Showing 45001 words to 48000 words out of 80019 words

Chapter 16 - Auren Babban Mutum Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

270

a kayi agun dogo me fad'i gashi da kwana kwana ,,,musamman aka yishi dan masu koyon mota.







Suna isa momy tace to Zarah seki kalli yanda zan kunna motar dama yanda hannuna da kafafuna ke tafiyar da tuk'in kin fahinta?








Zarah tace to momy Anan tafara koya mata tana shiga duk wata kwana dk gun idon zarah ko na ganin yanda momy keyi .




Seda sk jima momy tace to zoki gwada .




Zarah hannu na rawa tasa key ta tashi motar cikin ikon Allah ko tafara tuk'i kamar dama ta jima tanayi.






Momy na gefenta tn kallo tn dariya tace kai masha Allah kinada saurin gane abu.




Zarah tai murmushi tace ashe motar ma koyonta ba wuya.




Momy tace eh ynz se gobe kuma da kanki zaki kawo mu nan nida khairat dariya sukai sk juyo gida inda momy sam bata amshi driving din ba tace zarah ce zata kawosu gida.





















Suna dawo wa sk tadda fa eza da khairat a inda akeshan iska wato runfar bunu da kujeru suna shan ice cream da cake.




Fa eza ganin zarah tai kawai tn yin parking tace kan uba har mota aka fara koya mata ummmm lalle ne .





Khairat tataso da gudu ta rungume momy tana oyoyo momy.






Seda zarah ta fito fa eza ta dauke kai tace momy sanni da zuwa """ momy tace yauwa baki fara zuwa gun aikin bane?








Eh se gobe zanje "" ok gara ki fara zuwa nan da wani time ma zarah zata fara zuwa.







Fa eza cikin ranta tace wai duk inda nk kenan seta kasance agun
? Wlh bazata yuwuba .






Palo sk dawo akabar fa eza a waje tn sak'a da warwara.










Af kinga na manta ba muje d'aya gidan ba """koda yk da yamma maje ko.





To zarah tace kawai kowa yai hanyar daki











Se yamma sukaje sk d'ebo abinda zarah ke bukata ciki kuwa harda wayarta .







A sace ta hau upstair room d'in musayyet ta dakko book din nan ta 6oye ajikinta snn ta fito sk dawo gida.




























Da kwatance Naseer yaje gidan su Aysha inda tasha mamakin ganinsa a waje sk tsaya suna gaisawa kunyata duk ta isheta dan ba dawata kwalliya sameta ba kasancewar aikima take yi akace ana sallama """ tn fitowa ta ganshi zata koma ciki yai saurin shan gabanta ya jawo kofar gidan ya rufe inda bazata iya shiga gidan ba ya rufe gamida tsareta da ido.









Kanta na k'asa yace to yaude gani kuma har gidan da akemi rowama na samu da ftn kina lfy.








Cikin jin kunya ta gaidashi tace bari ta debo masa ruwa """" ciki ta shiga ta zubo ruwa a jug ummanta tace wazaki kaiwa ruwa?



Murmushi tayi tace umma bak'o nayi dg Abuja idan a shigi zan gayamiki """baki umma ta bud'e tace Abuja kuma garin yaya kk had'u?



Aysha da sauri ta fita tn dariya ..







Tinda ta fito yk kallonta yayinda itama murmushi ya zauna aface dinta tace gashi.








Kar6a yayi yn smile yace ngd shikam inda ba gidansu wacce yk so bane babu ta yanda za ai yasha ruwa irin wnn""" yasaba da ruwan roba """ amma jiyake ko ruwan kwatane ze iya sha akan Ayeshan sa .

















Hira sk sosai wanda mafi aka sarin hirar Naseer ne keyi ita kam sede tace eh ko a a .




Da zetafine ya bata kudi masu yawa ya bude boot ya shiga fito da ledoji kamar shida wanda duk kayane aciki na kwalliya dana sawa se kayan ciye ciye.









Da kyar ta amsa ya kalleta yace wnnan kunyar sena cireta yarinya idan ba damuwa zan iya shiga na gaida ummammu?












