Showing 54001 words to 57000 words out of 96510 words

Chapter 19 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

242

ta fasa aurensa wlh duk da tasan itama ba budurwa ba ce Amma baza ta auri namiji me neman mata ba,Hafcy dai kafarta daya na ciki daya na waje.
Ahleef Yana can bai San me akeyi ba Yana ta gwada wayar Shukura Shuru Umma da Baba kuma sai dai suce masa Shukura tana Nan cikin koshin lfy kar ya damu,abin ya fara damunsa.











AsmaBaffa
[7/22, 1:13 PM] Sis Asma: 🍱🍱🍱
JIN DADI SABO







36-40







Official






By
AsmaBaffa









Sabo da Jin dadinku masu Sharhi na baku wannan....kuna birgeni tnx all.















Shukura kwance kasa ta sume,alummar kauye Ana kallonta dangin Innarta dana Baffa babu Wanda ya tausaya mata ko ya tsaya ya saurareta kowannensu ji suke kamar su kashe kowa ya huta da wannan abin kunya,wani Dan matashi ne cikin dangin Rabe ya kwara mata ruwa ta farfado tana zare Ido tana kallonsu tare da Kara tsanar danginta na rashin Zumuncinsu tare da nuna mata kiyayya sabo da iyayenta basa Raye,Nan Mutuwar iyayenta ta dawo mata sabuwa ta fara zubar da Hawaye masu dumi, su kuma manya da Yara mata da maza suna Kanta a tsaye suna mamakin ganin yanda Shukura ta goge ta Kara kyau da Haske,cikinsu wata tsohuwa tace ta tababbata juna biyu gareta gashi duk sai kyalli take.

Wata yar budurwa ta fashe da kuka tace shike Nan ta jawo Mana Babu Wanda zai auremu a garin Nan tayi Mana tambarin da bazai gogu ba,yanzu Ja'e nasan fasa aure na zaiyi yace muma bamu da tarbiya, kawu Babban banza yace share hawayenki ko da suratul Yusufa sai kin samu me sonki kuma yau zan fara rubuta Miki kina shanyewa maganin farin jini haka suka dinga cakaki akan Shukura har suka fara tafiya gidajensu Ana Allah wadai da Shukura,a hankali ta mike ta nufi gidan Kawu da niyyar shiga,Kawu yace Ahir dinki aradu kina tako kasar gidana zan karya Miki kafafu,tasan Halinsa ba Imani,sai ta nufi gidan wani Shima ya biyota da sanda,haka ta dinga zagawa kowa na korarta ta rasa Ina zata shiga,da kyar ta roki Megari ta zauna a gidansa zuwa wani lokaci Amma Megari guda yaki yarda yace saidai ta kwana a yar bukkarsa ta kofar gida ya bata Amma ba a gidansaba, haka ta hakura ta shiga dakin kofar gida kowa Yana kallonta. Matar Megari Talliya tace yo Kai Malam ai kawai ta dawo cikin gida da zama kaga na samu yar aiki,yo me zaisa mu Bata wajen kwana da abinci kyauta a banza tazo ta dinga min aikin gida Ana Bata wajen kwana da abinci

Megari yace Talliya kin kawo Shawara ga dakin cikin gida a Bata ta dawo,haka Liman yasa ta shugo da kayanta akwatuna, har Biyu,Talliya tace oh amma Shukura a barikin masu kudi kike harkalla dasu? Irin wannan Kaya haka ga kyau kin Kara,Shukura takaicin ya rufeta tace da aurena fa ni ba bariki nayi ba,mijina Yana Nan,Talliya tabe Baki tayi tare da cewa ke kika sani ni Dalla tashi ki Kai min Nika,ki dawo kuma aikace aikace na jiranki ba hutu kikazo yi ba abinci da wajen kwana fa zamu Baki duk lalacewarki danginki kaf sun gujeki Amma mu muka dauko wa kanmu,da can sanda iyayenki suna da Rai wanne irin iyayi ne bakiyi a garin Nan ba da tabara ke ga yar gata,to yanzu Ina gatan?

