal ne, ita batayine dan wani birge miji ba, tun fil azal wannan shine dressing nata. Batare data kallesa ba ta wuce gaban mirror ɗinsa dake cike da turarruka da mayukan gyaran gashi sai abinda ba'a rasa ba. Gashinta taƙe ƙoƙarin tifkewa. Kwanciya ya gyarama AA tare da miƙewa, dai-dai tana tattare gashin cikin hannunta bayan ta zare ribbon ɗin data ɗaurosa da shi sukai ido huɗu da shi a bayanta. Yay wani tsaiwar ƙasaita irin na isassun maza yana kallonta da mayatattun idanun nan nasa. Sosai ta ƙara jin ƙirjinta ya motsa, tai azamar janye idanunta tamkar bata ganshi ba. Idanun ya rufe ya buɗe a lokaci guda yana ɗan ƙara matsawa jikinta daf ya mata runfa, sai kuma ya ƙarasa rungumeta a hankali tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. A tare suke ja numfashi da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Yanda yake wani bin wuyanta da shinshina idanunsa a lumshe ya sata jin tana neman zubewa a ƙasa, saurin riƙo hannayensa duk biyu da ke zagaye da ita a saman cikinta tai, hakan ya sakashi sake ƙanƙameta tsam-tsam kamar za'a ƙwace masa ita ya wani busa mata numfashi a cikin kunne....
     Harga ALLAH bazata iya ɗaukar wannan salon nasa ba, dan haka tai ƙoƙarin jan jikinta da saurin faɗin, “Wai nikam minene haka?” cikin rawar murya data lips. A cikin kunnenta ya raɗa mata “Saƙon barka da zuwa mana. Haka ya kamata ki tarbi mijinki _My Final Choice_”.
    Kanta ta matsar gefe tana taune lip ɗinta na ƙasa, cike da basarwar nan tata cikin son janye jikinta ta ce, “Kama nemo Final Choice ɗin naka bana son iyayi”.
         Sake ruƙota yay sosai yana murmushi. Idanunsa ƙyar a kanta ta cikin mirror ɗin ya ce, “Kowa yasan na nemo abita ai tuni. Dan duniya duk ta san Mawaddatan'warahmah ce Heart controller ɗin Aliyu Hydar Mika'il Mawashi”.
    “Kai dai ka sani”.
  Ta faɗa tana janye jikinta a nashi. Bai hanata ba ya saketa tare da harɗe hannayensa a ƙirji. Kallonsa tayi ta ɗauke kai da rusinar da idanunta. A hankali ta ce, “Malam matsamin na wuce”. Dan ya tsare mata ko ina. Bai matsa ɗin ba, bai kuma daina kallonta sama da ƙasa ba. Kallo irin mai haka mutum sukuni ɗin nan da ji iska ma na maka wahalar shaƙa. Ƙoƙarin raɓasa tayi ya tare, ta sake komawa ɗayan ɓangaren, nan ma ya tare, ta koma tsakkiya nan ma ya tare. Sai kawai ta zabga masa harara tana tunzura baki. Hannayensa ya warware da ƴar murmushi har sannan a fuskarsa ya ɗan matsota, baya ta matsa ta manne da mirrorn. Shima sai ya dafe hannayensa a mirror ɗin ta gefe da gefenta ta koma tsakkiyarsa, ya ranƙwafo sosai yana busa mata numfashinsa a fuska. Ga son su haɗa idanu da yake faman yi. Cikin daburcewa ta furta “Aliyu!”.
       “Uhmyim Mawaddat!”.
    Ya amsa mata kafin ma ta gama rufe bakinta, sai taji ma ta sake daburcewa dan yanda yay kiran sunan nata da amsawa acan ƙasan maƙoshi da busa mata numfashin yasa ƙafafunta ma suka fara rawar son kasa ɗaukarta. Ɗago idanunta da suka tara ƙwallar da ita kanta bata san dalili ba tayi, hakan ya bashi damar ɗaura lips ɗinsa akan nata kamar dama abinda yay target kenan. Kafin tai wani yunƙuri ya tallafi kanta da ƙyau da hannun damarsa, ɗaya hannun kuma ya saukesa akan bayanta. Sam bata da wani sauran ƙarfin yin wani yunƙuri, dole ta haƙura dan tasan wani buyaginta bazai sa ya fasa ba in dai shi ne, sannan ita kanta kawai ƙarfin hali ne tana buƙatar mijinta. Jin tsaiwar na neman gagararsu yay ƙoƙarin tattarota zai ɗaga. Da sauri ta tattaro nata ɗan hankalin waje guda itama ta kai masa ɗan duka a gefen cikinsa....
