Showing 90001 words to 93000 words out of 96510 words

Chapter 31 - Jin Dadi Sabo Book 1 Hausa Novel Complete

19 Jan 2025

251

Ne a shirye suke aka sa biki wata daya tal.

Hafcy da Zahra tare da Mama har gida suka je suka bawa Momee hakuri tare da Ahleef har Shukura suka yafi juna sannan suka ci gaba da mutuncinsu sama sama da Momee.
Duk da Haka Basu da kwanciyar hankali da zarar sun tuna fa Mama da Dad dinsu suna tare da cutar HIV ko yaushe zasu iya fecewa lahira.

Shukura cikinta ya cika 7mnths ya fito kato dashi ga makaranta kullum tana zuwa,tana kula da mijinta sosai ga Tsafta ga iya kwalliya,girki gashi tayi wani irin wayewa ta daban,fagen soyayya kuwa Shukura ba a cewa komai,Umma wannan shekarar Ahleef ya Kuma biya musu Hajji da Umra,sannan idan sun dawo zasu tattara gaba daya suje Niger wurin dangi,Shukura ma rigima ta ajiye Wai idan Sunyi hutu sai ya biya Mata ta Kara aikin Hajji da Umra,Ahleef Kuma yace sai ta haihu zai biya musu suje tare da zaga kasashe.

Zaune Ahleef yake saman luntsumemiyar kujera dake palonsu na kasa,Karar door bell yaji,bude kofar yayi ya iske Farhan da Amaryarsa Fatima sun Sha kyau, uhm manyan gari Ashe kune Amma ko ku sanar damu zuwanku sai dai mu ganku, Bayan sun zauna suka gaisa Ahleef ya mikawa Farhan hannu suna gaisawa,Shukura ta fito taci wanka cikin doguwar Riga ta wani lace tsadajje,tayi mugun kyau,da Dan cikinta a gaba ya Mata kyau,Gefen Ahleef ta zaune tare da kwantar da kanta a saman kafadarsa tare da narke masa.

Fatima ta kalleta tana dariya,Ahleef yace bashi kike ci Fatima akwai time zamu Rama muma,Farhan Wanda ke dariyar shima yace sai dai ku rame, sun Sha Hira kafin daga bisani su Shukura suka shirya suka fita tare su hudun,Gidan su Sultan suka je,sannan suka wuce gidan Niima da Latifa,karshe har gidan Momee sukaje sannan suka biya yawon shakatawa suna ciyen ciye gwanin birgewa sai soyayya ko wannensu ke zubawa Dan uwansa, Shukura duk ta fitsare kafafunta Bata kunyar mutane zaman Abuja cudanya da arna duk sun jawo ta rasa kunya mijinta ko a gaban waye ba ruwanta, Fatima ce take Dan jin kunyar Ahleef ma Amma shi ko a jikinsa Hankalinsa Yana ga Shukuransa.

Wani kallon so Shukura ta zubawa Ahleef shi kanshi dariya abin ya bashi Bai San sanda ya Shiga murmusawa tare da cewa Allah ya shiryeki Honey,dariya itama tayi taci gaba da bashi Ice cream din da suke Sha, kowa ya wuce sai ya kalli wannan masoya,Fatima Kuma Farhan ke Bata da kansa suna hirarsu, sun Gama suna niyyar tafiya sai ga Niima da Mubaraq dinta Suma sunzo,Har ga Allah Niima a rashin Ahleef ta auri Mubaraq tafi son Ahleef Amma ya ta iya yafi karfinta,Dole ta rungumi minjinta Haka,Ahleef yace Ashe Nan zaku zo Kuma,Mubaraq yace bamu yi niyya ba kaga sarkin yawon da ta matsa sai mun fito,dariya sukayi gaba daya sannan suka wuce,Farhan motarsa tana gidan Ahleef suna komawa suka koma motarsu suka wuce gida.