Cikin inda inda tace to a tare sk shiga umma tasa masa tabarma ya gaidata cikin nutsuwa kansa ak'asa umma tn kallonsa itama irin kallon sirikai """" kudi ya aje mata masu yawa snn yai sallama da umma tn masa godiya da mamakin a ina aysha tasamo wannan yaron kuma?





















Seda sk dawo kofar gida tai ms godiya yace no banaso kidena wlh aysha inasonki da yawa zaki aureni? Idonta ta rufe shikam cikin wasa yace na shiga 5 kenan bakya sona.




jin hakan yasa ta bude ido tana dariya """ shima dariyar yayi yace inna ce zan fito zaki amince.?





Tai smile tace eh nima insonka tn fada ta ruga gida da gudu.





Jin gina yai a jikin motarsa yakama dariya yace yarinya me kunya kenan ba kamar nagarimmu ba nagode Allah ina zuwa gida zan shedawa Abba komai .


Ummulo


*⚜BRLLIANT WRTS* *ASSOπŸ–Š*



πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€


*AURAN *BABBAN*
*MUTUM*


Crtn And Wrtn By


_UMMEE_ _MUKHTAR_🎁


πŸ…Ώ32





Da daddare Aysha ta kira Naseer tai ms yaje gida lfy """yace lfy lau ya soyaiyarsa azuciyarta ? Shiru tayi tn juyi kan bed ta lumshe ido """" shima juyi yayi gamida gyara kwanciyarsa yace a gidanku za a bari mi aure nan da 2months?

Aysha zumbur ta mik'e zaune tana waige waige fatan ta shine Allah yasa umma bataji me yace ba duk da umman tata bata d'akin.



Yace kinyi shiru"""" cikin muryar shagwa6a tace habade kamar wata bazawara":"


Naseer dariyace ta kamashi ya mik'e zaune yn 6alle botir d'in rigarsa yace au zawarane sk aure a wata 2?

Smile tayi """yace toni na gaji da zaman danake wlh"""" aure nakeso ya fada yn sauraron mezatace """ aiko aysha tai ms Shiru abinda yΓ  bashi daria kenan yasan kunya takeji dan hk """" yace dan Allah tafadawa Abbanta nan da sati daya za a turo"..



Aysha tace au harka yanke shawara ma?

Yace tin yaushe ma sunjima sn hira dg baya sukai sallama """ Aysha ta kalli phone din tace lalle wannan bashida kunya.







Zarah ta kira suka gaisa cukin d'okin juna 'aysha tace kenifa naji shiru har yanzu banji kinfara amaiba """"


Zarah ta had'e rai tace wlh daba dan daba dan ba dana zagi aman shi kansa .



Aysha ta kwashe da dariya tace yi hkr Kin samme ?


Zarah tace a a,,,,, aysha tace wai wani saurayi nayi sunanshi naseer wai soyake mi aure nan da wata 2 kamar wata bazawara.



Dariya zarah tayi sosai tace a ina yake ?
Aysha tace kema de kyayi daria wai anan abujan yake """inaga megidankia yasan Babansa .



Zarah tace gara ayi musha biki kice zanzo kano 'ai sati uku zanyi idan nazo.


Aysha tace hmmm ina sonsa wlh ya had'u baki ganshi ba """" Zara seda ta maida k'wallah snn tace saurayine ko?




Aysha tai saurin gyara zancen tace ah ah kawai de yn da hankali ne .


Hira sk jima sunayi inda zarah take gayawa Aysha kinsamme wata magana zan fada mk amma dan Allah karki fadawa kowa pls.



Aysha tace kema banda abinki wazeji sirrimmu.


Zarah tace kin tina wanda yake kirana awaya daf da zanyi aure?



Aysha tace yes taya zammanta dashi koba me muryar laraba wan nan ba?

Zarah ta goge hawaye tace shi.


Aysha tace meya faru ko haryanzu kiranki yakeyi.?.



