Showing 30001 words to 33000 words out of 96510 words
Chapter 11 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete
materials iri iri masu tsada da kyau dinkin kuma dai dai ita kamar an aunata na zamani iri iri, sai mayafai takalma da jakankuna, Uniform dinta kala hudu Har Sandals da schl bags kala uku da littatafai komai an hada ba abinda zata nema.
Inna tace Mashaallah gaskiya Dan uwanki yana ji dake wannan kaya haka kamar lefe,murmushi Shukura tayi ta kwanta tana latsa wayarta,sabo da Baffanta yana da waya tun tuni tana dauka shi yasa bata Bata wahala ba ta gano kanta,Tana Kwance Inna tace tashi mu kara gyara gidan nan sai muyi girki,Shukura ba musu ta Mike Sabo da tuntuni tasan Fadan Inna idan tace ayi ka zauna wasa masifa zaka sha Bata daukan raini kuma Bata bada kofar da zaa rainata sai irin su Hafcy da Niima marasa Tarbiya.
Shukura ta zage akayi gyaran duk inda baiyi dai dai ba sai Umma Saudatu tasa ta tisa wajen ta iya dole,Duk ta gaji likis,Umma Bata bari ta huta ba tace girki zasu yi yanzu, suna girki Umma taga Shukura Bata iya ba, haka ta dinga fada sai da ta koya mata dole sannan tace tayi girkin a gabanta tana Guiding nata,tanayi Umma na koya mata,ta kusa gamawa ta dauki waya ta latso Number Ahleef,tayi Ringing me tatsawo sannan ya dauka Sabo da yayi saving Number din nata,yana dagawa ta kwalla da karfi tace girki nake ta yi kai tun dazu,dariya ta bashi sosai da kyar ya danne yace Dan Allah fa? Na rantse baka ji kamshin bala'i ba Allah ta furta cike da murna, murmushi ya saki yana rubutu a Office dinsa yace to ya da dadi? Ban Sani ba Umma ta hanani dandanawa tace ba a dandanawa wai sai anjima,yace wow Har miyau na ya tsinke ya zubo,dariya ta kyalkyale da ita tare da cewa yau ga Babana wajen kwadayi,Bari idan Umma ta barni na Dandana to zan kiraka na fada ma irin dadinsa Ko kasa Driver yazo na zuba ma ya kawo maka Office ai dai ni ba kazama bace zaka ci,to yace kawai ta dinga Murna zaici girkinta karshe tace ka fadawa Abokinka na manta sunansa me suna kamar za ace Fari,Oh Farhan ? yawwa ae shi kace na iya girki ina ta yi,Dariya Ahleef ya saki ba tare da ya shirya ba yace Ok zan fada masa yazo yaci girkin Amaryarsa,cike da Shagwaba tace kaifa ka iya sa mutum kunya Allah ai tunda Baffa ya rasu to ni wa zai daura min aure,yace danginki mana,baki ta tabe Auren dole zasu min fa na tsere ka bari watarana zan baka lbr kaci dariyar kawunmu yanda na siyar masa da Akuya naci dadi da Kudin.to Allah kaimu yanzu jeki wajen girkin idan ya kone bazan ci ba,kashe wayar tayi,Umma tace keda Yayan naki ne ? tace ae mana lbr na bashi na iya girki,Dariya Umma tayi sosai,Shukura ta kafeta da Ido tare da cewa Umma wlh kama kukeyi da Yaya sosai,Umma tace rufa min asiri Tsohuwa da ni kina hadani da me kyau haka,Baba ne ya dawo daga Office ya gama aikinsa har Ahleef ya sallameshi ya dawo gida ya Iske Shukura da Saudatu suna girkinsu,Umma tace gafa Shukura yar Uwar Alhaji Ahleef ce wacce nake baka lbr ashe yarinyar nan yar uwarsa ce amma take zuwa muna soya doya a titi,Baba yayi dariya Shukura ta tsura masa ido tace yeee... Baba ma Irin yaya Ahleef ne kalli wlh Dimple dinku iri daya har hancin kamar wa da kani,Baba yace haka ake ta fada a Office kuma kama haka take yanzu idan za aje Turai sai kikaga mai kama dake Shukura ai duk Dan Adam ne yan uwane shi yasa ake samun wani yayi kama da wani, suna ma wani iri daya,Shukura tace hakane nima sanda muka je makka naga me kama dani Balarabiya,Baba yace gaskiya yayanki mutumin kirki ne,Shukura tasan karya tayi tace uhmm kawai tare da canja zancen tace Baba harfa Muryarka da tasa wlh iri daya,Umma cikin wasa tace ke kin damemu da kama kama fa, Sun dade suna Hira har suka gama girkinsu.
