Showing 87001 words to 90000 words out of 96510 words

Chapter 30 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

247

taimakeshi Bata samu taxi ba,sai kuka take a gefen titi tana tafiya, Horn ya Danna Mata tana tabbatarwa Ahleef ne sai ta Kara sauri zata tsallaka titi saura kadan mota ta bigeta, ransa ya mugun baci,parking ya gyara ya fito da sauri tare da jawota daga titi tana kokawar kwacewa ya wanke ta da gigitaccen Mari,kafin tayi magana ya Kara Mata wani sabon Marin sannan ya finciketa ya jefa ta a mota yasa lock kana ya Shiga shima tare da Jan motar suka koma gida tana dafe da kumatunta Wanda yasha Mari yayi jajir dashi.

Yana parking niyyarsa ya kaita wajen Umma ta lallasar Masa ita,amma Yana parking tana kukanta ta balle murfin motar ta fice tayi part dinsu da sauri, kansa ya daura saman sitiyari duk abin duniya ya Masa zafi,ya rasa meke Masa dadi a duniya sai daya gaji da Zama sannan yaje wurin Umma tare da cewa Umma Dan Allah kizo ki lallasheta ta hakura,Murmushi Umma tayi tace ba ruwana wa yace ka fada Mata,kaje ka shawo kanta tun wuri.

Fita yayi ya kyale Umma Yana Jin haushi taki zuwa ta shawo Masa kan Shukura,Shukura kuwa bedroom dinta ta shige Bata leko ba,yayi yayi ta bude Amma taki Haka ya hakura shi kadai ya kwana har gari ya waye da kyar yayi bacci Shukura ma Haka sun rigada sun Saba kwana tare suna manne da juna.

Bata fasa ayyukanta ba ta fito tayi komai har breakfast ta shirya kamar yanda ta Saba sai dai tana yi tana hawayen kishiya,tana tsaka da shirya Dining Ahleef ya fito sanye cikin jallabiya,suna hada Ido yaga har yau kukanta takeyi,mamaki da dariya a bin ya bashi,wani dadi ma yake ji duk a kansa ake wannan kuka Lallai Ana sonsa sai ya godewa Allah.
Kallonta yake Yana sakar Mata Murmushinsa ita Kuma tana harararsa ga Hawaye nabin kumatunta, Ahleef yace sannu da aiki Honey har kinsa naji yunwa wannan kamshi Haka,Banza ta Masa.

Tsokanarta yayi yace da Zaki hakura ma ai da na Baki kyautar gida da mota sannan na kaiki Makka,ai kafin ya rufe Baki tace bana so ko duniya ce ka rike abarka,me zanci dasu tana Harara tare da ajiyar zuciya, dariya yayi sosai yaci gaba da tsokanarta ke da Zaki ma huta da aiki idan na kawo Miki Amarya tana tayaki, Jin ya Fadi Haka a ranta tace Lallai da gaske ne abin Sai ko ta Kara barkewa da kuka sosai take rerawa, Ahleef Baki bude yake kallonta ta shige Bedroom ta dakko takarda da biro tace sai ya Rubuta Mata saki, Bai kulata ba yace Ni ai Ina sonki tare dake nake so na rayu kima daina tunanin wani rabuwa, wucewa tayi zata koma dakinta Bai hanata ba ta Shiga ranar Haka ya yini ba dadi har aka kwashe 3days Shukura taki sakkowa ta hakura, shiryawa yayi ya fita Bai tsaya ko Ina ba sai Gidan Momee.

Bayan sun gaisa ya zauna gefenta sannan yace Momee kiyi hakuri wlh alfarmarki baza ta samu ba,matata baza ta iya Zama da wata ba, Allah ya Bata Wanda ya fini Amma bazan iya auren Niima ba,Momee Bata takura ba tace babu damuwa Ahleef Nima sai yanzu naga Niima Bata Dace da Kai ba sai yaushe zaka kawo min Shukura mu gaisa ko sai nazo? Ahleef yace soon zan kawo Miki ita Momee,Bayan sun Dan taba Hira Ahleef ya dawo gida Bayan ya tsaya yayi musu take away na kayan tande tande.