Shuru Shukura tayi tasan yanda Yan kauyen suke mata hassada tun asali sabo da ta fisu, karshe dai cike da bakin ciki ta fito Kai Nika,sai nuna ta akeyi a kauyen tayi cikin shege ta dawo daga bariki,ko bako ya shigo kauyen sai ya ji labarin, bayan Shukura ta kawo Nika ita tayi abincin gidan me gari ga uban yawa kamar na gidan biki ba karamar azaba Tasha ba,bayan ta gama sai da tayi wasu ayyukan a Daren sannan ta samu Talliya ta barta tayi wanka tare da sallah karshe aka Bata tuwon taci Wanda Babu dadi sabo da yawansa kuma ba kayan Hadi ne a cikin miyar ba,Amma duk da haka ranar da kyar aka samu miyar dumamen safe ta ragu kadan sabo da dadin girkin Shukura kowa yaji dadinshi.

Ko da Shukura ta kwanta in Banda tunanin mijinta Ahleef Babu abinda takeyi Nan ta tuno irin Jin dadin da sukayi ranar da suka kwana tare,Nan take ta lumshe Ido tare da dakko rigarsa jallabiya cikin kayanta tasa abarta ta kwanta tana tunaninsa Nan bakin cikinta ya yaye Baki daya duk da frnd dinta ne tana muradin kasancewa dashi har karshen rayuwarta.

Washe gari tun da asuba Talliya ta tasota a masife ta damawa Yan gidan Koko ga Yara kana na har da almajirai a gidan birjik, megari bayan yasha miyar jiya yaji kamar ya tsinke yatsansa sabo da dadi yau ma ya kurbi Koko a fili ya firta shegiya bariki badan ba abune me kyau ba ai da ka tura matarka ko Dan ta koyi girki,Harara Talliya ta watsa Masa tare da cewa to me kake nufi? Murmushi yayi tare da cewa ja'irar yarinya da ita Amma ta iya girki haka duk shagwabarta Ashe ta iya girki gaskiya ki koya,tsaki Talliya tayi ta bar dakin fuuuu a fusace.

Da Rana Shukura duk ta gama aikin da aka sata,sai rike kugu take ta gaji sosai tana rokon Allah kar cikin Ahleef ya zube, Amma Talliya ba Imani tace daura girkin Rana kiyi Mana dafadukan shinkafa da manja, Shukura ta gingima tukunya ga itace hayaki ga Rana haka ta kwaciba girkin,tana sani tayishi yanda bazai dadi bama, Ana zubawa me gari da almajirai da sauran yaran gida haba kowa Santi yake zubawa har ita kanta Talliyan,Shukura ta kasa cin abincin sabo da ba dadi Amma su a haka yafi na Talliya sau dubu,Megari sai washe Baki yakeyi,mamaki ya kama Shukura tana cikin haka ta fada tunanin Ahleef dinta Wanda ya fiye mata komai ita kadai sai gashi tun tana Murmushi ta koma sheka dariya, dukkan yaran gidan da Me gari kansa kowa kallonta ya koma yi Baki bude, wani cikin yaran yace Wlh wannan me kyau ce, Me gari yace ke Lfy?shuru Shukura tayi Nisa har kanta take girgizawa tana dariya,Talliya Baki bude tace ke Dan Uwarki ba dake ake ba iyeeee ta zabga mata duka a baya, da sauri ta dafe wajen tana sosawa cike da Shagwabarta tace wayyo Mijina,Talliya tayi zaton da Megari take ta kirashi da mijinta, tace karuwa uban waye Mijinkin?
Nan take Shukura ta saki sabon Murmushi kamar ka saceta sabo da kyau sannan ta kalli Talliya tare da turo mata Yan lips dinta jajaye tace Mijina fa can kin San sunansa ma abin so ne,Ahleef,kyakyawa,duk kyauna ya fini,Babu abinda nafi so a jikinsa irin idonsa,da Murmushinsa wlh Anty Talliya idan kika ganshi sai kin kusa Suma,ga kudi,ga ilmi,ga addini,ga hankali,ga nutsuwa,ga iya soyayya ni kadai naji me naji dole na haukace ko....Dalla rufe Mana baki Lallai Babban bariki kika buga,Shukura tace wlh mijine na sunna, Me gari yace Ke karki Raina mana hankali fa yanzu Kya bar Mana gida.kinje Karuwanci ae kinyi ki Mana shuru kawai ki ajiye iskancinki gefe can.