Lafiyayyar Fried rice tasha kayan hadi iri iri, ga hadin Couslow sai soyayyar kaji,kunun Aya sukayi da lafiyayyan zobo, duk Umma yau ta koyawa Shukura su sunyi tare.
Umma tace to Shukura kinga yanzu mun gama girki sai Yayanki kije bangaren su Momee Ki karbo foodflask da za a zuba masa kinga mu flask dinmu duk da masu kyau ne amma irin nasu na daban ne,kije ko yan aiki, ko Niima ko kuma Latifa su baki kizo a hada a bawa Driver ya kai masa.
Tsoro ya shigi Shukura yanzu fa ta dawo gidansu da zama,gashi ta daki Latifa watarana ga abinda tayiwa Niima rannan wai wai Yau ya zatayi.Shukura ta kware wajen satar Hanya ta shiga waje ba tare da kowa ya ganta ba ko Bata San hanyar shiga ba sai ta nemo ta da kanta,haka tabi ta barauniyar hanya ta hanyar Garden har ta samu nasarar shiga cikin Palon ba kowa,ta lalubi kitchen ta shige da sauri ta tarkato duk abinda take so,har zata fita ta bude fridge dinsu na kayan sha,ta dauki wani hadin lemo da Niima ta zauna ta Bata lokaci wurin hadashi Sabo da zatayi bako,yayi masifar dadi kuwa cikin wani juck na roba me kyau, Shukura ta bude juck din robar karami dashi ta kurba taji dadi,kawai ta kafa kai ta shanyeshi tas ta Ebo ruwa ta cika juck din ta mayar inda ta dauka, wani flask ta gani hadadde karami an shirya abubuwa kusa dashi a saman tire,sai ta bude a hankali tayi arba da farfesun Hanta da Koda kawai sai ta fara ci taji dadi ta dinga ci tana cewa nasan na wannan yan iskan ne,da Momee tana gidan bazan ci ba tare da na fada mata ba, amma tunda su Niima ne kadan zan rage,dama Shukura Bata ci komai ba,jira take sai tayi sallah sai taci Wanda suka dafa da Umma to yanzu ta fasa cin nasu sai zuwa dare yau Allah ya ciyar da ita nasu Latifa,baifi Guda Shida ta rage hantar ba duk tacinye,romon ma bata barshi ba sai da ta yagi bread a kitchen taci dashi kadan ta maida komai inda yake ta dauki kwanikanta ta kara bi ta barauniyar hanya ta koma Part dinsu,Niima tana daki sai kwalliya take zubawa,taji motsi tunaninta yan aiki ne suke zirga zirga, Latifa ma yau Sunday tana gida tana jin karar kwanika a kitchen amma tayi tunanin Niima ce.
Bakon Niima yazo taci uban wanka kamar zata je Dinner, sai da taje ta shigar dashi palon baki sannan ta dawo kitchen domin kai masa abinci,bata duba flask din da hantar ke ciki ba kawai ta dauki katon tire din data jera komai a kai,juck din kuma Shukura ta cikashi da ruwa nan ma Bata duba ba ta daura saman tire komai da komai taje wajen babban bako tare da ajiye masa a gabansa tana karairaya, saurayi yace yau zanci dai girkin Amaryata da ake ta fada min a waya za ayi min. Murmushi ta saki tace yau gaka gashi sai ka manta hularka, yayi dariya baki da dama Amarya ta shi yasa yau ba yanda Mama batayi dani ba kan naci abinci wlh naki ci Sabo da nasan me Amaryata zata shirya min.