a kwana a tashi Ana zaune lfy da juna,Shukura cikinta ya Shiga wata tara, Ahleef tafiya ta taso Masa zuwa Canada Amma yace ba zai je ba sai Matarsa ta haihu zasu tafi tare, yau Monday Ahleef Yana Office Shukura ta fara Nakuda,Umma ta shigo dubata ta isketa tana murkususu Bata bi ta kan Ahleef ba tasan halinsa a kan Shukura sai yaje yayi hatsari a banza, Driver tasa ya wuce dasu asibitin kudi,kamar jira sukeyi Ana zuwa Shukura ta haifo danta Namiji katon gaske kyakyawa jajir dashi, Shukura tayi juriya sosai Babu wani kuka ko wani surutai ta birge Umma kwarai,Bayan an gyarata tare da jariri yasha adduoi, Umma tasa aka gogeshi tas da Man zaitun Dana habba,dake Private ne dakin kowa shi daya,kamar wani Hotel, anan Shukura tayi wanka ta da ruwan zafi tare da gasa kanta sosai sabo da Umma ta Gama nuna Mata darajar gasa jiki, Bayan sun Gama komai an rubuta Magunguna na Karin jini da wasu masu warkar da rauni aka sallamesu, suka dawo gida part din Umma.

Nan Umma ta Kara dafa Mata ruwa akayiwa jariri wanka fes itama ta sakeyi ta shirya cikin wata atamfa hadaddiya riga skert sun kamata daf kamar ba itace ta haihu ba tayi Masifar kyau ita da jariri,dama Ahleef tunda ta kusa haihuwa yake ta siyan kayan jariri, kamshi suke zubawa kawai,Umma ta kawo Mata farfesu da abinci lafiyayye suka ci suka koshi,Baba yazo ya dauki jariri tuni Yana sheka Masa Addua,yace Banga Ahleef ba,Shukura kamar zatayi kuka cike da Shagwaba tace Umma ta Hana a fada Masa Wai har sai ya dawo ya gani,Wai zaizo ya dameta da sintiri, wannan Shirme ne ai cewar Baba Bari na kirashi Yana latsa wayarsa ya Kira Ahleef Yana dagawa yace Allah ya sauki Shukura lfy kazo gida,Ahleef Bai San sanda ya buga ihun dadi ba Nan ya fara Godiya ga Allah sannan ko escort Bai wani jira ba ya figi mota ya figota a tamanin, sai gida direct part dinsu ya nufa,sai ya iske a kulle,Part din Umma yayi Yana fyalla uban sauri kamar zai tsinke kafafunsa fit ya shige Palon Umma ya manta da wata sallama,Umma tana rike da jariri a palonta Shukura tana gefenta tana cin Apple.

Tsayawa yayi a tsakiyar Palon tare da tsurawa jaririn Ido Yana kallonsa Yana wani Murmushi me kayatarwa, sumarsa me yawa da santsi ya shafa,Baki bude Umma ke kallonsa,Shukura Kuma Ahleef take kallo itama tana wani Murmushin Jin dadi sun haifo dansu, Sai da ya dauki lokaci sannan ya Karasa wajen Umma ya Kai hannu cike da zumudi zai dauki jariri,Umma ta Hana shi, sai ka koma kayiwa mutane sallama,da sauri ya koma yayi sallama suka Amsa sannan ya shigo zai karba Umma ta sake hanashi,kamar zaiyi kuka yace Ohhhhh Umma pls mene Haka,dariya Shukura tayi tace Umma ki bashi kina sa Masa Rai,Mika Masa Umma tayi tana Masa dariya ta Shiga kitchen, adduoi ya Dinka zubawa dansa sai da ya Gama sannan ya zauna kusa da Shukura kafadarsu na gugan juna.

Yaro ya kalla ya kalli Shukura sannan ya Kara kallon kansa yace Dani yayi Kama yarinya,Amma dai kasan na Dan fika haske kadan sabo da Haka skin Dina ya gado, Musu suka dingayi har Umma ta iske su kowa Yana cewa shi jariri ya gado, banza Umma tayi musu ta wuce Bedroom taga ba kunya garesu ba.

Momee da sauran dangi,kawaye da abokan arzuka duk an sanar musu,Gida Kullum cika yake da Baki taf,fnds din Ahleef ma suna ta zuwa kullum Yana sintirin daukan jariri Ana nunawa abokai,Dan ma Umma tana hanashi,Haka kullum sai yazo da safe a gabansa za a bawa jariri Nono da dare ma Haka,wataran ma dakin da Shukura take a part din Umma a Nan Ahleef yake nacewa ya kwana.

Shukura ma an sanarwa da danginta kaf,Ana gobe suna kuwa Yan uwan Shukura maza da Mata sun zo mota guda Bus,Washe gari yaro yaci Sunan Abba Baban su Niima Abubakar,Ahleef yace ana kiransa da Farhan,sabo da yanda suke Aminan juna, an jefi tsuntsu biyu da Danko daya,Real name na Dad Nick name Farhan.