Shukura yau tayi sati guda a gidan Me gari Amma kullum aiki take kamar jaka a gidan, komai an sakar mata,duk tayi duhu ta rame kadan,ga tunanin Mijinta da ya addabeta,yanzu duk kayanta akwati Biyu manya Bata sawa sai Jallabiyar Ahleef da kuma wata rigar shaddarsa light blue,duk inda zata a garin a haka take fita sai dai ba kazanta zaka ganta fes kullum sabo da Megari Yana Bata kudin sabulun Dan ma watarana idan son dadi ya motsa sai ta siyi kifi soyayye da kudin taci abinci dasu.

Shukura ta koma wajen dangin mahaifinta Dana Innarta ko zasu karbe ta Amma sunki yarda taje yafi a irga Amma sunkiya,sai wahala take Sha gidan Megari da girki, gashi Me gari yaji dadin girkin ta baya so kowa yayi Masa girki sai Shukura,bashi da aiki sai yabon Shukura da iya girkinta Yana cewa kuma badan bariki ba ai tana da hali me kyau,kullum maganarsa Bata wuce ta Shukura a gaban abokansa,Liman ma abokinsa ne kawai sai ya bashi Shawara ya auri Shukura kawai,Me gari yace wuuuu tafi karfina wannan kaji yanda take bariki a gidana yanda Kiri Kiri take bamu labarin farkanta,yanda take sonsa kullum har mun gaji da ji,abin ya Kai kaga tana sheka dariya ita kadai idan ta motsa ma kuka zaka ga tanayi tana magana da turanci ko me take cewa oho,ni kuma kasan Liman ni mutum ne me tsananin kishi.

Liman dai ya karfafawa me gari Lallai ya auri Shukura ko ta wanne hali ne tunda shine me fada aji a garin,Da kwarin gwiwa Me gari ya dawo gida Nan ya iske masoyiyar tasa Shukura tana kwance saman wata Tsohuwar tabarma gindin bishiyar dake cikin gidan,Tana Hawaye sannan tana Dan Allah kazo gareni My Ahleef,Ina jiranka nasan zaka zo,Mijina I really missed u,my best frnd my Everything pls am waiting....sai maganganu take a fili kamar me aljanu,kishi ne ya soki zuciyar Dattijo MeGari Nan take zuciyarsa ta baci a fusace ya buga mata tsawa keee wai wannan turancin da kike me kike nufi ne idan zagin sauran Masoyanki kike yau kina fifita Farkanki a kan sauran to ki sanar min wlh naje har can na kwade shege da sanda mene amfaninsa.
Shukura kallon Me gari ta fara ba shiri ko dai ya haukace ne?ita Bata Fahimci me yake nufi ba Sam, amma duk da haka tace nufina nayi kewarsa,shi nake jira yazo gareni ya daukeni mu tafi,Me gari yace uban wa? Mijina Mana.

Talliya ce ta fado gidan gabanta ya yanke ya Fadi ganin Me gari gaban Shukura kamar me rokon Gafara,Salati ta saki tare da cewa da mutuncinka?wlh tashi maza kafin na Tara muku jama'ar gari ki bar min gida,har abada Baki Kara ko 1hr a gidan Nan,Megari zaiyi magana Amma Talliya tace na rantse da sarkin dake busa min numfashi kayi magana ko ka hanata tafiya sai na Tara ma jama'ar gari kaf nayi Maka sharrin da baka zato, Tabarya Talliya ta dauka a Haukace tayi kan Shukura da gudu Shukura ta fada dakin da take kwana,ta fito da kayanta dake akwatuna fit tayi waje Hawaye Suna shararo mata yanzu Ina ta nufa,Talliya kuwa cewa take daga sati daya har an fara zagayowa Nan ta ingiza keyar Megari ta kulleshi a daki Dan karma ya fita ya taimaki Shukura.

