Showing 78001 words to 80019 words out of 80019 words

Chapter 27 - Auren Babban Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

277

yayi yace ai hkr dady bamason wahalar dakune.


Zama sukai kan carpet din dk malale a palon suna gaidasu yayinda suke amsawa cike da kulawa.



Tini aka cika ms gun da kayan ciye ciye yayinda musayyet yace su shigo da kayan dk cikin motar.


Kayan tsarabane kala kala harda kayan wasan khairat wanda zarah ta siya mt .


Dady na kallon musayyet da zarah yasan lalle suna cikin kwanciyar hankali sunyi kyau dasu .



Bangaren musayyet suka wuce da dare yayi tace bazata kwana a inda yakeba yayinda ya rufe kofar yace ba inda zata .


Haba dear ai se a ace bamuda kunya taha zamu kwana waje daya.

Dariya yayi yadauketa yace lalle yarinyar nan nine banda kunyar koke?


Murmushi tayi tana wasa da hannunta ya kamota ya kwantar da ita yn mata wasa gamida kashe fitila.



Bikin aysha yarage sati daya dan hk suka shirya gaba dayansu suka nufi kano.


Anan ne momy ta kula da yanayin zarah tagane cikine da ita.


murna sosai tayi sannan tayi ftn Allah yaraba lfy.



Gidan ammi suka sauka musayyet ko hotel ya koma crn Bristol palace""" bayan sun gaisa da Ammi.



Abinci aka dire musu ammi da murnarta tarbesu .



Kayan tsarabarsu aka fiddosu amota ammi se murna ake.

Da dare yayi malam yadawo aka gaisa .


Ammi tini ta kula da yanayin zarah dan hk suke bata kulawa komai idan zatai se momy tak saurin amshewa ko kuma ammi.




Aysha na shirin fita Zarah ta shigo ai da ihu sk rungume juna har umman aysha ta jiyosu ta leko taga zarah ce da murnar ta tace a a yau kune agari amarya ya megidan .


Zarah tai fara a ta gaidata tace lfy lau umma da ftn mumsameku lfy
Lfy lau sannu da zuwa




Tare suka fita dama gun gyaran jiki zata dan hk suka wuce tare.


Musayyet kullun ya kanzo sugaisa yayinda yake zama da zarah susha hira insun gama ya shiga gari da mota yn ganin yanda garin kano yk.



Ranar daurin aure musayyet yazo harda dady guri ya cika bayan gama daurin auranne yace zarah fa shi tafiya zasuyi .


Momy tace baka isaba abunda ko gama Bikin ba aiba .


Ammi tace yaran zamani kenan dariya sukai shide ya fita yn sosa kai.


Aysha da zarah yagani sun shigo tamakar itace amaryar ya tsareta da I do yna kallo.


Aysha tai murmurshi tacd ina yini""""" yai fara yace lfy lau amarya kinsa matar tawa se yawo tk ko.



Dariya tayi tace amin afuwa ciki ta shige ta barsu nan Zarah ta shafi face dinsa yajawota jikinsa ya shafi cikinta yace kinga idan wani abu yasami baby na akanki zan rama .


Dariya tayi sannan sukai hira ya fice.



Gaba daya suka shirya aka tafk gidan bikin yayinda aka kama waje babba kuma me tsada .




Washe gari tunda wuri aka wuce zuwa Abuja amotoci yayinda sukai sallama dasu ammi.





Wajen la asar sk isa Musayyet tun a hanya ya dauje hanyarsa ta zuwa gida tunda momy tace seya kyale zarah taje gidan amarya haushi yaji don hk ya dauke hanyarsa tun suna tafe.






Gidane mekyau ma alfarma komai yayi






Zarah daki guda sk koma da aysha sunata hira yayinda sauran jama ar suke masu bangaren daban .



Se goma naseer ya shigo da abokansa yayinda ya tabbatar da mutan agidan .


Dariya abokan sk shiga yimasa yacire hula yace akn uba wlh sena shiga dakin matata suna nufin dan sunzo shikenan bazan kwana adakin matataba.



Khaleel yai dariya yace to kai mara kunyar ina ne dazaka Shiga dakin matarka danginta na nan .




Naseer yai Murmushi yace kude kumuje.







Seda sk wuce 6angaren bakin sk isa bangaren amarya .




Suna kwance kan gado itada zarah sunyi rub da ciki sunta hira sukaji sallama.



Da sauri aysha ta figi mayafi tayafa zarah se dariya tk yayinda tafara shirin tashi.












Kai zarah yanzu tafiya zaki dan Allah """ zarah ta juyo tace a a zama zanyi a hada dani ta kuma shekewa da dariya aysha taja mayafi tana dariya itama.










