Showing 15001 words to 18000 words out of 80019 words

Chapter 6 - Auren Babban Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

265

tsoron kada wancen ya kuma kiranta.




Amma ai koba dan shiba zatai amfani da wayarta ko dan mahaifanta da kuma aysha.

Nan tasa hannu ta kunna ta gabanta n fad'uwa seda wayai tai minti goma a hannunta bataga alamar kiraba sannan ta saki jikinta gamida sauke ajiyar zuciya.



Da wurwuri Musayyet yabar gidan bayan ya shiraya kansa cikin k'ananun kaya sosai yai kyau amma kallo d'aya zakamai kagano idonsa ya d'an fad'a kad'an.






Kota kan drivern sa bebi ba wanda tin daya fito yake gaidashi amma ko kallonsa beba ""' hk ya figi mota yabar gidan.


Da mamaki drivern yabi motar da kallo sbd wulak'anta mutun ba halayyar Musayyet bane.




Babban Company ne wanda a time d'in karfe 7am ma 'aikata masu goge goge ne kawai sukazo kasancewar se 8am kowa ne ma'aikaci ke zuwa .


Amma se gashi yau tin kafin time yayi Musayyet ya riga kowa zuwa """ wanda shi baya tashi zuwa se wajen 9am ko zuwa 10 .



Da sauri suka 6ude babban gate d'in me adon golden suna sara masa gamida gaisuwa """ sama sama ya amsa yai ciki suka biyoshi da laptop d'insa da wata bak'ar bag k'arama wacce papers ne a cikinta masu mahin manci.




Har office suka bishi suka a jiye mΔ…sa sannan sk fita.


Sosai office ya had'u iya had'uwa kujera yasamu ya zauna ya kifa kansa da table yana k'wallah .



Wayarsa ta hau ruri har wajen so 4 ana biyar 5 d'in ya daga murya kasa kasa yk magana ""ok kawai yace zaku iya samuna ina nan daga hk ya aje phone d'in.






8 dede breakfast ya kammala agidan amarya zarah amma ta kas fitowa """ yunwa ce ta isheta dan hk cikin sand'a ta fito da sauri ta nufi dining .



Tea ta had'a ta zuba potatoes da waina kad'an a plate ta plantain ta soma ci.



Kamar daga sama ta hango shi ya fito fuskarsa dauke da smile yana nufo ta"" ai da sauri ta had'iye tea d'in data kur6a tai k'asa da kantΓ₯.


Sanye yake da jallabiyar dazu setaga yayi kyau sosai kamar yaro sede shekarun dayake dasu.



Har yazo gun kanta na k'asa bata d'agoba .



Salamu alaiki ya gimbiyar mata Abumma ba gayyata ? Da ftn sahibar tawa ta kwana lfy a gidan mijinta. ? Yai maganar fuakarsa ck da smile yana me jan kujera ze zauna.



Murmushi ya k'arayi yace baby ina kwana tinda baza a gaisheni ba.

Da sauri ta d'ago kai suka had'a ido setaga yamata kwarjini bakinta na rawa tace dama dama yanzu zan gaisheka """sosai ta bashi dariya nan ya kama kwaikwayonta yanda tk magana.

Mamakinsa tk amma tai shiru yai dariya yace to a hadamin tea nima""' cikin rawar jiki tagyad'a masa kai alamar to nan ta kai hannu zata d'uki cup shima yakai nasa hannun ze d'au spoon aiko hannunsu ya had'u dana juna "


Da sauri ta kalle shi shima idonsa akanta ko kiftawa bayayi sbd wani shock yaji.