Zarah tace uhmm ashe wai d'an miji nane aysah kiji wani kwama cala """"


Aysha ta mike zaune gamida dafe kirji tace ke zarah dan Allah da gaske?
Kuka zarah tasa tace wlh aysha bakiga sabon da mukai dashiba har gida daya mk zauna ashe wai shine kuma wlh ina sonsa araina ta k'arashe maganar da kuka



Aysha tace innalilahi kinga ki dena kuka yanzu hk kuna zaune gida daya?



Zarah tace baya gari yai tafiya ga dukkan alamu shima yn sona sosai har rashin lfy yayi .


Aysha tace ki hkr hk k'addara tk kowa da yanda tk zuwar masa ke kuma irin tk kenan"""" amma fa ina yawan yi mk wani mafarki zarah"""

Nameye kuma aysha? Wlh ko shekarn jiya sedanayi wai gashi kin auri wani kyakykyawa dashi kuna cikin farin ciki so uku inayin mafarkin nan """tona dauka kawai avun mafarkine ba lalle yazama gaskiyaa tinda gashi kinyi auranki amma de mafarkin nan yn raina .



Zarah dadi taji harda dariya tace kici gaba da yimin irin wnn sweet dream d'in harkinsani frn ciki


Aysha tace ya kikeji aranki game dashi""".zarah tace a dyk sanda naganshi ji nk kamar na shige cikinsa dan son danake masa nakasa sarrafa zuciyata .

Aysha tai dariya tace ya sunan sa ? Musayyet zarah ta bata amsa""" umm suna me dadi daka jin sunan kinsan ya had'u """ hk sukaita hira har wajen goma da rabi snn sukai sallama.















Da safe bayan anyi breakfast suka zauna a palo suna hira kadan kadan itada momy "" khairat ce ta fito sanye da uniform za akaita school rigima tasa wai ita zarah ce zt kaita.


Momy tai dariya tace sarkin rigima ai driving d'in zarah be nisaba jiya aka fara koya mt.


Kuka tasa gamida aje basket dinta wanda shak'e yk da juice da snacks se flask d'in abinci dan k'arami dashi.


Zarah ta taso tace kuka kuma oh no don't cry um zomuje ni zan kaiki ba wandaze bimu.
Momy tai dariya tace rabu da rigimar khairat nina kaita """


Khairat nok'e kafad'a tayi ita wai a a .




Zasu fita kenan fa eza ta fito ta gaida momy amma ko kallon zarah ba taiba.


Ke ina zaki baki ganin mutane ne bazaki gaida suba?



Se anan tasaki fuska dan dole ta gaida zarah """ta amsa snn tai ficewarta .









Momy tace muje tare tsoro nakeji ace dg fara koyon mota na barki ki dita ke daya.

Tare suka kai khairat school daga nan suka wuce inda sukaje jiya zarah ta kar6i driving d'in tayi har sk zo gida.


Fa eza na zuwa gun aiki already ciki ta nufa tn meyin bangaren musayyet.
Knocking tai akace yes """"



Zaune ta ganshi ya juya baya da alamu waya yake """tsaye tk se faman cika take """tana wani kalle kalle.

Sedaya gama waya snn ya juyo wankan tarwada ne dogo yanada hanci da idan duna da fuskarsa mayalwaciya me tarin annashuwa .





Da murmushi yace zauna ko"""turo baki tayi tace kaga malam ina ne inda zan zauna nazo ka nunamin bawai zama ba"""" ta fada tn harararsa.






Smile yayi sorry fa shi musayyet d'in be nuna mk inda zaki zaunaba?




Tattaki tayi har gabansa ta kalle shi tae ummm wato an baka rikon kwarya shine harda fadawa mutane magana ko wato kai ka shigo gari.



Tsaye umar ya mik'e ya kalleta sosai yana zagaye ta kamar me neman abu ajikinta snn yai smile yace rikon kwaryar ma ai iyawane """ wani a bashi mana.




Da zafi ta juyo tace ni kk fadawa hk.


Eh na fada seme?


Gaki kyakykyawa amma se dan banzan izza da fadan tsiya.


Jikinta ne yai sanyi domin aduniya tanaso taji ance mta tana da kyau.