Sallama sukai zarah ta amsa sk shigo ita kuma tai saurin ficewa tini ta daura nik'af dan kar wani ya ganta.


Waya taiwa musayyet ya dasuri ya dauka tace kazo ka daukeni ina nan Area B .


Murmushi yayi yace ai na dauka kwana zaki ayi amarcin dake.



Dariya tayi tace kafiye tsokana fa


⚜BRILLIANT WRTS ASSOπŸ–Š

πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


AURAN BABBAN

MUTUM


From Ummee Mukhtar

πŸ…Ώ54


END


Kwatance tai masa yazo har inda take ya dauketa suka tafi gida""""


Kai tsaye wani katafaren gida suka wuce wanda nesa yk da gidan momy .


Tace a a yanaga munwuce kuma ba gidan momy zamuba .


Musayyet kallonta yai yana mu murmushi yace munta kwana agidan momyn kenan ni hanani sakewa sukeyifa shikenan mutun ba dama ya huta da matarsa .



Mumushi tayi batace komai ba har suka iso.


Yn parking ya bude murfin kofa ya dauketa cak yai cik da ita tana dariya.


Kai tsaye wn room ya ajeta gamida cire mt kayan to jikinta shima yana kokarin cirewa tatashi da gudu tai hanyar wani toilet yak saurin kamota ta rufe idonta dariya yayi ya rungumeta gamida daukanda ya shiga toilet




Wanka yai mata bayan yacika bahon wanka da ruwan d'imi wanda yasha kayan kamshi da sabulai masu kamshi .

Cewa yai itama seta masa sannan zasu fita """tn murmushi ta hau yimasa shi kuma yana mata cakulkuli tana zamewa cikin ruwan shi kuma yana rungumota .

Alwala sukai sannan sk fito bayan sun gogd jikinsu ne sun shafa mai suka sanya kaya gamida tada sallah.



Koda sk idar sleeping dress ta sanya zata kwanta yace lalle setaci wani abun kafin tai bacci """tace nakoshi yanzuma amai nakeji sosai wlh.


Kamota yai ya kwantar da kanta zuwa lap dinsa yn shafa gashin kanta yace me kikeson ci yanzu.


Tace ba komai bacci kawai nakeji.


Yace ok .

Rungumeta yai ya rage hasken fitilun room din ya canja launi zuwa light blue .






Da asubah sukai sallah suka koma bacci se wajen goma ya farka ya zame jikinsa ya wuce kitchen ya dafa indomie waccd tasha vegetables da kifi ya hada tea se juice ya aje kan dining.



Karfe goma da rabi dady yakiarashi awaya yace ya baka fito sallar asubah bane banganka ba.


Musayyet ya hau sosa kai yace umm umm dama danaga dare yayi shine mk wuce daya gidan amma ayi hkr.


Dady yai murmushi irin nasu na manya yace bakomai ai hakamma yayi dede momy na gaidaku .


To dady zanzo anjima.

A a kai zamanka ka huta kajiko nan da sati 1 kazo kasan ba jimawa zakai anan ba sosamune nafison zamanka acen kana kula da harkokin cen .



Musayyet dama hk yakeso yace to dady ba matsala hakan za ai.



Dady yai murmushi dan ya gano bayason zaman nan




Zarah ce ta fito dg toilet brush tayo sanna tayo palor .


Yn ganinta ya aje wayar suka rungume juna yana jan jelar gashinta yace se yanzu da alamu wanna cikin yanada son jiki .


Kallonshi tai tn smile tace to ai kai yayo

Kallonta yai yace iyyee lalle yarinyar nan gama breakfast din yau zakiga yanda ake son jiki yinin yau bazan barki ki hutaba.
Zarah ta mara raice haba dan Allah nifa tsokanarka nk.


Dariya tabashi yace ai dankinga na kyalekine vakison tausayinki nakejiba sbd ga cikin jikinki ga kuma gajiya amma tinda hk kikace zakigani yau.



Zarah tai dariya tafada cin abincin ya matso daf da ita yafara bata itama tn bashi har suka kosar da juna.






Yinin ranar hk suka yishi cikin farinciki yayinda ya matsa mata da abu daya har sedata shiga wani room ta kulle door tn dariya sannan ya kyaleta .


Murmushi yk ya tsaya dede room din yace daga yau kyasa cemin baby na ni yayo .



Dariya take sosai tace bazan sakeba dan Allah katafk gidan momy .

Au korata ma kike ba inda zani .



Se bayan kwana 2 sannan sukaje sk gaida momy yayinda sk sameta se amai tk.


Hankakin zarah yatashi tace akira doctor momy tace a a kawai zazza6ine kuma ze dena.