I love you All😊
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€




*AURAN* *BABBAN*

*MUTUN*

Creating and Written by

UMMEE MUKHTAR🎁

Kwana 2 anjini shiru nayi d'an zazza6ine nagode k'warai da kulawarku ina ganin tex d'inku naya jiki nagode sosai sede ba turon kayan dubiyabaπŸ€­πŸ˜‚






πŸ…Ώ12

K'ok'arin janye hannunta tai amma setaji ya rik'e yana shafa hannun kallon ta yai cikin wata murya me saukar da kasala yace meyasa bakiyi lalle a hannnba ? Dan motsi tk da mouth dinta jikinta se rawa yake duk sanyin AC dake palon amma gumi take yi"""""""" murmushi yayi haryanzu hannunta na rik'e a cikin nasa cup d'in ya d'auka ya soma shan tea amma be saki hannuntaba seda yasha rabin cup sannan ya kalleta yace kona baki a bakine kingani na k'oshi """" da sauri ta girgiza alamar a'a.

Murmushi yayi yace tatashi suje room d'insa gabantane ya fad'i da sauri ta kalle shi ya d'aga mata gira alamun eh''' tsam ta mik'e tsaye tace ya shige gaba dad'i yaji aransa dan hk ya yatashi ze rik'e hannunta tace a a suje hk tana biye dashi.


Dole yai gaba tana binsa abaya yana waigowa se su had'a ido yai mata smile itako duk ta takura .

Seda sukai tafiya me dan nisa ya murza key yace to muje baby na """"" meze gani wayam babu zarah babu alamunta.


Da gudu ta shiga room d'inta ta danna key ta k'ara shigewa cen d'aya d'akin ta haye kan bed tn maida numfashi.



Hannunsa ya had'a a k'irjinsa yana dariya yace au yarinyar nan guduwa tayi?


Murmushi yayi ya shiga room dinsa yai wanka ya kimtsa phone d'insa ce tahau k'ara sallama yayi yace gashi nan fitowa dg hk ya kashe ya fito.


Bangarenta ya nufa yai knocking amma bata bude ba girgiza kai yayi kawai ya fita """" yn fitowa suka hau gaidashi mota suka bude masa sannan suka bar gidan.


Amotane driver yace yalla6ai ina muka nufa ?

Seda ya gyara glass d'in dk face d'insa yace muje gidana.



Driver yace to yalla6ai.


Momy sanye cikin atamfa super light pink zaune ita da khairat a dining danko fa'eza bata fitoba "" a gogon dk manne a palon ta kalla taga 12 amma har yanzu cikinsu ba wanda ya fito ''koda yk taya zasu fito bayan sun san lefin da sukai.




Momy tacewa Khairat kije dakin ya musayyet kice yazo ina kira""" da sauri khairat ta mik'e yayinda ta aje wainar data gutsira tace to mama da gudu ta nufi sashen Musayyet sede tai Knocking harta gaji ta dawo da gudu tace mama baya nanfa cikin muryar yara""" Momy ta aje cup tace kinyi knocking ba a bud'eba ? Khairat tana k'ok'arin zama tace eh mama.


Momy da kanta ta tashi taje taita knocking amma shiru ""' k'wafa tayi tace wato yaran nan fita yayi ko zuwa ya gaidani ma beba ?

Ya min lefi amma shize yi zuciya dani?

Bakomai zedawone.



Koda ta dawo tace taje ta kira fa'eza .


Fa 'eza na kwance cikin bargo se bacci take dan daren jiya batai bacci ba sbd murna Musayyet zezamanata '"'




Anty Anty kizo inji mama muryar khairat kenan dk bak'in k'ofa danta buga ba a budeba.



Mik'a tayi sannan tai saurin tashi ta kalli agogo setaga rana tayi da sauri ta tashi tace kice wanka nk gani nan zuwa """


Khairat tace to anty .


Tana ina? Cewar Momy khairat tace an wanka tace wai ""'' murmushi Momy tayi me ciwo sukaci gaba da breakfast .



Seda ta kimtsa sannan ta fito kamar munafuka jiki duk ba k'wari ta zauna dg cen gefe tace momy ina kwana.


Kan momy nakana TV ko kallon ta bataiba tace fly .