Niima tayi wani fari sannan ta dauki plate da spoon bari na zuba maka kar yunwa ta illata min kai,tana Bude flask wayam sai yanka shida rak a ciki roman kuwa babu ma,Rudewa Niima tayi kunya ta kamata ta rude gumi ya fara feso mata ta shiga tunani,yace Lfy Sweetyna? Da Ina ina tace kaga wlh nayi na....a... Jiye..amma kalli babu a ciki to ko Aljanune? Dariya yayi yace wanne Aljanu ko dai bakiyi ba karya kikayi nasan yan matan yanzu da karya Ko kuma yan gidanku Sun cinye ? Wlh daga ni sai Latifa masu aikin ma basu taba yi mana haka ba kuma yanzu babu wacce ke shigar mana kitchen Momee ta hana tace sai dai muyi girki da kanmu,tace bari na zuba ma lemon kasha kayi hakuri idan ka dawo next zan sake maka, yace Ok ba damuwa,ta fara tiltilo lemo tsiiiiiii sai farin ruwa shaaaaa ya cika cup,dariya ya kwashe da ita tare da cewa amma Kin iya rainin hankali wannan ne girkin da kike ta yi min kuri ? Kin hanani cin na uwata,haushi Niima taji ya kasa fahimtarta,tace karfa ka raina min hankali kasan dai nan gidan munfi karfin karya idan kudine gidansa kazo ya zaka zo ka dinga fada min magana,kune Matsiyata wlh ba mu ba,Saurayi ya saki baki tare da cewa ashe baki da tarbiya dabba Ce ke? Fada ya kaure sukayi kaca kaca yaja motarsa ya bar gidan yana godewa Allah da ya gano Niima Bata da tarbiya.
Sabo da bakin ciki sai da Niima tayi kuka tana bawa Latifa labari,latifa ta dinga salati tace naji motsin kwanika dazu tunanina yan aiki ne,nima haka cewar Niima,Suna ta tunani to waye yayi musu haka,kaf yan aikin gidan sai da suka tara su aka tambayi kowa,amma suka rantse basu dauka ba,Niima tace duk ranar da na kama Wanda yayi wlh sai ya bar gidan.
Shukura kuwa tana komawa tace Umma yau kamshin girki ya cika min ciki sai dare zanci nawa,Umma tace to zubawa yayan naki, nan Shukura ta shirya komai daban daban kalar yan gayu,aka zubawa Driver a mota ya tafi kai masa.
Ahleef yayi mamakin ganin girki lafiyayye Haka lallai Shukura ta samu uwa ta kirki Saudatu Zata koya mata komai, abinci ya zuba ya fara ci wani shegen dadi Wanda bai taba cin girki irinsa ba me dadi haka yana cikin ci yana santi Shukura ta kira wayarsa,ya dauka tace Yaya ya kaji ? Yace na nadaki sarauniyar iya girki ta Africa,ta dinga dariyar Jin dadi,Yace yau nasan sai na manta hanyar gidana nan ma ta tuntsire da dariya an yabi girkinta,ya cika baki da abinci da kyar yake magana yana Sani yayi haka dan taji dadi ba kyau ayi maka abin gwaninta ka kasa yabawa,yace yar kauye tafi yan birni iya girki tazo ta kwace musu bokonsu na iya girki,Tace kai Sir to gobe ma zanyi maka wani,yace dolenki ma ai naga waje,an nunawa kurciya baka,yanzu zan fadawa saurayinki shima yazo yaci,Shukura tace to idan yaci anjima da dare ka kirani ka bani labarin irin santinsa,yayi mata ta yara yace tam tare da kashe wayar.
Ahleef ya biyewa Shukura ya takurawa Farhan lallai sai yazo Office yaci abincin Amaryarsa wai dole Farhan yazo.
AsmaBaffa.