Shukura kuwa hadiye kukanta tayi ta ta fara bugar kirjinta tace Shukura Hadiye kukanki ki zama me zuciya,kinje birnin tarayya ma kinyi abinda kika ga dama bare kauye gidan kwana ya gagareki?kamar bake ce kika iya satar shiga gida ba komai kyansa da lalacewarsa, a fili ta furta kalamanta a ranta tana cewa zan iya canja gari ko state ma Amma Nan garin kadai Ahleef zai San Ina Nan,Nan zai zo ya daukeni mu tafi muji dadinmu.da murna har tana rera wakarta ta ja akwatunanta sai Gidan Aishalle wacce akayi mata aure tun suna Yara basa shiri da Shukura Amma Shukura yau ta yarda Aishalle tafi Yan uwanta kawai ta kwada sallama a gidan,Mijin Aishalle ya ganeta to shi Allah ya bashi hakuri shi yasa ya kasa korarta akwai Kara da alkunya a tare dashi,Shukura ta gaisheshi tare da cewa dan Allah kar gabanka ya Fadi ba wajen kwana na zo nema ba,yar Iskar matarka zaka Kira min na Bata ajiya,Sai ga Aishalle ta fito daga Bayi ta kalli Shukura sannan tayi Murmushi tare da cewa kina Nan dai da halinki to Dan Uwarki kawo ajiyar ki tafi kin San dai ko sanda kina garin Nan zaneki nakeyi,Mijin Aishalle ya kallesu yayi dariya ya tabbata kaf dinsu kuruciya ce ke taba su basuyi hankali ba tunda Yara ne har yanzu.

Kafin ya gama tunaninsa Shukura tace ke ja can da muninki Amma ni Baki ga Mijina ba wlh duk ranar da yazo garin Nan na tabbata sai kun sume inda kika San aljani kin San bana karya zaku gani kuma kyau ne ya auri kyau ba irinki ba Muni ya auri kyau,Mijin dai dariya yake suna ta zagin juna karshe Shukura ta bada ajiyar akwatunanta tayi gaba,tana fitowa sai da ta zage gidajen danginta kaf Bata kuma yiwa kowa magana zata fito abinta, ko ma ka kulata baza ta kulaka ba,gidan Kawu ne na karshe Matar sa ta gama miyar ta tare da tsame Naman kaza ta ajiye kazar a gefe tana gyara miyarta,Shukura ta shigo idonta ya sauka kan kwanon da kazar guda take ci har murfin kwanon ba ya iya rufe kwanon sabo da kazar ta tokare ko Ina, Alhmdllh Shukura ta furta tare da cewa an Dade ba a hadu ba, Kawu na gefe a zaune Yana jira a kawo kaza, Shukura ta tuno rashin mutuncin da Kawu ya mata kawai ta dauke kwanon kazar ta koma kofar gida abinta ta zauna gefe ta rike kazar Nan da hannu biyu tana yaga a nutse tana ci,sai da taci tafi rabi,Kawu da Matarsa tare da yaran gida duk Baki bude suke jira suga Shukura ko zata dawo da Kazar Amma shuru,har Kawu ya kasa Hakuri ya zari katuwar sandarsa ya fita neman Shukura sabo da kazar ma Bata da lafiya da kyar ya bari aka yankata Dan yaga zata mutu ne Amma shine tazo a banza to wlh sai ta biyashi kudin kazar indai taci.yana fita ya iske Shukura tana yagar kaza,tana ganin Kawu ta mike tsaye kuma tana ci gaba da yaga tana uhmmmm dadi wlh Kawu gaskiya nagodewa Allah da Kaine Dan uwan Babana na jini,kayan wa mutum ya Isa ya taba idan bana Dan uwansa ba,shi yasa nake Alfahari da samun Uba kamarka.