Shirune ya biyo baya wanda a time d'inne Alhaj ya shigo Momy da fara'a ta tarye shi tace ango se yanzu kaida kk tashin wuri '"" dariya yayi yace wlh fa yanzumma sauri nk anata jirana .

Fa 'eza tace ina kwana dady cikin kulawa ya juyo yace lfy lau fa'eza ya kwanan gida?


Tace lfy lau dady "" nan yace kinbawa Musayyet paper kuwa?


Momy ce ta watsa mata wata harara wacce tasa ta yin qasa dakai tace a a a cikin rawar murya.


Yace to ai gara kibashi ko zaman hk ba dad'i nizan wuce jibi ina da tafiya kuma inaga zan 2weeks acen America so ina tinanin barin yarinyar nan hk ita kad'ai nafiso ace wani nawa haka yana gidan a zaune amma de zanyi tinani nan ya mik'e yace seya dawo.


Momy ta bishi tace Alhaj ka manta da batun 2million d'in danace maka inaso ?


Juyowa yayi yace karki damu bari na dawo yanzu ana jirana sbd ke nakasa wucewa senazo mungaisa ""' dariya tayi tace a a Alhaj wasa kk kade samu yarinya kanaso kamin wayo.



Dariya yayi yace inna biyeka zan makara dg hk yai waje.



Duk fara'ar da momy take tana shigowa palor ta dauke wuta ta kalli faeza tace sekije ki karya ko in kinga dama.


D'aki suka wuce ita da khairat suka barta nan .


Ita kam ko Momy zara yanki naman jikinta bazataji komaiba burin ta yn gaf da cika.






Misalin 3pm Musayyet na kwance a office hawaye yake kansa na kallon saman office d'in knocking yaji anayi da sauri ya share hawayensa yace yes.



Nan aka turo k'ofar aka shigo yalla6ai dama megidane yayo waya yace ya kira phone dinka a kashe .


Musayyet ya kalli phone d'insa yace eh hakane namanta na kashe ta ""meya faru ?



Eh dama cewa yayi wai kaje gidansa dake cen white palace Area B kad'akko masa wasu papers.



Dafe kai Musayyet yayi yai shiru cen yace to .



Mutumin fita yayi ya rufo k'ofa .


Wai meyasa dady keson aikena gidan waccen mara kunyar Amaryar ?

Gaskiya gaskiya haba dan Allah wlh banson zuwa dole kawai za amin.


Nan ta shi yanufi gidan Zarah.





Zarah jin tashin mota yasa tasan cewa ya fita ba kuma ze dawo yanzu ba.



Palon ta dawo ta kunna kallo tana k'arewa haduwar gun kallo "" merry ce tai sallama tace sannu madam Zarah ta juyo tace yauwa "" merry tace me kk so adafa yaune?

Zarah tace kawai ki dafamin shinkafa da manja da salak setumatir da albasa "' merry tai shiru dan bata ta6a yin irin girkinba duk da cewa tasan shi.


Tace to madam nanta ta shi ta tafi zarah kam murna tk yau zataci abinda tafiso acikin abinci.





Kallo tk cikin kwanciyar hankali nan bacci ya d'auke amma setai rub da ciki yayinda dan kwalin dk kanta ya rufe mata fuska.




Da sallama ya shigo gidan sede shiru farin top ne ajikinsa se bak'in jeans hannunsa sanye yk da agogo fari se farin glass.


Sallam yakeyi amma shiru nan yai tsaki yace sekace gidan arna """ da gudu merry ta zo ta durkusa tace welcome sir kai ya daga mata yace are you alone ? Tace no sir to meyasa se aita sallama kamar gidan ba kowa """" tace kai hkr ina cen cikine kasan munada nisa a tsakani . seyanzu ya tino yace hakane .


Nan tai masa nunu da zarah wacce ke bacci dan kwalin rufe a fuskarta amma duk wata sura ta jikinta ta bayyana kasan cewar rigar ta matseta .