Wuri Ahleef ya kama me tsada anan akayi suna, Farhan sai Murna,Haka su Momee ma,anci an Sha anyi pics,ga kida ansha, frnds na Shukura Yan schl dinsu sunzo,bayan suna duk Baki sun tafi na kusa Dana nesa.Shukura Tasha kyauta iri iri,Farhan kuwa kayan da yayiwa jariri harda na hauka ma.
Bayan Shukura tayi sati biyu da haihuwa Ahleef ya nemi Umma ta bashi Shukura su koma part dinsu,Fafur Umma taki yarda, yau ma Ahleef na zaune kusa da Umma yace Dan Allah Umma da Nan da can ai duk daya ne,Ban yarda da Kai ba Ahleef,Ana yi ma abinci,part dinku kullum a gyare yake to me kake nema?.

Shuru yayi ya gaji da magiyar a bashi Matarsa,Shukura Kam ita tausayin mijinta take ji tasan Halinsa da Sha'awa baya jira,gwara tana kusa dashi Kar ya Shiga wani Hali,Shukura ya samu a Bedroom tana lallaba Little Farhan yayi bacci Ahleef ya zauna gefen bed Yana hadiyar yawu yanda Shukura ke kashe wanka yafi gaban ya iya hakura har sai tai 40days.

Itama Zama tayi kusa dashi tare da cewa ya akayi ne My Hero,sai da ya Dade kafin yayi magana cike da takaici ga Shagwaba da wani narke Mata da yakeyi kansa ya kwantar a kafadarta ita Kuma tana shafa Masa gemunsa na matasa, yace Umma tace baza ki koma part dinmu ba sai kinyi arbain,wannan wacce alada ce Haka? Ni bazan iya jira ba,ai ma kin warke Kuma kina sallah kawai ki sato jiki anjima kizo pls Honey.

Tausayi da so yasa Shukura tace karka damu zanzo da dare,murna sosai ta bayya a fuskarsa,kiss ya manna Mata sannan ya mike yace ina jiranki, Shukura tace to.

9pm Shukura tasan yanzu Umma tuni Sunyi bacci ma sabo da dama da wuri suke bacci,wanka tayi ta Sha turaruka tasa wasu shegun kayan bacci sannan tasa Hijab har kasa tana kamshi ta fito cikin sanda Sadaf Sadaf,idan ba kuruciya ba Taya zata bar jariri shi daya a daki,Amma haka ta bude kofar a hankali kawai taji Muryar Umma Ina Zaki je? Ba tare da ta juyo ba ta rumtse Ido sannan ta juyo cike da kunya ta fara kame kame ah...ahm....uhmm...can..can part din zanje dauko wasu Kaya,to koma ki kwanta ba inda zakije ai duk na San plan dinku,Ni zakuyiwa wayo,Sum sum Shukura ta koma Bedroom sannan ta Kira Ahleef a waya ta sanar Masa Umma ta kamata,Ahleef yace to zanzo Ni anjima,karfa a kamamu cewar Shukura,wayar ya datse,ita Kuma Umma tuni ta garkame kofar Palon da key Kuma ta bar key din ajiki yanda baza a iya budewa ba,Ahleef yazo yayi yayi kofa taki buduwa,yasa spare key shima yaji akwai wani a jiki.

Dole ya hakura ya koma part dinsu,Ya sanarwa da Shukura ta waya, Dole suka hakura yau.
Duk yanda Ahleef yaso suyiwa Umma wayo abin yaci tura,gashi har Shukura ta kusa arbain,Yana Murna Umma tace to Kauyensu zamuje sannan mu wuce Niger idan mun dawo daga ziyarar ganin dangi sai ta koma part dinku,takaici ya Hana Ahleef magana, Shukura Kuma sai dariya take Masa a boye.

Barin gidan yayi sai Gidan Momee,Momee ta ganshi hankali tashe, da sauri tace lfy son? Momee pls kije kiwa Umma fada mutum da Matarsa ace baza ta zauna a gidanta ba,dakin mijinta yafi karfinta sai can wurin Umma,Dan Allah kiyi magana Ko na bar kasar nan,Dariya Momee tayi sannan tace nasan Halinka Ahleef kayi hakuri Haka akewa masu jego,Akan Mace har yaji zakayi Haka me yayi zafi za a dawo ma da matarka,Takurawa Momee yayi sai da ta shirya ya kaita wajen Umma,Umma tace au karata ka Kai wajen Momeen taka,Umma da Momee sukayi magana Lallai baza a bashi Shukura ba sai tayi arbain,Ahleef tunaninsa Momee ta gyara komai,Amma sai yaga ba abinda ya faru.