Hakimar tasa Shukura taci Uwar kwalliya kamar zata je Dinner sanye take da gown me karamin hannu gefe da gefe tsaga ce har cinya rigar readymade ta fito Mata da surarta sosai kamar ka sace ta sai kamshi take zubabawa bakinta da alawa tana tsotsa a hankali tana kallon Tv abinta a Palo.
Sallama dauke a Bakinsa ya shigo da kyar ta amsa Masa tana basarwa ko sannu da zuwa Bata Masa ba,kawai tv dinta take kallo,kamar Bata San da mutum ba, abin duk ya dameshi,sai yaji ba dadi,kusa da ita ya zauna jikinsu na gugan juna,gaba dayansu wani Yar suke ji a jikinsu sunyi 3days ba tare ba, ji suke kamar sun shekara rabonsu da juna, Bata ce Masa komai ba ya fara magana cikin Muryar sa me dadin saurare, wato Shukura Haka zamuyi dake ko? na yarda dake nazo bana boye Miki komai Ina sanar dake Amma baza ki tsaya ki Fahimci abinda nace ba sai ki dauki zafi kina gaba Dani daga maganar da Baki San wani tushenta ba wacce ba gaskiya bace,to na rigada na fada ma Momee bazan aure ta ba,Kuma an kashe maganar ma,Son da nake miki ya wuce na hadaki da wata sabo da bazan iya adalci ba,Amma idan Baki yarda kiyi ta fushinki ke kika sani, ki sani dai bana Miki karya, sannan rayuwar nawa take,zan iya Mutuwa ko yaushe,Kinga dai yanda maza ke Mutuwa,sai mutum ya mutu mata su kama kukan banza komai na duniya hakuri akeyi.

Jikin Shukura yayi sanyi musamman da taji yace mutuwa Kuma tasan baya karya a zancensa,sai taji tausayinsa,tasan Bata kyauta ba,Mikewa yayi zai bar Mata wajen,da sauri ta ruko hannunsa da nufin ya zauna Amma yaki ya fara tafiya,da sauri ta mike tare da Shan gabansa ba zato yaji ta hade bakinsu waje daya da zafi zafi tana tsotsa kamar ta samu alawa, tun Yana jinta ita kadai shima ya tallafi fukarta da tafukan hannayensa masu laushi ya Shiga tsotsar bakinta da sauri sauri an Dade ba a hadu ba,Yana kissing nata itama Haka tana I'm so sorry My Hero,tana Haki kamar wacce sukayi tsere.

A wajen ya fara rabata da kayan jikinta ta wani lumshe Ido tare da taimaka Masa,Kasa karasawa sukayi sama Bedroom a palonsu suka ci gaba da shakatawa da juna,Shukura I missed u kawai take iya furtawa,mazarkwailar Ahleef ta gusar Mata da hankali Baki daya,Shi kanshi ji yake yau tafi ko yaushe mazarkwaila domin yaji kamar ma yau first night ya Gama haukace Mata,Bai San Umma tana tsuma Masa Shukuransa ba shi yasa take Kara mazarkwaila, sun Dade suna gwangwaje juna da zumarsu kafin su samu nutsuwa tare da tsarkake jikinsu,Sai lokacin ta Kara gyara Palon neat sannan suka koma bedroom tare da lumtsuma a saman bed,ita Kuma tana jikinsa tana Wasa da yatsunsa masu daukan hankali, a hankali yace Ki saurareni kiji Honey ke bakya tsayawa ki fuskanci mutum sai ki yanke hukunci,da sauri ta rufe Masa Baki da tafin hannunta me matukar laushi da kamshi kana tace bana bukatar wani magana na hakura ka aureta ai Allah yace ku Kara wlh na hakura tunda sunna ce, Ina sonka zan zauna Haka,tana Gama furtawa Hawaye suka shararo Mata,Dariya Ahleef ya Shiga yi Mata.

Haba ya rike tare da zura Mata Ido kamar zai Shiga cikin Fuskarta,ita kuma Hawaye na zubowa tana kokarin Sharewa Amma sun kasa daina zubowa karshe ma sai ta rushe da Kuka sosai ta fada jikinsa tare da rungumeshi tana ta faman shesheka.