        “Ouch!”.
    Ya faɗa yana sakinta yana dafe wajen. Sai kuma hankalinta ya tashi ganin yanda ya duƙe, cikin rikicewa ta ruƙo hannunsa dake riƙe da inda ta bugesan duk da dai ita tasan kaɗan ta masa. Muryarta har rawa take wajen faɗin, “Please kayi haƙuri ALLAH ban san zai maka zafi ba, wayyo ni”.
         Sake langaɓewa Smart yay kamar gaske, ta kamashi ta jinginar da mirror ɗin tare da ɗan daga rigarsa tasa hannunta a wajen tana murza masa a hankali. Sake langaɓe murya yay yana faɗin, “Wayyo zafi Ammah kizo ta targaɗa miki ni”. Harga ALLAH Lulu ta ɗauka da gaske yake, dan haka ta sake ruɗewa har idanunta na tara ƙwalla, duk yanda yaso riƙe dariyarsa hakan na neman gagara, dole ya saketa dai-dai tana kwantar masa da kai a kafaɗarta.
      Galala tai tana kallonsa ga hawayen da suka cika mata ido na neman fara zubowa. Cikin son danne dariyar da ke ƙara tunƙuro masa ya ce, “Dama haka kika damu da Aliyu? Madam!”.
       Hararesa ta ballara masa da raɓawa ta gefensa ta wuce tana jan ƙafa da ƙyar dan ji take tamkar zata zube ƙasa ma. Shima sai yaja nasa jikin yana murmushi zuwa ƴar ƙyaƙyƙyawar kujerar dake gefe da ɗan table mara tudu dai-dai ita da zaka iya miƙe ƙafa a kansa ya zauna yana sauke numfashi da ƙaramar dariya. Sai da ya bada kusan mintuna biyu hankalinsa ya dawo jikinsa sannan ya tashi zaune da ga kwantar da bayansa da yay ya buɗe idanunsa a kanta. Tama kwance kusa da AA ne idanunta a lumshe ta wani dunƙule jikinta waje guda kamar wata baby. Ƙaramin murmushi ya saki da miƙewa ya fara zame kayan jikinsa da faɗin, “Ya kamata ki fara cin abinci kafin ki kwanta barcin ko”.
     Shiru kamar bazata amsa masa ba, sai can a takaice ta ce, “Ba buƙata”.
   Bai sake cemata komai ba ya nufi bathroom. Da kallo ta bisa, sai kuma rashin sake cewarsa koman ya bata haushi ta wani tura baki da hararar bayansa tana murguɗawa ta maida idanunta ta rufe. Ya ɗan jima kafin ya fito ɗaure da towel yana goge jiki da ƙarami. Kai tsaye wayarsa da ke ring ya nufa yana ɗan yamutsa fuska da kallon agogo. Bai niyyar ɗauka ba, sai dai ganin Ahmad ne ya sashi ɗagawar tare da ɗaukar bluetooth ya manna a kunnensa ya cigaba da abinda ke gabansa da alama Ahmad ɗin yake saurare.
       “Ka kira dai kayi gulma ɗan sa ido”.
    Dariya Ahmad ɗin ya kwashe da shi da ga can. Ya ce, “Ai kai dama ba'a maka abin arziƙi. Ni yarona na kira naji yaya yazo bai jigataba dai ko?”.
            “Ga shi nan na samesa yana kwasar barci dan sun shigo gidan na fita. Yaya kun gama da mutanen?”.
      “Har yanzu dai ana cuɗawa, naga sun ɗauki burin duniya sun ɗaurama wajen. Amma dai za'a dai-daita in sha ALLAH dan naga da Yaya yace zamu haƙura kuma kamar sun damu.”
   “Oh kuma dai?”.
“Ai kasan dama irin wannan matsalar ba daga masu kayan bane masu sayarwar ne”.
           A hankali ya ɗan furzar da iska da faɗin, “To duk yanda kukai dai?. Ya batun wancan aiki? Yaushe ne kuma shigowar taka?”