Handbag d'in ta ta dauka ta fita yabita da kallo yace nasamu matar aure.













A wani palo ta zauna tana kallo office din da umar ke ciki tana kwafa duk wanda ya wuce seya gaidata amma ko kallon mutun bazatai ba sema kallon raini ne daze Shiga tsakaninsu.


Tn zaune har wajen 1pm a time dinne umar ya fito aiko karaf sk hada ido ta murguda masa baki ta dauke kai.

Dariya ta bashi yazo har gunta gamida tsugunawa ya kaa kunnensa yace pls bazan sakeba dan Allah .




Sanyi taji aranta domin ya k'ask'antar da kansa gareta """ juyowa tayi tace na hkr kaima kai hkr.


Smile yayi yace ai ni nai mk lefi """ tace no nide.

Yace zanje nai sallah idan nadawo pls zaki rakani restaurant ?




Kallonshi tai se anan taga ashe kyakykyawa ne ajin farko.
Ba musu tace eh """ yace ok ngd my heart yana fada ya wuce yn daga mt gira.






Baki ta saki tn kallonsa wai my heart.


Murmushi tayi snn ta nufi wani room me dauke da komai na office se k'aramin bed na hutawa da kujera doguwa .





Toilet ta shiga tai alwala ta fito ta shimfida dadduma ta tada sallah.



Hk kurun tafara tinanin umar sede data fara zata ta6e baki se kuma ta tino abunda sukai.







Bayan ya dawo ya nemeta sk tafi cin abinci se surutu yk mata ta mai shiru har ak dawo.



Bayan an tashi ne yace z kaita gida tace ai da mota tazo dg hk ta shiga mota tabarshi tsaye agun yn murmushi.






Se bayan kwana 2 musayyet ya kira momy wayarta na kashe sbd I de dare yayi kashe phone takeyi.



Tinani ya shiga yi kode ya kira zarah.


Daga Wanka ta fito d'aure da tawol ajikinta wayarta ta hau k'ara a zatonta aysha ce batako duba sunan ba tai picking cikin annaushuwa .




Muryar musayyet ce ta doki kunnenta tawaol d'in jikinta ya su6ale tai saurin taroshi harda tsugunawa kamar yn ganinta gamida sakin ajiyar zuciya.










Shiru yayi yana sauraren yanda tk ajiyar zuciya """: kwanciyarsa yayi yace mom na kusa ?




Har yanzu tn durkushe tace a a ka sauka lfy?


Lfy lau yace """Zarah tace akwai abunda kk sone? Runtse ido yace idan ma inason wani abu ya zanyi tinda yafi k'arfina yana fadar hakan yai saurin kashe wayar yn danne 6arin k'irjinsa .











Zarah kuka tasa tana kokarin tashi ta fada kan bed tasaki kuka.





Ahankali ya fara kuka shikam bayajin ze iya auran kowace 'ya mace """" amma ze auri fa eza ya zauna da ita kodan farin momy ze fada mata a daura musu aure inyaso aturo da fa ezan ta biyoshi """ bayajin ze iya jure ganin zarah .
















Ummolo



*⚜BRILLIANT* *WRTS* *ASSOπŸ–Š*


πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€πŸ‘³πŸ»β€β™€



*AURAN *BABBAN**

*MUTUM*


Crtn And Wrtn By

_UMMEE_ _MUKHTAR_🎁




SADAUKARWA GA MASOYA WNN NOVEL 😊




πŸ…Ώ33







Kwana 2 tsakani musayyet ya kira momy yake sheda mata ya amince ze auri fa'eza """"Momy dataji batun seda tai tsai domin tasan akwai dalili"""


Tace masha Allah bakomai idan dadynka yadawo mayi maganar .





Satin dady 3 yadawo momy tatareshi da zancen shiru yai mata bece komaiba yagama cin abincinsa ya fita.




Umar ko kullun seyaje office din fa eza hira amma bata sakar ms fuska sosai ,,,,sede inya fita ko sun rabu haka zara wuni da tinaninsa wanda tarasa dalili.