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO
10
official
By
AsmaBaffa
Kuyi Hakuri readers kwana biyu ina Busy ne shi yasa baku jini ba.
Ina matukar godiya ga masu Sharhi Allah ya biya ku,karku gaji pls aci gaba ina gani kuma zanyi kokarin ganin kowa na masa reply.
ASYCOOL,DIYAR KATIBI, HAFSAT KHAIRAN and ZEEMAMA wannan page din naku ne Sabo da Kauna.
Farhan yana shiga Office din yace na Niima ba.. Kafin ya karasa Ahleef yaja wani mugun tsaki Wanda bai taba yi ba, me zanyi da ita Allah ya kiyaye, Farhan yace Niimar taka ? Dama sai yanzu na gane wlh ba so Bane kawai Shakuwa ce ta zama waje daya da kuma son kyautatawa Momee da Abba,Kallonsa kawai Farhan yake yana mamaki,dama ba so bane kace ? Kwarai kuwa Allah ya taimakeni Bata aureni ba ni sai yanzu ma nake kara sonta kuma ta birgeni wajen taimaka min da tayi ban aure ta ba, Farhan ya fara dariya tare da cewa kaifa kace tafi matan duniya kyau, Lokacin ban gane ba amma Ko yar yarinyar nan Shukura ai ta linka ta sau dubu saba'in na tsaya ina batawa kaina lokaci,Uhm yanzu Shukura ta fita kenan ? Farhan ya tambaya,Nesa ba kusa bama budurwarka ta fita kyau, Ashar Farhan ya dura masa tare da cewa munafikin banza zakayi bayani,sai kazo kana fakewa dani budurwata budurwata munafuncin banza,Dariya Ahleef yayi tare da cewa Kasan Allah ba wani so tsakaninmu kawai taimako ne,ni me zanyi da mace yanzu babu class dina fata nake ma ka aureta wlh, harara Farhan ya watsa masa tare da cewa Allah kiyayeni kazo kana bibiyarmin mata,nan Gaba zaka yi bayani,baki Ahleef ya tabe baka ganewa wlh malam ga abincin nan ci ka tafi,Farhan yaci abinci shima yana zuba santi iri iri.
Da dare Ahleef sai yaga gidan yayi masa fadi,ba dadi shi kadai kamar maye gaskiya yayi missing Shukura, haka yayi shirin bacci ya kwanta 12am ya tuna bari ya kira Shukura ya bata labarin santin Saurayinta Farhan lokacin da yaci girkinta,Har yayi Dialing ya tuna dare yayi ya kashe ganin gobe Zata fara zuwa schl.
Washe gari da sassafe Umma Saudatu ta tashi Shukura, dake Shukura haka kawai Allah ya sa mata tsoron Saudatu da wuri ta tashi tayi shirin makaranta Uniform White and Green din yayi mata kyau Hijab dinta iya mazaunanta,Schl bag dinta ta shirya tsab sannan tayi break fast tare da mikewa taje har dakin Baba ta gaida shi da labadi,yace Shukura makaranta za aje tace ae Baba, to Allah bada sa'a ya zaro dari biyu ya Bata kudin makaranta,tayi Godiya ta amsa cike da murna ta rataya jakarta tare da musu Sallama ta fito,tana fitowa motocin Ahleef Suna shigowa gidan wasu sababbi dal dal guda shida tare da escorts nasa,Shukura ya hango tayi kyau cikin Uniform dinta,Guard ya bude masa motar ya kara 5mnt bai fito ba Sabo da Izza sai daga bisani ya zuro kafafunsa abin kallo yana fitowa Kamshinsa ya gauraye wajen,Yasha uban kyau cikin kana nan kayansa.