Kallonta yk sosai harda cire glasa din dk face dinsa ya ta6e baki yace baruwana da wadda ke gidan amma yanada kyau kuringa kasancewa kusa kusa sbd koda wani zezo kinganeko """ merry tace to sir




Merry tace me kk bukata yace no yanzu zan fita jeki kawai.

Tashi tayi ta koma gun aiki.



Nan ya soma taku yafara tafiya har inda zarah take ya qarw mata kallo ya ya tsine face yace koda banga face dinta ba yarinyace kuma kyakykyawa shima dady wallahi se a barshi me makon ya auro dede dashi yai tsaki yai ciki abinsa.




Dakin ya bude ya jawo drower yaita dube dube sannan yaga papers ya maida kofa ya kulle ya fito.




Koda ya fito bata palon bayan ta kawai yagani tana tafiya hannunta rik'e da phone d'aya hannun kuwa dankwalin kanta ne rik'e dashi yayinda gashin kanta ya zuba har baya.




Tsayawa kawai yayi yana kallon gashin dk kanta yace anya yarinyar nan ba aljana bace karo 2 kena sede naga bayanta amma bana ganinta .


Wata zuciyar tace masa to kai meye ruwanka da ita ma .


A fili ya furta hakane fa meyai ruwana da ita.



Yace to ai matar babanace dole naso nasanta .



Wata zuciyar tace ba dole bane.

Daga haka ya fita yabar gidan .











Ai hkr banjin dad'ine πŸ˜”
[31/08, 16:19] β€ͺ+234 905 934 3174‬: πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€

*AURAN* *BABBAN*
*MUTUN*

Creating And Written By

*UMMEE* *MUKHTAR*🎁.



Dedicate to (Maryam Mamee) barka da dawo wa ina tsarabataπŸ™ˆπŸ˜Œ


Masoya wannan novel inajin dadin comments dinku Allah yak'ara zumunci.😊😘



πŸ…Ώ13



Zarah na shiga d'aki ta kwanta kan bed ta kira wayar Aysha Amma a kashe dan tsaki tayi tace kawai seki kama ki kashe waya """ to kode batada cajine ? Wayar ta aje tasake kwanciya tai shiru tana tinanin yanda zamanta ze k'are a gidan ""'


Wayar tace tai k'ara tana d'auka setaga sunan Alhaj sa'id ne gabanta ne ya fad'i hannunta na rawa tai pckcall amma tai shiru batare datai magana ba.


Yana daga kan chair me juyawa seda ya tsiyayi juice ya d'an sha sannan yai magana yace baby na wato shine d'azu harda yimin wayoko? To nima zan rama ""'murmushi yayi ita kam kamar wacce aka sassak'a tai shiru se motsi tk da baki :::;;:;""" yace yade kinyi shiru Zarah kina min rowar abubuwa da yawa daga ciki harda muryarki """ yau inason kasancewa dake domin na jima ina muradin ranar dan Allah karki k'i pls I need u ya k'arashe maganar cikin salon soyaiya .


Zarah phone d'in tabi ta da kallo cikin ranta tace taf wlh bade ni zarah ba sede ka nemi wata ba ayoni dan wani dattijo yaji dad'i dani ba tai maganar cikin zuciyarta.



Yace yau zami hira me yawa kinji nan da 7pm zan dawo""" yana cikin waya ne d'aya wayar tai ringing anan ne yaiwa zarah sallama batare datace masa k'ala ba.




Yana kashe wayar zarah tai dariya tace lalle mutumin nan ji yanda yk wani kashe murya waishi yaro Lalle kanada aiki """' Ahaka zaka gaji ka sallameni .




Musayyet koda ya fita seda ya biya wani babban office ya kaiwa Alhaj papers """" waje ya samu ya zauna Alhaj sa'id yace harka tashine? Musayyet yace eh Dady banajin dad'i ne .