Kawu ji yake kamar ya hadiya zuciya har wani cije Hakora yake Sabo da masifa,Ki nemi ubanki,ni ba ubanki bane bana fatan ki zama yata ko wata yar uwata,kuma wlh tunda kika Ci kazar Nan ban yafe Miki ba ko yanzu kika mutu sai munyi sharia dake a gaban Allah sabo da Baki da gadona, Shukura ta fara yar dariya tana ja da baya gudun kar Kawu ya kamata tasan kawai ta mutu,ta yagi kaza tace ka Fadi kudinta naci bashi idan Mijina yazo zai biya,ba kunya Kawu ya dinga tsine tsine akan kaza sabo da son abin duniyarsa, Shukura tace za a biyaka Kawu relax calm down Ok,Kawu yace kin zagi Uwarki ta kabari ba ni ba,kuma tunda kika zageni da turanci wlh sai Naga bayanki a garin Nan,sai na tabbatar Miki barikin naki bai je ko Ina ba,yaja kwafa ya shige gida,Amma Shukura sai ta tabe Baki ta mayar da ragowar cikin kwanon ta rufe ta shiga har gaban Matar Kawu ta ajiya da sauri tace a rabawa Yara su maida yawu ni kuci na baku kyauta,ku Yan uwan nane na siyi kazar wurin Kawu, wata yar Budurwa wacce Kawu yace zai fara Bata rubutu Tasha, tace talaka Ina kika ga sisi? Me kikayiwa kanki bare wani,Shukura tace na tabbatar Miki ki bani lokaci kadan sai na siye garin kaf na bar muku kyauta ku zauna Zaki gani, Da ace ke ba yar uwata bace to siyenki zanyi ki koma baiwata Amma kinci darajar zumunci,Kawu ta kalla tace da sannu duk mutanen garin Nan sai sunyi nadama indai Allah ya bamu Rai da Lfy tana gama fadin haka ta Kara gaba abinta.

Gidan yar Uwar Innarta Yafendo take kallo daga nesa tana tsara yanda zata dinga shiga gidan ba tare da an gane ba, masifaffiya ce ta gaske gashi komai ita ta iya wani bai iya ba,tana da zaratan samarinta guda biyu suna zamansu a gida daya tare da matayensu,Yafendo akwai Tsafta da komai ita ta sani wani bai iya ba. Shukura ta zabi zama a gidan sabo da gidan Kato ne baza a gano ta ba, har dare tana can bakin Rafi tayi sallar Isha sannan ta karaso gidan dama su katangar Kara ce kawai ta Buda yar kofa dai dai ita ta baya ta shige gidan ta gyara musu katangarsu yanda take ta bi ta jikin rumbu ta buya a bayansa tana kallonsu suka Gama hirarsu da cin tuwonsu kowa ya tafi ya kwanta gida yayi Shuru, Yafendo tuni tayi bacci a kan Dan gadonta,Shukura cikin duhu ta lallaba sabo da ganganci ta shiga dakin Yafendo ta sadada ta shige karkashin gadonta dake gadon karfe ne me rumfa tun irin na zamanin da,Ko Ina a Tsaftace Shukura ta shaki baccinta har gari ya waye, Yafendo ta fita tana shararta da ta Saba har kofar gida take Sharewa Shukura ta fito a sace ta ebi ruwa a botiki da buta ta shige Bayin Tsohuwa da sabulunta tayi wanka da Alwala tare da maida kayanta da sauri ta koma dakin,tayi sallar asuba Yafendo Ana can Ana share share sarakan Tsafta,Surukar Yafendo Indo ita ta shigo dakin lokacin tuni Shukura ta koma karkashin gadon tana gani ta ajiye Koko da fanke me sugar,sai ga daya Surukar ma Gaje ta ajiye kosai da Kunun tsamiya yasha Nono lafiyayye a samansa,suna fita Shukura ta janyo Kunun da kosai sai ta dakko sabon ludanyin Yafendo Tasha dashi yanda take so ta mayar ta rufe komai ka rantse ba a taba komai ba haka aka kawo yanda taci da dabara ta mayar ta ajiye komai yanda aka kawo,haka ta jawo fanke ma taci guda uku ta mayar,Ludayin Yafendo kuma ta boyeshi can gefe cikin kasan gado.

Yafendo kuwa tana gama aikinta tayi wanka sannan ta dawo dakin tana masifa mata Basu iya abin duniya ba haba Ina rayuwa zata tafi a haka,ba tare da ta kalli kasan gadon ba ta zura hannu ta jawo kwandon kayan kwalliyarta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login