Yau tunda ya shigo da dare Bayan Isha yaki tafiya jariri Yana hannunsa,duk inda Shukura tayi sai ya bita yuuuu da kallo,Umma ta koreshi yaki tashi,Kazo ka tafi bacci muke ji mu zamu rufe kofofi,Ahleef yace to Yana Jin haushi yayi fushi ya fice a fusace.

Haka yayi ta fushinsa ya daina zuwa part din Umma Baki daya,Shukura duk ta damu Ahleef Yana fushi da ita,tana yin arbain Shukura da Umma har Baba suka tafi garin su Shukura, Ahleef Yana ta fushi yace ba zai je ba,Suna dawowa suka wuce Niger abinsu,sati daya sukayi sannan suka dawo,Amma Umma tace Shukura sai ta je ziyara gidajen frnds da Yan Uwa,gidan su Momee,Niima,Latifa,suhail,Farhan etc Ahleef duk ya canjawa gidan tsari ya Kara haduwa an canja komai, Bayan ta Gama yawonta yau Sunday yaune Umma tasa masu aiki suka Kara gyara part din Shukura sannan aka Kai kayanta tare da Dattijuwa me taya rainon little Farhan.

Shukura wani wanka data dauka ka rantse ganin sarauniyar England zata je,Kamar sabuwar Amarya ga Umma dama ta Kara tsumata sosai.
Abin mamaki tunaninta Ahleef zaiyi fushi da ita sai taga ba abinda yayi jaririnsa ya dauka Yana Masa Wasa suka koma Bedroom,Shukura tace My Hero nayi tunanin baza ka kulani ba,Akan me? Ai ba Ke kika min laifi ba kuma idan banyi hakuri ba me zanyi,Rungumeshi Shukura tayi tare da cewa I love my Heart, love u more, dare Yana yi Farhan Yana wajen nanny dinsa, Ahleef sai zumudi yakeyi kamar Bai San Shukura ba,ji yake kamar yau aka kawo Masa ita Amarya.

Shukura kuwa har wani tsoro ma take ji yanda taga yanayinsa,Wanka yayi sannan ya karaci kakalen sa jikin mirror,Shukura ma tana wanka ta fito ta shirya tare da shafa turarukanta zata sa kayan bacci kenan Ahleef yayi sama da ita sai bisa bed ya zare Dan towel din ya jefar dashi, sannan ya Shiga Sarrafa ta yanda yaga dama tun tana nokewa har itama ta fara maida martani,maitarta ta tashi, suna tsaka da Holewa suka jiyo kukan Farhan Yana tsaga uban ihu,Ita kanta Nanny ta kasa lallashinsa, Shukura tace kaji kukan Farhan fa yaki yin Shuru mu Bari na lallashe shi idan yayi bacci sai muyi abinmu, Ahleef ko kulata baiyi ba,yaci gaba da aikinsa,Shukura tace Farhan fa Yana ta ihu kana jinsa,Ahleef da kyar ya saita muryarsa yace idan ya gaji ya daina,yaro bazai tashi kuka ba sai dare zai na Hana mutane sakewa.

Shukura Kuma uwa sarkin son danta ta ni dai bazan iya ba hankali na Yana kansa ka tsaya naje na dawo,Wlh kinji na rantse yaron Nan ko mutuwa zaiyi tsabar kuka baza a dakko shi ba, yaro sai kukan dare idan ya gaji ya daina.Tunda Shukura taji ya rantse kawai ta hakura suka ci gaba da soyewa,Yaro Kuma Yana ta tsaga uban ihu can kasa wurin nanny har ya gaji yayi bacci, ranar Sai da gari ya kusa wayewa Basu rabu da juna ba suna soyewa.

Haka rayuwa taci gaba cikin kwanciyar hankali da nishadi,Shukura tana kula da mijinta yanda ya kamata,shima Ahleef Haka,Momee da Umma Kuma sosai suke muamula,yayin da Matan su Sultan suka samu ciki, Fatima matar Farhan ma ta kusa haihuwa,Niima da Latifa ma suna dauke da juna biyu, Zahra da su Hafcy sunyi aurensu Suma suna Shan Amarcinsu.