Subahanallahi amma ka kira doctor Safyan kuwa?


Yace a a zanje hospital d'insu idan na fita "" Dady yace idan bazaka iyaba kaimasa waya yazo mana banson kana lalura amma sekaita harko kinka bazaka kulaba harse taci k'arfinka sannan dg baya kazo kana kuka wayyo Momy wayyo Momy """"gaba d'aya suka sa dariya Musayyet yace ai yanzu nadena wannan ma ina yarone.


Dady yai dariya yace oh yanzu an girma ko?

Musayyet murmushi yayi dady ya kalle shi yace musayyet yaron mama """


Dama inaso miyi magana amma inaga se gobe idan nazo gidan """ Musayyet yace to Dady .


Wayarsa ya ciro yana danne danne yayinda Dady ya maida hankali wajen tura wasu tex ta laptop d'insa.



Number Zarah ya kira tana ringing yayinda shi kuma murmushi Shinfid'e akan face d'insa .



Zarah na Zaune tanacin Abinci a room dan tak'ima fitowa palour dan karsu had'u da megidan.


Number de ta kuma gani aje plate d'in abincin tayi yayin da ta tsinci zuciyarta ta dason d'aga wayar wata zuciyar tana me ce mata kinada aure fa yazaki aikata hakan ?

Runtse ido tayi ita kam tanason jin muryar guy nan domin kuwa tana mata dad'i.

Cikin rawar hannu ta d'auka '''"Musayyet yana gani an d'aga yai murmushi ya tashi ya fita Dady na kallonsa ya girgiza kai yana smile yaci gaba da aiki.



Cikin murya me sanyi yace my beauty da ftn kina lfy """" idon ta ta rufe batare da tace komai ba ya shafi kansa yana kallon korayen flowers d'in dk harabar gun yasaki numfashi yace dan Allah ina neman Alfarma agunki I know u can do it for me "' pls my one don't say no.


Tin daya fara magana ta kwanta akan bed tana lumshe ido har cikin kanta voice d'insa ke mata yawo.

Sbd tanajin dadin voice d'insa .


Yace dan Allah kifad'amin inda kike inasonki inasonki inasonki koya ya kike ina k'aunarki tin danaji muryarki wancen karon dana kira by mistake nakasa sukuni dan Allah kitema kan am really need u in my life ya k'arash maganar yana share k'wallah domin wannan itace damarsa idan har be fito da mata a wannan time d'in ba Momy fa eza zata aura masa.



Ita ma zarah k'wallah t share seda ta saita kanta sannan tai magana cikin sanyin murya "":" kai hk duk da banganka ba nima inasonka kuma ina kaunarka amma bazaka ta6a gani naba har abada kai hkr dg haka tai saurin kashe wayar gaba d'ayanta ta dira kuka .


Musayyet wayar yabi da kallo kamar wani yaro face d'insa ta canja se hawaye dk zubo masa yn gogewa kansa ya kifa a karfen silvan dk wajen yana numfashi sama sama .


Jin shirun yayi yawa ne yasa Dady fitowa nan ko ya ganshi se numfashi yk sama sama """ da sauri ya dafa shi yace oh my GOD jikinne ?


Nan musayyet ya d'ago kai ya rungume Dady yasaki kuka """" mamakine ya kama Dady na ganin Kukan Musayyet yaron da rabonsa da kuka tin yana shekΓ₯ra 7..



Hankalin Dady yatashi nan yakama shi suka koma ciki ya zaumar dashi akan sofa yana shafa kansa yace my son menene damuwarka ko jikinne ?

Musayyet cikin kuka yace a a Dady bata sona ne kawai kuma narasa inda take ""' Dady ya sake kallonsa cikin rashin fahinta yace itawafa?


Musayyet yace bansan taba dady amma nayi nayi tafadan inda tk tak'i .

.murmushi dady yayi yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login