Bayanta zuwa gashinta yake shafawa a hankali alamar lallashi har tayi Shuru sannan yace ki kwantar da hankalinki Zumata wlh kinji na rantse ba aure zanyi ba,bazan iya Miki kishiya ba sai kaddara wacce bana fata,naje gidan Momee na fada Mata gaskiya kinji na rantse kin San bazan Miki karya ba,Dan Allah ki daina kuka kina damun kanki 3days har kin rame.
Lallashi tare da dadan kalamai ya dinga fada Mata Yana nuna Mata yanda yake sonta,sai gashi ta yarda har ta saki ranta suna kyakyata dariya.
Farin ciki ya lullubeshi Ahleef Shukuransa ta daina fushi.ranar kwana sukayi suna farantawa juna rai.

Bayan Yan watanni ansha bikin Farhan da Fatima,Shukura babbar kawar Amarya,Ahleef a barin Ango sosai bikin ya kayatar.
Niima da Latifa suna gaban Momee,Sultan da Suhail Wanda jiya suka sauka a kasar suka shugo Suma suka nemi wuri suka zauna kusa da Momee, Sultan yace Momee munfa samu matan aure tunda muna da wadata aure zamuyi,Suhail tasa sunanta Basma Yar Kano ce suka hadu a schl,Ni Kuma Islam ce Yar Gombe ce yanzu sunce mu tura manya,Momee murna ta kamata tace Alhmdllh tunda dama kun dawo Nigeria Baki daya me ya rage kawai sai aure,Niima da cikinta Kato tace Hmm Bros na tayaku murna,Latifa tace Allah muma ya bamu sai a hada bikin,kowa yace Ameen daga Nan suka Mata sallama sun wuce gidan Ahleef zasu Kai Masa ziyara daga nan shima su sanar Masa sun samu matan aure.

Mubaraq dai har yau ba labarinsa tun Ana nemansa har an gaji an hakura,Mama Bata da aiki sai kuka sabo da duk cikin yaranta tafi son Mubaraq,Hafcy dasu Zahra su kansu abin Yana damunsu yanzu gidansu duk ya tarwatse Mama da Daddy Basu da nutsuwa,Alhaji Adamu yana cikin damuwa Wanda Dalilin Haka ya haifar Masa da ciwon Hawan jini,gashi Kuma wani Masifar Ashe Alhaji Adamu Baban su Hafcy manemin Mata ne kamar Dan akuya Haka yake,Koda ciwon Hawan jinin sa ya tashi Bayan yaje asibiti aka yi masa test iri iri Nan aka gano Yana dauke da cutar Hiv, Mama Basu sani ba ya boye mata,

Bayan wasu watanni Niima ciki ya tsufa sosai tana ja da kyar haihuwa ko yau ko gobe, da safe da wuri yau nakuda ta kama Niima Momee da Latifa suka tattara sai Asibiti,Latifa sai kuka takeyi sabo da yanda Niima ke azabtuwa da nakuda, Momee hankalinta ya tashi,su Sultan du suna asibiti,Ahleef Yana kitchen manne a jikin Shukura tana soye soyenta wayarsa tayi Kara ya dauka ganin Suhail ne ya Kira shi, hankali tashe ya fada Masa Niima na asibiti zata Haihu Rai a hannun Allah,da sauri ya datse wayar Yana sanarwa Shukura ta hade Rai tare da turo Dan lips dinta me shekin Pink color ta furta to Kuma ba sai ayi Mata Addua ba Kai mene naka ciki ko Kaine angwazoma din da zaka karbi haihuwar, haihuwar ma ta cikin shege har murna akeyi sabo da duniya tazo karshe to wlh sai dai mu tafi tare duk motsinka Ina gani bare ayi ma signa da Ido, gas ta kashe tare da wanke hannunta a sink da sauri tace muje na shirya mu tafi, dariya ma ta bawa Ahleef da wannan mitar Tata,wani farin ciki na ratsa shi Shukura na kaunarsa da yawa shi Kam ya godewa Allah Yana son yaga Ana kishinsa.