Baba maryam zaune sk itada Ammi a k'uryar d'aki suna hira """"keni kuwa ya amarya kin lek'ta kuwa ?

Ammi tai dariya tace naje har take cemin wai ita gidan akwai Aljanu kijini da ja'irar yarinya """dariya sukai baba maryam tace ina ruwan Zarah kinsan dama cen ita a kwai ta da tsoro kigafa lokaci datazo gidana wai daga nai musu ta tsuniya hard Aljanu da dodanni aciki fafur tak'i yarda su kwana itada zainab wai sede nima na kwana adakin """ dariya suka kumayi Ammi tace ai tanacen abinta wlh tayi kyau da ita saurare kawai muke nida malam muji an samu rabo.


Baba maryam tace wlh fa ai yaci ace tasamu zuwa yanzu nan de sukaita hira har dare yayi Ammi ta had'a mata goma ta arziki tasa driver ya kaita har gida.







Zarah zuwa yanzu ta dena sakin jikinta kullun tana d'aki tinanin musayyer kawai tk.

Abangarensa ma hk abun yake dan tinda yaje ba wani kula yk da aikin sosai ba sede ya shige room ya kunna AC ya kwanta yn tinanin zarah.





Ana gobe zarah zata gama idda momy da dady suka shiga dakin ta kwance sk sameta tayi zurfi a tinani se sallama taji.




Cikin dabur cewa ta sakko dg kan bed ta zauna kasan carpet tn gaidasu cikin ladabi"""" da fara 'a dukkan ninsu sk amsa sunai mata ya zaman shiru dan sungane tafison zaman kadaici yanzu.


Sunkuyar dakai tayi kawai tn murmushi.







Dady tai gyaran murya yace zarah dama munzone dan na fada mk wata magana kuma banaso ki tashi hankalink ko kice zaki fadawa wani ' a a kamar yanda na fada mk da kaina hk nakeso na fadawa duk wani wanda yadace na fadawa ""kama daga kan mahaifanki .



Zarah kanta na k'asa tai shiru """ dady yace batin yanzu ba nasake ki zarah sbd wani dalili.


Da sauri ta dago kai jitai kamar ta zin dima ihu idan su ammi da malam sukaji ai kasheta zasuyi

.




Momy na kallon yanayinta ta matso kusa da ita ta dafata tace karki damu kinji bazamu ta6ayin abinda ze cutar da keba .



Dady yai murmushi yace abu daya nakeso kimin shine ki yarda da duk za6in danai mk banaso naji kince a a kinjiko zarah?.



Zarah datake hawaye tace ai ni tunda yanzu kasakeni nafiso naci gaba da karatuna dan Allah karka fadawasu malam wlh duka zasumin koma sukashe ni tafada tn kuka .




Momy ta rungumeta tace yi shiru kina nan tare damu zarah ba abunda ze faru se alkhairi kuma suma bazasu yi mk komaiba idan har mk fada musu dalilimmu.






Dady yace inaso ki amince da za6in dazan mk badan niba dan Allah kiso abinda nakeso """ zarah tace na amince koma meneΓ±e .


Murmushi sukai momy da dady inda ya mik'e tsaye yace gobene kike gama idda kuma insha Allah jibi za adaura miki aure yana fadar hakan ya fita yn share kwallah.




Momy ta rungumeta tace ai ba kuka zaki ba ina zuwa " waje ta fita tabar zarah inda zarah ta kifa kanta jikin bed taname rusa ihu se kuma ta toshe bakinta dan idan tasaba ihu agidan Ammi to namfa ba nan baneπŸ˜‚.




Ba ajima ba momy ta dawo ta hau shafa phone dinta da alamu kira take.


Nan aka dauka momy cikin barbanci take magana harda dariya "" seda suka kwashe rabin awa suna waya zarah kam mamaki taki taya momy ta iya wannan yaren Alhali da fulani tai kama?



Yauwa zarah maza jeki ci abinci zami bakuwa tana fadar hakan ta kama hannunta kamar wata yarinya suka fito palo.



A dining

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login