Musayyet kallon momy yk takara haske yace karde ace cikine da momy """ya fada cikin ransa.







Sati 3 a tsakani sk koma Cairo anan ne sk bude sabuwar rayuwa me cike da farinciki yayinda sk ririta juna kamar sucinye juna .

Sun kara kyau da haske kamar ka ta6a jini ya fito .

Haka ya maida hankalinsa ga harkokin companyn dake cen .



Ryuwarsu abar burgewa ce ga duk wanda ya kallah yayinda yk matukar kishinta.





Seda watan haihuwarta ya kama sannan ya bigawa momy waya yasanarda ita """murmushi tayi tace ai na dauka bazama gayamana ba ninan natadani komai kasan me jego akwai son yaji
.
Zamuzo nan da sati daya base kunzoba .


Musayyet yace to momy.






Sati daya atsakani suka isa cairo harda su ammi da dady harda mahaifin zarah.

Mamaki sukai ganin momy da ciki ashe dama cikine da ita.



Sosai sukai murna zarah da musayyet dan ganin mahaifan nasu """"ammi se raba ido take wai yau itace akasar waje.



Bangare guda aka basu kowa da nasa momy da dady se ammi da malam


Musayyet da kansa ya jere musu kayan abinci .





Haka suka wuni sn hira washe gari sk fita ganin gari yayainda akabar zarah da musayyet agida khairat ko tn gidan fa eza bata zoba sbd suna exam.




Kwana uku atsakani tafara nakuda aka wuce hospital kasa haihuwa tayi har anye shawarar operation dg baya ta haifo danta na miji me kama da musayyef sak


.


Murna kam ba a magana washe gari suka dawo gida aka baiyaye baby kowa nason kasancea dashi sbd kyawunsa.





Fa eza aka bugawa aka sanar da ita haihuwar zarah """ baki ta ta6e tace Allah yaraya ta kashe wayar .




Umar na kallonta dawowarsa dg office kenan yace musayyet ne ya samu karuwa?


Kallonshi tai sama da kasa tace meye ruwanka.



Bedamuba yace ke yaushe zaki haihune ?



Tsaye ta mike tace haihiwa ? To ai cikinne baka iyaba da har zakace wai yaushe zan haihu.




Umar dariya taso kamashi ya mike tsaye yace wato ban iya cikin bako.


Shikenan zan karo aure na jarraba akanta nagani ko akanta zan iya ,,, yana fadar hk yai hanyar room da gudu ta bishi ta rungumshi tana kuka tace dan Allah karkamin kishiya wlh inasonka kuma yanzu ma Allah cikine dani.





Dariya yai ya juyo ya rngumeta yace wasa nk miki ai bazan iyai mk kishiyana inasonki ke kadai kin isheni rayuwa .



Rungume juna sukai fa eza najin kaunarsa cikin ranta .




Zarah ta bugawa amarya aisha tasanar da ita tace amma zasu Nigeria ne """mΓΉrna tayi gamida jin dadin kasancewar zarag lfy.


Haka taiwa ayshan cairo waya da kwatance sk zo gidan itada mijinta .


Taro sukai isu isu yayinda mijin aysha yabada tasa gudun mawar ta musamman dan wani bangare dg cikin hotel dinsa yabada wanda na musamman ne dama sbd taro .


Nan sukaje aka wuni ana hutawa gamida ciye ciye har seda dare yayi.





Aysha ko akwati uku tayo cike da kayan baby dayar kuma kayane duk na mata wanda na zarah ne.








Musayyet baya rabo da babyn koda yaushe yn manne dashi dan wani irin so yk ma yaron yayainda yaro yaci suna Muhammad suna kiransa da al ameen






Bayan kwana 3 suka fita sukayo siyaiya me yawa domin gida zasu koma ammi kaya aka jido kamar hauka .


Hka suka dawo Nigeria cike da farin ciki da kewar yaran nasu.










Masu aiki aka samowa zarah wata balarabiya harsu 2.








Wata daya atsakani momy ta haihu yayinda ta samu tagwaye mace dana miji.










Dady yace kada suzo se an kwana 2.






Seda akai wata daya sannan sukaje momyn fa eza ce agunta yayinda takeji da yaran kamar ita ta haifa.


















Hk rayuwarsu taci gaba da tafiya musayyet zarah ce kadai farincikinsa yayin da itama haka.




Seda ta yaye yaronta sannan ta musayyet yasama mata school anan cairo.








Ammi koda tazo gida hk tabi gidajen yan uwa ta dinga rabon kaya tanajin dadin duk a dalilin 'yartane zarah .


Haihuwa me rana .












Anan na kawo karshen wannan novel.








Ngd ngd ngd


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login