Tare suka wuce Bedroom ta Sa katon Hijab har kasa Amma duk da Haka tayi kyau,shi Kuma da 3qtr da Riga me shegen tsada da kyau,Shukura ta dauko jallabiya tace sa wannan so kake a kalle maka fata Ana hadiyar yawu, Murmushi ya saki me sashi sumar da mace ya manna Mata kiss a kumatu sannan yace I love u my wife,me too cewar Shukura ta fara tube Masa Riga sannan ta zura Masa Jallabiya akan wandon tace muje to,Bai Musa Mata ba ya bita tana rike da hannunsa,har Mota driver ya jasu sai asibitin da Niima ke nakuda.

Niima an Gama galabaita kamar zata mutu tuni su Shukura suna asibiti Kam Kam ta rike mijinta ta window ta leka ta dawo,Amma ta mutunta Momee sosai itama Momee haka,Su Sultan Suna ta tsokanarta saura ita Nan gaba tana dariya cike da kunya,Ahleef ya Rada Mata a kunne gaskiya ya kamata muma mu dage a samo Mana Baby, a hankali ta Dan dakeshi kadan da Wasa, Niima har ta fara barin wasiya iri iri tana kuka Allah ya taimaketa ta santalo yarta mace katuwar gaske zukekiya me kama da Mubaraq, Babu Wanda yayi Murna sai Niima ita taji tana kaunar yarta a ranta fiye da kowa.

Bayan ta samu sauki an gyarata tare da Baby Haka Su Ahleef suka dauketa ba tare da kyama ba aka dinga zuba Mata adduoi iri iri, a ranar aka sallamesu Bayan komai ya Lafa makwafta da Yan uwa sai tsegumi da gulma akeyi Dan ma a Haka Abuja ne ba ruwan wani da wani da arewa ne sai dai Niima ta koma kauye,Momee har gida taje ta sanarwa Alhaji Adamu da Mama Niima ta haifi Yar cikin Mubaraq, daga Mama,da Baban Mubaraq har su Hafcy ba Wanda bai zub da Hawaye ba,Amma Haka Dole suka je da Sha Tara ta arziki suka ga jaririya sak Mubaraq,Mama duk an fara saduda da Duniya sabo da balain da suke Sha kullum iri iri na kaddara.

Kafin Suna Mama tace a sa Mata Khadija kawai ko Allah zaisa tayi Hali na gari irin na Nana Khadija Matar Manzon Allah,hakika Ahleef ne ya yanka Mata rago manya har biyu taci gaba da raino Yarta ba tare da kyama ba,Haka dangi ma kaf tunda Momee ta sasanta tsakaninta da danginta,Haka ma da Dangin Abba.

Yau Niima tayi arbain yaune Kuma suna zaune suna kallon News suka ji labarin an kama wasu masu safarar kwayoyi zuwa kasar waje sai ga Mubaraq hannunsa daure da Ankwa ta ko Ina an kamasu a airport sannan an dawo dasu Nigeria za a Yankee musu hukunci.











AsmaBaffa.




Taku har kullum afwa bana typing da wuri Uzuri dai nake so ayi min fans Kar kuji haushi next Novel inshallah da time baza ayi Haka ba idan aka fara sai an gama.
Godiya dubu masu Sharhi 😍😍😍😍.
[7/22, 1:14 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SANO









END














91-100










Official







By
AsmaBaffa








ASMABAFFA FANS CLUB
JIN DADI SABO
HOUSE OF HAUSA NOVELS.
Ina Godiya sosai da kaunar da kuke nuna min,ga Sharhi akan lokaci Allah ya biya.









Yaune Friday yaune Kuma za a daurawa Niima da Latifa aure,ba wani biki za ayi ba sabo da Yan gulma da tsegumi,Latifa da Yousuf dinta sun so ayi party etc Amma Sabo da Niima za ayi ta surutu yasa Momee ta Hana tace Ana daurawa za a Kai amare ba wani gulma.