Direct wurin Umma ya nufa suka gaisa,Sai da sukayi Mintuna suna hira da Baba sannan ya musu sallama ya fito cikin takunsa na birgewa,Shukura ta rusuna tare da cewa Ina kwana Yaya,kin tashi lfy kawai yace sannan yace muje pls zakiyi Late,abinda bai Sani ba Shukura tafi son tayi late Sabo da bata son makaranta a rayuwarta, saida ta shiga Mota kusa da Ahleef gefensa sannan tace au nayi mantuwa ina zuwa ta bude ta fice tana tafiya kamar marar lfy wai dan tayi Late Bata so taje kan lokaci tafi so taje makaranta an kusa fita daga first period, cikin dakinta ta buya dan kar Umma ta ganeta,sai da ta dan dade sannan ta fito tana tafiyarta cikin sangaya har ta shiga mota,yace as from today Driver ne zai kaiki kullum, Baki ta turo tare da cewa ai makarantar ba nisa da kafa ma zan iya zuwa daga yau ni a kafa zan na zuwa ta furta dan kawai kar ta dinga zuwa schl akan lokaci,bata San makaratun birni dana kauye daban ba, shima bai ce mata komai kawai satar kallonta yayi kadan ta gefen ido,Kuruciyar tata tayi yawa Sabo da iyayenta Sam basu koya mata komai ba.
Jarida yake karantawa har Sukayi parking a Compound na schl din,wajen Principal ya kaita da kansa aka sa wata Senior student Namiji ya rakata Ss1 class dinsu tana tsoro tsoro yanda taji ana feso turanci ta ko ina. Ahleef ta kalla shima ita yake kallo, Hannu ya Mika mata Sukayi Handshake sannan yace jeki to bye,baki ta turo tare da cewa ya naji ana cewa Ss1 za a kaini ni fa a Ss3 nake repeating din yayi yawa,Baza ki gane ba sai nan gaba jeki class ya furta yana daga mata hannu, itama ta daga masa hannu tana kashe masa ido daya,dariya yayi kawai ta wuce.
Zata Shiga Class din malamar dake ciki tana koya darasi ta kalli Shukura tare da cewa Beautiful Lady can I Help u? Shukura tace Help ? Help...Help ta ci gaba itama ta tambayi malamar tare da cewa to Help me wiz Money or Wiz Meat, Chocolate,Ice Cream,Shawarma? Ta tambaya tana washe baki,yan Class har malamar suka kwashe da dariya wannan akwai son Dadi ga turancinta na Tsofaffin Hausawa Baza suce With ba sai wiz,Zey etc.
Malamar tace go and sit down,ta wuce sumi sumi ta zauna ita kadai can karshen baya,Maza da mata kallon Shukura akeyi ana gulmar kyanta kamar ita tayi kanta.
Tunanin yan class Shukura Bata da wani kokari tunda sunji kalar turancinta duk kyanta sai suka rainata,Period din Malama ta kare wani malamin Biology ya shigo,ya fara yiwa yan aji tambayoyi what is kaza what is kaza etc,yana yin tambayar farko ba Wanda ya daga hannu sai Shukura,shi kanshi ya girgiza da kyanta yace ta fada,ta Mike ta bada amsa dai dai kuma kawai turancinne idan anji an San Bata kware ba, Malamin yasa aka dinga tafa mata,ya kuma jefo ta biyu Shukura ta kara daga hannu tare da wasu yan aji ya kara nunata ta fada nan ma ta bada amsa dai dai Kafin ya bar ajin saida ta amsa questions hudu.
Wani ma ya shigo haka ta dinga kokari gaba daya sai gashi ta kankaro mutuncinta kowa yasan me kokari ce sai ga students mata da maza Sun fara mata magana dake ita Shukura zai wahala kaga tayi fushi ko ta Bata rai haka suka dan saba kadan ta saki jiki sama sama.
2pm suka tashi ta fito bakin Gate,Drivern Ahleef ta gani Yana jiranta ta shiga suka tafi gida,Yau ma tare da Umma sukayi abincin dare suka gama komai.
Washe Gari Driver ne zai kaita amma tace ita da kafa zata je,ta fito kenan Latifa ma ta fito Sabo da Niima ta bawa Latifa labarin cewa an kawo wata yarinya gidansu Bata da kunya an sata a schl ma Sabo da haka Zata yi mata transfer zuwa makarantar su Shukura domin hana Shukura karatu da