Bayan Shekara uku Shukura ta Gama schl dinta,danta Farhan dagwas dashi Yana yawo ko Ina,Kuma Bata Sami ciki ba har yanzu,Sunyi wani kyau ga zuwa kasashen turawa suna Hutawa,duk Shekara Kuma Ahleef kaf yake biya musu makka Umrah harsu Niima.
Lokacin Matan sultan sun haihu,su Niima ma Sun haihu,Haka Hafcy da yarta mace,Zahra da Habiba Kuma ciki tsoho garesu.

Ahleef ya dauki Shukuransa zuwa England wannan lokacin Farhan a gida aka barshi wurin Umma,idan ya gaji Kuma a kaishi wajen Momee ko gidan Farhan yayi hutu can.
Sai da suka shafe wata biyar sannan suka dawo Nigeria Shukura dauke da cikinta Dan wata Uku,Sai Murna sukeyi zasu Kara haihuwa.
Bayan wata 6 Shukura ta haifi yarta mace,aka sa Mata suna Noor,kyakyawar gaske ce ta karshe,Farhan karami duk ya dameta da tsokana.

Bayan wata 7 Shukura abar kallo ce yanda take tashen kyau da iya daukan wankan Sugar,ga wayewa ta Zama gogagiyar gaske ta gaban kwatance,Ahleef wani ji yake da ita,yaransu masu tarbiya gwanin Sha'awa,Farhan Fatimansa tana Nan da tsohon ciki,Momee kuwa sosai take ji da yaran Ahleef,Haka su Niima dasu Hafcy duk sun zama kawayen Shukura suna ziyartar juna, Haka mazajen ma suna zumunci.
Umma da Baba suna zamansu lfy,Shukura tana zuwa wurin danginta ayi musu Sha Tara ta arziki,suna Alfahari da ita.

Yau ma Shukura da Ahleef sun fito Noor tana kafadar Ahleef tasha kyau cikin kana Nan kaya farare,gashinta yasha gyara na Yan gayu,Little Farhan ma Yana cikin kana nan Kaya Dan gayu dashi sabo da ko aski ba a fiye yi Masa ba style ake Masa da gashin kamar Dan turawa, Shukura Tasha Riga Arabian gown wacce Tasha aiki ga tsada black and blue,Ahleef yasa light blue shadda dinkin zamani,kowa ya gansu sai sun birgeka,da gudu guards suka bude mota suka Shiga ta alfarma sannan ga driver yaja yau ba escort zasu fita,sai Wani hadadden park na wasan Yara yaran masu hannu da shuni ke zuwa.

Basu dawo ba sai dare,Nanny ta karbi yaran tayi musu wanka tare da shiryasu cikin kayan bacci suka kwanta sai bacci sabo da Farhan ya fara zuwa schl kasancewar Yana da wayo ga Saurin girma.

Ahleef bayan Sunyi Shirin bacci ya manne Matarsa a jikinsa,a hankali Shukura ta juyo suna Facing juna ga wata Shagwaba da takeyi Masa me kashe Masa jiki,a hankali ta tallafi kumatunsa ta Shiga kissing dinsa sosai kamar zasu cinye bakunansu,ga wani kamshi dake tashi a jikinsu,Albarkatun Kirjinta Ahleef ya fara wasa dasu tana wani shidewa,ya furta Allah ya Miki Kira Honey ki godewa Allah Ni nayi Dace wannan basa zubewa kamar Yar 16 to 17 Haka suke naji dadina,ya Shiga tsotsarsu,Shukura tace karfa ka shanyewa Noor milk dinta tunda Kai har milk din shanyewa kakeyi dariya yayi kadan yace zan rage Mata ke Ina ruwanku mu da abinmu namune Ni da yarana.

Sun farantawa juna Rai sosai kamar yau suka San juna,Haka suka dinga kalamai masu dadi kowa Yana yabon Dan uwansa,suna zubar da kalaman soyayya wa juna,Ahleef sai albarka yake sawa Shukura da yaransa, tace I love my Hero, love u too Honey wani shaukin kauna na shigarsu. Basu da matsala sai wacce ba a rasa ba,ga addini ba Sanya...Allah ka bamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login