Shukura sabo da Murnar Niima zatayi aure ta bar Mata mijinta tun Ana gobe ta addabi Ahleef ita sai tazo ta kwana,yace baza ta kwana ba,Amma ta dinga naci Dole ya kyaleta driver ya kaita,Ana idar da Sallar jumaa aka daura auren Niima da Mubaraq, Latifa da Yousuf, Bayan sallar laasar aka wuce da amare gidajen mazajensu a cikin garin Abuja,cikin Yan Kai Amarya harda Shukura tana motar Sultan,maimakon ta dawo gida sai ta koma gidan Momee, Umma tana gidan itama Driver Yana zuwa daukan Umma sai ta tasa Shukura gaba suka tafi gida, lokacin Ahleef Yana tare da Baba suna Hira yaga Shukura da Umma farin ciki ya Kamashi yasan Umma ce tayi Mata Dole suka dawo tare.

Baba ta gaisar sannan suka hada Ido da Ahleef ya kashe Mata Ido daya,Murmushi tayi kadan Wanda shi kadai yaga hakan, ba kunya ya mike tare da yiwa Baba sallama Yana me yiwa Umma sannu da zuwa yabi Shukura harda daukar Mata handbag ya rike suka jera part dinsu sai zumudi yakeyi sabo da kwana daya kamar shekara yake gani,suna Shiga ya fara warwarewa Shukura hadda da salon love dinsa, dama Shukura kadan ake jira ta Shiga maida Masa da martani yanda taga dama take sarrafa shi shima haka, albarkatun kirjinta ya fara sarrafawa Wanda yasan Yana taba su Shukura zata rude,a nutse suke sarrafa juna sai da suka zauce, Ahleef Wanda dama kwararre ne a wannan fagen rada Mata yayi a kunne da akwai Dadi? Shukura cike da Shauki tace sosai ma itama cikin siga ta rada,
Tambayoyi yake Mata iri iri ba kunya take bashi amsa sai su Kara rudewa, yaudai ansha love,tunda yaje Office washe gari ba abinda yake tsinanawa sai tunanin Shukura da Daren jiya yanda ta jiyar dashi dadi,ba shiri ya tattara ya gudo gida ya Kara kwasar harkoki ya samu nutsuwa ya sake fesa wanka Yana nishadi ya koma Office.

Niima Amarya Suma sun kwashi love dama sun Saba da juna,Haka Mubaraq yaji dadin harkar sabo da Tasha gyara, yarsu Khadija tana wajen Momee anyi Mata yayen dole sai sun Gama cin Amarci za a kawo musu yarsu suci gaba da rainonta,Mubaraq da Niima sunce sun barwa Momee ta rike ta, Momee ta karba hannu biyu kuwa tunda yarinya ba ruwanta Kuma yanzu Babu kowa a gabanta sai Yan aiki.
Latifa da angonta Yousuf suna can Suma Ana kwasar Amarci, abinda Latifa tayi shi mijinta yayi shima ya tuba Dan Haka ba Wanda zai wa wani Gori,Sunyi shaye shaye sun tuba,Niima kuwa dama tare suka sheke ayarsu Kuma suka yi aure Bayan Sunyi Nadama.

Maman Hafcy da Alhj Adamu sun kwantar da hankalinsu suna Shan magani sai ka rantse sunfi kowa lafiya ma,Babu Wanda zaice suna dauke da HIV, haka ake so mutum ya kasancewa me yadda da kaddara,ba Wai dan cuta ta samu mutum ba ya zauna yayi ta tunani duk ya rame bakin ciki ya kasheshi a banza,ayi Addua Ana fadawa Allah ko maganin ne sai Allah ya kawo ma,idan ma Bata da magani sai kuga Allah ya Hana cutar tashi har ta cutar da mutum.

Hafcy da Zahra sun samo miji amma duk ba Wanda ransu ke so ba Haka suka hakura domin dattijawa ne,Alhaji Danliti shine na Zahra Yana da Mata da Yara Bakwai duk manya ne yaran, Alhaji Zubairu kuwa tsohon tuzuru ne Wanda yafi shekaru ashirin ba tare da yayi aure ba Tunda Matarsa ta rasu ta bar Masa Yara uku Yan Mata dasu, Baban su Hafcy da kansa ya Kai Masa tallan Hafcy ya aureta.
Kasancewar mazajen masu kudi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login