      “Ai maybe ma na fasa, dan business ɗin bai faɗa ba har yanzu, kasan abinda ma lura da shi komai suna fara yinsa ne a tsare kafin su sakeshi a kasuwa, amma dai shi guy ɗin nan ya tabbatar min zai haɗani da ogan nasu saboda nace masa ni dila ne, sannan pharmacy ɗin nan ya kamata aikinmu ya fara ta kansu dan na sake zuwa da takardar nan still sun saida min jiya. Kaga tabbacin maganarka kenan ta fito”
       “Hummm aina faɗa maka dama. Sai dai inaga kafin hakan ya kamata musan mai pharmacy ɗin. Sai Companyn da yafi kawo musu kaya. Dan ina son mu fara da mutuminka ne”
     “Uhm wannan ma tunani ne mai ƙyau, sai dai kuma kamar abin zai mana wahala nake ga. Kasan fa kai ka fini dabaru ta irin waɗan nan fannin”.
          Murmushi Smart yayi yana ɗan lumshe ido. Cikin ɗan furzar da iska yace, “Kaima zaka iya Ahmad. Ka nutsu na maka bayani, yaro zamu samar da zai nema aiki a wajen, ta silar yaron ma zamu samu abinda bamu hasaso ba ma. Plan a kenan, idan wannan zai ja mana lokaci plan b muja yaro ɗaya dake pharmacy ɗin a jiki, ta hanyar masa alkairi kasan dai yanda mutanenmu suka ɓaci da wannan karɓar na goran, a cikin biyun nan zamu dace da ɗaya”.
          “Yess boss na fahimce ka, kuma tabbas wannan dabaran yayi, shiyyasa nake sonka”.
     “Ɗan iska waye boss ɗin naka?”.
  Dariya Ahmad ya sanya da faɗin, “Kai mana. Zanyi ƙoƙarin nan daga nan zuwa next week, Dan Cameroon ma nake son zuwa kawo shanun nan dai. Ya kamata ka shigo ayi harkar nan da kai ALLAH, dan na hango za'a samu alkairi a ciki.”
     “ALLAH mutumina! Kaifa nasan baka wasa dama da harkar ƴan canji. Yanzu yaya za'ayi?”.
            Cikin dariya ya ce, “Masheranci, kaima naga ai bawasan kake da su ba. Muyi magana kawai idan ka samu time, yanzu karna shiga lokacin Madam tana amaryarta. A huta lafiya tsohon ango”.
       Kafin Smart yace wani abu ya yanke kiran. Ya ɗan lumshe ido da girgiza kansa yana furzar da iska. Yana ƙoƙarin cire bluetooth ɗin idonsa ya sauka akan Lulu ta mirror da ke kallonsa.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣9️⃣



.......Sai dai yana waigawa ta rufe idanun ita a dole barci take. Nasa idanun ya rufe da sakin guntun murmushi ya ƙarasa shiryawa ya miƙe. Wando yasa 3quater da ƴar riga armless yasa turare. Baice da ita komai ba ya fita domin duba mima zai bata taci ne duk da yasan halinta bawai ta damu da abinci bane. Ganin babu wani abinda zata iya so sai kawai yay mata order na gasashen kifi da abinda yasan zata iya so. Cikin abinda baifi mintuna ashirin da biyar ba aka danna bell ɗin gidan. Tashi yay zuwa ƙofar dan yasan abinda yay order ne aka kawo. Shi ɗinne kuwa. Mai kawo saƙo ɗin na ganin shine ya wani washe baki, cike da zumuɗi da farin ciki ya ce, “Smart Mawashi”.
    Murmushi Smart yay masa. Shi kuma ya zaro wayarsa yace Please ya bashi dama suyi hoto ɗaya. Kai ya jinjina masa alamar babu damuwa. Ya gyara sukayi sai farin ciki yake yi. Shi kuma ya amsa kayan ya koma ciki. A falon ya ajiyesu ya nufi bedroom ɗin.....


       *_NIGERIA_*

   Kamar yanda ta saba a ƙarshen kowane wata take sake ƙulla silin zare ɗaya a jikin battar da malamin ya bata game da asirin da taima Smart da Lulu. Yau ma cikin nishaɗinta ta jawo battar hannunta riƙe da farin zaren kirtani tana ɗan raira waƙarta ta barmani coge alamar dai tana a cikin nishaɗi. Dan bayan Aunty Amarya da Ammah ta sanar mawa babu wanda yasan yau Lulu ta koma wajen mijinta a gidan.. Wani irin kwance-kwance ƙirjinta yay ya yanka lokacin da take jawo battar idanunta ƙyar akan zararrikan data ɗaura zube ƙasa a warware. Battar ta tukunyar ƙasa ƴar ƙarama ta wani tsage daga sama har ƙasa. Tana ɗagata ta rabe biyu tsokokin nama biyu da suka wani tsotse

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login